Skip to content
Part 5 of 6 in the Series Kushewar Badi by Kabiru Yusuf Fagge

ALMUSTAPHA ya tsayar da tunaninsa sannan ya wargatsa shi, ya kuma tsayar da shi a karo na biyu, ya maimaita tarwatsa shi. Sai da ya yi haka har fiye da bakwai, sa’annan ya runtse idanunsa, ya saki jikinsa tare da sakankacewa har sai da barci ya xauke shi.

Mintunsa talatin yana yin wannan barcin. Ya farka, cikin hanzari, ya je, ya yi alwala, kana ya dawo ya yi sallar nafila raka’a biyu. Ya shiga yin addu’o’i na tsawon mintuna, sannan ya koma mazauninsa, ya zauna. Sa’annan tsaftaccen tunani cikin nutsuwa ya rinqa dira qwaqwalwarsa.

Abin da ya fahimta, tunaninsa ya nuna masa shi ne dukkanin abubuwan da ya karanta kuma ya nazarto daga jawabin ‘Island of Hablan & the women of her century’ wasu abubuwa ne da aka fitar masa, ya fitar wa da kansa su, ya qaqqalesu, tare da samun tabbacin cewa akwai buqatar ya san shin wace ce matarsa Lajja? Daga ina ta samu?
“Wace ce wannan Lajjanatun? Mene ne dangantakarta da matata Lajja? Su waye tsatsonta a duniya?” Ya tambayi kansa. Ga dukkan alamu kuma a yadda ya fahimta shi ne samuwar waxannan amsoshi suna nufin tabbatarwa da kuma bayyanarwar wace ce matarsa?

Ya kuma shirya wa komai don wannan lamari.
Wani abu kuma a cikin abubuwan da tarihin ke nuna masa shi ne akwai nuna tabbacin ita ainihin Lajjanatu zata rayu, zuri’arta zasu rayu, su hayayyafa, su watsu a duniya, sashe daban-daban, su haifi masu tsantsar kamanni da junansu, su zamo masu xauke da abubuwan mamaki.

Idan kuwa haka ne to tabbas a bisa dalilai da dama za su sanya cewar matarsa tana cikin tsatson wannan mata. Dalilan kuwa sun haxa da yadda ta kasance mai tattare da wasu abubuwan mamaki masu yawa, ga kuma yadda Alhaji Hammad ya ganta ya ce matarsa ce. Wannan kuma a bayyane yana nuni ne da cewar ba shakka akwai ita ainihin matar Alhaji Hammad xin, amma ba Lajjarsa ba.
Hawaye mai xumi ya ci gaba da zirarowa daga idanun Almustapha, ya shiga tuna yadda al’amarin ya faru da yadda ake ciki.
“Alhaji Hammad ya karve min mata har ya haihu da ita.”

Ya yi qaraji, sannan ya fashe da kuka, cike da tausayin kansa, da nadamar yadda voyayyen al’amarin ya faru a kansa.

Bai damu ba, da yake shi kaxai ne a cikin xakin, ya jima yana rusa kuka abinsa, har sai da zuciyarsa ta gamsu, hawayen shi ya qafe. Ya rintse idanunsa ba wai da nufin yin barci ba, face zayyano faruwar al’amarin da abin da ake ciki, hakan ya zame masa kamar karatu, kuma kamar wani majigi. Vata lokaci ya zame masa jiki, don haka ya kasance a haka tsawon mintunan da suka gifta talatin, sannan ya miqe.

Ya jawo kan waya, ya daddana lambobin da yake buqata, ya kai ga lambar abokinsa Albashir, ya sanar da shi yana son ganin shi yanzu-yanzu.

Mintuna goma sha biyar a tsakani Albashir ya iso. Ya zauna a kan kujerar dake fuskantar Almustaphan, ya qura masa ido. A kullum baya rabuwa da yiwa abokin nasa kallon tausayi. Kuma yana yin duk wani abu da ya dace don taimakawa abokin nasa.
Almustapha ya sanar da Albashir abin da ake ciki.

“Babu shakka Lajjarka ta siffantu da dukkanin waxannan abubuwa, haka shima Alhaji Hammad xin akwai qwaqqwaran alamun dake nuna gaskiyarsa a wannan lamari, kuma ba shakka al’amarin ya faru ne bisa akasi da rashin sani. Haka nan tun farko Alhajin ya kuskurewa neman matar tasa ne da bincikar inda take. Me yiwuwa ma tana can Makkah, ko ta tafi wata qasar. Amma kuma haqiqa kuskurensa ya cucemu, ya zaluncemu…” Hawaye ne a fuskarsa. “Yanzu mene ne abin yi?” Albashir ya tambayi Almustapha cikin saduda.

