Skip to content
Part 19 of 43 in the Series Kuskuren Waye? by Aisha Abdullahi Yabo

Jama’a a ka yi ca kowa da abin da ya ke faɗa Husna ta zo a tsorace ta na faɗin “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Kar dai sace Zhara a ka yi?” Shiru Khadija ta yi ta na bin hanyar da motar tabi da idanu tamkar amsar tambayoyin da su ka cika ƙwaƙwalwarta ne za ta samu a wajan.

“Wannan ai laifin masu gadi ne taya mutum zai zo da mota har ya ɗauki yarinya su barshi ya fita saboda sakaci. Kai ƙasar nan a na tsiya wallahi!” Cewar ɗai da ga cikin ɗaliban. “Allah sarki Zhara Ubangiji Allah ya kuɓutar da ke da ga sharrin mutanen nan baiwar Allah ba ruwan ta ba ta shiga sabgar kowa. Khadija ya kamata a yi wani abun ba fa” lumshi idanunta ta yi ta na fitar da huci mai zafi.

A tsorace take kallon shi sai dai ta kasa cewa uffan ya yin da zuciyarta take dukan uku-uku sai da ya yi tafiya mai nisa ya samu waje wanda babu kowa filin Allah ya yi parking tare da kifi kan shi jikin sitarin motar. “Meye haka me ya sa za ka ɗauko ni ka kawo ni nan?” Banza ya yi mata hakan ya tilasta ta yin shiru tare da mayar da dubanta ga ƙofa ta na kallon waje muryar shi ta tsinkayo ciki da karkashi “me ye tsakanin ki da Anwar?” Da mamaki ta juyo ta na kallon shi ba tare da ta ce da shi komai ba “tambayar ki nake me ye tsakanin ki da Anwar?”

“Ni ai na rasa gane wannan tambayar ta ka ne” wata irin harara ya dalla mata ya na faɗin “kar ki mayar da ni shashasha wanda bai san me ya ke ba. Soyayya ku ke da Anwar da gaske hakan ne?” Shiru ta yi “ki faɗa na ce da gaske soyayya ku ke?”

“Eh soyayya muke yi wani abun ne?” Ta ba shi amsa cikin dakiya dan har ga Allah ta tsorata da yanayin sa. “Uhmmmm!!!!” Ajiyar zuciya ta ji ya yi mai ƙarfi bai sake cewa uffan ba idanun sa na kallon gefen ƙafa wani irin abu mai nauyi ya ke ji a kan zuciyar shi. Ganin shirun ya yi yawa ya sa ta ce.

“Ni ka mayar da ni gida ko ka ajiye ni in da zan samu abin h…” Kallon da ya yi mata da idanunsa da su ka rikiɗe da ga fari zuwa ja ya tilasta ta yin shiru zuciyarta na halbawa fat! Fat!! Fat!!!

“Ki na jin abin da ki ka yi daidai ne? Kar ki manta Anwar abokina ne shi ta ya za ki rasa wanda za ki so sai amini na?” Ya yi maganar cikin sanyin murya mai ɗauki da damuwa. Murmushi ta yi mai ƙara wa mutum haushi “na ga ai ba haramci yin haka ko da wanda kuka fito ciki ɗaya ne bare kuma aboki ko?”
“Au amsar ma da za ki ba ni kenan?”

“Hakan amsar ta ke ai shi yasa na ba ka ita a yadda ta ke. Bari na ƙara maka da ƙaramin misali ma wace ka ke aure a yanzu. Ƙawata kuma aminiyata ita ce ta ke zaune a gidan ka a matsayin matar aure ashe ka ga kenan babu haramci, da akwai na tabbatar ai ba za ka yi ba.” key ya yi wa motar ba tare da ya ce da ita komai ba har su ka ɗau hanya.

