Skip to content

Kuskuren Waye? 2

Part 2 of 20 in the Series Kuskuren Waye? by Aisha Abdullahi Yabo

Halima ta sa ta gaba da dariya tana mata tsiya yarinyar nan matsalata da ke tsoro wallahi kamar wata farar kura” Zhara ta harare Halima ta gefen ido tana faɗin “tsoro dai ai halat ne ko, ya fi mai neman rigima da kuɗin sa.”

“Ni kin san in dai rigima ce ba ni da ita sai idan an taɓo ne dama kuma Annabi ya ce idan har a ka maka laifi ka rama daidai yanda a ka maka, dan haka ni rigima ta ba na yin ta sai da dalili.”

“Iskancin banza amma kafin a ce ki rama daidai da yanda a kai maki me Annabi (S.A.W) ya faɗa ka yi haƙuri ka ya fe Idan ba za ka iya yafewa bane a ka ce ka rama daidai da yanda a ka maka, aka kara da cewa an fi so ka yi haƙurin.”

“Na dai ji ɗin sai a tashi a gyara fuska kafin a ce ki fito” tana hararar Halima ta ce; “ba wata kwalliyar da zanyi gara ya ganni a hakan idan zai so ni ya so ni a zahiran cin Zhara shi ne so na gaskiya” ta tashi ta zauna ta riƙo duka hannayen Aysha tana faɗin “kin san me?” Tana girgiza kai ta ce; “A’a sai kin faɗa “tunanin da nake yanzu idan har na ganshi bai min ba shi kenan ban isa na musa ba dole hakan zanyi biyayya wa mahaifina? To shi idan ban masa me zai faru?”

“Wannan tambayar daga ni har ke ai ba mu da amsarta Zhara kawai dai mu yi fatan idan har da Alkhairi Allah ya tabbatar idan kuma babu to Allah ya rusa maganar cikin sauƙi ba tare da ran kowa ya ɓace ba.”

“Uhm Amin Halima”. Bayan su Yaya Hafiz sun kammala cin abinci duk da ba sosai su ka ci ba ka san cewar a ƙoshi su ki su ka shigo cikin gidan su ka gaisa da Mama a mutunci ta tambaye su mutan gidan “suna lafiya Momy ta ce; “a gaishe ki” tana murmushi ta ce; “ina amsawa” a ranta ta san Hajiya Turai ba za ta taɓa aiko mata saƙon gaisuwa ba, bayan sun gaisa su ka koma falon Baban Zhara su ka zauna, Yaya Hafiz ya kalle abokinsa Anwar ya ce; “ba laifi yaran da mahaifiyar duk suna da natsuwa sai dai ita ɗin ko a ya take oho” Anwar ya fe; “shi ne matsalar rashin zumunci ai ƙanwar ka da Babanta da Baban ka uwa ɗaya uba ɗaya ya wuce wasa fa amma a ce ba ku san juna ba gaskiya ka ji kunya” yana harararsa ya ce; “amma kafi kowa sanin ai ba a ƙasar na ki a zaune ba to ta ya zan santa kawai dai idan har bata sauya a yanda na santa tana ƙarama ba tabbas a ko ina zan iya gane ta”
“Uzurin ka kenan ba ka ƙasar amma ni ba zai wani gamsar dani ba karka manta kana zuwa hutu me ya sa ba za ka dinga shigowa kana gaishe su ba?”

“Muna haɗuwa da Baban su a Kano shi ya sa.”

“Yawwa kaga dai maganata dai ta fito. Zumuncin ne ba ka so tunda ba ka damu da zuwa har gida ka gaishe shi ba.”

“Mtsw sarkin meta ni ba wannan ne damuwata ba, ina tsoron naganta na ji bata mun ba, kuma a yanda na fahimci Daddy a kan maganar nan za mu iya samun matsala matuƙar rashin amincewar ta fito daga wajena” gyara zaman sa Anwar ya yi yana faɗin “bana ma tunanin za ta ƙi yi maka ba, kawai ka sa a ranka za ta yi ma dama wani lokacin mu muke sakawa kanmu a bu.”