“Ka san dai halin d a nake ciki na rashin kwanciyar hankali.” Cewar Almustapha, “Don haka dole ne zan bi duk yadda zan yi don bayyana abin da nake zargi a zahiri.”
“Kamar ya ya?” Albashir ya buqata.
“Mafita ta farko ita ce zan binciko ainihin ita Lajjanatu matar Alhaji Hammad xin a ko’ina take a duniyar nan. Don haka buqatata gareka shi ne ka ci gaba da taimaka min da addu’a, kuma ina son ka zauna cikin shirinka, zan yi duk wani abu da ya dace don ganin matata ta dawo gareni, don ina matuqar qaunarta.”

A cikin kwanaki uku Almustapha da Albashir suka shirya tafiyar Almustapha Makka. Biza, fasfot, da tikiti duk sun kammalu. A cikin jirgin Kabo ya tashi.

A lokacin da jirgin ya fara sharara gudu a kan kwaltarsa don xagawa sararin samaniya, a lokacin ya shiga yiwa kansa da kansa tarin tambayoyin yadda zai cimma burinsa na abin da ya tafi nema.

Ba wai wannan ne karo na farko da Almustapha ya fara hawa jirgi ba, ya saba, to amma wannan tafiya ta bambanta, domin zuwa qasa mai tsarki ne, kuma ba wai aikin Hajji ko Umra zai je ba.

A can qasan zuciyarsa akwai wani vangare da yake xauke da mamaki game da wannan tafiya da kuma neman naqasu ga yinta, sai dai kuma ko kaxan baya tunanin akwai wani abu da zai hana shi yin wannan tafiya.

Ya so ya nutsu, ya yi qwaqqwaran shiri, ya yi tunani tare da nazari game da tafiyar amma sai qaguwa da tunanin abubuwan da zasu faru nan gaba suka hana shi.

Duk wasu abubuwa da matafiyi ke yi da aiwatarwa a cikin jirgi ko xaya Almustapha bai yi ba, hatta da shan shayi bai yi ba. Tun da dai ya zauna, ya kifa kansa a kan gwiwoyin hannunsa bai xago ba sai da ya ji sanarwar isar su Saudiyya.

A nutse, ya miqe cikin godiya ga Allah, tare da yabo ga fiyayyen halitta, Annabi Muhammadu (SAW) ya bi jerin gwanon mutanen da ke qoqarin fita.

A lokacin da ya fito daga cikin jirgin ya kalli yanayin garin tamkar mai yin nazarinsa, sannan a hankali cikin nutsuwa ya bi kan matattakalar jirgin ya yo qasa.

A unguwar Daka-Ali dake cikin garin Makka ya sauka. Kwanansa xaya da zuwa ya yi abota da wani Balaraben Saudiyya mai suna Saif-Ali. Ya qulla abota da shi ne don qoqarinsa na cimma dalilin zuwansa wannan gari.

Almustapha hafizin Alkur’ani ne, kuma ya yi makarantar Arabiya, qaramar sakandire xinsa ma ‘Arabic School’ ce, wannan kuwa ya taimaka masa gurin jin Larabci madaidaici. Jin Larabcinsa kuwa ya taimaka masa yin abotar sauri da Saif Ali. Shi kuma Saif Ali mutum ne mai son jama’a da fara’a, kuma yana jin Turanci, riba biyu.

Saurayi ne dogo, a bisa qiyasi shekarunsa sukan iya zama ababen lalube daga ashirin da biyu zuwa ashirin da huxu ko fi. Mahaifinsa Ali Al-Darda’i hamshaqin mai kuxi ne, shi ke da mallakin gidan da Almustapha ya sauka a cikinsa, da kuma wasu manyan gidajen saukar baqi dake nan unguwar Daka-Alin, ban da na ragowar unguwanni.

In san samu ne idan baqo ya je gari, ya dace ya yi nazarin yanayin garin da yadda zamantakewar al’ummar garin take, to amma shi Almustapha duk wannan bai shalle shi ba, bai damu da shi ba, da Saif Ali ma yana gaya masa yanayin zamantakewar al’ummar garin matsuwa ya yi ya gama.

“Ka ce wani bincike ne ya kawoka? Wane iri kenan?” Saif Ali ya buqata.

Almustapha ya bashi labarinsa da abinda ya kawo shi, da buqatarsa a lokacin, ya gaya masa komai.

Tsawon lokaci Saif Ali ya kwashe yana nazari da tunanin al’amarin. Abin ya ratsa tunaninsa, kuma ya ginu a zuciyarsa.

