Skip to content
Part 31 of 43 in the Series Kuskuren Waye? by Aisha Abdullahi Yabo

Kawar da kanshi ya yi daga kanta ya zauna a kan kujera wayarsa ta yi ringing ɗagawa ya yi “Anwar ina zuwa zan kira ka” bai jira jin me Anwar zai faɗa ba ya tsinki kiran “ya ban ga wutar ta fara tashi ba ne, meke ke jira maza kunna!” Takaici ya rufe ta wato ko ajikin shi ma ko me za ta yi ta yi ɗin, a tunaninta idan ya ga hakan zai tashi hankalin shi ne ya ce har auren ya fasa,yarda galan ɗin ta yi ta faɗi ƙasa tana gunjin kuka. Tsaki ya yi ba tare da ya ce da ita komai ba ya bar gidan. Sai da ta gaji dan kanta sannan ta tashi ta fitar da fetur ɗin ta kira mai yi mata wanki ya ɗauki sentar kafet ɗin. “Kai Hajiya warin fetur nake ji fa.”

“Mtsw! Nafi’u za ka fitar da shi ka wanke ko kuwa sai ka tsaya surutu!”

“Allah ya baki haƙuri” ya faɗa yana ƙoƙarin cire kafet ɗin.

Ɗaki ta shiga tana tunanin mafita tabbas idan har ta bari a ka kai Zhara wani gidan daban ba za ta taɓa samun yadda take so ba haƙarta ba za ta taɓa cimma ruwa ba. Huce ta yi ta furzar tamkar tsohun kumurci “dole na san abin yi tun kan wankin hula ya kai ni dare.!”

Zama ta yi kujerar da take daga bakin ƙofa ta zauna ajiye wayar shi ya yi a kan kujera ya taso ya zauna a kan kafet ƙafafunsa a tanƙwashe “har na fara tunanin zuwa cikin gida na ɗauko ki a gaban Mama” fito da idanu tayi tana faɗin “haba dai kuma sai ka zo ɗin?”

“Da kin ƙara minti ko da ɗaya ne da kin tabbatar da zan iya ko ba zan iya ba” murmushi kawai ta yi tana wasa da ƙasan mayafinta “wannan kunyar Allah ya nuna mini ranar da zan yayi ta na wullar da ita” dariya ta yi tana rufe fuska. “Wai da gaske komai ba za ki yi ba na shirin bikin?” Cikin gyaɗa kai ta ce. “Za mu yi walima a islamiyyar mu”
“Bayan ita fa?”

“Komai ba za mu yi ba” murmushi ya yi yana faɗin “ai shi kenan tunda amaryar tawa Ustaziya ce. Am komai an haɗa na lefe set biyu ne amma Abba ya ce ba sai an kawo nan ba a barshi acan ɗin, kuma sunyi magana da Dady a Kano za a ɗaura aure”
“Haka ɗazun Mama take faɗa mini, shi yasa ma a ka mayar da walimar ranar Alhamis tunda juma’a za mu zo Kano”

“Allah ya kaimu” ya zuba mata idanu ta sunkuyar da kai tana murmushi “ni fa ji nake kamar ki biyu ni kawai mu tafi yau ɗin” shagwaɓi fuska tayi “haba ni ai ko juma’ar ma kawai dan babu yadda zan yi ne banƙi na zauna anan ɗin ba” harararta yayi yana faɗin “ji bakinta kamar nawa kina magana kamar idan an ce ki zauna za ki zauna ɗin”

“To a gwada a gani ɗin idan ba zan iya ba” duba agogon da yake maƙali a tsintsiyar hannun shi yayi yana faɗin “faɗuwa wannan jarabawar za ki yi dan kuka za ki sawa su Abba don Allah a kai ki gidan Hafiz” dariya ta yi marar sauti “Kinga Anwar ya danno mini kira ya kamata mu tafi kar mu yi dare” shagwaɓi fuska ta yi “mene ne?” Ya yi tambayar yana kallon cikin idanunta sukunyar da kanta ta yi “ba komai”

“Da dai kin yi magana, ba kya so na tafi?” Kanta a ƙasa ta gyaɗa kanta murmushi ya yi mai sauti “nima hakan nake ji sai dai idan na tuna kwana uku ne suka yi saura sai na ji farin ciki domin kin kusa ki zama mallakina za mu rayu a waje ɗaya har iya numfashi na.”

