Kallon Aunty Husna ta yi tana murmushi ta ce. “Aunty ki zauna hakan ki huta, tunda na zo sai kai da kawo ki ke.”
“Ina na ga ta zama babban ƙanwat a kawo mini ziyara”
“Hahaha kai Aunty don Allah ki zauna wannan abincin ai har yawa ya mini”
“Ina dai zuwa” ta faɗa tana shiga kichen jim kaɗan ta fito riƙi da filet ta zuba kayan furut a kai ajiye wa ta yi gaban Zhara tana faɗin “Bismillah” cikin murmushi ta ce. “duk na kai waɗan nan ina ai sai na kasa tashi”
“Ai kuwa komai ba na buƙatar ki rage” suma cin ɗanwakin ta yi da murmushi a fuskarta “wai ni kam ina yaran tun da na zo ban ji motsin su ba”
“Sun tafi Katsina tare da Abbansu za a yi auren ƙanwarsa ni ma jirgin yamma zanbi ranar juma’a in sha Allah”
“Allah ya dawo da su lafiya. Ashe za ku sha Katsina”
“Amin Ya Rabb. A’a Lahadi za mu dawo ranar asabar ne bikin, ai kin san karatu ba zai barni ba. Ya labarin Hafiz?”
Murmushi Zhara ta yi ba tare da ta ce da ita komai ba, zungurunta ta yi tana faɗin “wato dai ba za ki yi magana ba ko, har yanzu kin kasa sakin jikin ki da ni, ni fa ina jinki ne tamkar ƙanwata da muka fito ciki ɗaya”
“Ba hakan ba ne Aunty ni ma ina jin ki tamkar hakan, kawai dai ban san me zan ce ba ne, Yaya Hafiz fushi ya ke da ni.”
“Me ya haɗa ku?” Bayan ta gama sauraren Zhara kallonta ta yi tana mai gyaɗa kanta “gaskiya ko ni ce dole zan ji haushi me yasa za ki yi saurin yanke masa hukunci har hakan, komai na son uzuri Zhara, da da ku ka zo sai ki zuba masa idanu ki ga iya gudun ruwan shi yanzu kin ga saurin yanki hukuncin na ki in da ya kai ki”
“Ni ya zan yi ne dole na tsorata ya ce dama so yake mu keɓanci mu yi magana kawai sai na ganmu a hotel dole na tsorata”
“Kin kira shi kin ba shi haƙuri?”
“Uhm na kira amma matar shi ta ɗauka har sai muka ɗan yi sa’in sa da ita, kuma ya daina zuwa gida bare ma na gan shi na ba shi haƙurin.” shiru ta yi cikin nazari kafin daga bisani ta ce. “Yanzu ɗauki waya ki kira shi”
“Na ce masa me”? Ta yi tambayar da sauri cikin harara ta ce. “Sai ka ce ba mace ba, ke komai sai an koyar da ke. Kira shi ki ce ya zo ya dauke ki”
“To ai mun yi da direba zai zo ɗaukata”
“Sai ki kira ki ce ya zauna za ki dawo da kanki” shiru ta yi ta kasa cewa komai, wayar da take ajiye gefen Zhara ta ɗauka karɓi kira shi”
“To a bari na gama cin abinci”
“Ba wani nan ai da zafi-zafi a kan bugi ƙarfe sannan ba gara ya sani da wuri ba kar wani uzurin ya shigo” ba yadda ta iya karɓar wayar ta yi ta kira shi har ta tsinke bai ɗaga ba Aunty Husna tasa ta ƙara kira bai ɗaga ba “dama na faɗa ma ki ba lallai ya ɗaga ba”
Karɓi wayata ki sa number ki kira”
“Haba zubar da kan ai sai ya yi yawa”
“Wannan rashin wayo ne da yawancin mata suke, lallaɓa namiji da nuna ƙololuwar kulawa a gare shi ba laifi ba ne, in dai wanda ki ke aure ko kuma soyayyar ku ta yi ƙarfi har ta kai ana maganar aure ba zubar da kai ba ne. Zubar da kai shi ne irin namijin da ba ki da tabbacin soyayyar shi gaskiya ce bare kuma har a kai ga aure, idan har ki ka ce za ki yi sanya ki na ji kina gani za ta kwace ma ki shi ko kuma wata ta waje ta zo ta yi ma ki wuf da shi kamar dai yadda ki ka yi sakaci tun a farko.
