Miƙewa ta yi kamar wacce a ka tsikara ta fita daga ɗakin da sauri. Aunty Laila ta yi ajiyar zuciya kafin daga bisani ta ce. “gaskiya Yaya da an bamu shawara wallahi ba za a yi wannan auren ba, haba wannan cin amanar dame ya yi kama?”
“Yo ya na iya ya ɗaɗɗaureni da kalaman da ba zan iya cewa a’a ba, amma ni kaina ban so hakan ba, uhm! Koma dai meye mai afkuwa ta riga da ta afku sannan wani baya auren matar wani mu ɗauki hakan a matsayin muƙaddari daga Allah.”
Ta na zuwa ta samu Zhara da wasu daga ƙawayensu “Ina Halima?”
“Ta shiga wanka” Zhara ta bata amsa, daidai lokacin da ta fito wanka ta na goge jikinta da tawol Mama ta fincikota ta na kai mata duka ta ko ina irin dukan nan na huce haushi ihu tasa ta na faɗin “wayyo Hajiya me na yi maki ne?”
“Kin cucemu Halima kin cuce kanki ki rasa wacce za ki ci amana sai ƙawarki wacce ta zama tamkar ‘yar’uwarki tir da halinki!” Zuwa ta yi ta janyeta da kyar ta na faɗin “ba laifinta ba ne ko me ya faru KUSKURENA ne ba na ta ba ne don Allah ki daina dukanta” ta ƙarasa maganar ta na kuka.
“Wai me ya faru ne? Ban san a kan me kuke maga… Marin da ta mata ne ya sa ta haɗiye sauran zancen ba tare da ta shiryawa hakan ba, “har kina da bakin magana ko, shi kenan an ɗaura aurenki da Hafiz ki je ki tsinci abinda za ki tsinta a auren na shi kuma wallahi tunda har ku ka ci amana daga ke har shi sai kun yi dan… Saurin rufe mata baki Zhara ta yi tana kuka “don Allah karki yi mata baki wallahi ko me ya faru KUSKURENA ne ba na su bane” gaba ɗaya ta shiga ruɗani ji take kamar a mafarki wai an ɗaura aurenta da Hafiz wannan wani irin mummunan mafarki ne take?
Cire hannun ta yi daga bakinta ta na faɗa “za ki janye mini daga gabana ko sai na haɗa har ke?” Idonta ya kai kan wani maburge ta ɗauko ta yi kan Halima, Zhara ta yi saurin rungume Halima a ka sameta a goshi, idonta ya riga ya rufe ta haɗa su biyun tana duka da ƙyar Aunty Laila ta janyeta daga ɗakin ta na bata baki, kowa ya zuba masu idanu tambayoyi fal a zukatan jama’ar da ke gidan.
“Zhara ki fitar da ni duhu me ya faru?”
“Mene ne na kuka tunda burinki ya cika kin samu muradin zuciyarki, ba dai auren cin amana ba ki je ki gani idan za ki ci riba” Aunty Laila da take tsaye daga ƙofa ta faɗa ta na harararta kamar idanunta za su zazzage. Tashi ta yi ta kalle Zhara ta kalle Aunty Laila duk sun sake jefata a ruɗani,
“Na sa ni kina soyayya da Yaya Hafiz duk da kina ƙoƙarin ɓoye mini, wannan ya sa na faɗa wa su Dady suka kuma amince yau an ɗaura aurenki da Yaya Hafiz” durƙushe wa ta yi a wajan kanta a ƙasa ta kasa ɗago kai ta kalle Zhara wasu hawaye masu zafi ne suke bin fuskarta ta kasa tantanci yanayin da take ji tsakanin kunya baƙin ciki abinda kawai ta sa ni bata jin farin ciki ko kaɗan a tare da ita. A ka shiga kallon-kallo tsakanin mutanen da suke cikin ɗakin nan fa magana ta tashi a na magana ƙus-ƙus.
Rungumeta Zhara ta yi ta na faɗin “karki damu wallahi har cikin raina ban ɗauki hakan komai ba, wani ba ya auren matar wani dama can ba ni ce matar shi ba, faruwar hakan ba zai sauya komai daga alaƙarmu ba” ta kasa cewa komai kamar yadda ta kasa iya ɗago kanta bare ta iya kallon idanun Zhara. “Allah ya kyauta ni kam zan tafi,” cewar ɗaya daga cikin ƙawaye su, “Haba dai tun yanzu?”