“Haza kalamun azim.” Cewar Saif Ali, yana gyaxa kai. “Su dai mutanen Masar idan suka zo qasar nan mafi yawansu a Jidda suke zama, bincikar wadda aka zo nema kuwa na nuni ne da lallai sai an dangana ga muhajirun (immigration), domin samun tabbacin zuwanta, da kuma jin shin tana nan xin ko ta tafi, idan aka taki sa’a ba ta yi tafiyar rashin qa’ida ba, wato irin tafiyar bayan fage to abin zai zo da sauqi, domin za a san a inda take da unguwar da take idan ba ta tafi ba, in kuwa ta tafi za a san inda ta dosa, wato qasar da ta nufa. Taimakon Allah shi ne abin nema.”

Shiru suka yi. Almustapa yana kallon Saif Ali a wayance, musamman da ya fuskanci maganar ta ratsa shi.

“Amma abin babba ne.” Cewar Saif Ali.
Suka qara yin shiru.

“Na tausaya maka, kuma na xauki alqawarin taimaka maka da yardar Ubangiji.” Saif ya yi maganar cikin tausayi.

Da taimakon Saif Ali Muhajirun suka basu damar binciken sunayen baqin da suka zo daga Masar tun daga shekara ta 1990 zuwa wannan lokaci. Almustapha ya riga ya san ba don Saif Ali ba da babu yadda za a yi ya sami wannan dama cikin sauqi, sannan sun haxa da samun izini daga ofishin jakadancin Nijeriya, kuma abin ya zo musu cikin sauqi.

A cikin na’ura mai qwaqwalwa (computer) duk wasu bayanai na mutumin da ya zo qasar akwai shi a ciki, musamman wanda ya zo ta sahihiyar hanya. Wannan sai ya zo wa da Almustapha da sauqi, kuma zuciyarsa ta yaba da ci gaban da qasar ke da shi.

Aka bashi dama ya buxe kwamfiyutar, ta hanyar buga lambar mavallin buxewa (password) da suka bashi.

Ya danna harafin (L) wanda kai tsaye hakan ya kai shi ga jerin sunayen da suka fara da wannan harafi na (L). A kan suna na dubu da xari shida da shida Almustapha ya ga sunan kamar haka: ‘Lajjanatu Usm-Khairy’. Hotonta dake gefen sunan daga vangaren dama shi ya fi jan hankalinsa fiye da komai, har ya so ruxewa. Hoton matarsa Lajja ya gani.

Wannan na nuna mafarkinsa ya zama gaskiya kenan? Ko kuwa voyayyen al’amarin ya fito fili?

Hoto dai, hoton matar Alhaji Hammad ne, hoton Lajjanatu ne. Shi kansa ya yarda da hakan. Idanunsa suka cika da qwalla.
Ranar Alhamis 4 ga watan 4 ta zo qasar.
Bincike ya nuna musu tana qasar bata bar ta ba, sai dai kuma tana Jidda, a unguwar Hindawiyya. Qarin samun tabbaci kuwa sai dai in har sun je can Jiddar.

Saif Ali ya tsayar da motarsa a gefen wani tafkeken kantin sayar da kayayyakin qarau (Jewel), ya kalli Almustapha.

“Anan zamu ajiye motar, zamu qarasa cikin unguwar a qasa, domin ba a shiga unguwar da lambar motar Daka-Ali. Kuma akwai tafiyar aqalla biyu cikin ukun kilomita xaya daga nan.”

Almustapha ya yi murmushi, wanda a zahiri bai dace da a kira shi da murmushi ba face yaqe.

“Ba komai.” Ya amsa. Yadda yake magana da yanayinsa suna nuni ne da kai tsaye ya miqa al’amuransa ga wannan bawan Allah da yake taimaka masa bil-haqqi.

Garin na Jidda yana da kyakkyawan tsari da abubuwan qayatarwa, gwanin sha’awa. Su Almustapha sun isa unguwar Hindawiyya ba tare da xaya daga cikinsu ya nuna alamun gajiya a tare da shi ba, musamman da yake dukkaninsu ma’abota motsa jiki ne.

Daf da wani gida, Almustapha ya tsaya qyam, kamar wanda aka yi amfani da linzami gurin tsayar da shi. Kamanninsa da yanayinsa suka sauya.

Abokin tafiyarsa Saif Ali, wanda har ya yi gaba yana ta magana shi kaxai, ya juyo yana tunanin dalilin tsayawar abokin nasa. Mamaki da tunaninsa suka qara ninkuwa a lokacin da ya ga yadda kamanni da yanayinsa suka sauya. Ya fara takawa a hankali, ya dawo gare shi, yana kallon shi sannan daga bisani kuma ya kai ganinsa ainihin inda Almustapha yake kallo.

