Skip to content
Part 29 of 30 in the Series Ƙuda Ba Ka Haram by Sadik Abubakar

“INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI’UN!”

Mummy da Anty Sakina suka furta a tare cikin kidima. Da sauri Anty Sakina ta matso kusa da Humairar da ke kwance shame-shame tamkar gawa, ta kai hannu ta kama ta da nufin ta tashe ta, ji ta yi zafi mai tsanani ya ratsa tafin hannun, sai firgicin nata ya kara ta’azzara. Duban Mummy ta ce, “Ai ba ta da lafiya ma, zazzabi ne a jikinta kamar wuta.” Ta fada tare da jan Humaira jikinta ta rungume.

“INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI’UN! Wai me yake faruwa ne? Wace irin jarabawa ce take shirin faruwa da mu?”

Mummy ce ta fadi haka cikin tsananin firgici gami da matsowa wajen da Humaira take, bayan ganin wani jini yana naso ta kasan Humairar wajen cinyoyinta. Gyara kwanciyar Humairar da Anty Sakina take yi, sai ita ma ta yi tozali da wannan jini. Nan fa razanar tata, ta fi ta Mummy.

“LA’ILAHA ILLALLAHU!” Ta fada cikin wani irin kuka mai tsananin tayar da hankali sannan ta ci gaba da cewa, “Usman Allah Ya isa tsakaninmu da kai.”

Mummy kuwa salati da sallallami kawai take, Anty Sakina ta mike da sauri ta zari hijabinta sai titi. Ta taro Mai Adaidaita Sahu domin a dauki Humaira zuwa asibiti, cikin sa’a kuwa mutum na farko da ta tsayar ya biyo ta zuwa lungun nasu, tun bai gama tsayawa ba ta dire ta nufi cikin gida. Tana shiga suka dan gyara wa Humaira jikinta, suka ribanya mata zannuwa sakamakon jinin na ci gaba da zuba. Anty Sakina ta saba ta a baya ta fito da ita zuwa cikin Adaidaitar. Kai tsaye Asibitin Murtala suka nufa, sashen ba da kulawar gaggawa. Har lokacin Humaira a sume take babu alamun numfashi ma a tare da ita, sannan kuma jinin nan na ta ambaliya ta gabanta.

Da shigarsu kuwa cikin sa’a aka wuce da Humaira bangaren kula da masu ciki, hakan dai ya so ya ba wa Mummy mamaki, to amma kuma ba abin mamaki ba ne. Sai abin da bincike likitocin ya nunar. Likita ya baza komarsa akan Humaira ya fara bincike irin nasu na masana harkar lafiya. Gabanin hakan dai ya fahimci suma ta yi, don haka na’urar taimaka wa numfashi aka saka mata kafin daga bisani ya dora da bincikar sauran cututtukan da suke damun ta. Fiye da mintuna arba’in da biyar likitan ya kwashe yana ta gwaje-gwaje, a karshe dai binciken ya bayyanar da cewa, jininta ne ya hau sosai bisa matsananciyar damuwa da tsoro da ta shiga. Kuma a sanadiyyar hakan ne ma cikin jikinta wanda ya kai tsawon watanni uku da rabi ya zube, shi ne musabbabin zubar jinin nan na gabanta. Wannan shi ne sakamakon farko da ya bayyana, kuma kamar haka likitan ya sanar da su Mummy. Nan dai ya rubuta musu magunguna da allurai ya ce a yi sauri a nemo su. Anty Sakina ta karbi katin ta fito bakin asibitin asibitin shagunan da ake sayar da magunguna, har tuntube take saboda tsananin sauri, ta saya cikin hanzari ta koma ta kai.

Allurai kawai aka yi wa Humairar tukunna yayin da aka ajiye magungunan sai ta farfado. Mummy ta yi matukar girgiza da jin cewa Humaira na dauke da ciki watanni uku, abin ya tsaya mata a kahon zuciyarta, yana kokarin kifar da ita. Amma sai Ubangiji Ya tallafe ta da agajinSa ta rika maimaita, “INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI’UN!”

Babu shakka ita da kanta ta zargi kanta akan saken da ta yi har Humaira ta yi ciki ba tare da ta ga alamu ba tun farko. Sai yanzu ta fara hakaito tsawon lokacin da ba ta ga Humaira cikin al’ada ba, domin duk watan duniya idan Humairar tana al’ada, Mummy takan gane kasancewar ciwon mara da ke addabar Humaira na yini daya ko biyu haka, to amma kusan watanni ukun ke nan rabon da ta ji Humairar ta yi mata korafin ciwon marar. Wannan tunanin Mummy ta yi lokacin da ta zuba uban tagumi, Anty Sakina ce ta katse tunanin ta hanyar cewa, “Mummy bari na kira Abba na fada masa ko?”

Ba ta iya amsa mata ba, sai wani numfashi da ta sauke hade da ajiyar zuciya, Anty Sakina ta zaro waya ta lalubi lambar Abba ta kira shi, bayan sun gaisa ta dora da cewa, “Abba da ma Humaira ce ba ta da lafiya, ka gan mu nan a Asibiti Murtala bangaren Emergency.”