“Uhm! Allah ya nuna mana” ta ƙarasa maganar tana rufe fuskarta. Suna tsaye a bakin ƙafo ya kafeta da idanu “ki zo mu tafi sai na kama maku hul kuyi walimar ku”

“A’a to ni ai ba kowa na sani ba a can, kaga nan duk ƙawayena da ‘yan’uwa suna nan, ka bari kawai mu yi anan ɗin”

“Shikenan tunda hakan dai kike so, amma ai kowa kike so yaje a kwai motocin da za su kaisu su dawo da su. Kawai abar zancen Allah ya kaimu, zan yi matuƙar kewarki” tana jujjuya idanu ta ce. “Nima haka, har ma na fara kewar ka, yawwa Yaya ni kam me yasa kowa gidan sa daban zai zauna?” Zuba mata idanu ya yi cikin nazari kafin daga bisani ya ce. “ina ga kamar hakan ya fi zaman lafiya, saboda ba na son fitina ko kaɗan, na kuma san zaman ku a waje ɗaya ba lallai ya haifar da ɗa mai ido ba”

“Um ni a wajena ba za ka taɓa samun wata matsala ta rigima ba, amma tunda har ka riga da ka ga hakan ya fi kuma har ka yanki hukunci ina fatan hakan ya zama mafi alkhairi” ya amsa da amin cikin farin ciki koyaushe yaba hankalin Zhara yake. Anwar ya zo ya na faɗin “anya ƙanwata za ki barshi ya fito kuwa” fito da idanun ta yi waje cikin jin kunya ta ce. “La Yayana ba fa ruwana”

“Anya kuwa” rufe fuskarta ta yi da sauri ta juya zuwa ciki tana faɗin “na ma tafiyata Allah ya tsare hanya a gaida kowa da kowa” duka ya kai masa yana faɗin “kawai malam ka zo ka kora mini ita”

“Eh na dai ji dama da gangan na zo dan na fahimci idan har banyi hakan ba ba iya tafiya za ka yi ba, ga shi dare zai mana a hanya.” Hafiz na meta suka tafi wajan mota. Ta suron gidan ta zo tana leƙen su har suka wuce, ajiyar zuciya ta yi “Allah na gode ma da ka dawo da farin cikina a sanda na cire tsammani da samun sa.”

Hafiz ya kalle Anwar da yake tuƙi da murmushi a kan fuskar shi “na gode Anwar ba zan taɓa manta wa da abin da ka mini ba, domin ka bani matuƙar gudumuwa wajan ganin ban rasa wannan fure mai matuƙar kyau da ni’imtaccin ƙamshi ba”

“Kar ka damu Hafiz ina matuƙar farin ciki da auren ku da Zhara zai tabbata domin tun a ganin farko na yi maka sha’awar aurenta saboda nagartar da nake gani a tare da ita. Ka godewa Allah”

“AlhamdulilLah!”

Bayan Biki.

Rana ta biyu da kawo ta, suna kwance a ka dinga bugun ƙofa da ƙarfi, Hafiz ya buɗe idanunsa cikin magagin bacci ya janyo wayarsa da take a jiye a kan wadurop ɗin gado duba a gogon wayar yayi ‘waye yake buga mana ƙofa yanzu da sassafen nan?’ ya yi maganar a zuciyarsa jin bugun da ake babu ƙaƙƙautawa hakan yasa ya janye Zhara da take bacci a kan ƙirjinsa ahankali ya kwantar da kanta a kan filo ya sauka daga kan gadon, har ya kai ƙofa ya kalle kansa daga shi sai gajeren wando hakan yasa ya dawo ya sa jallabiyar da ya cire bayan yayi sallah asuba. Fita ya yi zuciyar shi na dukan uku-uku dan yasan lafiya ba za ta sa a zo masa gida cikin duhun asuba ba.

