Skip to content
Part 17 of 43 in the Series Kuskuren Waye? by Aisha Abdullahi Yabo

Kallonta ya yi da murmushi a fuskarsa ya ce. “ina za mu tafi yanzu?” Murmushi ta yi ta na faɗin “ai tafiya a wajan ka ta ke ni da na ke ‘yar rakiya.”

“Au hakan ma za ki faɗa, to shi kenan mu je gida ki gaida Mama, idan mu ka fito sai mu shiga gari ko?” Ta gyaɗa masa kai. “Na tambaye ki?”

“Allah ya sa na sani” fuskarsa da murmushi ya ce. “kin ma sani sai dai idan ba za a bani a masa ba” da murmushi a fuskarta ta ce. “haba dai idan har na sa ni me zai sa na ƙi bayar da amsa”
“Saboda halin ku ne mafi yawan ku mata ba kasafai ku ke bayar da gaskiyar amsar irin wannan tambayar ba idan an ma ku.”

“Humm to ka cire ni a wannan layin duk da dai ban san wace tambayar ba ce amma da yardar Allah ina da tabbacin zan ba da amsa ta gaskiya idan har na sa ni.”

“Na yarda da ke Zhara” ya ɗan ja numfashi ya furzar a sannu kafin daga bisani ya ce. “Na san zuwa yanzu kin tsayar da wani a matsayin zaɓin ki ma’ana abokin rayuwar ki ko?”

Shiru ta yi ta na mayar da dubanta gefen hanya ta na kallon ababin hawan da su ke kai da kawo ‘uhm! Yaya Anwar kenan ni soyayya sam ba ita ce a gabana ba a yanzu an sha ni har yanzu ban warke ba. Ban sa ni ba ko a gaba son Yaya Hafiz zai bar ni har na iya sa wani a zuciyar nan tawa’ “ya dai kin yi shiru” maganarsa ce ta dawo da ita da ga zancen zucin da ta ke. “Ba amsa ko?” Ya yi mata tambayar ya na kallonta, gyaɗa kanta ta yi alamar a’a. Ya mayar da kallon shi ga hanya ya na faɗin “au amsar ta kurame ce kenan” murmushi ta yi ta na faɗin “a’a gaskiya ban tsayar ba, Yaya Anwar ni da na ke karatu ina zan haɗa soyayya da karatu ai taura biyu ba sa taunuwa a lokaci ɗaya” shiru ya yi tamkar mai nazari kafin da ga bisani ya ce. “Hakan ne gaskiya, uhm! Amma kin san me na ke so da ke?” Ta gyaɗa masa kai alamar a’a. “Wani alƙawari na ke so ki mini.”

“Alƙawari kuma?” Ta masa tambayar da mamaki a fuskarta gyaɗa kansa ya yi ya na faɗin “eh alƙawari na ke so ki mini, amma fa alfarma ce za ki mini ba dan na kai ki mini ba.”

“Humm Yaya Anwar ka na da matsayin da zan ma ka ko meye matuƙar hakan ba zai saɓa da addini na da kuma al’adata ta Hausa Fulani ba.”

“Na gode sosai na kuma ji daɗin hakan. Kin san me na ke so da ke”
“A’a sai ka faɗa” tsabar mamaki har ba ta san ya a ka yi ta kafe shi da idanu ba, ya ɗan kalleta da murmushi a fuskar shi ya sake mayar da duban shi ga hanya, “na sa ni za ki yi mamaki dama, amma ki kalle hakan da kyakyawar manufa” shiru ta yi tare da sunkuyar da kanta ta na wasa da zoben hannunta ita har ma ta rasa me za ta ce da shi. Tsayar da motar ya yi daidai wani gida ya na faɗin “zan ba ki lokaci ki yi tunani, sai dai ba zan so na ji kalmar a’a a bakin ki ba zuciyata ba za ta iya jurar hakan ba. Ba kuma zan hana ki faɗar ra’ayin ki ba. Mu je ko mun ƙarasu” ya ƙarasa maganar ya na mai buɗe ƙofar. Fitowa ta yi jiki a sanyaye ta bi bayan shi su ka shiga cikin gidan.

Da sallama su ka shiga falon gidan Fatima ce kaɗai a falo ta na kallo ta amsa ma su sallama “sannun ku da zuwa Yaya” ta faɗa idanunta a kan Zhara, kallon Zhara ya yi ya na faɗin “bisimillah zauna.