“Idan na fahimta kenan ramuwa ce ki ke so ki yi ko?” Dariya ta yi kafin da ga bisani ta taƙaita dariyar ta na faɗin, “Ramuwa kuma? A’a sam-sam kar ka ma yi wannan tunanin wallahi to me ma a ka yi mini ne da har zai sa na riƙi a raina na ce zan rama. Ka ma daina wannan tunanin a ranka.”

Banza ya mata har suka je gida a bakin gyet ya a jiye ta, ta na fita ya ja mota a fusace ya tafi.”Yau ni na ga ikon Allah to ina ruwan sa ma da duk wanda zan aure?” Kaɗa kai kawai ta yi ta shiga gida.

Khadija ta samu tare da Momy a falo Momy sai faɗa ta ke, “Wato na ga alamar Hafiz idan ba na tasar ma shi tsaye ba sai ya cusa mini baƙin ciki a rai.” sallama ta yi ko amsa mata ba su yi ba “gidan uban wa ku ka tafi?” Dafa kan kujera ta yi kanta a ƙasa ta ce. “Ba in da muka je.”

“Ƙarya ta ke yi idan babu in da ku ka je me ya sa zai zo ya ɗauki ke. Momy kin ga wai yadda ya zo ya wani riƙo hannunta ya sa ta a mota? Humm ‘yan makaranta kowa ya yi ca! Sai da na masu bayanin ko waye na samu na kawar masu da tunanin ko sace ta a kayi” harara Momy ta dalla mata ta na faɗin “idan ma wani abun ku ka ƙulla ke da uwar ki to tun wuri ku je ku warware shi, Hafiz dai ya ma ki nisa har abada ba zai taɓa auren ki ba” murmushi ta yi tare da ƙoƙarin mayar da hawayen da su ke ƙoƙarin fitowa ta ce.,

“Ki yi haƙuri kamar yadda ba kya son aure na da Yaya Hafiz haka Mama ba ta so hasalima ta yarda da maganar auren ne kawai dan Abba ya ci ƙarfin ta. Kuma ni wallahi tun da a ka fasa auren ban sake kallon sa a wannan bigirin ba bayan na Yaya a gare ni.” Ta kalle Khadija ta na faɗin “idan har za ki faɗi gaskiya kin sa ni ba ni na kira shi ba shi ne ya zo kuma a gaban ki a kayi komai.”

“A’a a’a kar ki wani tuge ai ba tare mu ke ba na sa ni ko kiran shi ki ka yi a waya. Momy wannan yarinyar fa ba za ta taɓa barin Yaya Hafiz ba tun da har yanzu ba ta da mashinshini dole ta nemo duk hanyar da za ta bi dan ganin ta samo zuciyar shi ta aure shi.”

“Ai kuwa za ki mutu ba ki da aure in dai Hafiz ne. Sannan da ki ke cewa Maman ki ba ta so ƙarya ne ba abin da ban sa ni ba burin ta a yi auren dan dukiyar Alhaji da ta shi ta zama ta ku musamman idan ki ka haifi ɗa Namiji… Barin wajan ta yi da sauri ba tare da ta bari Momy ta diri maganar ta ba ta ga lamarin ya wuce tunanin ta ƙarya ƙiri-ƙiri. “Iyee lallai kan ɗan mage ya waye, magana ki ke ta na tafiya wato ki yi da iska.”

“Barni da ita wallahi ko uwarta mun buga da ita ta barni bare ita karan kaɗa miya. Shi kuma zai zo ne ya same ne.”

Ta na zuwa ɗaki ta kwanta a kan gado idanunta a rufe ‘AlhamdulilLah Allah da kasa ka mini juriya duk da har yau ina jin son Yaya Hafiz amma hakan bai sa na ji dole da shi zan rayu ba bare har baƙin ciki ya kashe ni. Momy da yardar Allah ko shi ne autan maza ba zan taɓa auren shi ba!’ kiran waya ne ya dawo da ita da ga zancen zucin da ta ke. Ta kai hannu ta janyo jakarta da ta jefar gefen hello ta ɗauki wayar Yaya Anwar ne, ɗaga kiran ta yi bayan sun gaisa ta ji kamar ta faɗa masa abin da ya faru ta kuma fasa. Har su ka gama wayar babu wanda ya yi wa wani zancen Hafiz.

