Skip to content
Part 22 of 43 in the Series Kuskuren Waye? by Aisha Abdullahi Yabo

Abba ya nuna ta da dan yatsa “ina mai ƙara tabbatar ma ki matuƙar Zhara ba ta dawo yanzun ba har Hafiz ya tafi wallahi hukuncin da zan yi ba zai ma ki daɗi ba” kaɗa kanta kawai ta yi ta shiga uwar ɗaki zama ta yi gefen gado ta yi tagumi a yadda take jin tafasar zuciyarta ji take kawai duk abin da zai faru ya faru amma ba za ta ce Zhara ta dawo ba. Muryar sa ta jiyo yana faɗin “kin dai ji me na faɗa ma ki ko!?” ajiyar zuciya ta yi a zuciye ta ɗauki waya ta kira Yaya Fati a ka yi sa’a Zhara ce ta ɗaga kiran “Hello Mama Momy na banɗaki.”

“ki dawo gida yanzun nan!”

“Me ya faru ne Mama?”

“ki dawo dai na ce ko sai kin tsaya tambaya ta, matsw!” Ta tsinki kiran ranta a ɓaci “ya je ya aura wa duk wanda ya so ‘yarsa ce ai idan ma kwaɗayen abin hannun su ne Allah ya ba da sa’a, dama hausawa sukan ce kwaɗayi mabuɗin wahala!” Ganin Abba ta yi tsaye a gabanta sam ba ta ji shigowar sa ba, kallonta yake mamaki ciki da fuskar shi, “ke da kan ki ki ke tunanin kwaɗayi ne ya sanya ni cewa sai Zhara ta aure Hafiz da kan ki Maman Zhara?” ajiyar zuciya ta yi tare da kawar da kanta tana kallon gefe “Ni ba hakan nake nufi ba, amma dai ai abin da kake shirin yi ne dole ko ma waye ya yi tunanin hakan.

Ka manta duk irin cin zarafin da Turai mahaifiyar sa ta zo ta mana? Ka manta abin da ya faru bayan mun tara dubban jama’a domin ɗaurin auren ‘yar mu? Ka manta irin cin zarafin da ta mun a lokacin da na je bikin ɗanta? Duk da waɗan nan kuma shi ne har za ka amince ka sake ɗaukar ta ka ba shi saboda ita ɗin ba ta da galihu ya ƙi ta a sanda ya so ya dawo ya so ta a sanda ya so saboda ta zama mai arhar samu ba. Irin wannan ma ko auren ya yi tsab zai sako mana ita daga baya kuma ya dawo ya ce bai yi ba alamu sun nuna kai kuma sake mayar masa za ka yi!”

Gyaɗa kansa ya yi fuskarsa na nuna wani irin yanayin da ba za ta iya tantanci ko na miye ba, “ya yi kyau na kuma gode da har ki ka faɗa mini irin yadda zuciyar ki take kallona. Sai dai a matsayina na uba kuma wanda ya ke jan ragamar duk wani abu mai numfashi da yake gidan nan na yanki hukunci Zhara ba ta da wani mijin da ya wuce Hafiz da yardar Allah.” juya wa ya yi ya nufi kofa ya ɗaga labule ya juyo a ka yi sa’a ita ma ɗin shi take kallo “ba zan hana ki yin ko wani tunani ba, kamar yadda ba zan hana ki yi wa hukuncin na wa ko wani irin fashin baƙi ba, kawai abin da zan daɗa jajjada ma ki babu wanda ya isa ke ko ita ya hanani yin abin da na yi niyar yi ba!!” Ya fita a zuciye. Jan numfashi ta yi ta furzar da ƙarfi, har ma ta rasa wani irin kalar tunani za ta yi.

A tsakar gida suka haɗu da Momy tana fitowa banɗaki tsayawa ta yi turus tana kallon Zhara “ke kuma ina za ki tafi?”

“Mama ce ta kira ta ce na dawo” harararta ta yi tana faɗin “amma ai ita tace sai gobe za ki koma ko.”

Momy ki kira ta ki ji ita ce ta kira a wayar ki ta ce na zo.”

“Ina zuwa” ta faɗa tana shiga ɗaki jim kaɗan ta fito “na kira ta ki je Allah ya kyauta, amma wallahi ina mai ja ma ki kunne da ki riƙi mutuncin kan ki ki kuma riƙi wa kan ki darajar da Allah ya ba ki a matsayin ki na ‘ya mace, idan har kika biye wa mahaifin ki ki na ji ki na gani za ki faɗa cikin matsala da motar wulaƙanci, dan motar kwaɗayi ƙarshen ta ba ya kyau” duk da har ranta ba ta son wannan hukuncin na Abba amma har ga Allah ba za ta so a dinga cin zarafin mahaifinta ba. “ki yi haƙuri amma ina da tabbacin duk a bin da Abba ya yi ba wai ya yi ne dan kwadayin abin hannun sa ba sam ba ya da irin wannan zuciyar yana yi ne domin zumunci.” fito da idanu momy ta yi tana faɗin “oh wai har kare Abban na ki ki ke, gaskiyar Maman ki da ta ce har yanzu son nasa ki ke.”