“h to ai an riga da an ɗaura kuma anjima kaɗan za a tafi kai amarya gara mu ta fi, Allah ya sanya alkhairi, Allah ya musaya maki da wanda ya fi shi” tasa kai ta fita murmushi mai haɗi da kuka kawai Zhara ta yi, haka sauran duk suka watse dan gulma na cinsu.
*****
“Anwar na shiga ruɗani so nake na ji yadda a ka yi har wannan sauyin ya faru amma ka ga Dady ya ma yi tafiyar shi sam ya ƙi ba ni fuskar yi masa tambaya”
“to kai me ye abin damuwa bayan ka godewa Ubangiji da ya cika maka burinka ka samu muradinka” ya yi maganar fuskar shi babu annuri domin har cikin ranshi yake jin ciwon wannan sauyin ya na jajanta wa abokin shi rasa mata kamar Zhara. Shiga mota ya yi ya na faɗin ni zan tafi Kano ana ta kirana asibiti.”
“Kamar ya za ka tafi yau ɗaya ba za ka iya ɗaukar hutu ba? Ina ce yanzu za mu je mu ɗauki amarya” cewar Mansur “ƙyaleshi ya fi ruwa gudu kada Allah ya sa ya tsaya!” ya yi maganar a fusace tare da barin wajan, Mansur ya kalle Anwar da ya shiga mota ya na faɗin “wai me ya faru ne? Gaba ɗaya kun samu a ruɗani an sauya amarya ga shi kuma ku na faɗa me ya faru?”
“Ba faɗa muke ba kawai uzuri ne, sauyin amarya kuma ka tambaye shi” ya rufe marfin motar da ƙarfi tare da jan motar a guje ya bar unguwa. “uhm! Dole a kwai abinda yake faruwa, sai dai kun fi kusa.”
Wayar shi ta yi ringin ya duba Abba ne ya ɗaga kiran cikin ladabi kamar ya na kusa da shi “barka da wuni.”
“Yawwa Hafiz kana ina ne?”
Mu na masauki”
“Ya kamata motocin ɗaukar amarya su zo a tafi yamma na yi ga kuma hanyoyin ba su da kyau, sannan ina son ganinka kafin ku tafi” jiki a sanyaye ya ce. “to Abba” ya tsinke kiran “Mansur ina su Ƙasim don Allah su fito a na jiran motoci.”
“Ok bari na kirasu sai mu tafi dama duk sun shirya” ya faɗa tare da barin wajan, ya nufi motar shi dake a jiye wajan ajiye motoci a cikin hotel ɗin.
*****
“Hafiz ka saki jikinka ni ban ɗauki wannan lamarin komai ba face abinda Allah ya riga da ya tsara mun so a yi wannan haɗin domin zumunci ya ƙara ƙarfafa sai dai mu na namu ne Allah na na shi kuma na Allah shi ne gaskiya, fatanmu Allah yasa hakan ya zama alkhairi ya kuma ba ku zaman lafiya da zuri’a ɗayyaba”
“Ina mai neman gafarar ku Abba, ban taɓa faɗa wa Zhara ba na sonta ba, duk da na san na yi KUSKURE da har na biye wa zuciyata na so aminiyarta ba tare da na yi la’akari da alaƙarsu ba am… “ya isa hakan kar kuma wannan ya dameka kamar dai yadda na faɗa maka tun a farko Zhara ba ta ce ka ce ba ka sonta ba kawai dai ta fahimci Halima ce zaɓinka dan haka wannan hukuncin da a ka yi shi ne daidai da a zo a aura maka abinda ba zaɓinka ba matsala ta zo ta biyu baya zumuncin da muke ƙoƙari ƙarfafawa ya zo ya lalace kaga kenan an ɓata goma biyar bata gyaru ba.”
Shiru ya yi ya kasa cewa komai wata irin kunyar dattijon yake ji a ce ya yi abinda har suka gane baya son ‘yarsa wannan lamarin da kunya me zai ce shi, maganar Abba ya tsinkayo ya na faɗin “na kira mahaifin Halima na faɗa masa za ka zo ku gaisa dan haka ka je ka gaishe su dan ku san juna kafin ku tafi. Allah ya yi maku albarka ya yi wa rayuwar aurenku albarka.”
“Amin na gode Allah ya ƙara lafiya” ya yi maganar kan shi a ƙasa.