“SubhanAllah! Me ya same ta kuma? To Allah Ya sawwake, gani nan zuwa, da ma yanzu muke shirin rufe shago.”

“To shi kenan sai ka karaso din.” Ta fada tare da kashe wayar sannan ta dubi Mummy wacce ta gaza yin magana, sai dai tsantsar tunani. Su duka biyun zugum suka yi, yanayinsu kawai ya isa ya labarta muku abin da ke cikin zukatansu.

To a can kuwa, likita ne ya hada wa Humaira allurai hadi da saka mata na’urar oxygen don taimaka wa numfashi. Dab da Magariba sai ga Abba ya iso shi da Najib, daidai lokacin ana kiran sallah a Masallacin asibitin. Sallar suka fara yi tukunna sannan suka isa wajen su Mummy, bayan ya kira Anty Sakina ta yo musu iso. Najib ya gai da Mummy cikin girmamawa sannan ya tambaya ya ya me jikin?

Abba ya tambayi Mummy me ke damun Humairar? Ba ta fada masa hakikanin abin da ya faru ba, saboda ba shi kadai ya zo ba, sannan kuma tana gudun kada ya ce zai yi fada har ya tara musu jama’a. Don haka sai ta ce masa, “Wallahi dai larura ce ga ta nan, muna zaune a gida sai ta jiri ya kwashe ta ta fadi, daga nan ba ta sake sanin inda kanta yake ba har yanzun nan. Likita ya ce wai jininta ne ya hau.”

“SubhanAllah! Hawan jini kuma? To Ubangiji Allah Ya ba ta lafiya Allah Ya sawwake!”

Najib ma ya kadu sosai da jin ciwon da masoyiyar tasa take fama da shi, addu’o’i ya kara yi mata na fatan samun sauki cikin gaggawa.

To, da alama ba za su samu sallama da wuri ba, kasancewar jikin marar lafiyar na da tarin matsaloli muhimmai, domin a sanadiyyar zubewar cikin akwai bukatar a yi mata hoto. Saboda haka sai Anty Sakina ta biyo su Abba gida domin ta daukar musu kayayyakin da za su yi amfani da su a yayin zaman asibitin kafin a sallame su. To wannan ke nan.

***

Idan muka koma wajen gogan naku kuwa, tun fitar Anty Sakina yake kwance, ya rasa me ke masa dadi, shi ma ya san ba shakka ya tafka kuskure, tunani yake. To sai dai tunaninsa ya bambanta da nasu, shi yana tunanin abin da zai fada wa iyayensa ne idan suka fahimci ba ya tare da matarsa, shin me zai fada musu? Wannan ne tunaninsa. Amma sam babu nadama a tare da shi. Sai dare sannan ya tashi ya yi wanka ya garkame gidan ya fice abinsa. Barikinsa ya nufa kamar yadda ya saba, a ranar ma ko gida bai dawo ba, can ya kwana ya hantse da matansa na banza.

A asibiti kuwa, misalin karfe biyu na dare numfashin Humaira ya fara daidaita, a lokacin har ta farka. Tsintar kanta ta yi kwance a dakin asibiti, ta waiga dama da hagu ta ga duk mararsa lafiya ne kwance fululu. Mintuna kamar biyar da farkawarta, wata ma’aikaciyar asibitin mai kula da masu jinya ta shigo katafaren dakin mai dauke da gadajen kwantar da marasa lafiya sama da arba’in, kuma kowanne gado Dan Adam ne kwance yana karbar kulawa.

“Sannu ya jikin naki?” Ma’aikaciyar ta fada lokacin da ta isa kusa da gadon Humaira. Ba ta iya furta komai ba sai dai kallo da ta rika bin matar da shi, duk kuwa da cewa ta yi yunkurin yin maganar, amma sai ta gaza. Ga shi tana da bukatar sanin wanda ya kawo ta asibitin, motsawa ta yi da nufin ta mike koda zaune ne, sai ta ji cikinta da mararta sun dauki wani azababben ciwo tamkar za a zare mata rai. Yayin da ta ji wani abu mai dumi yana  fita ta gabanta yana kwaranya jikin cinyoyinta,  dayake a kwance take ba ta iya ganin ko mene ne ba. Jini ne ya sake balle mata, ta fara murkususu saboda radadin ciwon. Da sauri ma’aikaciyar nan ta juya ta nufi ofishin babban likitan da ke aikin dare ta sanar da shi, tare suka juyo zuwa ga Humaira.

Nan dai likitan ya yi ‘yan siddabarunsu na masana kiwon lafiya, ciwon ya lafa wa Humaira, sannan kuma jinin ya tsaya da zuba, har ta samu damar komawa barci. Washegari da sassafe ta tashi, likitan ya sake dawowa duba marasa lafiya kafin ya mika ragamar aikin ga wanda zai karbe shi, wato wanda zai yi aikin rana ke nan. A nan ne ya yi umarni da lallai aje a yi wa Humaira hoton cikin.