“Uhm!” Ya numfasa yana mai yin shiru yana tunani a ransa tabbas baya son mace wacce ta yi zurfi a boko amma kuma baya son kidahumar mace marar wayewa, ya fi son wayayyer mace ‘yar gayu da ƙwalisa wacce ba zai ji kunyar nuna ta a ko ina ba.

“Wai da gaske ki ke ba za ki yi kwalliyar ba?”

“Halima kinfi kowa sanin halina tunda har na ce ba zanyi ba, dama alƙawari ne duk mijin da zan aure a zahirin Zharata zan fito masa ina so na samu miji wanda zai so ni domin Allah ba dan wani ƙyale-ƙyale ba.”

“Na san da wannan amma dai da kin shafa ko fauda da kwalli haka ba dole sai kinyi kwalliya sosai ba”
“Aifa sai ki yi” cikin jin haushi ta ce; “matsalata da ke kafiya ka da Allah ya sa ki yi!” Rungumeta Zhara ta yi tana dariya ta ce; “haba rabin ran ba dai fushi ba ko?” Daga waje Mama ta ƙwalla ma su kira “wai Halima Zhara me kuke yi ne har yanzu ba ku fito ba kun bar su suna jiran ku.”

“Gamu nan fitowa Mama!” Halima ta yi maganar tana mai ture Zhara daga jikin ta ta fito Zhara ta biyu bayan ta su ka fito suka jira a tare tufafi iri ɗaya su ka sa ka har ɗinkin Halima ta sa mayafi amma ya rufe ko ina na jikinta Zhara ta sa Hijab mai hannu har ƙasa, Halima ta sa ƙafart ɗaya daga cikin falon kira ya shigo wayarta, ta yi baya Zhara ta dube ta Halima ta yi ƙasa da muryarta ta ce; “ki shiga ina zuwa” ta yi maganar tana mai tura Zhara ciki ba yanda Zhara ta iya dole ta ƙarasa shiga Halima ta koma daga baya, kanta a ƙasa ta ƙarasa shiga falon ta zauna a kan kafet daga ɗan nisa da su kaɗan cikin jin kunya da tausasa murya ta gaishe su Anwar ya karɓa da fara’a ya ce; “Barka da fitowa Sarauniyar mata, ya gida ya karatu?”

“Alhamdulillah!”

“Ma sha Allah hakan a ke so” ya dinga janta da zance da zolayar ta sai dai ta yi murmushi ta kasa cewa da shi uffan, Yaya Hafiz ya zuba mata idau so ya ke ya mata kallon tsab amma sam taƙi bada damar hakan, dukan su su ka yi shiru Anwar ya ɗauke wayar s ya miƙe yana faɗin “shi kenan bari na baku wuri tunda na zama sirikin ku kun barni ina ta zuba kamar ‘ya’yan kanya.”

Ƙasa ta yi da kanta tana murmushi, haushin Halima ne fal a ranta, ta je ta yi zamanta ta barta ita kaɗai kunya na shirin ɗauke mata numfashi, kusan a tare su ka ɗago suka kalle junansu saurin yin ƙasa da kanta ta yi a ransa ya ce ‘ba laifi tana da kyau sannan kamanninta na yarinta bai sauya ba sai dai kawai ɗan abinda ba a rasa ba da girma zuwa wa su sauyi-sauyi, cikin sakin fuska ya ce; “ni dai ƙawanta da na sani a da mai yawan surutu ce ga kuma ƙiriniya amma wannan gaba ɗaya naga magana ma wahala take mata kamar mai ciyon baki, ko dai an sauya min ita ne?” Ya yi maganar idanunsa na a kanta, sake sunkuyar da kai ta yi tana dariya marar sauti, duk yanda ya so ta sake jikin ta da shi su yi magana ta kasa Zhara mace ce marar saurin sabo tana da kunya sosai, a jiyar zuciya ya yi kafin ya ce; “na san tun kan zuwana Baba ya ma ki bayanin komai ni dai ta wajena babu matsala duk abinda Daddy ya yanki a wajena banda ja na kan karɓe shi hannu bibbiyu, sai dai a wajan ki ne ban san ya ki ka ɗauke al’amarin ba.”