Halima ta na zaune falo ta na chat ya shigo yanayin da ta ga ya shigo ya sa ko uffan ba ta ce da shi ba har ya shiga ɗakin shi. Taɓi baki ta yi ta na faɗin “yau kuma ko wa ya taɓo shi ne Oho. Ko gani na ma ba za ka yi ba bare har ka sauki haushin a kaina” barin falon ta yi ta shige ɗakinta.

Gaba ɗaya ya rasa me ya ke yi masa daɗi zama ya yi gefen gado ya na tsaki a ranshi ya na faɗin, ‘Wai ni me ye ma ruwana ne da soyayyar su su je can su ƙarata ko waye ma ta je ta aura sai me?’ Ya miƙe ya na rage kayan jikin shi ya shiga banɗaki ya sakarwa kan shi ruwa so ya ke ya manta komai so ya ke tunanin ya bar zuciyar shi zafin da ya ke ji a zuciyar shi ya cire sai dai ina sam ya kasa daina ko ɗaya. Hakan ya fito wanka ya shirya ko Halima bai nema ba ya bar gidan.

Sai dare ya dawo ya duba ba ta ajiye masa abinci ba, bai neme ta ba ya shiga kichen ya dafa wa kan shi ruwan zafi ya sha shaye. Bacci ya ƙaurace wa idanun shi ya janyo wayar shi ya lalubo numberta har zai kira kuma ya fasa “to na ce ma ta me? Me ye ma zai sa wai na kirata? Mtsw! Ya yi tsaki tare da gyara kwanciyar shi. Ya jima kafin ya samu bacci ya yi awon gaba da shi.

“Me ya sa Momy duk abin da yarinyar nan ta zo ta faɗa ma ki sai ki yarda?”
“Dan me ba zan yarda ba, ba ka je makaranta ka ɗauko ta ba ne?” Ajiyar zuciya ya yi kafin da ga bisani ya ce. “eh na ɗauko ta amma ai hakan ba ya na nufin wani abu ba ko kuma abin da ki ke tunani” hararar shi ta yi ta na gyara zama ta ce. “ai sai ka mayar da ni ƙaramar yarinya wacce ba ta san me ta ke ba tun da haifa ta ka yi.”

“Uhm! Ki yi haƙuri am… “Ba na son jin komai abin da kawai nake so kasa a ranka auren ka da Zhara haramtacce ne kamar yadda Khadija ta haramta da kai. Ka kuma je gidan ƙawata Hajiya Na’ima ka duba ‘yarta” fuska babu annuri ya ce. “Ba ta da lafiya ne?”

“Na san duk ka san me nake nufi amma tun da ka fi so na ma gwari-gwari ina nufin ka je ku gaisa da ita dan mun yi magana da uwar za a haɗa ku aure.”

“Aure kuma Momy? Haba don Allah ki bar wannan zancen duka yaushe na yi aure da har zan fara yi mini zancen ƙarin wani auren haba don Allah” miƙewa ta yi ta fara tafiya ta na faɗin “babu sauyi a maganata aure ne babu fashi, auren ‘yar matsiyata har aure ne a wajan ɗa kamar ka wanda bai nemi komai ya rasa ba. Ka bi umurni na sai a zauna lafiya” ta haura sama ta barshi zaune kamar bunkin da a ka sassaƙa baƙin ciki kamar ya haɗi zuciya ya huta dan takaici.

