Skip to content
Part 18 of 43 in the Series Kuskuren Waye? by Aisha Abdullahi Yabo

Kanta a ƙasa duk jin ta ta ke a takure musamman kallon da ya ke mata, “kin yi shiru.”

“A’a ba shiru na yi ba.”

“To me ki ka yi?” Ya yi tambayar ya na mai kafe ta da idanu, murmushi kawai ta yi. Gyara zaman sa ya yi kafin da ga bisani ya ce. “Zhara ke ƙanwata ce babu ɓoye-ɓoye a tsakanin mu idan har kin ji a ranki ban ma ki ba a matsayin wanda za ki zaɓa abokin rayuwar ki ki fito ki faɗa mini gaskiya, duk da ba zan so na ji hakan ba sai dai kuma son da na ke ma ki so ne na gaskiya ba wai so na son kai ba” shiru ta yi har ma ta rasa me za ta faɗa masa magana ta gaskiya ba ta taɓa jin son shi a ranta ba kawai ta na yi masa kallon Yaya ne, amma ta ya za ta fito ta faɗa masa hakan gaskiya da nauyi.

“Ke na ke saurare ki faɗa mini abin da ya ke ranki kar ki ji nauyi hakan kin ji ko?”

“Yaya Mahamod kamar yadda na faɗa ma ka a baya ni karatu na ke a yanzu, ba zan iya haɗa soyayya da karatu ba” ajiyar zuciya ya yi kafin da ga bisani ya ce. “Ni kaina ba zan so na shiga cikin karatun ki ba, abu ɗaya na ke so na sa ni shi ne tabbacin soyayya ta. Yanzu ni kaina fafatukar neman aiki na ke bayan nan a kwai abubuwa da yawa a gabana, kafin ki gama karatu na sha kansu ko.”

Maigadi ya buɗe masa ƙofa dab da zai fita ya tsaya tare da saukar da gilas ɗin mota ya yafito mai gadi da hannu da sauri ya zo ya na faɗin “ranka ya daɗi barka da fitowa”

“Yawwa Malam Bello. Am na ce baƙon da Zhara ta shigo da shi ya tafi kuwa.”

“A’a su na falon baƙi gaskiya” ya bashi amsa ya na gyaɗa kan shi, “Okay na gode” ya ciro kuɗi ya ba shi karɓa ya yi fuskarsa ciki da farin ciki “na gode sosai Allah ya ƙara lafiya da arziƙi”
“Amin” ya amsa tare da ficewa gidan zuciyarsa na yi masa wani irin nauyi shi kan shi ba zai iya cewa ga dalili ba.

Zuba ma ta idanu ya yi ya na faɗin “ke na ke saurare.”

“Humm to Allah ya zaɓa mana mafi alkhairi.”

“Kin amince kenan?” Murmushi ta yi kafin ta ce. “duk abin da Allah ya yi shi ne daidai, mu dai barwa Allah zaɓi.”

“Halayyar ki ya na ɗai da ga cikin abin da ya sa ki ke ƙara shiga raina Zhara ki na da tawali’u. Ina addu’a Allah ya sa ki kasance rabona da na kasance namiji mai matuƙar sa’a a rayuwata.”

“Na gode Yaya Mahamod.”

“Riƙi godiyar ba na so” duba agogon da ya ke manni a hannun shi ya yi ya na faɗin “ya kamata na zo na tafi tun kan ki ce na dame ki da surutu.”

“Haba dai a’a” tashi ya yi tsaye ya ciro kuɗi cikin aljihu ya ba ta ya na faɗin “ga shi ko sweet ki saya ban samu na saya ma ki komai ba” saurin yin baya ta yi ta na gyaɗa kanta “a’a ka bar shi na gode wallahi.”

“Kin san Allah sai kin karɓa idan kuma so ki ke raina ya ɓaci to shi kenan” ganin ya ɓata rai ya sa tasa hannu biyu ta karɓa.” Na gode sosai Allah ya ƙara buɗi.”

“Amin” ya amsa da murmushi a fuskar shi. Ta raka shi bakin gyet.