Zaune a kan kujera, a harabar wani farin gida mayalwaci, wata kyakkyawar mata ce, hannunta riqe da littafi, ita ma dai qurawa Almustapha idanu ta yi cike da wani irin yanayi, sai dai ya bambanta ainun da irin yanayin da shi Almustapha ke ciki.

Mamakin Saif Ali ya ninku, ya yi ajiyar zuciya. Babu shakka wadda suka zo nema ce ta samu. Zancen abokinsa ya zama gaskiya, baxinin da yake tunani ya zama zahiri. Ya juyo muryar Almustapha na faxin, “Lajja!”

Ga dukkan alamu cikin mamaki ya furta hakan, tuni maqoshinsa ya bushe, yawun bakinsa ya qafe. Har a wannan lokacin yana ganin wadda yake gani matarsa ce ba wata ba. Abin da ya haddasa masa zuwa wannan qasa shi ya hana masa sakankancewa matarsa yake gani a wannan lokaci, kuma hakan na tunatar dashi abin dake gudana don kar ya ruxe.

Yanayin fuskar matar ya sauya. Musamman da yake ta ji ya kirata da wani irin suna, akwai wani lavavven murmushi xafe a kan fuskarta. Ba ta san waxannan mutane ba, ba ta tava ganinsu ba, amma haka kawai ta ji tana sha’awar kallon fuskar xayansu (Almustapha). Abin mamaki kuma gashi yana qoqarin kiran sunanta, don dai kawai ya taqaita ne, ko ta ce bai iya faxa ba, haka kuma amo da karin sautin kiran da ya yi ya bambanta da waxanda ta saba ji.

“Laysal huwa. Ismi Lajjanatu” (ba haka yake ba, sunana Lajjanatu) Ta faxa a hankali, to amma hakan bai hana su Almustapha jin abin da ta ce xin ba.

Cikin halin da suka sami kansu a ciki suka fara takawa a hankali tamkar waxanda qwai ya fashewa a ciki, suka nufi wurinta.
Kallonsu kawai take yi.

Suka yi mata sallama, ta amsa musu. Mintuna biyu babu wanda ya buxe baki bare ya ce wani abu, illa wannan ya kalli wancan. Kowanne dai akwai abin da yake tunani, yake saqawa a zuciyarsa, musamman Almustapha wanda yake ganin ai wannan ita ce matarsa, zuciyarsa na barazanar dagula masa lissafi. Saif Ali ne ya kawar da shirun.
“’Yar uwa, gurinki muka zo.”

Ta kalle shi da alamun mamaki, “Wurina? To ina sauraronku.”

Suka xan yi shiru.

“Maganar tana da tsayi, kuma tana buqatar nutsuwa. Ko za mu samu isasshen lokaci yanzu daga gareki?” Saif Ali ya buqata. Shi kuwa Almustapha kallonta kawai yake yi, duk da cewar ita ma tana kallonsa jefi-jefi da idanunta masu kwarjini, hakan bai hane shi ci gaba da kallonta ba.

Ta kawar da kanta wani vangare daban, tunani da nazari ta yi a taqaice. Ta kalli Saif Ali “Yanzu ina shirye-shiryen shiga karatu, don haka babu lokaci. Sai dai idan ba damuwa kwa iya dawowa gobe misalin qarfe goma sha biyu na rana ina da lokaci.”

Babu wanda ya ji daxin wannan amsa tata a cikinsu. Domin shi Almustapha ji ya yi tamkar ya matsa mata don ta amsa musu buqatarsu. Magana ma gagarar shi ta yi don takaici.
“Abin da ya kawo mu yana da muhimmanci, zamu yi farin ciki idan kika saurare mu a yanzu.”

Ta yi murmushi a taqaice “Ku yi min haquri, ni ma uzurin nawa babba ne. Yau ne ranar qarshe da zan yi hadda.”

Haka kawai ta sami kanta tana rarrashinsu, har dai suka saduda. Ba wai haqura suka yi ba, ba yadda za su yi ne kawai. Duk suna magana ne da Larabci.

