Skip to content
Part 10 of 43 in the Series Kuskuren Waye? by Aisha Abdullahi Yabo

Mama ta shigo ɗakin ta same ta cikin wannan yanayin da sauri ta ƙarasa gabanta tana faɗin “Zhara me ya faru?” Tashi ta yi ta rungume Mama tana mai ci gaba da yin kukan,  “ki zo mu tafi ɗakin Abbanki ya na kiran ki” ta yi maganar jiki a sanyayi. Dukansu suna zaune akan kafet sai Dady da Abba da suke zaune akan kujera “ni wallahi da ta kirani hankalina ya tashi na ɗauka mutuwa a ka yi sai da na zo na samu kowa na lafiya na ɗan samu natsuwa”


“kaima dai Yaya sai ka biye wa shashancinta ka tasu cikin daren nan ka zo.”

Idanunsa a kanta ya ce. “Ba wani shashanci tunda har ta kirani da tsohon daren nan tana kuka dole a kwai babban dalili, Mamana faɗa mani me yake damunka?” sunkuyar da kanta ta yi tana mai ci gaba da yin kuka ta kasa cewa komai  Abbanta ya daka mata tsawa “ba da ke ake ba!” ƙara shigewa ta yi jikin Mama tana magana da tsoro a tare da ita “Dady ku gafarceni kuma don Allah ku fahimcini banyi wannan hukuncin dan na tozartaku ba” ta yi  shiru tana shisshiƙa “wai mene ne ki faɗi abinda kike son faɗa ba wai ki samu gaba da kuka ba tunda anan ɗin ba wanda yake sa’anki” Mama ta yi maganar cikin faɗa “zo nan Mamana” Dady ya yi maganar yana ƙyafutata da hannu, ƙarasa wa ta yi gabansa da rarrafe ya dafa kanta yana magana cikin tausasa murya.

“Ki natsu ki faɗa mani abinda yake faruwa In Sha Allah za mu fahimci ki” sunkuyar da kanta ta yi tana kallon kafet tunani take a ranta abinda za ta faɗa zai iya janyo mata ko wani irin ƙalubale a wajan iyayenta sai dai ba ta da mafita da ta wuce hakan tsawar da Abba ya daka mata ne ya sa ta zabura kamar za ta tashi Dady ya zaunar da ita yana yi wa Abba faɗa  “kar na sake jin bakinka anan, ki natsu ki faɗa mani ko meye karki ji tsoro kinji ko?” ta gyaɗa kanta  tana ƙoƙarin haɗiye kukan da take ta fara magana kanta a ƙasa “Dady ku yi haƙuri ni dai a fasa auren nan bana so.”

Dukansu maganar ta zuwar masu a bazata ta kuma sanya masu shokin Abba ya zabura zai kai mata duka Dady yasa hannu ya zaunar da shi sai huce yake “wannan wani irin maganar banza take yi ne, Yaya ka barni na daketa ko zanji sanyi a raina”

“bana ce bana son sake jin maganarka ba” shiru Abba ya yi zuciyarsa na wani irin tafasa wani irin tozarci Zhara take neman janyo masa Mama ko motsin kirki ta kasa yi har a zuciyarta tabbas bata son wannan auren, amma kuma bata ji daɗin wannan abin kunyar da ‘yarsu take shirin janyo masu a idon duniya ba. 

Tambaya Dady ya sake jiho mata  “me ya sa za a fasa dama ba kya son Hafiz ne?”

“Yaya Hafiz yana da wacce yake so ba ni ce zaɓinsa ba” Mama ta ɗauki takalmin da yake kusa da ita ta jefa mata cikin faɗa ta ce. “inji uwar wa! Shi ne ya faɗa maki hakan?” tana shafa goshinta dan taji dukan sam ta daina kukan zuciyarta a bushe take jinta ko me zai faru ba za ta taɓa auren Hafiz ba.   “Mama da iduna da kuma kunnena naji, sau biyu ina ganin shi a gidansu Halima. Ranar naje wajanta Hajiya ta faɗa mani tana tare da baƙo naje ɗakin da suke ina ɗaga labule na gan shi hakan ya sa na yi sauri sakin labulen ba tare da na bari sun ganni ba na tsaya naji duk abinda suke faɗa. Haka ɗazun da na je muka samesu a tare suna magana” ta ciro wayarta jiknta tana faɗin “ga shi duk maganar da suka yi daga ranar har zuwa yau na naɗa a wayata” ta kunna masu ɗakin ya yi shiru ana saurare duk sai jikinsu ya yi sanyi, bayan sun gama ji ta ƙara da cewa