Kakan abokin shi kaɗai ya iya duba wa ya bar asibitin. Ta na kichen ta jiyo dawowar shi, fitowa ta yi ta samu har ya shige ɗakin shi. A kwance ta same shi ya yi rub da ciki zama ta yi gefen shi ta na shafa sumar kansa ta ce. “Lafiya ka dawo yanzu ka ce da ni sai dare za ka dawo” rufi idanun shi ya yi kamar mai jin bacci ya na faɗin “lafiya lau. Za ki iya tafiya ina son kaɗaituwa don Allah” fito da idanu ta yi “ikon Allah da ga tambaya sai kora, to asha zama lafiya” tabar ɗakin a zuciye. Juye ya yi ya gyara kwanciyar shi sam ya rasa me ya ke yi masa daɗi. Ɗaukar wayar shi ya yi dan kiran Anwar ya kuma fasa “to me ma zan ce masa? Mtsw! Ya rasa yarinyar da zai so sai Zhara to akan me, ai wannan ni ya ke so ya tozarta!” Saukowa ya yi da ga kan gadon ya din ga safa da marwa a cikin ɗakin na shi, ya dawo ya zauna gefen gado ya riƙi kan shi da ya ke matuƙar sara ma sa. A daren ranar bai iya yin baccin kirki ba.

Washegari ƙarfe bakwai ya fito ya samu Halima ta na bacci tashin ta ya yi ta buɗe idanunta ta na miƙa “mene ne?”

“Kin yi sallah”

“Eh tun asuba”

“Ok. Zan samu ko ruwan shaye ne fita na ke so na yi” tashi ta yi ta zauna ta na sauko da ƙafafunta ta ce. “Na ɗauka bayan rashin buƙatar kasancewa a kusa da kai har abincin nawa ba ka buƙata ai shi yasa na yi kwanciyata” zama ya yi gefen ta ya riƙo hannunta ya na faɗin “ki yi haƙuri ki kuma yi mini uzuri jiyan nan akwai abin da ya ke damuna shi yasa ki ka ganni wani iri.”

“Humm kuma shi ne zai shafe ni, ai na ɗauka ko me zai ɓata ma ka rai a waje ba zai taɓa shafa ta ba am… “Ki yi haƙuri Baby kin ji ko”?”

“Shi kenan ya wuce, bari na ɗora ma abin kari” duba agogon da ke manni a hannun shi ya yi “uhm lokaci ya tafi zan sha dai ko shaye ne na fita”
“To bari na ɗora ruwan” su ka fita ɗakin a tare.

Zhara ta na zaune a falo ta na duba karatu “Assalamu alaikum”

“Amin alaika salam Malam Abba shigo” ta yi maganar ta na kallon ƙ kofa, durƙusa wa ya yi da ga gefen kujerar da ta ke a bakin ƙofa “barka da hutawa”

“Yawwa barka, ya aiki?”

“AlhamdulilLah. Dama wajan Khadija na zo” miƙewa ta yi tsaye ta na faɗin “ta na ɗaki bari na kira ma ita” ko rufe baki ba ta ƙarasa yi ba Khadija ta sauko ta na harararsa ta zauna a kan kujera ranta a ɓace ta ce. “Uwar me kuma ka zo ka yi mini?”

“Ki yi haƙuri wall… “Dalla can ba na son jin komai me za ka faɗa mini, tsabar iskanci da neman tozarta ni ya sa ka barni a makaranta ina jiran ka, na kira wayar ka ka ƙi ɗagawa sai adaidaita na shigo”
“Ki yi haƙuri ranki ya daɗi wallahi motar ce ta tsaya mini ahanya sai da na kira bakaniki, waya ta kuma na gida na barta ta yi caji. Bayan an gyara na je makaranta na tarar kin dawo”

“Dalla can ɓaci mini da ga ni! Kuma wallahi ka kuskura ka sake yi mini irin hakan ranka sai ya fi nawa ɓaci” tashi ya yi jiki a sanyaye ya fice, Zhara da kanta ya ke a kan littafi sai dai hankalin ta duk ya na kan Khadija duk sai ta ji ba daɗi wulaƙanta ɗan’adam ba ya da amfani, kamar ta yi ma ta magana sai kuma ta ja baki ta yi shiru gudun kar faɗan ya dawo kanta. Tashi Khadija ta yi a zuciye ta haura sama ɗakin Momy ta shi ga ta na faɗin “gaskiya Momy ki yi wa Yaya magana ya barni na din ga jan mota ta kawai dan sau ɗaya na bugi wani kuma bisa kuskure sai ya hanani tuƙi”

Momy ta ajiye wayar hannunta ta na faɗin “me kuma ya faru”

“Ɗazun fa na faɗa ma ki wulaƙancin da dreba ya yi mini, shikenan hakan zan zauna ya na yi mini yadda ya ga dama” janyota ta yi ta zaunar da ita kusa da ita cikin lalllashi ta ce. “In dai wannan ne an wuce matsalar da ga yanzu na janye dokar zan masa magana. Amma ke ma kuma ki din ga kula wajan tuƙi dan idan ki ka ƙara ba Hafiz ba har wajan Alhaji ba za a kwashe da daɗi ba” rungome Momy ta yi ta na faɗin “yawwa My Momy na ji daɗi sosai.”