Tun bayan tafiyarsu ta shiga tunani da mamakin abin da suka zo nema gare ta. Ba ta sansu ba, ba ta san daga inda suke ba, haka nan ba ta san abin da ya kawo su gare ta ba. Ta yi nadamar sallamar su haka cikin sauri ba tare da ta san wasu daga cikin waxancan amsoshin ba. Sannan kuma a can cikin zuciyarta, ta ji zuciyarta tana matuqar jin garxin kallon fuskar Almustapha har kuwa zuciyar tata tana nemo mata fuskarsa garai-garai a cikin allon majigin zuciyar. Yanayinsa ya burgeta. Wani kallo da ya yi mata ya burgeta, amma a ranta takan raya wata tambaya qwaya xaya “Shin kallon me yake yi min haka?”

Nadamar rabuwa dasu ya rinqa havaka a zuciyarta salo-salo, kamanninsa suka zama madubi a cikin zuciyarta, ta xokanta, al’amarin kamar shigar sartse.

A daddafe ta ci gaba da aiwatar da al’amuran gabanta, har zuwa lokacin da ta kwanta barci, barcin ya gagara. Surar Almustapha ta zame mata tabaron mafarki. Ta rinqa tambayar kanta, tana baiwa kanta amsa.

*****
Dare guda cur bai iya rintsawa ba, in ban da tunani da saqe-saqe marasa iyaka babu abin da ya yi. Qarfe bakwai na safe ya kammala shiryawa. Ya matsu don ganin lokaci ya yi, lokacin kuwa yana tafiya daidai kamar kullum, amma a ganinsa tamkar riqe lokacin ake yi. Gani ya yi daqiqar agogon da ya sanya a gaba yana tafiyar tsutsa, a yayin da kuma mintuna ke tafiyar hawainiya.

Haka ya ga abin ba mai qarewa bane, kuma ba yadda zai yi da ya ja lokacin da gudu. Dole dai ya ga babu abin yi face ya xauko Alkur’ani ya shiga karantawa. Qarfe tara daidai na safe ya bar masaukinsa zuwa gidan Saif Ali.

Zaune a cikin motarsa. Ya gama shirin tafiya. A haka Almustapha ya tarar da Saif Ali. Ya yi masa sallama suka gaisa.

Saif Ali ya dubeshi “Yanzun nan zan je gurinka don mu tafi da wuri. Shigo mu tafi ko?”
Almustapha bai ce komai ba, ya zagaya, ya shiga. Tun da Saif Ali ya haxu da Almustapha ya fahimci bai fiye surutu ba, to hakan ya qaru tun lokacin da suka je, suka riski matar da ya kira Lajja ta biyu.

Ita ma dai tun da sassafe Lajjanatu ta fito, ta zauna a gurin da suka sameta a jiya.

Tunaninta ya ninku, mamakinta ya yawaita. A da dai ta rasa takamaiman dalilin faruwar wannan abu, amma da ta ware lokaci ta yi nazari sosai, sai ta gano a can qarqashin zuciyarta ta yaba da yanayin al’amuran Almustapha, tana sha’awarsa, a taqaice tana son shi.

Amma kuma a garesu, su me suka zo yi gurinta? Da wacce suka zo mata? A tsammaninta samun amsar waxannan tambayoyi da waxanda ke voye a ranta sune zasu zamo gammon xaukar kayan da take shirin kinkimarwa kanta.

A yanzu haka ta xokanta ta ga zuwansu, har ma ta manta lokacin da ta ba su. Aqalla ta shafe sama da awa xaya da mintuna tana jiransu, har dai ta fara saduda, ta ji kamar tana qoqarin sauya tunaninta. A lokacin kuma ta hangosu tafe, su biyu kamar jiya. In ban da suturu da suka sauya, wato yanzu ba sa yin suturun to kuwa babu abin da ya sauya da yadda suke zo mata a jiya.

Ta yi ajiyar zuciya, a lokaci guda kuma ta yi qoqarin daidaita nutsuwarta.

Suka qaraso, suka yi mata sallama. Ta amsa musu cikin ladabi da nutsuwa. Haka kawai ta sami kanta tana mai yi musu ladabi, kuma tana jin kunyarsu. Ta yi musu iso zuwa cikin falon dake daf da harabar da suke. Bayan sun shiga sun zazzauna, ta gabatar musu da ruwa mai sanyi, lemon gwangwani, kaza soyayyiya, da kuma tuffa.

Kamar yadda ya faru a jiya, yau ma haka Almustapha ya kafa mata ido, har kunyar shi ta lilliveta, ta nemi dabarbarcewa.
“Na ji kuna ce min Lajja, alhalin sunana Lajjanatu.” Ta faxa kanta a duqe.

Babu wanda ya amsa mata, face nutsuwa da suka qara yi. Mintuna biyu zuwa uku, shiru. Lajjanatu ta xaga ido tana wani abu wanda ya fi kama da murmushi-murmushi, dariya-dariya.

