Skip to content
Part 26 of 43 in the Series Kuskuren Waye? by Aisha Abdullahi Yabo

Nuna mata ɗan yatsan shi ya yi cikin kausasa murya ya ce. “Halima ki dinga iya bakin ki kuma ki dinga tauna zance kafin ki kai ga furzarwa, domin ba zan lamunci ki raina iyayena ba. In har da mutunci har kya buɗe baki ki ce wai ke ba dolen shi ba ce, ko kare ne yake a tare da ni ai kya mutunta shi saboda ni bare kuma mahaifina!”

“Ni fa tsaya tsaya kar ka kai ne in da ‘yan ƙuda suke salati suna kiran amin amin. Zagin shi na yi ko kuma wata mummunan magana ka ji na faɗa a kan shi da har za ka ce ban mutunta shi ba.”

“Ban da lokacin jin kalaman ki na rainin hankali ki tashi yanzu mu tafi!”

Kwanciyarta tayi tana faɗin,

“Ni fa ba za ni ba.”

“Lallai kuwa dole ki je in har ina amsa sunana mijin ki, idan kuma ki ka zaɓi ƙin zuwa sai ki tattara ina ki ina ki ki bar mini gida dan ba zan lamunci abin da ki ka zo da shi ba!! Ina mota ina jiran ki” ya fita a zuciye.

Ranta ya yi matuƙar ɓaci wato har ita ya ke yi wa barazana da ta tafi gidan su. Kwanciyar ta yi har a ranta ba ta da niyar tafiya ya je tana jiran shi ya dawo ya bata takardar ta sai ta tafi gidan na su da dalili, tunawa ta yi da Mama da Aunty Laila da ƙiris dama su ke jira su mayar mata da jawabi, ga kuma mutanen gari tabbas dariya za su yi mata.

Tsaki ta yi cikin fushi ta miƙe ɗaukar mayafinta ta yi ta fito tana masifa a ranta. Har suka isa babu wanda ya ce wa wani ko ci kanka.

Ba kowa falon hakan yasa ya haura zuwa sama ya barta zaune a falon, Kande ta fito tana yi mata sannu da zuwa ko kallon ta ba ta yi ba bare har ta amsa mata.

‘Baƙin hali ko za ki haɗiye zuciya ki mutu da yardar Allah sai Maman masu gida ta aure yallaɓai Hafiz’ ta yi wucewar ta zuwa kechin.

Ya samu Momy tana waya sai bayan da ta gama ta dawo da kallonta kan shi “har kun zo kenan?”

“Eh wai me ya ke faruwa ne Dady ya ke kiran mu wallahi duk a tsoraci nake.” Cikin taɓi baki ta ce. “me kuwa ya faru bayan taɓa ‘yar gwal da matar ka ta yi.”

“Matata wai Halima? Wace ‘yar gwal ɗin ce ta taɓa kuma?”

“Ah ba ka ji mutuwar ɗan sarki a bakina ba ka je wajan mai kiran na ku za ka ji komai” ta faɗa tana tashi tsaye “don Allah dai Momy ki faɗa mini me ya faru duk kin ƙara jefani komar tunani.”

“Me wai kake ci na baka na zuba. Tun da har ka zo ko ma meye ai za ka ji ne.”

Ba yadda ya iya hakan ya biyo bayanta suka sauko zuwa falo suka samu Khadija tana zaune a falon ta yi kamar ba ta san da zaman Halima ba duk da hararar da Halimar take aika mata “bari na kira Dady” cewar Hafiz da ya nufi hanyar fita falon.

“Yaya Dady fa cewa ya yi na faɗa ma idan ka zo ka jira shi yana zuwa.”

“Shi ne kuma ba za ki faɗa mini ba har sai da ki ka ji nayi magana.”

“Ka yi haƙuri ai zan yi magana ne sai ka rigani yi.” tsaki ya yi ya koma ya zauna “ina wuni Momy.”

“Lafiya lau yarinyar kirki kwana biyu ba ki leƙo mu ba” ta mayar mata da murmushin tana faɗin “ba na jin daɗi ne shi yasa amma kuna raina” kai dubanta tayi ga Hafiz da ya cika da mamakin yadda Momy ta sakarwa da Halima fuska wacce ya san a yanzu Momy ba ta yinta “kai kuma ka kyauta ka san ba ta da lafiya shi ne ba ka faɗa mini mun duba ta ba.”