Anwar na rufe ƙofar ɗakin shi Hafiz ya shigo “ah mutumina da ga ina haka?”

“Asibiti na fito. Ina ta kiran wayar ka ba ka ɗaga ba, na biya ta office ɗin ka ba ka nan.”

“Na manta wayar ne a gida shi ne dalilin ma da ya sa a na yin Azahar na dawo gida ɗauka. Fitar nan ma da ka ga zan yi zan biya ta wajan ka ne sannan na koma office” ya yi maganar ya na buɗe ƙofar. Bayan sun zauna ya zuba ma shi idanu cikin nazari “me ya faru Hafiz na ga kamar ka na cikin damuwa.”

“Uhm! Ba komai yanayi ne kawai. Yawwa wai wace ce yarinyar da ranar ka ke faɗa mini ka tsayar?” Murmushi Anwar ya yi kafin da ga bisani ya ce. “Ba ka ce ba ka so ka sa ni ba har fushin ya ƙare kenan.”

“Mtsw! Kai fa Anwar wani lokacin ɗan rainin wayo ne to na ji faɗa mini wace ce don Allah”
“Au dama tambayar da ta sa ka ke nema na kenan ruwa a jallo?” Lumshi idanunsa Hafiz ya yi ransa ya suma ɓaci sam ba ya son wannan jan ran da Anwar ya ke yi masa, amsa ya ke so dan tabbatar da zargin shi gaskiya ne ko akasin hakan.

Dafa kafaɗar shi Anwar ya yi ya na faɗin “ka kwantar da hankalin ka ai kasan dole zan faɗa ma ka bare kuma kai ne ja gaba a tafiyar” zuciyar sa ce ta ba da dum!! “Ni ne ja gaba a tafiyar kamar ya? Fahimtar da ni don Allah. Sannan da gaske ne koyaushe ku na tare da Zhara?” Shiru Anwar ya yi ya na mai zuba ma shi idanu “Malam ba kallona na ce ka yi ba amsar tambaya ta na ke buƙata” cikin gyaɗa kai Anwar ya ce.

“Hakan ne gaskiyar zance ban yi niyar faɗa ma ka komai ba a ɗan wannan lokacin, amma tun da har an fara kawo ma ka zancen gara ka ji komai a bakina” shiru ya yi Hafiz ji ya ke kamar zuciyar shi za ta fashe saboda baƙin ciki da takaici yanayin fuskar sa ya sauya sosai fuskar shi ta ke bayyana abin da ya ke zuciyar shi. “Am ni da Zhara mu na son juna, na san za ka yi farin ciki ko ba komai na san za ka fi kowa farin ciki da son wannan haɗin.”

Miƙewa tsaye Hafiz ya yi ba tare da ya iya cewa komai ba ya kama hanyar fita, Anwar ya biyu bayan shi da mamaki a fuskar shi ya ce. “Ina kuma za ka tafi mu na magana?”

“Me ka ke so na faɗa ma ka? Da ka na so na ce wani abun da tun kan ka yi magana da ita ka fara yi da ni” murmushi Anwar ya yi ya na faɗin “shi kenan na yi kuskure babban Yaya a yi haƙuri ba zan sake ba”

“Anwar shin ka manta wace ce Zhara a wajena ne da har ka bari zuciyar ka ta faɗa soyayyar ta”

“Zhara ƙanwar ka ce wannan ne ya ba ni ƙwarin gwauwar karfafa soyayyar ta a zuciyata. Ko ba komai na san zumuncin mu ai zai ƙara ƙarfi” wani irin huci Hafiz ya yi tare da furzarwa da ƙarfi. “Ƙwarai da gaske ƙanwata ce bayan wannan kuma ita wancan alaƙar ka manta da ita ne?”