“Fatima ina Mama?”

“Ta na kichen”

“Shi ne ki ka zauna ki na kallo ki ka barta da aiki” ya yi maganar cikin faɗa, ta na susa kai ta ce. “Ita ce ta ce za ta yi da kanta.”

“Za ki sani ne idan har na tambaye ta ta ce ba hakan a ka yi ba, kuma ba ki iya gaida baƙi ba ne kin wani zuba wa mutane idanu.”

“Yanzu dama zan gaishe ta, ina wuni Aunty” da murmushi a fuskarta ta ce.
“Lafiya lau takwara ya gida.”

“AlhamdulilLah” ta amsa ta na mai mayar mata da murmushi. “Zhara ina zuwa bari na kira Mama” ya faɗa tare da ficewa falon. Fatima ta je ta kawo mata ruwa ta a jiye a gabanta, “na gode” Mama ta ƙarasu falon da murmushi a fuskarta “maraba da Zhara’u yau dai Allah ya nufa an kawo mini ke kusan koyaushe sai Anwar ya yi mini zancen ki.” zamowa ta yi da ga kukerar da murmushi a fuskarta “Ina wuni Mama.”

“Lafiya lau, ya mutan gidan na ku” ta faɗa ta na mai zama a kan kujera kusa da Zhara, “duk su na lafiya, sun ce a gaishe ki” Fatima ta zame jiki ta bar falon ɗakin su ta shiga ta samu Nabila ta na kwance ta na chat “Aunty Nabila tashi tashi ki ji.”

“Mene ne kuma ba na son takura fa, kema fa kin iya yanzu ba dama mutum ya zauna sai kin takura shi.”

“Kai Aunty ba fa wani abun ba ne, dama Yaya Anwar ne ya zo tare da budurwarsa shi ne na zo na ke faɗa ma ki za ki wani gwale ni” fito da idanu ta yi ta na fadin “kai Fati da gaske Yaya Anwar ne ya zo da budurwa gidan nan.”

“Wallahi da gaske na ke kin gansu can falo” diruwa ta yi da ga kan gado ta nufi falon da sauri ta na mamaki a ranta bata taɓa jin Yayan su na da budurwa ba ko da wasa bare har ya kawo ta gida, lallai kuwa ko wacece ta musamman ce.

Ta samu Mama ta cika gabanta da abinci da kuma cincin sai abin sha, ta kai duban ta ga Anwar da idanunsa su ke a kan Zhara sai murmushi ya ke kamar gonar auduga. “Yawwa Nabila zo ku gaisa da Auntynki.” Mama ta yi maganar ta na yafitota da hannu. Ƙarasa wa ta yi wajan Zhara da ita ma ta ke kallon ta, “sannu da zuwa Auntyn mu.”

“Yawwa sannu Nabila.” Sosai ta ji daɗin ziyarar har sai da ta ji kamar kar su rabu. A hanyar su ta komawa ta kalle shi ya na tuƙi hankalin shi a kwance “kasan Allah na ji kunya, ban kawo wa Mama komai ba amma ita ta ba ni na karɓe.”

“To mene ne a ciki dan uwa ta yi wa ‘yarta kyauta ta karɓa watarana ai ke ma za ki yi ma ta ne.”
“Humm, to Allah ya ba ni iko. Mutanen gidan ku su na da kirki da son mutane har sai na ke ji kamar kar mu rabu da su.” Murmushi ya yi tare da kallon ta “idan kin so za ki iya zama ɗaya da ga cikin su, kema gidan ku ne ai” sunkuyar da kanta ta yi ta na murmushi ba tare da ta ce da shi uffan ba, shi ma ɗin mayar da hankalinsa ya yi ga tuƙin.

Dawowar yamma ya yi ya tarar da gidan ba kowa sai Kande da ta ke zaune a kan kafet ta na kallo kasancewar sun gama girkin dare. “Kande ba kya jin sallama ne?” Da sauri ta waigo “a yi mini afuwa Alhaji sam ban ji shigowar ka ba, sannu da dawowa an dawo lafiya” zama ya yi a kan kujera ya na faɗin “yawwa sannu, lafiya lau, ina mutanen gidan ne?”

“Sun fita unguwa, sai Zhara ce a gidan.”