“Ni fa ba hakan nake nufi ba”

“Idan ba hakan ki ke nufi ba to me ki ke nufin? Ki je Allah ya ba da sa’a, ai duk abin da ki ka ga muna yi saboda mutuncin ki ne tunda kin ce kin ji kin gani duk da abin da suka yi ma ki za ki aure shi Allah ya taimaka jiki magayi, zan faɗa wa maman ki ta cire hannunta a zancen nan kawai dan kunya za ki ba ta!” Zhara za ta yi magana ta ɗaga mata hannu “Ni ba na son jin komai maza ki je!!” Jiki a sanyaye Zhara ta kama hanya ta fita.

Hafiz yana zaune a ka kujera yana waya Abba ya shigo da sauri ya tsinki kiran, “Hafiz an bar ka kai kaɗai”

“Haba A’a Abba ba komai ai”

“Mamanta ce ta aike ta amma ta na hanya yanzu za ta dawo ka ɗan yi haƙuri” cikin gyaɗa kai ya ce. “Ba damuwa Abba” zama Abba ya yi suna fira yana yi wa Abba tambayoyi a kan familyn su, ƙarar napep yasa Abba ya miƙe tsaye yana faɗin “ina zuwa” ya fito ta ƙofar waje ya sami Zhara tana tsaye tana ba ɗan adaidaita kuɗin sa juyowar da za ta yi suka haɗa ido da Abba gaban ta ta ji ya ba da dum! Turus ta yi ta tsaya suna kallon kallo da Abba, matsowa ya yi kusa da ita fuskar sa babu annuri hakan ya ƙara faɗar mata da gaba muryar sa ta ji ta dakar mata dodon kunne “kin kyauta Zhara wato da ke da mahaifiyar ki so ku ke ko tozarta ni.”

Gyaɗa kai ta yi tana zubar da hawaye “a’a ka yi haƙuri sam ba na burin ɓata ma bare har na zama silar da zan tozar ta ka Abba.”

“Ki na da mana tunda har ki ke shirin sa ƙafa ki shure hukuncin da na yi wanda a tunanina na isa da ‘yar da na haifa” sukunyar da kanta ta yi tana sa bayan hannu tana share hawayen da suke zarya a kan fuskarta “ka yi haƙuri ba zan sake ba”
“Ki je yana jiran ki saura kuma ki nuna masa ban isa da ke ba kin ji ko?” Ƙasa cewa da shi ta yi komai ya nufi hanyar shiga cikin gidan tabi bayan shi jin motsi a bayan shi yasa ya juyo da mamaki a fuskar shi ya ce. “Au ba za ki ba kenan?”

“A’a zan shiga na faɗa wa Mama na dawo ne.”

“Ba sai kin shiga ba idan ya tafi kya shiga” wasu hawayen masu zafi suka zubo mata ta juya tana tafiya kamar wacce ƙwai ya fashe wa a ciki. Tana zuwa bakin ƙofa ta tsaya ta goge hawayen fuskarta sannan ta shiga da sallama a bakin ta, Hafiz da tun fitar Abba ya ke tsaye bakin tagar falon yana kallon su duk da ba ya jiyo me Abba yake faɗa ya dai san tabbas faɗa yake yi mata duk sai ya ji babu daɗi, ganin tana zuwa yasa ya yi saurin juya wa ya koma ya zauna a inda ya tashi.

Bayan sallamar da ta masa ta samu waje ta zauna ba ta sake ce wa da shi uffan ba, zuba mata idanu ya yi yana kallon ta da murmushi a fuskar shi, shi ya rasa waci irin yana ce ta zo ta rufe masa idanu da zuciya da har ya kasa hango abin da a yanzu yake hanga. Ajiyar zuciya ya yi kafin ya gyara zamansa “sannu da zuwa Zhara na”
“Sannu. Zharan mai rabo dai” ta amsa masa a taƙaici “uhmm! Wai fushin ne har yanzu ba a daina ba? Ki faɗa mini me zanyi da zai sa ki manta komai ki karɓe ni fiye da farko har mu zama abu ɗaya.”

“Ni na ce ka mun wani abun ne?”