Zhara ta sauko ƙasa ta na riƙi da mataji da man kitso kanta babu kallabi “yawwa Kandala ga ni na fito zo ki mini ko ba yawa ne” ta yi maganar idanunta a kan Kande da ta ke fitowa kichen. Hafiz suman zaune ya yi karon farko kenan da ya ganta babu Hijab sanye ta ke cikin riga da wando na kanti gashin kanta ya zubo har kafaɗa idanu ya kafeta da su ba ko ƙyabtawa, “mu je ɗakin ki ki mini ban san wa zai faɗo ba, zafi kuma nake ji” ta faɗa ta na kama hanyar ɗakin “ai kam dai kin makaro” Kande ta yi maganar ƙasa-kasa.

Ta ɗan sunkuya ta na gaishe shi “Barka da zuwa Alhaji ƙarami.” sam bai ji ta ba domin ya yi nisa wajan kallon Zhara. Sai a lokacin ta fahimci da a kwai wani a falon ta juyo da sauri su ka haɗa idanu ta bar falon da sassarfa Kande ta bi bayanta ta na dariya. Ajiyar zuciya ya saukar cikin wani irin yanayi ya bar gidan tuƙi ya ke amma sam hankalin shi ba a nan ya ke ba Allah kaɗai ne ya kai shi office lafiya. Aiki ya ke amma idanun shi da zuciyar shi su na hasko ma shi kyakyawar surarta.

Tsayawa ta yi tsakiyar ɗakin Kande ta na mayar da numfashi “kai Maman masu gida wannan gudu haka sai ka ce kin ga dodo” Kande ta yi maganar ta na dariya “haba don Allah ba sai ki faɗa mini da mutum ba sam ban ji daɗi ba wallahi ban san ya na nan ba da ba zan fito ba” zama ta yi ta na yin tsaki ciki da takaici har cikin ranta ba ta ji daɗin ganinta da ya yi hakan ba. “Gyara zaman ki a yi kitson tun kan lokacin ɗora girki ya yi kin san Hajiya ba ɗaga ƙafa.”

“Wallahi dai ban ji daɗin hakan ba sam!”

“Wai meta na me mai afkuwa dai ta riga da ta afku sai dai fatan kiyaye gaba. Ki hutar da zuciyar ki da zancen.” Shiru ta yi ba ta sake cewa uffan ba.

Wajajan ƙarfe goma ya dawo gida ya na tsaka da ciri kayan jikin shi ta shigo ɗakin ta tsaya da ga bayan shi ta na faɗin, “Wai me ka ke nufi da ni ne?” Shiru ya mata har ya cire kayan jikin shi ya na ɗaura tawol ta ce “ka na fa ji na.”

“Ban fahimci tambayar ta ki ba ne bare na san amsar da zan ba ki.”

“Tun jiya ka yi banza da ni kamar ba na cikin gidan nan, haka yau ka shuri ƙafa ka tafi yanzun ma da ka dawo ko ka neme ni. Girki na ma yadda na yi shi jiya da rana haka ka bar ni da shi yau ma hakan me wanna ya ke nufi?”

“Kawai ba na cikin yanayi ne, ke kuma ko a jikin ki ba ki neme ni ba ba ki tambayi lafiya na ke ko akasin hakan ba shi ne yanzu za ki sa ni gaba da mita.”

“Eh ban zo ba ne saboda na ga ranka a ɓaci gudun kar ka sauke a kaina.”

“Ya yi kyau tun da hakan karatun ki ya nuna ma ki” ya ƙara sa maganar ya na shige wa banɗaki ya barta tsaye riƙi ƙugu ta yi “lallai ma wato laifi na ma ka gani, shi ne har da wani shigewa ka barni. To wallahi ka yi da gwana in dai Halima ce sai ka neme ni” ta fita ɗakin a fusace. Tun ranar da ya ganta babu Hijab ba ta sake yarda sun haɗu ba. Hakan ya sa shi damuwa sosai ya rasa me ya ke damun zuciyar shi kwana biyun nan tunaninta ya hana shi sukuni. Zaune ya ke a office ya kifi kan shi jikin tebur Anwar ya shigo da sallama a bakin shi shiru babu amsa, ƙwanƙwasa tebur ɗin ya yi ahankali ya ɗago kan shi ganin Anwar ne ya sa shi gyara zaman shi.