“Kai Kande babu ko kara Maman nawa ki ke faɗa hakan a gabana” rufe baki ta yi kanta a ƙasa “a yi haƙuri suɓul da baka ne na yi” murmushi ya yi ya na faɗin “ba damuwa, kira mini ita.”

“To” ta faɗa tare da miƙewa tsaye, remote ya ɗauka ya na sauya tasha, ganin ta nufi hanyar ɗakin ta ya ce. “A’a ba Mamana na ce ki kira ba.”

“Eh ita zan kira ai a ɗaki ɗaya mu ke.” mamaki ya cika masa zuciya ya kafi hanyar da idanu, jim kaɗan Zhara ta shigo falon da murna ta ƙarasa gaban shi ta zauna “sannu da zuwa Dady, an dawo lafiya”
“Lafiya lau Mamana.”

“Dady ai ban san yau za ka dawo ba.”

“Hakan ne ban faɗawa kowa ba, ba dai wata damuwa ko?” Gyaɗa masa kai ta yi ta na faɗin “ba komai Dady”

“Masha’allah hakan a ke so, bari na je na huta na kwaso gajiya” ya miƙe tsaye “a kawo abinci Dady?”
“Me ku ka girka ne?”

“Jalof ɗin makaroni da busasshen kifi” tsaki ya yi “barshi kawai kin san na fi son Tuwo da dare.”
“Akwai garin dawa da Maman su Yaya Anwar ta ba ni na kawowa Momy yanzu sai na tuƙa ma”
“A’a Mamana dare ya yi a bari gobe sai ki yi.”

“Ba wahala fa yanzu sai na gama tun da a kwai komai.” Shafa kanta ya yi cikin murmushi “Allah ya yi ma ki albarka.”

“Amin” ta amsa da murmushi a fuskarta. Ya na tafiya ta faɗa kichen. Cikin ƙanƙanin lokaci ta gama tuwon ta kwashe ta na buɗe ɗaya tukunyar dan kaɗawa Khadija ta shigo ta na faɗin “kukun gidan mu me a ke dafa mana ne ƙamshi har harabar gida?”

“Humm, tuwo ne na ke yi wa Dady. A she kun dawo.”

“Kai yaushe Dady ya dawo ba labari” ba ta jira amsar Zhara ba ta fice da sauri.

Momy ta na zaune gaban Dady sai santi ya ke “kai Mamana ta iya girki wannan daɗi haka, ko da ya ke ba abin mamaki ba ne raino… Katse shi ta yi a ƙufule ta ce. “Alhaji idan wani ya ji wallahi sai ya ɗauka ni ban iya girkin ba, ka wani sa abincin ƙaramar yarinya gaba ka na ta ya bo, kamar wanda bai saba cin girki mai daɗi ba.”

Murmushi ya yi ya na faɗin “wane ni na ce ba ki iya girki ba, kin iya irin na ku na zamani, sannan yaushe rabon ma da ki girka da hannun ki ki ba ni sai dai kisa mai aiki ta girka. Wallahi da za ki tsaya ki koyi abincin gargajiya a wajan Mamana da na ji daɗi tun da kin san ina so.”

“Tabɗijam Allah ya tsare gatari da sarar shuka. Tun kan a san za a haifi ta na ke girki a duniyar nan sai yanzu dan mai da kai baya zan ce ta koya mini girki lallaima Alhaji. Ita dai tai ta girka ma ka dama ai cimakar su ce.’

“Ai shi kenan za ta din ga girka mini ɗin, idan na kusa aurar da ita sai na samu ‘yar gargajiya irinmu na auro” jan numfashi ta yi ta furzar da ƙarfi “na dai fahimci wannan dawowar da wata ka zo a ranka.”
“Allah ya ba ki haƙuri babu wata da na dawo da ita a raina sai alkhairi, dan haka ki mayar da wuƙar” ya faɗa da dariya.

Ta idar da sallah Azahar ta na shafa mai Kande ta shigo ta zauna gefen katifa ta na faɗin “ɗazun na shigo ki na bacci”

“Eh jiya ban yi bacci da wuri ba na yi karatu, wani abu ne?”