Yana buɗe babbar ƙofar falon ya yi arba da Halima tsaye a bakin ƙofa da uban jakunkunan kayanta a gefe, maigadi yana tsaye a bayanta “don Allah kayi haƙuri Doctor babu yadda banyi da ita ta tafi ba amma taƙi tafiya”

“Ba komai Malam Isiya za ka iya tafiya” da sauri ya bar wajan, kallon Mamaki yake yi mata har ma ya rasa me zai ce “ba ni hanya na wuce.”

“Ki wuce ina?”

“Ciki mana” ta bashi amsa cikin dakiya da nuna babu wasa a fuskarta. “Wai kinyi hauka ne Halima ya za ki zo mana gida tun ƙarfe shida, sannan su waɗan nan kayan na meye? Ko kina nufin duk banbakin da nayi ma ki jiya a banza ba zauna maki a kai ba.” Kawar da fuskarta ta yi daga kallon da yake yi mata tana faɗin “a zaton ka dama na yarda ne, dama ai na faɗa maka ba zan taɓa yarda da hakan ba” ta shiga nuna gidan tana faɗin “ka duba ka ga irin yadda ka fantsama mata fankacecen gida na ji da gani, har da maigadi, ni kuma sai na yarda da wancan ƙaramin gidan tsabar ni ba kowa ba ce a wajan ka ko maigadi babu duk abin da zai sameni ko a jikin ka!”

Riƙi kansa ya yi “oh Allah wai ke shi kenan ba kya so a zauna lafiya, kince dole duk abinda na sanya mata a lefe sai na saya maki na yarda nayi hakan, kince na baki kuɗaɗe ban musa ba na ba ki duk dai dan a zauna lafiya, amma ke sam kin kasa fahimtar hakan koyaushe ƙoƙarin ki shi ne ki zaƙulo fitina.”

“Duk abinda ka lissafu ai dolen ka ne domin haƙƙina ne ba zan yarda kuma adanni mini ba ihe, gida kuma wallahi ba zan zauna wancan ɗin ba sai dai mu taru mu zauna anan ɗin ko kuma ka bani irin wannan ɗin.”

“Kinga ki tattara ina ki ina ki ki bar gidan nan tun muna shedar juna.”

“Wallahi ka ji na sake cewa wallahi babu inda zan tafi zama daram daram!” Komai bai ce da ita ba ya fara ƙoƙarin rufe ƙofar wuf tayi ta shige ta gefen shi. Bin ta yayi da kallo har ga Allah tausayinta yake ji saboda juna biyun da ke jikinta tabbas ba dan hakan ba da sai ya ce ta tafi gida ta huta. Zama ta yi a kan dugowar kujera ta miƙe ƙafafu “ga kayana can a waje ko ka shigo da su ko kuma kasa a shigo da su ka kuma nuna mini ɗakina.”

“Waye ya kawo ki?”

“Motar ka na hau kaga na ma manta key ɗin ajikin motar ka je ka ɗauko, ina ne ɗakina”
“Yadda ki ka kawo kanki ai sai ki bawa kanki ɗakin” miƙewa tayi tana faɗin “wannan ai shi ya fi komai sauƙi” ta fara dudduba ƙofifin da suke cikin babban falon da a ka ƙawata. “Baby kai da waye ne kamar magana nake ji” Zhara ta fito ɗakin baccin su tana murza idanunta dan bacci ne a idanunta, sakin baki tayi tana kallon Zhara rigar bacci ne a jikinta ko cinyoyinta basu ƙarasa rufewa ba “uhm sabuwar rayuwa sabon bariki!” Da sauri Zhara ta buɗe idanunta sosai mamaki ya cika ta ko kaɗan ba tayi tsammanin ganin Halima gidanta a irin wannan lokacin ba. Saurin ɓoyewa tayi bayan Hafiz tana ƙanƙame jikinta kai bakinta ta yi saitin kunnensa cikin raɗa “ba sai ka faɗa mini baƙuwa muka yi ba kar na fito hakan.”

