Skip to content
Part 34 of 43 in the Series Kuskuren Waye? by Aisha Abdullahi Yabo

Tana fitowa wanka ta ji ana bugun ƙofa ta share ta ci gaba da shirinta dan ta ƙudurta a ranta dole sai ya ji a jikin shi ba zai mari banza ba. Hafiz ya kalleshi “ba na faɗama ba ba fa za ta buɗe ba ka zo kawai mu tafi”

“Mu dai ɗan ƙara jira ba mamaki tana wani uzurin ne.” Doguwar riga kawai ta zura na kanti, fitowa tayi ƙaramin falonta ta zauna tana shan Ice cream ta jiyo wata muryar da ba ta Hafiz ba ana kiranta “kamar Yaya Anwar.”

“Ƙanwata don Allah ki buɗe ƙofar nan Anwar ne” murmushin gefen baki tayi kafin ta ce. “wato ma zuwa ya yi ya ɗauko abokinsa, ko ma waye zai ɗauko ba zan taɓa buɗe ƙofar nan ba!” Ganin ya ci gaba da buga ƙofar yana yi mata magiya sai ta ji ba za ta iya ƙyale shi ba domin shi ɗin tana matuƙar girmama shi. Hijab ta ɗauko tasa sannan ta je ta buɗe masu ta ja tunga “Ina kwana Yayana” ta gaishe shi kanta na kallon ƙasa, “lafiya lau ƙanwata zan iya shigowa” da murmushi a fuskarta ta ba shi hanya suka shigo tare da Hafiz zama suka yi a kan kujera, ta zauna ɗan nesa da su a kan kafet.

Idon Hafiz a kanta “ba za ki gaishe ni ba ni?” Tana turo baki ta ce. “Ai ban san tare kuke ba an tashi lafiya” haushi ya rufe shi wato ma ba ta gan shi ba banza ya yi da ita, Anwar yayi murmushi kafin daga bisani ya ce. “Ƙanwata na zo na taya abokina ba da haƙuri ba tare da tashin-tashina ba, ko me ya faru a manta da shi komai ya wuce don Allah ki mini wannan Alfarma” murmushin ƙarfin hali tayi a ranta tana jin haushin yadda ya sanyo Anwar saboda kawai yasan tana jin nauyin shi “um za ki mini wannan alfarmar?”

“Ba komai Yaya Anwar komai ya wuce, amma mar… “Ai na ce banda tashin tashina ko, kiyi haƙuri na tabbatar ma ki da hakan ba za ta sake faruwa ba” gyaɗa masa kai tayi “na gode, to Malam Hafuzu tare za mu tafi ko ya?”

“Ji ka kawai za mu yi waya.”

“Dama na san ai za a rina shi yasa na ɗauko motata.”

“Eh ji ka dai” fita ya yi yana faɗin “za ka neme ni ne ai.” Bayan fitar shi ta tashi za ta shiga uwar ɗakinta ya janyo ta ta faɗo jikin shi kai bakinsa yayi saitin kunnenta “kiyi haƙuri ba zan sake ba, idan kuma ramawar ne zai sa zuciyarki tayi sanyi ga fuskata ki rama.” ya yi maganar yana ɗora hannunta a kan fuskar shi shafa sajen fuskar shi ta yi da murmushi a fuskarta “har abada hannuna ba zai iya taɓa wannan kyakyawar fuskar mai matuƙar daraja da sunan duka ba sai dai tausasawa.”

Haɗe fuskokin su yayi waje ɗaya suna shaƙar numfashin juna goga hancinsa yake a kan nata “na gode Sweet Baby, na maki alƙawari duk rintsi ba zan sake kwantata irin wannan ba.”

“In sha Allah nima ba zan sake faɗa wa Momy magana ba zuciya ce ta ɗibe ni har na faɗa mata magana” ɗaukarta ya yi kamar jinjira yana faɗin “manta da wannan mu je ki ji nayi matuƙar kewar ki” za ta yi magana ya manna bakinsa a kan nata ya kashe bakin maganar, ɗakin baccin su suka shiga da ƙafa ya rufe ƙofar.