“Dama Alhaji ne da zai fita ya kirani ya ke tambayata a ina ki ke zama”

“Allah dai yasa ba ki faɗa masa ba?” Ta mata tambayar cikin tsoro. “Sai dai ki yi haƙuri ke ma kin san tunda har ya tambaye ni ai dole zan faɗa masa gaskiya, bare kuma jiya ya ga na shigo nan kiran ki”
“Uhm! Me ya ce to da ki ka faɗa masa”

“Gyaɗa kansa kawai ya yi ya ce na tafi” tashi ta yi ta na sauya kayan jikinta da ga riga da wando na kanti zuwa atamfa, “to Allah dai ya sa kar hakan ya janyo wata fitinar, ni dai ba na so a yi wata rigimar saboda ni wallahi”

“Amin dai, amma ko me ya faru ai ita ta janyo tun da taƙi bin umurnin shi” komai Zhara ba ta ce da ita ba, ta ƙarasa shiryawa ta na sa Hijab ta ce. “Ni kam na tafi makaranta sai na dawo”

“A dawo lafiya, yau ma Anwar ne zai ka ki?”

“Eh ya na waje ya na jira na, nayi-nayi ya daina zuwa ya ƙi”

“Ai ya na da kirki, kuma wallahi kun dace musamman yanayin halayyar ku ya zo ɗaya da shi” kallonta kawai ta yi kamar za ta yi magana kawai ta yi shiru tasa kai ta fita bayan ta ɗauki jakarta. Murmushi Kande ta yi a ranta ta na addu’ar Allah ya tabbatar da lamarin “ko ba komai wallahi da ta yi dace da ga shi har babar shi masu kirki da ƙaunar ta.”

Ɗakin Momy ta haura ta samu ta na fitowa da ga wanka, “Momy na ga an gyara ɗakin nan na kusa da ni an sa komai sabo waye zai zauna a ciki?”

Zama ta yi gaban madubi ta na goge ruwan jikinta da tawol “yadda ki ka ga ni ni ma hakan na ga ni banbancin kawai ya kira ya faɗa mini za a shigo a sa kaya”

“To me hakan ya ke nufi kenan?” Ta yi tambayar fuskarta ɗauke da mamaki. “Ina zan sa ni sai ya dawo mu ji.”

Da dare ta na waya da Mama Khadija ta shigo ta mata tsaye a ka “kuku ki zo Daday na kiran ki” ta na faɗa ta fice, “Mama ina zuwa”

“Waye a ke cewa kuku?”

“Mai yi masu girki a gidan su ke kira da hakan, ina zuwa Mama Dady ne ke kira na” ta tsinki kiran tun kan ta sa ke jiho mata wata tambayar dan sam ba ta so ta san matsalar da ta ke fuskanta da mutanen gidan. Zaune ta same su a falon, zama ta yi dab da ƙafafun sa “Mamana me yasa ki ka fiya zaman ɗaki ba kya fitowa fira?”

Murmushi ta yi ta na faɗin “ba komai Dady”

“Mu je to na nuna ma ki ɗakin ki” ya faɗa tare da riƙo hannunta ta miƙe tsaye, Momy da Khadija su ka kalle juna kafin daga bisani su ka mayar da duban su ga su Zhara da har sun fara hawa matattakala. “Momy kar dai Zhara ya gyara wa ɗakin nan?”

“Alamo kam ya nuna hakan, tashi mu bi su mu ga ni.”

“Masha’allah Dady komai ya yi kyau sosai wallahi, Allah ya ƙara lafiya da yalwar arziƙi alfarmar Annabi (S.A.W)”

“(S.A.W) amin. Idan da akwai abin da bai ma ki ba ki faɗa sai a sauya ma ki, ko idan a kwai abin da babu a saya ma ki” gyaɗa kanta ta yi ta na dariya “Dady ai har yawa sun yi idan su na yawa, komai ya yi kyau sai sambarka”

“Dady ni kuma fa? Gaskiya sai dai ta dawo ɗakina ni na zauna a nan ɗin” kallon ki kiyayeni ya mata ta tsuki baki ta na turo baki “Alhaji ba harararta za ka yi ba, maganar gaskiya wannan ɗakin ya ma ta girma, kawai ka bar wa Khadija ita sai ta koma na Khadijan, Allah na tuba ta yi da wannan ɗakin wacce ta saba da rayuwa ɗaki mai kama da na akur ki”

