"INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN!"
Mummy da Anty Sakina suka furta a tare cikin kidima. Da sauri Anty Sakina ta matso kusa da Humairar da ke kwance shame-shame tamkar gawa, ta kai hannu ta kama ta da nufin ta tashe ta, ji ta yi zafi mai tsanani ya ratsa tafin hannun, sai firgicin nata ya kara ta'azzara. Duban Mummy ta ce, "Ai ba ta da lafiya ma, zazzabi ne a jikinta kamar wuta." Ta fada tare da jan Humaira jikinta ta rungume.
"INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN! Wai me yake faruwa. . .