“Alaƙa kuma wace alaƙar? A sani na dai babu wata alaƙa bayan ta zumunci a tsakanin ku da ita”

“Ka dai sake tuna wa”
“Me zan tuna kuwa ai ban manta komai ba, an ba ka Zhara ka ce ba ka son ta ka aure zaɓin ranka. Sannan a sanda na ke ba ka shawarar da ka aure ta me ka ce da ni? Cewa ka yi ka bar mini na je na aure ta. Wannan ne ya ƙara ƙarfafa mini gwuawa har mu ka fara soyayya da ita” ficewa ya yi a zuciye ba tare da ya iya cewa da shi komai ba, Anwar ya koma ya zauna ya na mamakin dalilin fushin Hafiz “kai da ka ce ba ka so to mene abin damuwa dan wani ya so ta.”

Kwana biyu duk ya rasa me ya ke yi masa daɗi a rayuwar nan, baccin kirki wannan ya gagare shi, idan ma office ya je aikin neman gagarar sa ya ke. Ciwon kai mai tsanani ya sa shi gaba hakan yasa ya bar office ɗin tuƙi ya ke amma hankalin shi sam baya a jikin shi kiris ya rage ya kaɗe wani Allah ya taimake shi ya riƙi kan motar ya yi gefe, sai zagin shi a ke hakuri kawai ya ba jama’a ya wuce zuciyar shi a ƙuntace.

Ta na zaune a harabar makaranta gefen da babu mutane sosai ta zauna ita kaɗai ta na chat a wayarta Husna ta zo ta zauna a kusa da ita, “Zhara sai ki zo ki zauna ke kaɗai” murmushi kawai ta yi. “Ina jiran mijina ne ya zo ɗaukata na gan ki ke kaɗai na ce bari dai yau na zo mu yi fira duk da na fahimci kamar ba kya son hakan kin fi son kaɗaituwa”

“A’a ba hakan ba ne”

“To ya ne?”

“Kawai na fi son zama ni kaɗai ko a gida” gyaɗa kanta ta yi “kin huta ai da gutsuri tsuma ni ma kusan hakan na ke shi yasa ma na ji ta wa da ta ki ta zo ɗaya”

“Na gode Aunty Husna” Khadija ta zo ta tsaya a kanta “ke kuku tashi mu tafi. Kawai Yaya da son shiga hakkin ɗan’adam ya ce dole sai na din ga ɗaukar ki ya bar ki ki na shiga daidaita ma na tun da da ita a ka saba a gidan tsohu” ta ƙarasa maganar da yin tsaki ta yi gaban abinta, jiki a sanyaye Zhara ta mike ta na tattara littafan ta da jakarta “sai anjima Aunty Husna”

“Wace ce wannan Zhara?”

“Ita ɗin ‘yar’uwata ce”

“Allah sarki hala ma a gidan su ki ke zama ko?” Kan ta kawai ta iya gyaɗa ma ta. Hun Khadija ta dannu ma ta hakan yasa Zhara ta juya da sauri ta na tafiya. “Allah ya tsare Zhara, don Allah gobe idan ki ka shigo ina so mu yi magana kin ji ko?” Husna ta yi maganar fuskarta na nuna yanayin damuwa a kan fuskarta.

“Allah ya kaimu” Zhara ta amsa ma ta ta na mai ƙara yin sauri.

Ta buɗe mota za ta shiga wanda tu ni Khadija ta yi wa motar key Zhara ta ji an finciko ta da ƙarfe har sai da ƙassan jikinta ya amsa so ta ke ta ga wannan waye mai ƙarfin halin sai dai ya ƙi bata dama sai bayan shi ta ke iya gani jan ta ya ke da ƙarfi “kai meye haka waye kai lafiya?!!” Khadija ta fito motar a tsorace ta na faɗin “lafiya waye ne?!” Ta na tambayar tare da bin bayan su. Juyowa ya yi ya na faɗin “za ku rufe mini ba ki ko sai kun ga jini a jikin ku!!” Sanƙame wa Khadija ta yi a wajan ta na masa kallon tsoro, ya yin da numfashin Zhara ya ke neman fin ƙarfin ta, sai ƙoƙarin fizgo numfashin ta ta ke ta ƙarfi turata ya yi cikin motar ya rufe tare da juya wa mazaunin dreba ya yi wa motar key mutane su ka yo kansu tuni ya bar makarantar a guje tamkar zai tashi sama.

<< Kuskuren Waye? 17Kuskuren Waye? 19 >>

5 thoughts on “Kuskuren Waye? 18”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×