“Ki yi haƙuri” abun da kawai ya iya ce mata kenan dan sam ba ya cikin natsuwar sa saboda rashin sanin dalilin kiran na Dady ga kuma maganar da Momy ta yi wai Halima ce ta taɓa ‘yar gwal duk ya shiga ruɗani suna haka Zhara ta yi sallama dukan su suka bi ta da kallo duk sai ta ji ta tsalgu babu wanda ya amsa mata sai Hafiz da ya kasa ɗauki idanunsa daga kanta “ina wunin ku.”

Kowa ya yi mata shiru sumai-sumai ta wuce ta gaban su za ta wuce ta jiyo muryar Hafiz yana kiran ta “zo nan Zhara” cak ta tsaya ita ba ta tafi ba ba ta kuma juyo ba zuciyar ta sai dukan uku-uku take tasowa ya yi ya tsaya gabanta yana kallon fuskarta “me ya same ki a fuska naga ta yi jawor?” Sunkuyar da kanta ta yi tana kallon tayes “hahaha tafi ta sha ai.”

Kallon Khadija ya yi da mamaki ya na faɗin “kamar ya fahimtar da ni” nuna masa Halima da ta yi tsuru ta yi tana faɗin “ga amsar ka nan tambaye ta ka ji” kafin ya yi magana Dady ya shigo hakan yasa ya kasa cewa komai sai dai tabbas maganar ta dake shi kenan Halima ce ta dake Zhara ita ce Momy ke nufi da ‘yar gwal.?

“Ina wuni Dady?”

“Lafiya lau Mamana zo nan” zuwa ta yi ta zauna kusa da shi “Ina wuni” Halima ta gaishe shi yi ya yi kamar bai ji ta ba. “Hafiz mene ne dalilin da zai sa matar ka ta je har makaranta ta ci mutuncin Mamana har da duka kalli fuskarta kwancin hannun matar ka ne!”

“Ka yi haƙuri wallahi ban san ta tafi ba dan ni gida na barta kuma ba ta faɗa mini za ta fita ba sai yanzu ne ma nake jin ta je ɗin” ya mayar da idanunsa a kan Halima da ta sunkuyar da kai “da izinin wa ki ka fita!?” Ta masa shiru “wai ba za ki yi magana ba ne?”

“Ka ga ƙyaleta ai ko ba za ta yi magana ba na san dole kunnenta na ji” mayar da kallon shi ya yi gare ta yana faɗin “laifin me ta yi ma ki ki ka dake ta da ci ma ta mutunci a cikin makaranta?”

Shiru ta yi masu “tambayar ki nake ki ba ni amsa” har ga Allah ba ta yi zaton tintsiya daga Dady ba ko da a ka ce yana neman su zaton ta a kan wata maganar ce daban ko ta auren Zhara da Hafiz ɗin.

“Tun da ba ki ba da amsa ba ta tabbata dai babu dalili. To ki ji ni da kyau ba zan lamunci cin mutunci ba bare kuma har ta kai ga dukan mini ‘ya ba gaira babu dalili daga yau kar na ji ko na sake jin irin hakan ta sake faruwa idan kuma ba ki ji ki ka daina ba lallai hukuncin da zan yi sam ba zai taɓa yi ma ki daɗi ba.

Ki riƙi mutuncin ki muga juna da mutunci hakan sai ya fi alkhairi”

Kuka ta fashe da shi “ka yi haƙuri Dady hakan ba za ta sake faruwa ba.”

“Ka riƙi wani ban hakurin ka ina dai faɗa ma ka ja mata kunne kar ta sake kwantata irin hakan, mutunta juna shi ne mafi alkhairi a gare ta!”

“Ki ba ta haƙuri!” Hafiz ya yi maganar cikin tsawa tausayin ta ya sa Zhara ta ce. “Dady ku ƙyaleta kawai ni na yafe mata ta yi hakan ne a tunanin ta ko auren Yaya Hafiz zan yi shi ne kawai yasa ta yin hakan” ta shi ta yi daga in da take ta je ta zauna kusa da Halima ta riƙo hannunta tana faɗin “ga Yaya nan a gaban ki gaban kuma kowa ki tambaye shi idan har da a kwai maganar aure a tsakanin mu wataƙil idan ki ka ji amsar a bakin shi kuma gaban manyan mu za ki fi gamsuwa da samun natsuwa a ranki.”