“Ke ce Lajjanatu Usm-Khairy kenan?” Cewar Almustapha.

Ta kalle shi da mamaki qarara a fuskarta. A lokaci guda kuma ta xokanta da jin abin da wannan sharar fagen ke xauke dashi. Ta kwana tana son jin me ke tafe da su.
“Ba shakka.” Ta amsa tambayar a taqaice.
“Hakan na nufin ke ce?”

“E ni ce.”

Almustapha ya kawar da kansa daga gareta, amma hakan bai hana shi ci gaba da tambayarta ba. “Kin san Alhaji Hammad?”
Nan da nan yanayin fuskarta ya sauya, ta dubi Almustapha da Saif Ali, sannan a hankali ta furta.

“Hammad Almubasshir Almisry?”

“Shi.” Almustapha ya tabbatar mata.
Ta saddar da kanta qasa.

Mintuna waxanda suka kama daga biyu zuwa uku suka wuce ba tare da wani daga cikinsu ya ce uffan ba. Da Almustapha ya nutsu, ya karanci fuskar Lajjanatu sai ya ga yana qoqarin gano wasu abubuwa da dama. Don haka cikin bayanai na dalla-dalla ya kwashe labarin dalilin zuwansu gareta kaf ya gaya mata. A qarshe ya miqa mata hoton ainihin matarsa Lajja, wadda suka yi matuqar kama, kana ya miqa mata hoton Alhaji Hammad.
Labarin ya girgizata, ya ba ta haushi. Sai dai kuma ya fi ba ta mamaki. Ta tausayawa Almustapha da matarsa.

Labarin tarihi da girman zuri’arsu da mahaifiyarta ta tava gaya mata ya zo ranta.
“Ashe har a Najeriya akwai irin zuri’armu?” Ta ce a ranta.

“Yanzu dole ke za ki zamo mawarwara ga wannan matsala, zamu je Najeriya in gabatar da ke ga mai shari’a, in nuna wa Alhaji Hammad ke, domin ya bambance tsakaninki da matata. Kotu ta tabbatar da gaskiyar lamari.” Almustapha ya ce da ita.

Lajjanatu ta xaga kai, ta kalle shi. Tun xazu kallon hoton Lajja take. Babu wani bambanci a tsakaninsu, sai dai da yake ita ce, ta gano bambancin da wani zai yi wuyar gano shi.

Xaya daga ciki shi ne akwai wani xan xis xin xigo akan hancin ita matar Almustapha (Lajja), ita kuma ba ta da wannan xigon, sai kuma ragowar canje-canjen da ya zamo ita ce kaxai ta iya ganinsu, sai dai ko ita Lajja idan ita ma ta ganta.

Ta yi ajiyar zuciya, fuskarta na xauke da jayayya dangane da maganar Almustapha. Ta kalle shi, kamar za ta ce wani abu sai kuma ta fasa, ta ci gaba da kallon hoton Lajja.

Saif Ali na zaune. Bai yi motsin cewa komai ba, amma a nutse yana nazartar al’amarin.
Ta maimaita yin ajiyar zuciya a voye. “Idan son samu ne, ku bari sai gobe, zan yi nazari sannan ina da magana nima.”

Ran Almustapha ya vaci. Kafin ya furta maganar dake xafe a bakinsa, Lajjanatu ta riga shi da faxin. “Kar ku damu. Komai mai sauqi ne.”

Saif Ali ya yi qoqarin ganin Lajjanatu ta gaya masa abin da take tunanin sai goben za ta faxa, amma sam ta qi, domin a tunaninta kuma a tsarinta zuwa goben ne abin da ta tsara zai tafi kamar yadda take so.

Ba Almustapha ne ya buga waya Nijeriya ba, Albashir ne ya bugo masa don jin abin da ake ciki. Ya sanar da shi dukkanin abin da ake ciki, kuma ya sanar dashi cewa ya yi shirye-shiryen xaukakata qara.

Washegari qarfe tara na safe, Saif Ali da Almustapha suka isa gidan su Lajjanatu. Gidan yana xauke ne da mutane huxu a cikinsa, kuma duk mata, ‘yan haya. Xaya daga cikin matan wadda ta girmi ragowar ita ce wakiliyar mamallakiyar gidan, kuma ‘yar qasar ce. Sai kuma Lajjanatu da wata mai suna Hindawy duk ‘yan qasar Masar ne, girma da shekarunsu na iya zama xaya. Sai kuma wata budurwa ‘yar qasar Syria.

A cikin falo suka tarar da ita tana karanta littafin Hadisi (Bukhari), ta yi musu iso, tare da ba su mazauni kana ta harhaxa littattafan da ke gabanta guri guda.