A yadda na fahimci Hafiz yana son a nuna masa soyayya da kulawa ke kuma kunya ta hana ki yin hakan, wanda hakan zai cutar da ke har a gidan auren ki matuƙar ba ki a jiyeta a gefe ba, ba wai na ce ki daina kunya ba a’a kunya ai adon mata ne, amma kuma ba a kan komai a ke nuna hakan ba. Yanzu dai kira shi daga baya ma ɗora firar” jiki a sanyaye ta sanya number ta kira. “Ina zuwa bari na duba na ji ana sallama” Husna ta faɗa tana miƙewa tsaye.
Kwance yake a kan gado ya lulluɓe cikin bargo kasancewar yau ya tashi da zazzaɓi hakan yasa bai fita ba, kira ya shigo wayar shi a tunanin shi Zhara ce hakan yasa bai ko duba wayar ba sai dab da za ta tsinki ya janyo wayar yana duba wa ganin number ba suna yasa shi ɗaga wa. “Hello”
“Barka da wuni Yaya” lumshi idanun shi ya yi lokacin da ya ji zazzaƙar muryarta ta daki dodon kunnensa, ba zai iya ƙyaleta ba kamar yadda yake ji ya yi ɗin muryarta ta karya masa duk wani lugun shi. “Lafiya lau Zhara, fatan kin tashi lafiya”
“Ni ba zan ce eh ko a’a ba”
“Me yasa”?
“Saboda ba ka damu da kasan hakan ba tunda ba ka nemi ni ba kuma ba ka ɓukatar jin nawa tunda har wayata an yi wa ya ji” ta yi maganar cikin shagwaɓa kamar za ta yi kuka, wani irin abu ya ji yana yi masa yawo tun daga kansa har zuwa ƙafafunsa cikin sauyawar murya ya ce. “Ki yi haƙuri yanayin aiki ne”
“Uhm-um Yaya kai dai kawai fushi ka ke da ni ko ma na ce mantawa ka yi da ni”
“Bari na kira ki, wannan layin fa na ki ne?”
“A’a na Aunty Husna ne” tsinki kiran ya yi ya kirata wayarta. “Ki daina tunanin zan iya mantawa da ke idan har zan manta da ke ashe zan iya manta kaina kenan. Kawai ban ji daɗin irin yadda ki ke kallona ba ne hakan yasa na ɗan ɗaga ma ki ƙafa”
“To ba tun a ranar na ba ka haƙuri ba, ka yi haƙuri ba zan sake ba ka ji”
“Wannan shagwaɓar ta ki ai tuni tasa na manta da wani fushi can. Uhm! Ina so na gan ki, na yi kewar ki sosai”
“Anya kuwa”
“Da gaske fa”
“Uhm shi kenan ina gidan Aunty Husna amma sai zuwa yamma zan bar wajan ta” ya yi bargon ya yi wanda tuni zazzaɓin ya neme shi ya rasa, “ba zan iya jura ba ko kwana biyun nan da na yi ni kaɗai na san irin wahalar da nake sha na rashin ganin ki, ki ba ni address ɗin gidan zan zo yanzu na ɗauke ki.”
Murmushi ta yi tana ƙara manna wayar a kunnenta ta masa kwatancin gidan. Su na yin sallama Aunty Husna ta shigo ta zauna a kan kujerar tana faɗin “da ganin wannan murmyshin da yake shimfiɗi a kan fuskar nan ta ki komai zam-zam” rufe fuskarta ta yi tana dariya. Cikin dariya ta ce. “Ko ke fa ki saki jiki ki nun masa soyayya da kulawa ba ke kaɗai ba ce dole sai kin yi da gaske matuƙar ki na son gina fadar martabar ki mai girma a zuciyar shi”
“Na gode Aunty”
“Riƙi na goden na ki ba na so, ke dai ki gyara” ta yi maganar tana harararta.
A falo suka haɗu da Halima tana fitowa kichen “ina kuma za ka tafi na gan ka da key ɗin mota?”
“Zan ɗan fita ne amma ba jimawa zan yi ba” haɗi fuska ta yi tana faɗin “Humm yanzu na barka kwance ba ka da lafiya, a gabana ka yi waya ba za ka je asibiti ba to ina za ka tafi kenan?”