“Shirmen banza dama wai duk saboda wannan ne, ke Halima idan har da tunani da gaskiya kya tsangwami Zhara a kan auren Hafiz ko kin manta baya ne? Ai kuwa auren Hafiz da Zhara tabbas babu fashi da yardar Allah wata mai fita za a yi bikin. Sai ki sanya wa zuciyar ki salama idan kin so idan kin so kuma ki yi akasin hakan, amma dai ki sani ba zan lamunci duka ba.”

Dukan su maganar ta zo masu a ba zata wani irin sanyi da farin ciki ne ya ziyarci zuciyar Hafiz har ma ya rasa kuka zai yi ko me ma zai yi dan murna, ya yin da Zhara ta ji wani irin shokin a jikinta har ga Allah ba ta yi tsammanin jin wannan kalmar ba da ba za ta yi kuskuren magana ba, farin ciki za ta yi ko baƙin ciki oho. Sautin kukan Halima ya ƙaro.

“Dama tsoron da nake kenan dan ni ba ‘yar’ywarsa ba ce sai a nuna mini fifiko saboda ita ‘yar gida ce.”

“Kema idan kin so ki zama ‘yar gida za ki zama Halima ni ban da matsala da ke, matsala ɗaya ce za mu samu ki ce za ki taɓa Mamana nan kam ba za mu taɓa shiri ba” ya yi maganar da murmushi a kan fuskar shi “wai Alhaji ka kuwa san me ka ke faɗa auren Zhara za a yi wai da Hafiz? Me yasa wai kake yi mini hakan ne Alhaji saboda Allah ni ban da haƙƙin ka yi shawara da ni ne kafin ka yanke shawara a kan rayuwar ɗana ba. To wallahi ban yarda da wannan hukuncin ba dan ba na ra’ayin wannan auren!”

“Ni ne mahaifin shi na fi ki iko da shi da ki yi ra’ayi da kar ki yi ra’ayi na riga da na gama magana” kallon takaici ta bishi da shi har ya bar falon ba ta iya cewa da shi komai ba dan baƙin ciki a gaban ‘ya’yanta yake nuna mata ita ɗin ba ta isa ba. Da sauri Hafiz ya bi bayan Daddy. Halima ta fincike hannunta daga riƙon da Zhara ta yi mata miƙewa tayi tsaye tana faɗin “ba dai gidana ba Bismillah ina ma ki maraba!”

“Ke gafara can ko ma me ya faru ai ke ce duk Ummul’haba’isi tunda har ya bar maganar kin je kin nuna kishin ki na hauka kin sa ya tunzura ya yi hukuncin da ya so!”

“Humm dama can a na da niya ba wai ni ce nasa a ka yi ba, amma ta zo ta gani idan har za ta samu abin da take son” ta fita a zuciye.

Zhara ta miƙe sumai-sumai za ta wuce ta tsinkayo muryar Momy tana faɗin “ba dai kin na ce ba har sai da maganar auren ta tabbata, shi kenan sai a yi mu gani idan har tusa za ta hura wuta!”

Barin wajan ta yi da sauri ta haura sama a matuƙar tsoraci take ita kam wace irin jarabawa ne ta faɗa ita na ta auren da wannan rikicin zai zo mata. “Wai ni kam Momy meye matsalar Zhara ne da har ki ka tsane ta da yawa. Don Allah ki bar yarinyar nan ta ja numfashi mai daɗi wallahi ba ta da matsala na tabbatar da za… Filon da ta jefa mata ne yasa ta yin shiru “wato Khadija goyon bayan ubanki ma ki ke ko? To dan ubanki ba za a barta ta ja numfashin ba, sakaryar kawai wacce ba ta kishin abin da uwarta take so.”

“Allah ya ba ki haƙuri ni kawai dai na ga babu dalilin da zai sa a tsananta mata tsana har hakan.”

“Wai za ki yi mini shiru ko sai na sassaɓa ma ki ne!” Barin falon Khadija ta yi tana magana ƙasa-ƙasa a ka bar Momy tana masifa.

“Na gode sosai Dady Allah ya ƙara girma da lafiya.”

“Amin. Tabbatuwar godiyar ka ita ce ka riƙi mini amanar ta idan har ta samu farin ciki da kwanciyar hankali a auren ka hakan zai sanya ni farin ciki. Ina matuƙar son auren ku ya tabbata ne da zuri’a mai albarka hakan zai sanya zumuncin mu ya ƙara haɓɓaka.”

“In sha Allah za ka samini mai riki ma ka amanar ta, zan kula da ita fiye da yadda take a gaban ku.”