Bayan sun gaisa ne tana qoqarin miqewa tsaye, ta miqawa Almustapha wata takarda dake nannaxe.

“Zan kai waxannan littattafai cikin xaki, idan ka gama karantawa zan dawo.” Ba ta jira ya ce komai ba ta shige. Yanayinta yana xauke da jin kunya.

Suka bi ta da kallo har ta fice daga falon, sa’annan Almustapha ya kalli nannaxaxxiyar takardar da ta ba shi cikin mamaki.
Ya warwareta, ya fara karantawa. Rubutun Larabci ne.

Sahibi

Duk abubuwan da ka faxa haka suke. Al’amarin yana da matuqar ban mamaki da al’ajabi, na tayaka baqin cikin amshe maka mata da aka yi cikin rashin sani. Kuma ga shi har ta haihu da wanda ba mijinta ba.

Na yi alqawarin taimaka maka yadda ka buqata, sai dai kuma ina son ka yi min alqawarin za ka taimaka ka so ni nima, ka qaunace ni kamar yadda na kamu da son ka da kuma qaunarka a lokaci qanqani. Wannan shi ne hanyar warware dukkan matsalolinmu gaba xaya.

Alkairin Allah a gareka.

Sahibarka; Lajjanatu Usm-Khairy
Almustapha ya yi galala. Kan shi ya yi zafi kamar zai tsage, zuciyarsa sai harbawa take tamkar mai shirin faso qirjinsa ta yi waje.

“Wannan al’amari ba mamaki shi zai kawo qarshen rayuwata.” Ya raya hakan. Ran shi ya yi bala’in vaci, bai san lokacin da ya miqa wa Saif Ali takardar ba.

Kafin Saif Ali ya kammala karanta takardar Lajjanatu ta dawo xauke da lemon gwangwani, tuffa, kaza da kuma ruwa a kan faranti. Ta ajiye a kan xan teburin da ke gabansu, kana ita ma ta nemi wuri ta zauna, tana kallonsu xaya bayan xaya. “Bismillah.”

Ba su amsa tayin da ta yi musu. Almustapha ya xaga kai ya kalleta.

“Lajjanatu kin zo da wata irin magana, kuma….”

Ta kalle shi. “Na yi tsammanin jin wannan maganar daga gareka, to amma yana da kyau ka sani komai mai sauqi ne, duk wani abu da ake buqata zan yi don a tabbatar an cuceka a yayin shari’ar. Sannan kuma zan zamo mai share maka hawaye a madadinta musamman idan ka bar masa ita bisa la’akari da abin da ya faru. Idan kuma ka ga lallai kai sai an dawo maka da matarka wannan ba wani abu bane, tun da ga babbar shaida.” Ta nuna kanta. “Amma ni a ganina kawai ka saduda, ka sadaukar da soyayyarka gareni, tun da ba wani bambanci, mun yi kama da ita, haka nan kyawawan halaye ina fatan za ka sameni fiye da ita.”

Fuskar shi ta qara tsukewa, haushi ya mamaye shi.

Ta katsi hanzarinsa tamkar wacce ta ga me yake tunani a zuciyar shi ta ce. “Kar ka yi tsammanin abin da na faxa kamar da wasa na faxa ko almara. Ko kaxan ba haka bane, sonka da qaunarka su suka haifar da hakan. Za ka sameni ‘ya ce tagari.”

Suka qara yin shiru. Zuwa wani lokaci Saif Ali ya kawar da shirun.

“Bai kamata ace muna fuskantar wannan babbar matsala ba, ke kuma ki zo mana da wannan maganar. Yana da kyau ace kamar yadda ki ka karve mu to ki taimake mu, mu cimma wannan manufa. Ya kamata ace nan da ‘yan kwanaki an fara xaukar miqaqqiyar hanyar warware matsalar nan. Amma idan kika zo mana da wannan maganar ai kamar kina qoqarin damalmala al’amarin ne, ko kina neman xaura mana kayan da ba zamu iya xauka ba alhakin kin san ba za mu iya xin ba.”
“Ko kaxan, kuma ko alama ba ni da nufin hakan. Idan ma na ga wani zai aiwatar to ni zan kawar da shi. Kamata ya yi ku fahimce ni. Kuma wannan wata dama ce ta musamman da zamu yi amfani da ita a tsakaninmu.”

“Kina tsammanin ta hakan za ki taimaka mana?” Saif Ali ya buqata.

“Qwarai kuwa.” Ta ce. “Sai dai ku ne na fahimci kuna neman nuna ba abin da ya shafeku da ni…”

Saif Ali ya katseta.