“Ko da ba ki faɗa da bakin ki ba Zhara na sani na yi gagarumin KUSKURE a baya, sannan kuma kina nuna mun KUSKUREN nawa a bayyani.” murmushin gefen baki ta yi kafin daga bisani ta ce. “Humm ka daina wannan tunanin idan ma da wacce ta yi KUSKUREN ai ni ce da tun farko na fitar da mijin aure a cikin manema na ko da ba a ɗaura ba idan har an san da zaman sa ai babu ta yadda za ka zo da zancen ka bare kuma har a karɓa ma.”

“Hakan ki ke gani ko? To ko da a ce saura ‘yan sakanni a ɗaura tsab zan dawo na kuma same ki, auren ne dai idan an ɗaura wannan kam babu yadda zan yi dole na rungume ƙaddara, bare ma kuma ba na fata da yarda Allah ba ki da mijin da ya fi Hafiz.”

Cikin raunin murya ta ce. “Eh kam ba zan yi mamaki ba duk abin da ka faɗa zai iya yuwa tunda a yadda na fahimta Abba ya fi son ka da farin cikin ka a kan kaina” ta fashe da kuka cikin tashin hankali ya ta su ya durƙusa gaban ta “mene ne kuma abun kuka Zhara? Ki yi haƙuri ni ban fadi maganar ba ne dan ranki ya ɓaci don Allah ki yi haƙuri ki daina kukan nan.”

“Me yasa Yaya Hafiz ka ke son mayar da ni tamkar ‘yar tsana abar wasan ka a duk sanda ka so? To bari ka ji kamar yadda ka faɗa a baya cewar ba ka so na ni ɗin ba kalar macen da kake so ba ce to ni ma a yanzun ina faɗa ma ka ba na son ka ba kuma zan taɓa auren ka ba, ruwan ka ne kasan yadda ka yi ka warware maganar ba tare da na samu matsala da Mahaifina ba, ruwan ka ne kuma kayi yadda za mu samu matsalar, ka ga idan har ka ji ‘ya da uba sun samu matsala a sanadin ka sai ka zuba ruwa ƙasa ka sha dan farin ciki.”

Kallonta ya ke da idanunsa da suka yi jawor saboda ɓacin rai mikiwa ta yi za ta tafi ya yi saurin riko hannunta yana yi mata wani irin kallo mai ciki da shauƙi “yaushe na taɓa faɗa ma ki ba na sonki? Yaushe na faɗa ma ki ke ɗin ba kalar matar da nake so ba ce? Uhmm! Idan har za ki mini adalci Zhara ban taɓa furta ma ki hakan ba.”

Idanunta na kallon ƙofa ta ce. “Idan har ba ka taɓa faɗa mun ba ai ka faɗa wa wacce ita ce muradin zuciyar ka na kuma ji da kunne na ko ka ce ba a yi hakan ba?” Ta juyo ta kafe shi da kallo tana jiran jin amsar da zai bata “Alhamdulillah tun da har ki ka tabbatar da ban taɓa ba ɗin, dan haka wancan jin ki bar shi a jin kawai ne babu tabbacin ni ɗin ne ko ba ni ba ne.” Ya ƙara riƙo hannunta da dukan hannayen sa biyu yana ƙoƙarin sanya idanunsa a cikin na ta taƙi yarda ta kawar da kanta “wallahi wallahi wallahi kin ji rantsuwat musulmi ko Fatima Zhara ban taɓa ƙin ki a zuciyata ba ke ce ki ka rusa komai KUSKUREN ki ne Zhara ba wai nawa ba tunda ban taɓa zuwa na faɗa ma ki gaba da gab…

Tarar maganar sa ta yi a zuciye “oh hakan ma za ka faɗa ba, ba dai ka yarda ka fada wa ita zaɓin na ka ba?” Sa gwauwoyin shi a ƙasa ya yi sosai ya haɗa hannayen sa waje ɗaya cikin magiya “na yi KUSKURE ki yafe mun amma ki sani ban taɓa ƙin ki ba wallahi, na sani ganin farko da na yi wa Halima na faɗa sonta amma hakan ba ya na nufin wai ba n… Kallon ƙasa da sama ta masa zuciyarta na mata wani irin tafasa tamkar a yanzu ne ta jiyo irin kalaman da yake faɗa wa Halima gashi a yanzun ma faɗa mata yake yana son Halima a gabanta saboda ya raina ta.

“Ba sai ka ƙarasa ba, ka aure zaɓin ranka nima ka barni na aure nawa zaɓin” ta na gama faɗa tasa kai ta fita da sauri tun kan juriyarta ta ƙure ta fallasa ainahin abin da yake zuciyarta. Tun bayan da ta fita ya kifa kansa a kujera wani irin zafi yake ji a zuciyar shi ya yi kusan minti biyar ahakan kafin daga bisani ya miƙe tsaye ya shafa fuskarta kafin daga bisani ya shiga cikin gidan ta ƙofar ciki.