“Nima a wajena babu matsala” ta ƙarasa maganar tana mai ɓoye kanta cikin Hijab, murmushi ya yi, duk yanda ya so ya ja ta da fira dan ta saki jikin ta da shi amma kunyar ta ta hana hakan, wannan ya sa bai wani ɗauke dogon lokaci ba ya ma ta sallama, bayan ta shiga gida ya je ya yi sallama da Mama, su ka fito tare da su Hussain ya ba su saƙon Zhara da tsarabar su Anwar ya ja mota su ka bari garin.

Tana fitowa falon ta samu Mama na aiki ta tambaye ta Halima Mama ta faɗa mata Halima tun ɗazun ta tafi, ɗaki ta shiga sai bayan tafiyar su ta fito zuwa gidan su Halima, tana zuwa ta samu Halima tana aiki kichen shiga kichen ɗin ta yi ta Halima ta duƙa tana zuba albasa a kan naman kaji Zhara ta kai ma ta duka a baya har sai da Halima ta gantsara tana ihu ta juyo ganin Zhara ce a tsaye tana harararta ta yi ajiyar zuciya “wayyo wai dama ke ce gaskiya kin ɗau alhakina, Allah dukan ya shigeni” cikin harara ta ce; “babu ‘yar wulaƙanci da rainin wayo irin ki wallahi, kawai sai ki yi tahuwar ki ki barni.”

“Wayyo yi haƙuri jinin jikina wallahi ni kaina ba hakan na so ba, banji daɗin rashin ganin Yaya Hafiz ba Yaya Mahamod ne ya kirani wai ya kawo aiki Hajiya bata nan idan ina kusa na zo na gyara masa zai yi baƙi ne, na fara kawo ma sa uzuri tun kan na ƙarasa ya hau masifa kin san halin shi hakan ya sa dole na dawo amma ni kaina ban so hakan ba, ki yi haƙuri.”

“Mtsw! Gaskiya Yaya Mahamod bai kyauta min ba, kinga yanda na zama kamar a ce ar na arci na kare” dariya Halima ta yi ta rufe tukunya suka fito waje suka zauna a kan kujerar roba “bani labari ya haɗu? Ya yanayin sa ya ke? Yana da fara’a, ya kuma yi maki ma’ana kina son shi?” Tagumi ta yi tana kallon Halima har ta gama zuba kafin ta janye tagumin tana dariya ta ce; “to ni wannan tambayoyi haka kamar a gidan jarida, wanne zan amsa wanne zan bari” Halima ta kai mata duka a kan cinya tana faɗin “Malama duka nake so ki bani amsa faɗa mun dan Allah duk na zaƙu na ji aiki fa nake amma hankalina na wajan ku, na ji kamar na kama Yaya da suka dan haushi” murmushi Zhara ta yi kafin ta ce; “gaskiya ya haɗu In gaya maki a fakaice na ƙare masa kallo kinga kyakyawa ne kamar dai yanda ki ka ga Babanmu da Daddyn su suna kama to shi ma din su ya ɗauko sai dai kawai kinga shi a kwai yarinta da kuma yanayin inda ya ta su komai na sa har ya fi na su kyau, ga shi yana da sajin fuska kamar dai irin na Salman Khan ke har yafi na Salman Khan kyau fa” ta yi shiru tana lumshi idanunta Halima ta tintsire da dariya tana faɗin yarinya kawai dai ki ce kin faɗa Yaya Hafiz ya cire tuta” ta buɗe idanunta tana ɗaga mata gira ta ce; “Yes faɗi da babban murya” ta gyara zamanta tare da magana cikin natsuwa da nuna ba wasa ta ce; “magana ta gaskiya na faɗa ba ƙaramin faɗawa na yi a ƙoramar son shi ba har ina jin fargaban kar ya ce ban masa ba” Halima ta dafa kafaɗan Zhara tana faɗin “ki ma daina sa wannan tunanin a ranki ina da tabbacin zai ji fiye da abinda ki ka ji, domin ke ɗin kina daga cikin irin matan da ba ko wani irin namiji ne zai iya gani zuciyar sa ba ta buga ba har ya ji ina ma zai same damar ɗaukar wannan gwal mai ƙyalli da kawalwainiya.”