To sai yanzu da safen ne Humaira ta samu zarafin ganin su Mummy, dayake marasa lafiyar dakinsu daban, su ma masu jinya sashensu daban. Sai dai sukan shigo lokaci zuwa lokaci domin duba majinyatan nasu. Anty Sakina a kage take ta ga ta yi tozali da kanwar tata, don ta ji ya ya jikin nata? Suna isa suka iske ta ido biyu kwance tana kalle-kalle, “Sannu ya ya jikin naki?”

Anty Sakina ta fada daidai lokacin da ta zauna gefen gadon da Humaira take kwance tana shafa mata kai. Cikin siririyar murya a hankali Humaira ta ce, “Da sauki, Mummy don Allah ki yafe mini, mutuwa zan yi! Ina Abba yake? Ku yafe mini laifukan da na yi muku, ni mutuwa zan yi!”

Mummy ta ce, “Ki daina fadar haka, Allah zai ba ki lafiya, cuta ba ita ce mutuwa ba, sai kwana ya kare. Mun yafe miki duniya da lahira.”

Wasu siraran hawaye masu tsananin dumi suka sakko kan kuncin Anty Sakina, cikin yanayin tausayi ta ce, “Ya ya kike jin jikin naki yanzu? Ya ya ciwon marar?”

“Da sauki yanzu ba sosai ba yake yi mini. Anty ki daina kuka!”

Anty Sakina ta share hawayen ta ce, “To AlhamduLillah! Yanzu ma idan anjima za mu je a yi miki hoton marar domin a tabbatar da babu wata matsalar, Allah Ya kara sauki.”

To, tun jiya da dare da Najib ya koma gida, ya sanar da mahaifiyarsa an kwantar da su Humairar a asibiti. Ta so tun a daren ta zo, to amma hakan ba ta samu ba, don haka yau tun Asubar fari ta tashi ta hada kayan karin kumallo sosai. Tare da Najib din suka taho asibitin.

Su kam su Mummy ba ma ta abinci suke ba, burinsu dai bai wuce na ganin Allah Ya tashi kafadun Humaira ba. Shi ma Abba a nasa bangaren, abincin karin kumallon yake tunanin kai musu. Shiryawa ya yi ya dauki wani katon flas din shayi ya je wajen masu shayi aka cika masa shi fal! Sannan ya sayi manyan-manyan brodi guda biyu da madara gwangwani biyu, ya nufi asibitin. Zuwan su Najib bai wuce mintuna goma ba sai shi ma Abban ya iso.

Nan dai aka yi gaishe-gaishe, aka yi wa Humaira sannu da jiki. Abin sha’awa har hira aka dan taba da ita. Mummy da Abba suka dan kebe wuri guda suka saka labule, a nan take sanar da Abban dukkan abubuwan da suka faru tun daga farko har karshe. Ya yi matukar kaduwa da jin irin danyen aikin da Usman ya yi, ya ji zafi matuka a ransa. Shi ma kamar su Mummy, matakin bar wa Mai duka ya dauka, Shi zai yi musu hisabi.

Kafin Abban ya tafi, ya kira kira Anty Sakina ya yi mata nasiha mai ratsa jiki da kwantar da hankali, “Ki yi hakuri, ki dauki dangana! Allah zai saka miki da gaggawa akan mijinki, domin ya zalunce ki. Sannan kuma kada ki rike ‘yar uwarki a zuciya, kaddara ce ta faru. Ubangiji Yakan jarraba bawa da masifu iri-iri, ita kanta Humairar hakan jarabta ce a tare da ita, saboda haka kada ki saka damuwa ko tunani a ranki. Allah Ya yi muku albarka.”

Ta amsa da, “Amin Abba, na gode sosai kuma In Sha Allah zan yi dukkan abin da ka umarce ni. Ni da ma ban rike Humaira a raina ba, na san halin Usman sosai, neman mata yake. Yaudarar ta zai yi ta hanyoyi da dama har ya ga ta aminta da shi. Fatanmu dai Allah Ya ba ta lafiya.”

“Yawwa to madalla!”

Abba da Najib sun dan jima a asibitin kafin daga bisani su tafi. To dayake kowa ya yo shirin fita kasuwa ne, tare suka wuce. mahaifiyar Najib kuwa a nan asibitin ta zauna tare da su Mummy har kusan karfe goma sha-daya na safe 11:00am  sannan ta koma gida.

Bayan su Mummy sun karya, har da ita kanta Humairar ma ta dan kurbi ruwan dumin sama-sama, sai aka je wajen da za a yi mata hoton. sakamakon ya nuna babu komai a cikin mahaifar kuma jinin ya tsaya da zubar. Abu daya yanzu da bayyana shi ne, jikinta babu kwari sam, tafukan hannayenta sun yi fari alamun rashin jini wadatacce a jikinta. Gwaji aka yi mata  hakan kuma ta tabbata, akalla ana bukatar a kara mata jini lita guda. To fa! Ana wata sai ga wata, daga wannan sai wannan.

<< Kuda Ba Ka Haram 28Kuda Ba Ka Haram 30 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.