*****
“Ki daina kukan nan haka na faɗa maki ban ɗauki wannan a matsayin komai ba, da ni dake duk ɗaya ne, dan haka ki daina kuka ko damuwa fatana Allah ya baku zaman lafiya, kuma ki kular mini da Yayana sosai shekara mai zuwa ki bamu Baby ko Babys” ta yi maganar ta na dariya rungumeta ta yi ta na kuka “ban san da wace kalma zan nemi yafiyarki ba, haƙiƙa na tabka babban KUSKURE da har na bari zuciya ta kai ni ga cin amanar amintakarmu wal… Ta rufe mata baki ta na faɗin “ba KUSKURENKI ba ne nawa ne kuma mu manta da komai mu ɗauki hakan a matsayin ƙaddara kuma mai kyau”
“A’a Zhara KUSKUREN ba na kowa bane nawa ne ai cewa kika yi na gwada shi me ya sa na bari har son shi ya yi tasiri a zuciyata ba tare da na duba wace ce ke a wajena ba, ni ba inda zan tafi dole ne a warware wannan auren ba na son shi!” miƙewa ta yi ta na faɗin “ki daina faɗin wannan maganar in har ba so kike raina ya ɓaci ba, ki tashi ki shirya yanzu za a zo ɗaukarki ina maki fatan alkhairi a rayuwar aurenki” ta na gama faɗa tabar ɗakin da sauri saboda kukan da take ƙoƙarin dannewa da yake shirin fin ƙarfinta. Kifi kanta ta yi jikin katifa ta na kuka harda shisshiƙa anya bakin duniya kaɗai zai barta da wannan cin amanar da ta aikata wa aminiyarta.?
“Wai da kike ta faɗa da cewar dole sai an warware wannan auren shin ki na so ne ki ja da ikon Allah ko mun isa mu sauya wa kanmu ƙaddararmu ne? Haba don Allah ki sanya wa zuciyarki salama mu bi auren nan kawai da addu’a ta alkhairi tunda an riga da an ɗaura.”
“Ba wai na kasa karɓar ƙaddara ba ne, amma da wani idanun zan kalle Zhara da iyayenta wallahi da kunya yau fita wannan na tabbata sai ta gagareni a cikin unguwar nan tsegumi da ƙananun maganganu kuma sai wanda a ka manta..”
“Sai kiji baki ji ba, ki kuma gani ba ki gani ba, dama su mutane ai ba a iya masu ko warware auren a ka yi ba wai tsira za ki yi ba. Dan haka ki daina ma kawo wannan aranki komai na da lokaci duk wani abu da za a faɗa kamar gobe ne ya wuce kamar ba a yi ba” gyara zamanta ta yi tana fyace majina da haɓar zanenta “amma dai ai ba yau za ta tafin ba ko?”
“Hakan na faɗa wa Alhaji a bari sai mun shirya tunda ya zo babu shiri ya ce a’a ba abinda zai sauya da Zhara da Halima duk ɗaya suke a wajansu dan haka za ta zaune kayan Zhara yau za a kaita.”
“Kuma sai ka amince? Sannan su kuma ‘yan’uwa da basu san da maganar ba ko za a kaita ne babu danginta?”
“To zan ce a’a ne? Kin san yadda muke da shi babu abinda zai ce na ce a’a komai ya yi ya isa da ita ne, maganar ‘yan’uwa kuma dama wasu daga cikin ‘yan’uwanki har nawa ai sun zo bikin kin ga ta kwana gidan sauƙi sai su tafi tunda da yawa daga cikinsu sun zo da niyar zuwa har kanon” ta na gyaɗa kai ciki da takaice ta ce. “Allah sarki su na ta bamu kunyarmu an masu laifi amma kamar ba a masu komai ba sai saka mana da alkhairi suke a kan tsiyar da ‘yarmu ta yi ma su.”
“Ki bar wannan maganar ki zo mu je soro ku gaisa da shi”
“Shi wa?”
“Angon mana, ya zo gaishe mu ne” ta na gyaɗa kai ta ce. “Ni ba inda zan tafi” bai wani ja ba ya fita ɗakin dan ya fahimci har yanzu ta na kan dokin zuciya.
Ya samu ya na zaune a kan tabarmar da ya bar shi ya zauna a inda ya tashi ya na faɗin “ta na tare da jama’a daga baya kwa gaisa”
“To Baba na gode a ƙara bata haƙuri.”