“Don Allah karku tilastani auren nan, sam baya sona kawai dai ba yadda ya iya ne shi ya sa ya karɓi maganar, Dady ka mani alfarma ka yadda ya aure Halima don son Annabi karka ce a’a” ta ƙarasa maganar da magiya, dukansu suka yi shiru kowa da abinda yake saƙawa a ransa, Mama daɗi taji ko ba komai Allah ne ya karɓe addu’arta zai raba ‘yarta da ita kanta da masifar Hajiya Turai, a ɗaya ɓangaren kuwa tana jin rashin kyautata wa irin na Halima haƙiƙa ta ci amanar ƙawance.

“Shi kenan ji ki Mamana Allah ya yi maki albarka” ɗora kanta ta yi akan cinyoyinsa tana ƙara yi masa magiya “don Allah Dady karku ce za ku ɗaura auren nan, wallahi baya sona” shafa kanta ya yi yana faɗin “ki kwantar da hankalinki ba zan taɓa aura maki wanda baya sonki ba ai ba neman kai nake dake ba” cikin farin ciki ta ce. “na gode. Amma ai za a ɗaura da Halima ko”  Abba ya ce. “karka yi saurin yanki hukunci a bari muji ta bakin shi wannan shi ne shari’a.”

“ta bakin shi ya wuce wannan da muka ji, ko da a ce banji ba tunda har ta faɗa tabbas ba zan ƙaryata ba, ina da tabbacin ba za ta taɓa faɗa mana ƙarya ba. Dan haka babu maganar aurenta da Hafiz ba  dan ban isa na tilasta shi ba, sai dan ba zan yadda na aura masa ita ba ya je ya cutar da ita” ita da Mama suka tafi kamar yadda Dady ya umurcesu.

Kwance take jikin Mama ta yi shiru ji take kamar zuciyarta za ta fashe saboda azabar ciwon da take mata,  sai dai ta ƙudurci a ranta ko da son Hafiz ne ajalinta ta barshi har abada.  “na sani kina son shi sai dai hukuncin da kika yi ya yi matuƙar faranta raina In Sha Allah Allah zai fito maki da miji mafi alkhairi wanda za ki yi farin ciki da samunsa, su kuma ki barsu da halinsu in har cin amana abun ƙwai rai ne za ta gani a ƙwaryar shanta, sai ta san ta tabka wa kanta babban KUSKURE” tashi ta yi ta zauna tana kallon Mama  “kar ku zargi Halima Mama ko me ya faru ba KUSKURENTA bane”

“idan har ba Kuskurenta bane to KUSKUREN na WAYE? Hafiz ne?”

“aa ba ko ɗaya KUSKUREN nawa ne, ni ce na bata numbarsa ta gwada shi idan har yana kula wasu matan wannan shi ne KUSKURENA da na aikata wanda silar hakan komai ya faru?” zuru Mama ta mata da idanu kafin daga bisani ta ce. “kin yi ƙurciya Zhara wa ya faɗa maki a na ba ƙawa irin wannan yadda wannan zamanin ai ko ‘yar’uwarki ce ba kya bata wannan yadda ba,  Allah yasa hakanne mafi alkhairi. Kije ki kwanta kar kuma kisa abun a ranki ki ɗauki hakan a matsayin ƙaddara kuma mafi alkhairi” gyaɗa mata kai kawai ta yi ta mayar da kanta kan katifa ta kwanta bayan fitar Mama ta tashi ta ɗauro alwala ta fuskanci gabas tana kaiwa Allah kukanta.

*****

Ba abinda a ka fasa na shirye-shiryen ɗauren aure, cikin ‘yan’uwa babu wanda yasan abinda yake faruwa. Halima ta zo tun da safe suna ta hada-hada, sun fito suna tafiya za su tafi gidansu Halima. Kallonta ta yi tana faɗin “wai duk kewar gidan ce tasa duk kika yi wani iri? Ga dukan alamu kin sha kuka dan idanunki duk sunyi haushi” dariya Zhara ta yi ta ce. “to ai ba ni kaɗai ba har ke kin sha kukan dan fuskarki ta nuna, ni kam tsakanina da zaman gida zama daram, ki ce dai za ki shirya ban kwana da zaman gida” dukan wasa ta kai mata tana faɗin “ke ai ba kya rabo da shaƙiyanci”

“Amarya Allah ya sanya alkhairi” wasu samari da su Zhara suka zo wuce wa ta gabansu suka faɗa da fara’a ta ce. “amin Nasir, Hadi Lawal muna godiya.” a gidansu Halima suka yi taro tare da ƙawayensu. Suna zaune ɗaki kira ya shigo wayar Halima ta tsinke a ka sake kira ta sake tsinkewa “me ya sa ba za ki ɗaga ba?” Zhara ta yi maganar tana mai zuba mata ido “mtsw! Damuwa ne bana so” ta faɗa tare da kashi wayar gaba ɗaya, murmushi kawai Zhara ta yi ta ci gaba da shiryawa dan fitowarta wanka kenan.