Daga ranar komai ya wuce kamar babu abinda ya faru hakan ya ƙona zuciyar Halima ko kaɗan ba hakan ta so ba, amma abin takaici tun kan a je ko ina har sun shirya. Da ƙyar ta samu ya bata wayarta bayan ya ja mata kunne sosai. Ranar asabar bayan ya dawo masallaci sallah isha ya samu Zhara ce kawai a babban falon tana kallo “sannu da dawowa.”

“Yawwa sannu da hutawa” ya nufi ɗakin Halima yana faɗin “ki shirya za mu je gida Dady ya dawo” da fara’a ta ce. “Ai kuwa yanzu zan shirya.” Komai bai ce da ita ba ya wuce, ɗaki ta tafi zuciyarta ciki da fargaban haɗuwarta da Momy. Kwance ya sameta a kan gado “kar dai har kinyi bacci?” Buɗe idanunta da sukayi ja ta yi tana faɗin “shi ɗin dai nake ji da ƙyar na samu na yi sallah” cire kayan jikin shi ya suma yi “na dai gane yanzu kin zama ba mota bacci dai bacci ko ɗan fira kin daina yi da ni bare wata kulawa.”

Gyara kwanciyarta tayi cikin miƙa “ka yi haƙuri ai ba laifina ba ne laifin Babyn ka ne shi ne ya ke sanya ni kasala da bacci ko wani lokacin.”

Banɗaki ya nufa yana faɗin “haƙuri ai ya zama dole a sha bacci lafiya.” Har ya fito wanka ya shirya ba ta ko san ya fito ba, gyara mata kwanciyata yayi ya manna mata kiss a goshi. A falo ya sameta har tasa hijab ta na jiran shi “iyee duk ɗokin zuwa wajan Dadyn ne yasa ki ka shirya da wuri hakan” dariya ta yi tana faɗin “ba dole ba na jima ban gan shi ba, har Khadija ina kewarta ko sau ɗaya bata taɓa zuwa ta ganni ba.”

“Mene ne abin damuwa dan ba ta zo ba ba dai ni kina ganina koyaushe ba.”

“Uhm duk da hakan dai ina so na ganta.”

“Ai shi kenan yau za ki ganta, mu tafi” biyu bayan shi ta yi sun kai ƙofa ta ce. “Ina Halima ne ai na ɗauka tare za mu tafi.”

“Ta yi bacci ne shi yasa” ba ta sake cewa da shi komai ba har suka je wajan mota miƙo mata key ɗin motar ya yi “ga shi yau dai ke za ki tuƙa mu.”

“Tunda kana a gefena ai ba zan ji tsoron komai ba” ta faɗa da murmushi a fuskarta. Mai-gadi ya buɗe masu ƙofa ya raka su da addu’ar Allah ya kiyaye hanya. “Yaya” ɗauke idanunsa ya yi daga kan wayar sa “um sweet Baby.”

“Ni fa tsoro nake ji” dariya ya yi yana faɗin “dama na sani ai cika baki ne ni na rasa wani irin tsoro ne da ke da har kike kasa yin tuƙi duk da kin iya.”

“Uhm-um ni fa ba wannan nake nufi ba.”

“To mene ne me kike nufi?” Kallonsa ta ɗan yi kafin daga bisani ta mayar da kallonta ga hanya “kasan fa ba ni ce nake da girki ba kar wannan fitar ta janyo mana wata fitinar.”

Dora kansa ya yi a kan kafaɗarta kafin daga bisani ya ce. “Banga dalilin jin tsoro a kan abinda kake da gaskiya ba, da a tare za mu je ganin tana jin bacci ne yasa na ƙyaleta sannan dan girkinta ne meye a ciki idan har na fito da ke matata ce fa ba wata can daban ba, ku mata rigimar ku yawa ne da ita ko ranar girkin ki ne idan har fita ta kama nayi da ita zan ɗauketa na fita ba wani abun ba ne, dan haka ki kwantar da hankalin ki ki daina wani jin tsoro kinji ko” gyaɗa masa kai kawai tayi amma har ga Allah ta kasa samun natsuwa ta san halin Halima tsab za ta yi masu tijara.