“Ta ya zan faɗa maki bayan bacci na barki kina yi ban san da fitowar taki ba” ya bata amsa murya a ƙasa “oho dai idan ma munafuncina kuke wallahi babu wanda ya isa ya fitar da ni gidan nan!!” Murmushi Zhara tayi har cikin ranta taji haushin yadda ta zo masu gida da sassafe nan kawai dan tarwatsa masu jin daɗinsu. Kwanciya tayi a bayan shi ta saƙalo hannayenta ta gabansa tana janyo shi suna tafiya ta baya-bayan magana take cikin raɗa “taimaka mini mu tafi ɗaki na cire rigar nan” dariya ya yi marar sauti “mene ne za ki ba kanki wahala ai hakan take so ta ganki dama.”

“Uhm-um ni dai mu je don Allah na cire rigar” cikin ba zata ta ji ya sunkumeta ya goya a bayan shi yana faɗin “mu je mu fara wanka sannan a sauya ɗin.”

“Wayyo ka saukeni Baby ba fa mu kaɗai ba ne a gidan” shiru ya mata dama ai da gangan ya yi dan ya ƙonar zuciyar Halima ne. Ai kuwa ta shaƙa iya shaƙa ihu tasa tana zage-zage ba wanda ya bi ta kanta sai ma rufe ƙofar da yayi da key. A kan gado ya ajiyeta riƙi bayan sa ya yi yana faɗin “wash bayana! A cikin kwana biyun nan kin ƙara nauyi fa ko dai ko dai” shagwaɓi murya ta yi tana faɗin “ko dai ko dai me.”

“Uhm-um ni dai ba zance komai ba” janyo shi ta yi ya faɗo kanta “za ki karya mini kunkumina fa” dariya tayi tana lakuta hancinsa “kai ko, faɗa mini me ya faru naga Halima yanzu Allah dai yasa lafiya?” Komawa ya yi gefe ya kwanta rigingini ya janyota ta kwanta a kan ƙirjinsa cikin damuwa ya faɗa mata rigimar da suka yi tun kan ayi auren a kan wannan gidan har zuwan da tayi yau. ‘wato a dole sai mun zauna a gida ɗaya saboda ta ƙuntata mini, ai kuwa ta zauna ɗin ba ta isa ta ƙuntata mini ba sai dai mu ƙuntatawa juna’ ajiyar zuciya tayi kafin daga bisani ta ce.

“Ka ƙyaleta kawai mu zauna tare tunda a kwai ɗakuna a gidan nan.”

“Shi kuma wancan gidan nayi ya da shi, na fa sauya mata kayan ɗaki” shiru tayi tana nazari kafin daga bisani ta ce. “Ka bayar da gidan haya, kayanta kuma ba a kwai auren ‘yar Aunty Rahamu ta Dutse da za a yi ba kawai ka bata kayan tunda sababbi ne.”

“Ke nake jiyewa ba za ki iya da rigimar Halima ba, gara kowa na gidansa hakan sai ya fi” hannu tasa tana wasa da sajen fuskar shi “Allah in dai ni ce ka ƙyaleta kawai mu zauna, na tabbatar ma da ba za ka ji wata fitina daga gareni ba, ko da tayi ba zan biye mata ba”

“Allah ya yi ma ki albarka Sweet Baby, ba damuwa zan kira aunty Rahamu ɗin sai nasa a kai mata.”

“Amin Babyna Allah ya ƙara arziƙi” matseta ya yi sosai a jikinsa yana yi mata raɗa “kai uhm-um ni dai a kwai mai jiran mu a waje fa.”

“Manta ai ba baƙuwa ba ce, kawo kunnenki kiji.”