Anwar ya ja kujera ya zauna ya na faɗin “bacci a office kamar wanda bai yi bacci a daren jiya ba, ko dai… Ya yi maganar ya na dariya tsaki Hafiz ya yi kafin ya ce. “Ni na faɗa ma bacci nake?”
“Idan ba ka faɗa ba ai ga shi na gani a zahiri. Wai kwana biyu lafiya idan na kira wayar ka ba ka ɗauka na turo ma saƙo ta wtspp ba ka duba ba, ga shi na yi tafiya sai jiya na dawo cikin dare bare na zo na duba ko lafiya.”

“Lafiya lau kawai aiki ne ya yi yawa ban da lokaci sosai. Ina ka je ne?”

“Bauchi muka je tare da Mama ƙanen banbanta ne ya rasu.”

“Allah ya jiƙan shi da rahama. Shi ne ba ka faɗa mini na kira Mama na mata ta’aziya ba” hararar shi Anwar ya yi ya na faɗin “ka ji ɗan rainin wayo kira nawa na ma ka saƙo nawa na turo ba ka duba ba”
“Amma ai na faɗa ma uzurin aiki ne ko” murmushi ya yi “idan hakan ɗin ne idan ma ba hakan ba kai dai ka sani. Yawwa dama magana na zo mu yi za mu iya yin ta anan ɗin ko na bari sai zuwa dare na same ka a gida tun da yanzu ka zama agogo sarkin aiki kar na zo na shiga cikin aikin na ka” shiru ya masa kamar ba zai ce komai ba kafin da ga bisani ya ce.

“Ina jin ka wace magana ce?”

“Mun yi magana da Zhara ne” zuciyar shi ta ba da dum! Ya kafi Anwar da ido babu ko ƙibtawa “ina sauraren ka” numfashi ya ja ahankali ya furzar ya na faɗin “ta ce satin nan za su gama jarabawa su na gamawa za ta tafi gida. A taƙaici dai mun kai ƙarshe idan har ta je gida zan tura iyayena a yi maganar aurenmu. Mene ne shawara” fuska babu annuri ya ce.

“Har wani shawarata ka ke nema sanda ku ka fara soyayya ka zo ka nemi shawarata ne kafin ku fara?” Ya miƙe tsaye ya na tattara fayel ya a jiye gefe ɗaya ya ɗauki laptop da wayoyin shi.

“Wai me ye haka na zo ma da zance ka tashi ka na shirin tafiya babu amsa mai daɗi. Shi kenan na yi kuskure da har na fara neman soyayyar ta ba tare da na nemi izinin babban Yaya ba a yi mini afuwa, wannan ne dalilin ma ya sa na ke so na gyara kuskure na na ce zan nemi shawarar ka gami da tura su Baffa.”

“Ba na son gulma Anwar ka je ka yi duk abin da ka ga dama yadda ba ka sa ni tun farko ba a yanzun ma ba shiga zan yi ba.” Ya yi maganar ya na kama hanya Anwar ya bi bayan shi da kallo fuskar shi ciki da mamaki. Juyowa ya yi ya na faɗin “idan ka tashi tafiya za ka iya rufe mini office.”

“Me zan zauna yi ni kam ni ma fitar zan yi. Sai dai maganganun ka da kuma yanayin ka sun ƙulle mini kai na rasa me ka ke nufi da hakan” fita Hafiz ya yi ba tare da ya ba shi amsa ba. Kaɗa kai Anwar ya yi ya bar office ɗin jiki a sanyaye.

<< Kuskuren Waye? 18Kuskuren Waye? 20 >>

1 thought on “Kuskuren Waye? 19”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×