“Oh Halima rigima yanzu fitar fa ta kamani kuma ba jimawa zan yi ba na dawo” zama ta yi a kan kujera tana faɗin “idan dai an dafa ɓoye ai ba za a ci ɓoye ba” murmushi kawai ya yi ya fice ba tare da ya ce da ita komai ba ta raka shi da harara. Wayarta ta ɗauka ta kira wayar Mama har ta fara ringing kuma ta tsinki kiran “idan ma na kira ta na ce mata me? Na tabbatar da idan har ta ji wai Zhara za ta aure Hafiz dariya da Allah ya ƙara za ta yi mini, kuma sai ta fi kowa farin ciki. Mtsw!” Shiru ta yi tana tunani “to ko na kira Aunty Laila? Humm ba mafita ba ce, wayyo!” Jefar da wayar ta yi zuciyarta na yi mata zafi ta rasa madafa.
Tuƙi ya ke amma idanunsa na a kanta kallon sa ta yi cikin murmushi ta ce. “Yaya ka kalle hanya kar ka je ka jefar da mu a kan titi” kawar da kanshi ya yi daga gareta yana dukan sitarin motar cikin shauƙi “ke ɗin ce idan ina tare da ke sai na dinga ji na tamkar wani sabo a wannan duniyar, kin ƙara kyau ga dukan alamu ma ba ki yi kewata ba, au na manta ashe fa babu ni a cikin zuciyar” rufe idanunta ta yi tana dariya marar sauti “ni yaushe na faɗi hakan?”
“Au tambayata ma ki ke”
“To ni dai ban san na faɗa ba, kawai dai ina duba ya alaƙa ta da Halima za ta kasance duk da ko a yanzun ma ta yi rauni. Uhm! Sam ban jin daɗin yadda al’amurran suka juye mana amintar mu ta zama tamkar wutar karar da ta canye ta mutu ta zama tuka” ajiyar zuciya ya yi kafin daga bisani ya ce. “Ki daina sa wannan tunanin a ranki, ki ɗauka wannan ɗin yana faruwa ne tamkar a mafarki, za ki farka kiga ba hakan ba ma’ana komai zai sauya In sha Allah amintar ku za ta dawo matuƙar a ka sa haƙuri”
“Humm Allah yasa. To Momy kuma fa ba ta so ban kuma tunanin za ta taɓa son auren mu” murmushi ya yi yana faɗin “inji waye ya ce ma ki ba za ta taɓa so ba? Za ta so ki da yardar Allah ke dai kawai mu sanya haƙuri da kuma addu’a a gaba” ta ɗanyi shiru kafin daga bisani ta ce. “Allah yasa”
“Amin matar Hafiz” rufe fuskarta ta yi a karo na biyu tana murmushi, wani irin farin ciki take ji sai ta manta da duk wasu tarin ƙalubalen da suke a gabanta. Ita kanta ba ta ce ga dalili ba kawai tsintar kanta ta yi da sakin jikinta da shi suna fira cikin shauƙi. haka ya dinga yawo da su cikin gari kafin daga bisani suka tafi Nasarawa Welcare, sai yamma sosai ya mayar da ita gida, riƙi marfin motar ta yi tana faɗin “sai anjima, ki kular mini da kan ki”
“Au kai ba za ka shiga ba ne” gyaɗa kansa ya yi yana faɗin “sai zuwa dare”
“Allah ya kaimu” har ta juya ta fara tafiya ya kira sunanta, jiyowa ta yi tana kallon shi “Zhara ba zan taɓa manta wannan ranar ba a cikin tarihin rayuwata, uhm! Ina matuƙar ƙaunar ki wanda baki ba zai iya faɗar adadin sa ba” ƙasa ta yi da kanta wani irin sanyin farin ciki taji na ratsa dukan sassan jikinta har zuwa zuciyarta.”Ni ma hakan nake ji, ko a da can da nake tunanin na rasa ka na kasa juriya na kasa yarda zan iya rayuwa ba tare da kai ba. Zan ta sonka ba iya rayuwata ba har bayan ba raina domin soyayyar ka na a tare da ruhina” tana faɗa ta bar wajan da sassarfa tana dariya marar sauti.
Lumshi idanunsa ya yi wani irin abu yake ji yana yi masa yawo tun daga ƙwaƙwalwarsa zuwa zuciyarsa, yana jin son Zhara irin wanda bai taɓa yi wa wata ‘ya mace ba, tabbas yana matuƙar son matarsa sai dai son Zhara na daban ne a zuciyarsa. Haka yaja motar cikin wani yanayi na shauƙi ya bar ƙofar gidan na su ya nufi gida.