“Allah ya shirye ki Halima tunda ni taki ce ai dole ki kurantani hakan, amma rigar da duk ta yi wa wani to ba lallai ne ta yi wa wani ba abincin wani a ka ce gubar wani, ke dai kawai na barwa Allah duk abinda ya yi daidai ne.”

“Gaskiya ne Allah ya tabbatar mana da Alkhairi.”

“Amin” ta shi su ka yi Zhara ta kama mata aikin suna aiki suna ci-gaba da zancen Yaya Hafiz, a maganar da su ke da Zhara Halima ta fahimci Zhara ta faɗa so ba da wasa ba.

*****
A mota suna tafe dukan su sunyi shiru sai waƙar D.Y da ke tashi a motar, Anwar ne ya gaji da shirun ya ragi murya ya ɗan kalle gefen da Hafiz ya ke kujerar mai zaman banza yana dannar waya mayar da hankalin shi ya yi a kan tuƙin da ya ke kafin daga bisani ya ce; “Kuna kama da ita sosai kuma yarinyar ta burgi tana da kunya da natsuwa, ina fatan dai ta maka dan na san halin ka ba ƙaramin aikin ka bane ka ce ba ta ma ba” murmushi Hafiz ya yi kafin daga bisani ya ce; “ko ba ta min ba ai ban isa na ce a’a ba ka kuwa san yanda Daddy ya ɗauke lamarin auren nan?” Ya ja numfashi ya furzar kafin ya ci-gaba da magana “ni fa ban mata kallon tsab ba gaba ɗaya ta duƙunƙuni guri ɗaya, kunyar ta tayi yawa.”

“Ba wani yawa da kunyarta ta yi Malam kawai al’adar masu jajayin kunni ka ɗauko rayuwar wayewa, amma ni banga matsalar kunyarta ba fa, hakan mace dama ya kamata a ce ta kasance ko ba ka san kunya tana daga cikin adon mace ba, kuma ko a addinance ana son mace ta kasance mai kunya tana daga cikin alamomin mace tagari.”

“Malam duk na san wannan karatun amma fa na ta ya yi yawa fa, to ta ya zan san ainahin wace ce zan aure.”

“A she to ƙarya ka ke da ka ke cewa baka son wacce ta yi zurfin karatu, ni dai a sanina mafi a kasarin ƙanana yara masu ƙarancin shekaru irin Zhara da wahala ka same su da irin wayewar da kai ka ke so, dan sai ka je can jami’a ka ɗauke wayayyar mace babu kalar da ba za ka samu ba sai wacce ka so ɗauka, amma fa bance a jami’ar babu ma su kunyar ba, akwai amma kuma a can za ka sami irin kalar da ka ke so” harararsa Hafiz ya yi kafin ya ce; “kai iskancin ka yawa ne da shi so kake Daddy ya yankani ya yi tsire dani dan tashi hankali, sannan ni na ce maka bata min bane? Kawai dai yanayin da nake son matar da zan aure ne bata kai ba, amma ba komai tunda bana jin ƙinta zan iya auren ta a hakan.”

“Kada Allah ya sa ma ka aure ta ɗin!” Dariya marar sauti Hafiz ya yi ya ɗauke wayarsa ya ci-gaba da danna ya san abokin na sa ya shaƙa dama Anwar akwai saurin fushi.