*****

“Kasa waya a gaba lokaci na ƙaratuwa don Allah ka tashi ka shirya mu isa wajan ɗauren auren cikin lokaci” Anwar ya yi maganar yana ɗaura agogo a tsintsiyar hannunsa. Ajiyar zuciya Hafiz ya yi kafin daga bisani ya ce. “sam bana cikin natsuwata wallahi tun ɗazun nake ta kiran Halima sai tsinki kiran take, yanzun ma ta kashe wayar gaba ɗaya” kallonsa yake irin kallo nan mai ciki da takaici ya rasa me ma zai ce kawai ya yi tsaki ya cigaba da shirinsa baya so ya yi magana su yi faɗa har abokansu su fahimci wani abun, shi ma bai ce da shi komai ba dan haushin Anwar yake ji sam ya kasa fahimtar me yake ji a zuciyarsa, wayar Zhara ya kira itama a kashe tun jiya kawai ya ajiye wayar ya shiga wanka saboda azalzalar shi da abokansa ke yi.

Cikin gidan suka shiga suna gaisawa da ‘yan’uwa abokan wasa suka sa shi gaba yana ta biye masu ana raha. Za su fita ya hango Gwaggo Hari tana fitowa kichen ya je wajanta yana faɗin “Gwaggo  ina Zhara ne tun jiya nake kiranta bana samunta.”


“Yaran zamani idan ka yi haƙuri ai yau dai a gidanka za ta kwana ko” ya yi murmushi yana faɗin “ba fa wani abun bane dama wasu kayan ne nake so na bata.”

“Ku dai kuka sani tana gidan ƙawar nan ta ta ko ya sunanta ma ni na manta”

“gidansu Halima”

“yawwa ita fa suna can tare da ƙawayensu” gyaɗa kai ya yi tare da barin wajan.

“Mu je ka rakani gidansu Halima”

“Ba za ni ba”

“kai banza ne wallahi to wajan Zhara zan je ina so na bata kayan da za ta yi amfani da su wajan Dena”

Harararsa ya yi yana faɗin “ba inda zan tafi fa” kada Allah yasa ka tafi ɗin!”


 “Wai musun me kuke ko har rana irin wannan sai kunyi halin naku” cewar abokinsu Nasir, “manta da shi zo ka rakani don Allah” har za su tafi ƙarasuwar abokan karatunsa na ƙasar waje tare da wasu ‘yan’uwa ya ɗaukar masa da hankali ya fasa.

*****

Suna ta gaisawa da jama’a ana ta masa Allah ya sanya alkhairi, Anwar ya kai masa zunguri ciki da kiɗima ya ce. “Wai ka ji me na ji?”


“Me ka ji?” ya yi tambayar idanunsa a kan Anwar kafin ya ba shi amsa ya ji amun murya ta cikin bututun murya ana faɗin “AlhamdulilLah an ɗaura auren Muhammad Hafiz tare da amaryarsa Halimatu Sadiya akan sadaki naira dubu ɗari, Allah ya sanya albarka ya… Bai iya sauraron sauran zancen ba ya janyo hannun Anwar suka matsa daga gefe dan kaucewa jama’a “ya haka Anwar me ke shirin faruwa ne?”

“Kai ne zanyi wa wannan tambayar me ka aikata hakan?” ya ma shi tambayar idanun shi a kansa ciki da tuhuma, a jiyar zuciya ya yi  yana faɗin “na san ba lallai ne ka yadda da ni ba amma wallahi ban san komai a kai ba” zuwan wasu mutanen shi ne yasa dole suka bar maganar kallo ɗaya za ka yi wa Hafiz ka fahimci sam baya cikin natsuwa. So yake ya ke ɓance da Dady amma jama’a sun hana ba damar yin hakan haka suka rankaya hotel tare da jama’ar shi domin cin abinci. A gidansu Zhara kuwa rigima ce ta kaure babbar yayar Mama sai faɗa take

“Ai wannan cin mutunci ne da tsantsar cin amana wallahi da na san da wannan zancen da tun a jiyan na je na yi wa iyayenta ɗibar albarka kuma wallahi sai dai kowa ya rasa! Wannan cin amanar har ina, kenan mu duk baro sabgoginmu da muka yi ya zama aikin banza!”