“Wallahi ki kiyaye ni Turai, duk da na yi ma ku umurnin ta zauna a ɗakin Khadija da ga ke har ‘yar ta ki ku ka sa ƙafa ku ka shuri ku ka yi na ku hukuncin ban ce da ku komai ba shi ne har ku ke da ƙwarin gwauwar kawo mini wani zancen wufi. To shi kenan na sa ke jin kun ce ko da uffan ɗin ku ga yadda za mu yi da ku” jikin Zhara ya yi sanyi cikin sanyin murya ta ce. “Dady zan bar mata sai ni na zauna na ta ɗin”

“Mamana nan ɗin na ke so ki zauna, kar kuma ki kula zancen kowa a cikin su, kema ‘ya ce kamar kowa a gidan nan ki yi yadda ki ka so kin ji ko?” Ta gyaɗa kanta har ya kai ƙofa ya juyo ya kalle su “kar ku kuskura na ji wani abun ya biyu baya saɓanin nawa hukuncin ran ku zai yi matuƙar ɓaci”
“Ikon Allah yau na ga yadda bare ya ke zuwa ya fi ‘yar masu gida galihu” komai bai ce da ita ba yasa kai ya fice. Ranƙwashi ta kai mata a ka har sai da ta sunkuyar da kanta dan zafi “ga ki ga ɗaki ‘yar ƙauye yanzu ki ka fara ganin ɗaki irin wannan ga dukan alamu kuma har abada ba za ki taɓa samun wani ɗakin irin wannan dai ba” ta ja hannun Khadija da tsabar takaici ta kasa magana. Jiki a sanyaye ta sauka ƙasa Kande ta taya ta haɗa kayan ta ta na faɗin “gaskiya zan ji kewa wallahi kamar kar ki tafi”

“Hahaha kin ji ki da abin dariya kamar wacce zan tafi wani gari, mu nan tare fa”

“Zaman ɗaki ni kaɗai fa zan dawo yi”

“Ba sai ki zo mu dawo ɗaki tare ba” fito da idanu ta yi “kai rufa ni ki saya ai sai Hajiya ta sa ni a turmi ta kirɓe” dariya marar sauti Zhara ta yi ta na faɗin “Allah ya shirye ki Kandala, mu na tare babu mai rabamu.”

Ta na zaune ɗaki wanda ya zame mata komai in har ba aiki ta ke ba to ta na ɗaki ita kaɗai kamar manya. Kamar koyaushe ta na zaune ta idar da sallah la’asar ta na karatun Alƙur’ani wayarta ta yi ringing sai da ta kai a ya sannan ta ɗauki waya wacce har kiran ya tsinki kiran ya sake shigowa ta ɗaga “Assalamu alaikum”

“Amin alaika salam, barka da yammaci gimbiya”

“Barka da juna Yaya Mahamod, ya gida?”

“Lafiya lau, ki fito na zo ina ƙofar gida” fito da idanu ta yi a ɗan tsoraci ta ce. “Wani ƙofar gidan?”

“Wani gidan ki ke a yanzu? Kin ga da zan dawo ne na biya ta wajan Mama ta ba ni adris ɗin tunda ke kin ƙi ki ba ni” shiru ta yi har ma ta rasa me za ta ce “kin yi shiru”

“Ga ni nan fitowa” ta faɗa jiki a sanyaye. Bayan ta a jiye wayar ta yi shiru ta na tunanin yadda za ta yi ita sam ba ta so zuwan sa ba har ga Allah, ba ta son damuwa gida ba na su ba ta zo ta kawo shi wata matsalar ta biyu bayan zuwan na shi. Tashi ta yi jiki a sanyaye ta fito ɗakin Momy ta shiga ba kowa hakan yasa ta sauko ƙasa ta samu ta na falon.

“Sannu da hutawa” banza ta mata ajiyar zuciya Zhara ta yi kafin daga bisani ta ce. “Dama Yayan Haliman Yaya Hafiz ne ya zo mu gaisa”

“Ko babanta ne shi meye ruwana, kin ga don Allah kama gaban ki ni sha’ani in dai na ki ne babu ruwana da shi. Idan ma maza za ki din ga kawowa su na kwana a ɗakin ki ko a jikina ai ‘yar so ce ke wacce tafi ‘yar masu gida” dafa kan kujera ta yi ta na kallon ƙasa “ba za ki ɓace mini da ga ni ba!” Barin wajan ta yi da sanyin jiki ta fita. A tsaye ta same shi sanye cikin farin yadi ya sha kyau dama can ya fi Halima kyau nisa ba kusa ba. Sakin fuskarta ta yi kamar ba komai “sannu da zuwa Yaya” kafeta ya yi da idanu ji ya ke kamar ya janyo ta ya haɗiye dan so “yawwa sannu ƙi baƙi”