“Ko kaxan, in ban da abin ki mutumin da yake matuqar qaunar mai kama da ke, ya ke son taimakonki har ki yi tunanin zai qin qaunarki?”

Ta yi murmushi.

Dukkanin maganganun da suke yi ko uffan Almustapha bai ce ba, asalima kansa a duqe yake.

Saif Ali ya kalle shi cikin tausayi, sannanya ce “Zo mu tafi.”

A ranar Almustapha ya bugawa Albashir waya ya tambayi batun qara.

“An shigar da komai kamar yadda ka buqata. Kotu ta amince ta sanya zama ranar Talata mai zuwa sai dai kuma tana buqatar kasancewarku a qasa ranar Litinin. Kuma Barista Sufi Maina yana son zama da ku kafin ranar.” Cewar Albashir.

“Ba damuwa muna nan tafe. A dai ci gaba da yi mana addu’a.”

Albashir ya ce, “Allah ya taimaka.”

Qarfe hudu da mintuna uku na yammacin ranar Lahadi. Almustapha sanye da doguwar riga jallabiya, kansa dauke da makawiya, ya nufi gidansu Lajjanatu. Haka kawai ya sami kansa cikin wani yanayi na nishadi wanda ya bambanta da dukkan yanayin da ya shiga sama da shekara daya, tun dai kafin faruwar al’amarin rabonshi da samun kansa a wannan hali.

Yanayin garin ya gamsar da shi, qamshi da ni’imar garin ya rinqa wadatar dashi, yana jin dadi.

Bai sameta ba. An sanar da shi ta fita, sai dai ba a sanar da shi inda ta nufa ba, don ba su sani ba. Ya tsaya jiranta tsawon lokaci ba ta dawo ba. Qarfe biyar, shida, bayan magariba, bayan isha’i, har zuwa qarfe tara amma ba ta dawo ba. Hakan ya dameshi. Da zai tafi sai ya karvi lambar wayarta.

Yana isa gida, ko zama bai yi ba ya buga mata waya. A lokaci guda ya sameta.
Bayan taqaitacciyar gaisuwa.

‘Wai yanzu kina ina ne?’ Ya buqata tamkar wanda ya aiketa.

‘Babu buqatar sai ka sani.’ Ta fada a taqaice ‘Abin da kawai ya kamata ka sani shi ne abin da zan gaya maka.’ Ta yi shiru kamar mai jiran abin da zai ce.

‘Ba ka amsa min ba?’ Ta ce dashi. Duk da ba a kusa suke ba sai yake ganin kamar tana yi masa kallon ‘me za ka ce!’

Ya yi boyayyiyar ajiyar zuciya ‘Ya ya zai yi?’ Ya tambayi kansa a zuci, a fili kuma ya ce ‘Wai don Allah Lajja me ya sa kike haka?’

Ta katseshi daga can bangaren ‘Ba fa da Lajja kake magana ba, da Lajjanatu ‘yar Misirawa ka ke magana. Almustapha hanya daya ce mawarwara al’amura da matsalolinmu kamar yadda na gaya maka, don haka idan har ka yi qoqarin kuskure wa hanyar to ga dukkan alamu al’amura za su hadu su cabe, kuma ban taba tsammanin hakan za ta faru daga gareka ba.’

Nutsuwa ya yi yana tunani da nazarin al’amarin kamar mai yin mafarki a farke.
‘Wai me ya sa Lajjanatu ta zo masa da haka? Abin da ba zai taba yiwuwa ba. Qarar da rayuwarsa za a yi ko zautar da shi za a yi?’ Ya gaza cankar irin ‘yar gala-gala da ake yi da rayuwarsa.

Mene ne marabar matarsa Lajja da matar Alhaji Hammad Lajjanatu? A wane matsayi musamman ga abin da ya shafi shari’a, al’ada da dabi’ance matarsa take a yanzu, da aka qwace masa ita aka mallakawa wani. Ga shi har sun san juna, ta haihu? Ita kuma Lajjanatun Alhaji Hammad a wane matsayi take?

Ga dukkan alamu ire-iren wadannan tambayoyi suna nan danqar a zuciyarsa. Kuma hakan ne ya sa shi yankewa kansa hukunci ba tare da shiri ba.

‘Ina son ki Lajjanatu! Ina son ki….’
‘Ina fatan da gaske ka ke?’ Ta buqata.

‘Ai ba a fadar wadannan kalmomi da wasa.’ Ya amsa mata.

‘Komai ya zo qarshe.’ Ta ce.

<< Kushewar Badi 4Kushewar Badi 6 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.