Saura sati biyu biki ta tattara ina ta ina ta ta koma gida duk da kuwa ƙurrafin da Hafiz ya yi ta yi mata a kan bai so ta yi masa nisa, sai haƙuri ta bashi dan ita kam ta fara tsorata da matsalar Momy gara ta ɗaga daga gabanta idan anyi auren kuma ba gida ɗaya za su zauna ba komai zai zo da sauƙi.
Duk da Mama har cikin ranta ba ta son auren saboda matsalar da take hangowa Zhara hakan ta danni fahimtar da ta yi daga Abba har Zhara suna farin ciki, tasa ta gaba da gyaran jiki. Cikin mamaki Mama take kallon Halima “ke kuma daga ina haka da yamman nan?”
Zama ta yi kusa da ita tana ɗan murmushi “daga Kano, ban ta so da wuri ba ne shi yasa, ina wuni”
“Lafiya lau” bayan sun gaisa take tambayar Baba Mama ta ba ta amsa da yana kasuwa. Sallolinta ta yi bayan ta idar ta miƙe tana faɗin “zan fita Mama sai na dawo”
“Ina kuma za ki je ke da ba ki jima da zuwa ba, ko abinci ba ki ci ba”
“Mun ci abinci da dareba a hanya, zan ɗan je na dawo ba jima wa zan yi ba”
“Dama da direba ki ka zo shi ne ba ki faɗa a ka kai masa shimfida da abinci ba” tana sa mayafi ta ce. “Ajiye ni kwai ya yi ya tafi gidan kakanni sa” a dawo lafiya ta yi mata ta ci gaba da aikinta, har ta kai ƙofa ta ƙwalla mata kira ta juyo tana amsawa “anya kuwa zuwan nan na ki na lafiya ne?”
“Kai Mama me ki ka gani ne”
“A to na ga kin zo babu ko sanarwa sannan daga zuwa ko hutawa ba ki yi ba kin tsiri fita, yanayin ki kaɗai ma ya nuna a kwai damuwa a tare da ke” dariyar ƙarfin hali tayi “ba komai fa kawai dama na ce zan ma ku zuwan ba zata ne, sannan kuma zan je gidan su Jidda tun a can muka yi waya ba ta da lafiya shi ne zan je na duba ta tunda kin ga gobe zan koma”
“Uhm shi kenan, sai kin dawo.” Ficewa ta yi da sauri dan ba ta so Mama ta rumfuta tun kan ta yi abin da take da ƙudurin yi.
“Kai yau zafin garin nan ya yi yawa” Zhara ta yi maganar tana zuba ruwa a bokit “ba dai wani wankan za ki yi ba?”
“Wallahi Mama zafi ya yi yawa ga shi sun ƙi barin wutar”
“Hadari ne da alama yau za a mana ruwa, kuma farkon Damina ne dole sai an ji wannan zafin Allah dai ya kawo mana ruwa masu albarka”
“Amin” ta faɗa tana ɗaukar bokitin zuwa banɗaki. Bayan ta fito wanka tasa doguwar riga marar nauyi suna zaune tsakar gida tana taya Mama aiki, Hasana ta ce. “Aunty Zhara idan za ki koma Kano za ki tafi da ni”
“Hahaha eh ki shirya zan tafi da ke amma fa gaba ɗaya za ki zauna wajena kin yarda” da sauri ta gyaɗa kai tana faɗin “eh na yarda, ba ga Husaini nan ba sai ya taya Mama zaman gida” dariya Mama ta yi tana faɗin “Uhm-um rufa mana asiri kar ku sa Turai ta gasa mu da tsinken gashin tsere da ranmu”
“Haba ai ba za ta ce komai ba da ma dai a gidanta ne wannan kam tabbas za ta yi faɗa”
“Lallai Zhara har yanzu ba ki gama sanin Halin uwar ta ku ba, Allah dai ya kyauta kawai” ta faɗa tana mai shiga kichen dan ba ta son ta furta wata kalmar da za ta janyo wa Zhara karaya. Sallamar da Halima ta yi ne ya sa ta ɗagowa da ga yankan kabewar da take ta zuba ma ta idanu suka shiga kallon-kallo ya yin da zuciyar Zhara ta dinga dukan uku-uku.
Fulani
Masha,Allah
Na gode.