“Ba komai Allah ya sanya alkhairi, sannan ina ƙara tuna maka lallai ka bai wa iyayenka haƙuri ka kuma aure zaɓinsu matuƙar ka na son ka ga haske a rayuwarka to ka zama mai biyayya ga mahaifa” har cikin ran shi yake jin son dattijon wannan ne karo na farko da ya gan shi amma ya fahimci ya na da kyakyawan hali, sai dai ya na jinjina yadda zai iya zama da mace biyu kuma aminai, sai dai tabbas gaskiya ya faɗa ma shi domin Allah kaɗai ya san irin fushin da Dady yake yi da shi. Jiki a sanyaye ya masa sallama.
*****
Lokacin da a ka zo tafiya da amarya ta buga kai da ƙasa babu inda za ta tafi, Hajiya ta zo ta fincikota daga jikin Yayar Babanta ta wanka mata mari “uban wa kike faɗa wa ba za ki je ba ba kya so? Ba kya so ne kika yadda da shi har kuka yi cin amana!” Maman Zhara ta zo ta ƙwaci Halima daga hannunta ta na faɗin “haba Hajiya me ya yi zafi don Allah ki sanya wa zuciyarki ruwan sanyi, wallahi daga mu har Zhara duk ba mu ɗauka da zafi ba dan haka ki yi mata addu’a ki yi mata nasiha irin ta uwa domin ta samu ta shiga ɗakin aurenta cikin albarkar iyaye” haka taita yi mata nasiha har sai da jikinta ya yi sanyi aka fita a ka barsu daga ita sai Halima.
Ta je jikinta ta kwanta ta na kuka “ki yi haƙuri tabbas na aikata babban kuskure amma wallahi ƙaddara ce ban aikata hakan da son raina ba, kuma wallahi na yi ta ƙoƙarin mu rabu shi ne ya nace mini. Don Allah ki gafarceni”
Shiru ta yi bata iya cewa da ita komai ba, Mama ta zo ta na faɗin “ta so mu je ‘yata kar dare ya mana” haka Mama ta ja ta ta na kallon Hajiya da idanunta da suka yi kumbura magana take so ta mata amma ko kallonta taƙi ta yi bayan fitarsu Hajiya ta yi ajiyar zuciya har cikin ranta ba ta so wannan auren ba amma ya ta iya da abinda ya fi karfinta bayan ta yi mata addu’a da fatan samun zaman lafiya a gidan aurenta.
Motar amarya Mama da Yayar mahaifinta ne a ciki “ina so naga Zhara” ta yi maganar cikin shaƙaƙƙiyar murya da taci kuka. “Ki yi haƙuri da ko wace magana ce idan mun isa kika samu natsuwa sai ku yi waya da ita Babanku sai faɗa yake yi a kan mu tafi saboda yanayin rashin kyan hanya”
“Ba tare za mu tafi ba?”
“Eh za ta zauna tare da ‘yan biyu kar abar gida ba kowa, amma ki kwantar da hankalinki za ta zo daga baya” kifi kanta ta yi akan cinyoyinta ta na cigaba da yin kuka “me ya sa rayuwa ta juya mata haka ne? Yau ita ce ta yi aure kuma da wanda a da zai aure aminiyarta.!
*****
Dare ya raba gidan ya yi tsit tamkar ba a yi taro ba sai ita kaɗai zaune a tsakiyar katifa ‘yan biyu su na gefenta sun yi bacci, so take ta yi bacci ko za ta samu salama daga tunanin da ya addabi zuciyata yake neman fasa mata ƙwaƙwalwa, wani irin ciwo take ji da zafi irin wanda bata taɓa ji ba a zuciyarta. Da ƙyar ta iya miƙewa ta na dafa bango ta fito tsakar gida ta nufi wajan da a ka ajiye firij ta buɗe ta ɗauki ruwa masu sanyi har sun soma yin ƙanƙara ta kafa abakinta ta sha amma sam bata daina jin wannan zafin ba ta juyo da jan ƙafa jiri ya ɗibeta ta faɗi a kan wani tirin tasa da yake ajiye ƙarar faɗuwar ne ya sa Abba da shi ma bacci ya ƙaurace wa idanun shi ya fito ya na haska tsakar gidan da fitilar wayar shi “SubhanalLah Zhara! Me ya faru?” ya yi maganar ya na mai ƙarasawa wajan da sauri ya tallafota ya na kiran sunanta, shiru hankalinsa ya matukar tashi ganin idanunta sun kakkafi babu kuma inda yake motsi a cikin jikinta.