“Allah ya yi ma albarka. Yawwa maganar Halima ni ba na ce zan aura ma Zhara saboda ka wulaƙanta ta ba dukan su ‘ya’yana tunda har ta kasance a ƙarƙashin ka. Kawai rashin adalci ne ba zan lamunta ba dan haka ka ja ma ta kunne kar na sake ji ko ganin ta daki Mamana” gyaɗa kan sa ya yi yana faɗin.

“In sha Allah hakan ba zai sa ke faruwa ba.”

Daga nan ne suka faɗa zancen wani kamfanin robobi da Dady ya ke so ya buɗe.

Sanda ya zo ya ke tambayar Momy ina Halima ta ce masa ta tafi gida ko a jikin shi ya ɗauki wayoyin shi da key ɗin motar shi zai tafi ta kira sunan shi tsayawa ya yi idanunsa a kan ta,

“Zama za ka yi ba wai ka tsaya mini a ka ba kamar wani dogari.”

Zama ya yi kusa da ita yana mai riƙo hannayenta cikin sigar lallashi “na sani maganar ƙoƙi dai ba ta wuce ta gizo a kan dai maganar Zhara ne. Don Allah Momy kiyi haƙuri ki manta komai duk da dama can ba wai Zhara da iyayenta sun ma ki wani laifin ba ne.”

“Sun mini ko ba su yi mini laifi ba ni dai ba na ra’ayin wannan auren na ka ba na kuma son su bare har na yi sha’awar haɗa zuri’a da su. Dan haka ka je ka faɗa masu kamar dai farko, ba ka so ba za ka kuma aure ta ba!!”

Ajiyar zuciya ya yi cikin gyaɗa kai ya ce. “ki yi haƙuri ina sonta ba zan iya janyewa ba don Allah ki so ta ko dan saboda ni.”

Faɗa ta shiga yi masa kamar za ta dake shi haƙuri dai ya dinga ba ta da ƙyar ya samu ya lallaɓata a kan zai yi tunani. Har ya bar gidan ta na ƙara jajjada masa dole fa ya bar maganar auren nan.

Gaba ɗaya ta rasa farin ciki za ta yi ko baƙin ciki ta sani ta na son Hafiz amma fitintinun da ke cikin auren Hafiz ya sa gaba ɗaya ya fitar mata a rai sam ba za ta yi wani farin ciki ba. Sai dai kuma ba za ta iya yi wa Dady musu ba. Kande ce ta shigo da abinci a hannunta ta samu tana kwance ajiye abincin ta yi a kan lokar gadon tana faɗin “Maman masu gida ki tashi ki ci abinci.”

“Na ƙoshi” zama ta yi gefen ta “ki daina kukan nan don Allah, kar wannan hukuncin yasa ki cikin damuwa wallahi ni na ji daɗin wannan haɗin da a ka yi Hafiz mutum ne mai nagarta na kuma tabbatar da za ki yi farin ciki da auren shi” zama ta yi tana faɗin “ba shi na ke ji ba Maman shi da matar shi dukan su ba sa sona ba na son rigima ko kaɗan, na kuma tabbatar da duk a ka yi auren nan rikici ne za a yi ba kaɗan ba.”

“Mtsw! Manta da su duk masifar Hajiya kafin auren ne da zarar a ka yi auren ki na barin gidan shi kenan magana ta ƙare, ita kuma matar shi sai kin ɗaukar wa kan ki raini sannan za ta kawo ma ki tashin hankali. Bare kuma na san ba lallai ne ku zauna gida ɗaya ba, kuma ina da tabbacin Alhaji ba zai taɓa yarda su wulaƙanta ki ba. Kawai kisa wa kan ki natsuwa wallahi ki aure abin ki.”

Kasaƙi ta yi tana sauraren Kande da take ta ƙoƙarin kwantar mata da hankali da shawarwari hakan sai ya sanya mata natsuwa.

Har ya kama hanyar zuwa office ya fasa ya nufi gida gara ya duba ta ya gani idan ta koma gidan. Har cikin ransa ya ji ciwon abin da tayi wa Zhara duk da a wani ɓangaren hakan ya yi masa rana tunda ga shi a sanadin hakan burin sa zai cika. A waje ya ajiye motar shi. Tsoro ne ya shige shi sanda ya ke gab da shiga cikin gidan kunnen sa ya dinga juyo masa…

Fulani

<< Kuskuren Waye? 25Kuskuren Waye? 27 >>

1 thought on “Kuskuren Waye? 26”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×