Zhara da gudu ta ƙarasa ɗakinta ta kwanta a kan katifa tana kuka, ‘dole na jure na yaƙinci son da nake ma Yaya Hafiz ba zan taɓa iya auren mijin da aminiyata take aure ba, da ma wata ce tabbas da na manta komai sai dai mijin Halima! A’a ba zan iya ba ko da son ka ne zai zama ajalina’ ta ja numfashi ta furzar cikin kuka ta ce. “Tabbas ko me ya faru laifina ne KUSKURE NA ne da ban bata number shi dan a gwada shi ba da duk hakan bai faru ba. Uhmm! Na karɓi wannan hukuncin na Ubangiji ina fatan Allah ka bani ikon canye wannan jarabawar!”

Mama ta sa kaya gaba tana kallo sai mere baki take Abba ya shigo yana faɗin “kinga uban kayan da Hafiz ya mana tsaraba ko? Nayi nayi ya bar su yaron nan yaƙi har da kuɗaɗi.”

“Ka sha godiya mai siriki masu kuɗi” ta faɗa cikin gatsali tare da shigewa ɗaki.

Murmushi ya yi haɗi da kaɗa kai kawai ya fice zuwa kasuwa.

Sam ba ta wani ji daɗin hutun da ta yi a gidan ba kasancewar Mama na ta fushi da ita, ga Dady ya kirata a waya a kan ta dawo hutun ya isa hakan, zaune take ta yi tagumi har ga Allah ba ta so ta koma ita tafi so ta zauna a gaban iyayenta dan gujewa Hafiz da matsalar Momyn shi. “Mtsw! Ni na rasa wa ya basu sabon layina daga Dadyn har shi Yaya Hafiz din, mamakin ma me zan yi na san dai ba zai wuce Abba ba shi ne ma zai basu sabon layin nawa” tashi ta yi ranta ba daɗi tana haɗa kayan ta kasancewar sammako za ta yi, bayan ta gama haɗa kayan ta fito zuwa ɗakin Mama.

Ta samu Mama na karatun dala’ilu khairat, zama ta yi kusa da ita ta jira har ta idar ganin Mama na shirin tashi da sauri ta ce. “Mama” kallonta ta yi fuska babu annuri ta ce.

“Mene ne?”

“Ki yi haƙuri don Allah wallahi ni sam bana ba Yaya Hafiz fuska hasalima sai mu yi fin sati ba mu haɗu ba” koma wa ta yi ta zauna tana kallon Zhara “ni ba na ƙin Hafiz da ke Zhara, kawai dai ina jiye maki halin da za ki iya tsintar kan ki a ciki a lokacin da kika zama sirikar Hajiya Turai wanda na tabbatar da ko a yanzun ma ba wai kina jin daɗin zama da ita ba ne.”

“Ni ai ba zan yarda da auren ba ma Mama, na faɗa masa tun a ranar da ya zo kowa ya tsaya a kan zaɓin sa” murmushi irin na manya Mama ta yi tana faɗin “yana da wahala a ce ba a yi auren nan ba Zhara yadda naga Abban ku ya ɗauki maganar yana ririta wa, kawai hakurin za mu yi mu yi fatan Allah yasa hakan ya zama alkhairi, amma tabbas ina jiye maki tsoron zama da Hajiya Turai da kuma Halima domin duk wacce za ta iya yin irin wannan cin amanar ba tare da ta dubi dangantar ku ba komai za ta iya yi maki na cutarwa, kawai dai zan taya ki da addu’a.”

Dora kanta ta yi jikin Momy tana kuka shafa kanta ta dinga yi tana faɗin “kuka ba mafita ba ne kawai addu’a ita ce takobin mumini, ki riƙi addu’a a duk inda ki ke, ki kuma yi takatsantsan da su kin ji ko.”

Kanta kawai ta iya gyaɗawa bakinta ya yi mata nauyin da ba za ta iya buɗe wa ba bare har ta magantu, ta rasa farin ciki za ta yi ko kuka? Tabbas gaskiya Mama ta faɗa tsanar da take hangowa a cikin idanun Momy komai zai iya yi mata, uwa uba Halima da ta shayar da ita ruwan mamaki.

Tun da safe Abba yasa ta gaba suka kama hanyar Kano tare, da Dady ya ce zai turo direba Abba ya ce a’a zai kawo ta da kan shi dan a kwai maganar da yake so za su yi. Zuciyarta a tsoraci take wani irin tarba za ta samu daga wajan Momy domin bata manta da irin rabuwar da duka yi ba, haka ya za ta kasance tsakaninta da Halima idan har ta ji labari, ji take kamar ta suɓucwa Abba kawai ya neme ta ya rasa ta shiga duniya ya fiye mata rayuwa a tsakiyar mutanen nan.

Fulani

<< Kuskuren Waye? 21Kuskuren Waye? 23 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×