“Don Allah Yaya ku yi haƙuri ku bar wannan maganar, matar mutum kabarinsa ba wanda yake auren matar wani. Sannan komai muƙaddari ne mu ɗauki hakan matsayin ƙaddara mu yi kuma fatan Allah ya sa hakan ya zame mata alkhairi damu ba ki ɗaya”

“Wallahi yau sai mun je mun mata shigen duka shigiyar yarinya kamar ta kirki a she munafunci ne fal a cikinta maciya amana kawai!”


“Ban yadda kowa ya je gidansu Halima da niyar tashin hankali ba, in har kuka min hakan baku kyauta mani ba” da ƙyar ta shawo kansu su ka fasa tafiya sai meta suke suna faɗin to su zaman me za su yi bayan su tattara inasu-inasu su san inda dare ya masu.

*****
Hajiya da tun da suka gama aiki ta bar gidansu Zhara ta dawo gida ta yi wanka idan ‘yan ɗauren aure sun watse sai ta dawo. Ta gama sa kaya kenan Aunty Laila ta shigo uwar ɗakin Hajiya cikin tashin hankali,  kallonta Hajiya ta yi tana faɗin “lafiya Laila za ki shigo ko sallama babu?” Zama ta yi gefen gado ta buga uban tagumi hawaye shar suka fara fitowa a idanunta “SubhanalilLah! Lafiya me ya faru?” kuka ta fashe da shi mai sauti tana faɗin “Halima ta janyo mana magana Yaya, Halima ta yi cin amana cin amana mafi muni!”

“Ki faɗa mini abinda ke faruwa kin sakani a ruɗani”
“Yanzu na fito gidansu Zhara ana ta rigima basu ma san ina wajan ba sai zame jiki na yi na fito”

“rigimar me a ka yi kuma bayan fitowa ta me ye haɗin rigimar da Halima?” ta buɗe baki za ta yi magana shigowar Baban Zhara ya sa ta yi shiru samun waje ya yi ya zauna jikinsa a matuƙar sanyayi hakan ya ƙara jefa Hajiya cikin ruɗani da tsoro, Aunty Laila ta tashi za ta tafi “dawo ki zauna” Baba ya faɗa yana nuna mata wajan da ta tashi da hannu. “Don Allah ku faɗa mani abinda ke faruwa wallahi duk kun saka zuciyata a ruɗani da fargaba”

Jan numfashi ya yi ya furzar kafin daga bisani ya ce. “An ɗaura auren Halima a maimakon na Zhara”
“Wace irin tatsuniya ce wannan Baban Halima, hum sai ka ce wasan yara”

“na taɓa yi maki irin wannan wasan ne, tabbas an ɗaura auren Halima da Hafiz din da ada Zhara za ta aure a ka maye gurbin da Halima” zama ta yi gefen gado a kiɗeme tana faɗin “don Allah ka mani gwari-gwari yadda zan fahimta dan ni ƙara jefani a ruɗani kawai ka yi”

“bayan na fita salla asuba bayan an idar da salla mun fito masallaci Baban Zhara ya ce yana so za mu yi magana mu je gidansa. To bayan mun tafi yake faɗa mani wai a she akwai soyayya tsakanin Hafiz da Halima da suke yi a ɓoye wanda basu san ita Zhara ta sani ba, shi ne ita ta ce ba za ta aure shi ba sai dai a ɗaura da Halima. Na kaɗu sosai da jin wannan maganar musamman da ya neme alfarmar ɗaura auren da Halima kamar yadda a ka tsara za a yi a yau, wallahi ba yadda ban turje ba amma sai da  ya sa na yadda da magiya da ban baki ya nuna mani tarin jama’ar da suka tara a ce an fasa auren da wani idon za su kalle jama’ar.  Wannan ya sa na amince da… Kukan da Hajiya tasa mai sauti kamar ƙaramar yarinya ya hana shi ƙarasa maganar suka zuba mata idanu.

Fulani

<< Kuskuren Waye? 9Kuskuren Waye 11 >>

3 thoughts on “Kuskuren Waye? 10”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×