Takaici ya rufe ta kamar ta zuba wa gidan fetur kowa ma ya mutu take ji a ranta, taja iska ta furzar cikin huci “ba komai da sannu za ki ya bawa aya zaƙinta Zhara wallahi sai na shayar da ke maɗaci a cikin rayuwar nan.!”

Sai wuraren Azahar suka fito fis da su, suka samu ba kowa a falon “ka ga ina ta faɗama kar ta yi fushi ta tafi.”

“To ai da ta huta wa kanta idan ta… Shiru ya yi ganin tana fitowa kichen riki da filet ta zuba wainar fulawa da ta soya da manja, ga uban yaji a gefe. Zama ta yi a kan kujera ba tare da tacewa kowa komai ba. “Sannu da hutawa Halima” Zhara tayi maganar tana zama a kusa da ita, bata amsa mata ba sai ma cin wainar ta da take, zama ya yi gefen Zhara yana faɗin “ni zan fita, ga ɗaki nan ki zauna a ciki” ya nuna mata ɗakin da yake daga dama. “Don Allah Halima Zhara ina roƙon ku alfarma da ku zauna lafiya da juna, dukan ku kunsan kanku tare kuka tashi, dan ƙaddara tasa kun aure miji ɗaya hakan ba shi zai sa ku zama abokan gaban juna ba, dukan ku son da nake maku ne yasa na zaɓe ku a matsayin abokan rayuwata. Don Allah ku z…

“Ka ga idan har kana da abin faɗa bayan wannan ɗin ka faɗa ka tashi ka yi gaba dan surutun ya fara hawa mini kai” kallon Zhara yayi ta sakar masa murmushi mai nuni da gamsuwa da abin da ya faɗa, mayar mata da murmushi yayi yana miƙewa tsaye “zan tafi asibiti idan na fito zan biya wajan su Momy kafin na dawo” raka shi tayi har mota tana yi masa addu’a sai bayan da ya ɓacewa ganinta sannan ta dawo cikin gidan. Ta tarar Halima tasa tashar waƙoƙi ta sa murya sosai, ɗaukar remote ɗin tayi ta ragi murya “akan me za ki rage mini murya.”

“Saboda tayi yawa kuma kin sani ba son hakan nake ba.”

“Dan ba kya so sai kuma a ka ce ni ki hanani yin yadda nake so, nan fa gidan mijina ne ba gidan ki ba bare har ki ce za ki hanani nayi yadda na so.”

Dariya Zhara tayi kafin daga bisani ta ce. “Gidana dai domin da sunana a ka yi gidan kin ga ai ya zama mallakina kenan, dan haka alfarma ce na ma ki har na barki kika zauna mini kar ki ce za ki tukara mini.”

“Iyee! Sannu mai gida, wallahi na fi ƙarfin ki mini alfarma ke kin san da hakan, gida dai aure kike aure nake dan haka baki isa ki sa mini doka ba” dariya tayi tana faɗin “alfarma kuma ta nawa, kar ki manta fa wancan gidan ma nawa ne da sunana a ka yi duk abinda yake cikin gidan, na maki alfarma ki ka zauna a ciki, hatta da mijin da kike taƙama alfarmar da na maki ne ya ba ki damar ki ka ka mallake shi a matsayin miji, hakan wannan gidan ma dai an sake maimaita wa ba dan ni ba da ba za ki samu alfarmar zama a ciki ba” ta suma tafiya ta juyo tana kallon Halima da tayi suroro baki sake tana kallonta “yawwa ba fa gori na yi maki ba kawai dai faɗar wai kin fi ƙarfin alfarmata ce yasa na ce bari na tuna maki da waɗan nan ɗin tunda kin kasance ‘yar adam, wanda kowa yasani ɗabi’a ce ta ɗan adam manta alkhairi.”

Kallonta take irin wanda ya ma rasa abin faɗa ko tunanin wani irin hukunci ya kamata ta yi mata.

Fulani

<< Kuskuren Waye? 30Kuskuren Waye? 32 >>

2 thoughts on “Kuskuren Waye? 31”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×