“Kai yanzu sunan da za ka raɗa mini ma kenan” ta yi maganar ta na dariya marar sauti. “Eh mana koyaushe na ce zan zo sai ki na dojewa zuwan nawa”

“Ka yi haƙuri yanzu ba ga shi ka zo ba”

“Da Mama ta taimaka ta faɗa mini wajan ba”

“Ai dai na ba da haƙuri. Bisimillah mu shiga da ga ciki” motar Hafiz ta kunno kai ya na hon hakan yasa su ka tsaya da ga gefe maigadi ya buɗe masa bayan ya shiga su ka shiga. “Ka kuwa je wajan Halima?”

“A’a ban ma san hanyar da a ke bi a je gidan na ta ba ai ballatana har na je”

“Ai kuwa ya kamata a ce ka je”

“Manta da zancen zuwa wajan ta ke ba ga shi na zo wajan ki ba shi ne abu mafi muhimmanci a wajena” murmushi ta yi kafin da ga bisani ta ce. “mu je ku gaisa da Yaya Hafiz shi ma jiya ya dawo da ga tafiya” kallonta ya yi kawai ya kawar da kansa ba tare da ya ce da ita komai ba, “ka ji?”

“Shi ne ya kamata ai ya zo mu gaisa matsayin na na yayan matarsa ko? Idan kuma kin ce na je a matsayin Yayan matata shi kenan sai mu je” ƙasa ta yi da kanta ta na murmushi. Hafiz ya na fitowa mota ko kallon su bai yi ba ya shige ciki. “Uhm! Mu je ya riga ya shiga cikin gidan.” Falon baƙi ta kai shi bayan ya zauna za ta fita ya ce. “Ina kuma za ki tafi?”

“Zan kawo ma ka ruwa ne”

“Dawo ki zauna na gode”

“Haba dai ai ba zaiyu ba”

“Da gaske na ke na gode” zama ta yi a ranta ta na gode wa Allah dan ta na tsoron zuwa ɗauko ruwan ya janyo a faɗa mata baƙar magana.

Ransa ɓace ya shiga falon zama ya yi a kan kujera ya na huci, Momy ta kalle shi ta na faɗin “lafiya na gan ka cikin damuwa?”

“Waye na ga Zhara ta na magana da shi a waje?”

“Ta ce Yayan matar ka ne shi. Wai ma tsaya mene ne matsalar ka dan ta na magana da wani?” Ta masa tambayar da mamaki a fuskarta. “Ba komai” ya bata amsar ya na ƙoƙarin ɓoye damuwar da ta ke zuciyar shi. “Ina wuni?”

“Lafiya lau, ya gajiyar tafiya?”

“AlhamdulilLah”

“Kai da ka tafi da niyar sati uku sai ga shi kwana goma ka dawo” ajiyar zuciya ya yi kafin daga bisani ya ce. “Na gama abin da na je yi ne da wuri shi yasa na dawo”

“Humm kai dai tun da ka bar matar ka ai ba za ka iya daɗe wa ba” murmushi kawai ya yi azahirin gaskiya ba hakan ba ne, sai dai idan zai shekara faɗa ma ta ba wai yarda za ta yi da shi ba. “Na ga Anwar ma ai koyaushe su na tare da Zhara na ce ko ‘yar gida za a yi ne?” Zuciyarsa ta yi wani irin bugawa kamar za ta faso ƙirjinsa ta fito. “Momy Anwar da Zhara ne su ke tare?” Ya yi tambayar muryarsa a sarƙi, “eh, ai na ɗauka ka sa ni” tashi ya yi tsaye ya na faɗin “zan tafi asibiti akwai abokina da ya kirani ina hanya ya ke faɗa mini ya zo asibiti ya kawo kakarsa”

“To Allah ya ba ta lafiya”

“Amin” ya fice ya bar Momy da mamakin dalilin damuwar sa da Zhara dan ya ganta da wani.

<< Kuskuren Waye? 16Kuskuren Waye? 18 >>

2 thoughts on “Kuskuren Waye? 17”

    1. You should go to the main menu located on the top left corner of your app, click and scroll down to the item ‘Subscribe,’ also click it and follow the remaining instructions. It’s straightforward.

      Thank you

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×