ALMUSTAPHA ya tsayar da tunaninsa sannan ya wargatsa shi, ya kuma tsayar da shi a karo na biyu, ya maimaita tarwatsa shi. Sai da ya yi haka har fiye da bakwai, sa'annan ya runtse idanunsa, ya saki jikinsa tare da sakankacewa har sai da barci ya xauke shi.
Mintunsa talatin yana yin wannan barcin. Ya farka, cikin hanzari, ya je, ya yi alwala, kana ya dawo ya yi sallar nafila raka'a biyu. Ya shiga yin addu'o'i na tsawon mintuna, sannan ya koma mazauninsa, ya zauna. Sa’annan tsaftaccen tunani cikin nutsuwa ya rinqa dira qwaqwalwarsa.
Abin. . .