*****
Hajiya Turai tana zaune cikin babban Falonta ta yi shiga ta alfarma tana riƙi da remot a hannunta ta miƙe ƙafafunta tana daga saman kujera ‘yar aikin ta Dije tana zaune a gabanta tana ma ta tausa, Hafiz ya shigo falon yana waya yana sanyi da wando jins iya gwauwa sai riga mai ƙaramin hannu, “Anwar tashina kenan fa ka bari kawai anjima za mu yi magana” yana gama faɗa ya tsinki kiran ya ƙara sa cikin falon ya zauna a kusa da Hajiya Turai yana faɗin “Momy me a ka dafa mana ne yunwa nake ji.”

“Abinda ka fi so na sa a ka ma” cikin farin ciki ya ce; Momy sinasin a ka yi” ta gyaɗa masa kai tana murmushi ta ce; “har da farfesun da ka fi so farfesun kayan ciki” cikin farin ciki ya nufi dani ya zauna yana ci suna fira bayan ya gama ya dawo cikin falon ya zauna ta dubi Dije ta ce; “maza ki bar nan” da sauri Dije ta tashi ta fita, ta dawo da hankalin ta kan Hafiz fuskarta babu Annuri ta de; “tun bayan dawowar ka Jigawa ba ka ce dani komai ba, kaga yarinyar ta ma ka?” Shafa sajin fuskarsa ya yi yana murmushi ya ce; “ba laifi Momy ta yi.”

Ta ɗauke fuska kafin ta ce; “to idan har kai ta yi ma ni ba ta min ba ba kuma zan taɓa barin wannan auren ya yu ba” gysrs zaman shi ya yi ya riƙo hannayen ta cikin tausasa murya ya ce; “Momy dan Allah ki yi haƙuri karki nunawa Daddy ba kya son zaɓin shi bana so wata matsalar ta ta su a sanadin wannan auren ki yi haƙuri Momy komai ya wuce abinda ya ke tsakanin ki da Maman yarinyar nan daban itama yarinyar daban” fizgi hannunta ta yi kafin ta ce; “ba fa zan yarda ba Hafiz dole ka bi umurnina ka je ka faɗawa Mahaifin ka ka je yarinyar bata ma ba ya yi haƙuri za ka fito da wata, idan ya so ka je cikin ‘yan’uwana ko ‘ya’yan ƙawayena ka duba na tabbata ba za ka rasa wacce za ta ma ka ba a cikin su.”

Cikin damuwa ya ce; “Momy ta ya zan iya tunkarar Daddy da wannan zancen sanin kanki ne ba zai taɓa yarda ba faɗar hakan ma zai iya janyo matsalar da dagani har ke ba za ta mana daɗi ba” ya gyara zaman sa ya na kallonta cikin marairacewa da kwantar da kai ya ce; “dan Allah Momy k… Ta ɗaga ma sa hannu “na gama magana Hafiz bana son haɗa zuri’a da mugun iri, irin Mayu dan haka Umurni na ke baka ka faɗa ma sa kamar yanda na faɗa ma” tana gama faɗa ta tashi ta haura sama ta barshi zaune a wajan kamar mutum-mutumi, Hafiz mutum ne mai gudun zuciya yana matuƙar son iyayensa ya na da biyayya da gudun zuciyar su, gaba ɗaya ya shiga ruɗani har ya rasa wani irin tunani zai yi, haka ya tashi jiki ba ƙwari ya koma sashinsa ya kwanta rigingini a kan gado idanunsa a rufe ya faɗa duniyar tunani, idan har ya ƙi bin umurnin Momy shi kenan ya tarowa kansa rigima, sannan ranta zai ɓace za ta yi fushi da shi, haka uwa Uba Daddy idan har ya yi gigin faɗa masa hakan komai ma zai iya faruwa.

Bookmark

No account yet? Register

<< Kuskuren Waye? 1Kuskuren Waye? 3 >>
Share |

11 thoughts on “Kuskuren Waye? 2”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.