“Ina neman alfarma don Allah idan mun je ko me Dady zai tambaye ki kar ki faɗa masa zuwan Momy gida da zancen karatun ki” murmushin haƙori da a ka ce ya fi kuka ciwo ta yi tana faɗin “sam ni ban kawo tunanin na faɗa masa ba, na sani ina matuƙar son karatuna amma Momy uwa ce ta isa da ni komai ta mini umurni zan bi cikin ladabi, hakan yasa na haƙura da karatun har cikin raina” gyara zamansa ya yi yana faɗin “Allah ya yi maki albarka, In sha Allah ahankali zan shawo kanta ta amince ki ci gaba da karatun ki” murmushi kawai ta masa.

Ba su samu kowa a falon ba sai tv da take a kunne wayar shi ta yi ringing “duba ko suna sama zan amsa wayar nan” ya faɗa yana daga kiran, cikin tsoro ta haura sama, ta duba ɗakin Momy ba ta nan ta duba ɗakin Khadija itama ba ta nan, saukowa ta yi zaune ta same shi yana waya riƙo hannunta ya yi yana tambayarta da idanu “ba kowa a saman” ta bashi amsa murya a ƙasa, haƙuri ya ba wanda suke wayar da alƙawarin zai kira shi zuwa anjima.

“Ba mamaki suna sashin Dady.”

A can suka same su an baje kaya Khadija na dudduba wa, a jiye rigar hannunta ta yi da sauri ta je ta rungumeta “oyoyo Zhara”

“Iyee sunanta gatsai babu ko Aunty” Hafiz ya yi maganar yana harararta, “a’a Hafiz barni da ita ai ba da ku take yi ba da ni take yi da take faɗar sunan tsohuwata gatsai, dan haka ba ni kayana nan na fasa bayarwa” fito da idanu ta yi tana faɗin “Wayyo Allana na tuba Dady” kai duban ta ta yi ga Zhara da take murmushi “yi haƙuri mumsin Dady” riƙo hannunta ta yi suka ƙarasa gaban Dady zama sukayi dab da shi, “ina wuni Dady, an dawo lafiya?”

“Lafiya lau Mamana fatan kuna lafiya, ba kuma wata matsala ko?” Haɗa idanu ta yi da Momy da take ta harararta sunkuyar da kanta ta yi tana faɗin “lafiya lau ba komai.”

“Kin tabbatar da babu komai idan har a kwai abin da a ke maki da ba daidai ba ki faɗa mini na yi wa abin tufka tun kan ya yi nisa” ji take kamar ta faɗa masa zancen karatun ta sai dai tunawa da maganar da roƙon da Hafiz ya yi mata yasa ta kawar da tunanin da fara’a a fuskarta ta tabbatar masa da babu komai Hafiz da ya zauna a kusa da Momy ya ce. “oh Dady ni to ba za ka tambaye ni ko a kwai abin a ke mini ba.”

“Mamana na tabbatar da ba za ta yi ma wani abun da zai ɓatama ba sai dai kawai ajizanci na ɗan adam, ita fa mai sunanta mace ce mai matuƙar sanyin hali, biyayya ga miji tun da muke da iyayenmu daidai da rana ɗaya ba mu taɓa jin Baffa ya furta wata kalmar marar daɗi ba koyaushe yabonta ya ke da faɗar kyawawan halayyar ta, saboda kyautatawa ga mijinta da haƙurinta koyaushe mahaifin mu ya kan ce Zhara’u ‘yar aljanna ce tun a duniya dugadugin ƙafafunsu a ɗage suke” ya yi shiru idanunsa a kan Zhara da murmushi a fuskarta ya ce yadda kika ci sunanta haka a siffa babu abinda kika bari komai na ku iri ɗaya tamkar antsaga kara. A wajan hali ma daidai gwargwado kina kamantawa, duk sanda na ganki na kan ji matuƙar farin ciki ki kan ɗebe mini kewar mahaifiyar mu.”

“Iyee ashe dai sak tsohuwa a ka ɗauko shi yasa ma muryar tsofaffi ne da ita.”

“Shi kenan ki tabbatar da kin rasa tsarabar ki har ma motar na fasa sauyawa.”

“Oh Dady aradun Allah na tuba wasa nake nima ai tana ɗebe mini kewar kakata ko kakus” ta ƙarasa maganar tana riƙo hannun Zhara “ke ko humm”

“Ni ai na zama mai sa’a tunda na samu mai halin Hajiya tsohuwa a matsayin mata uwar ‘ya’yana In sha Allah” kunya ta rufeta shi ko kunyar su Dady ba ya ji yake faɗar hakan, Dady har da biye masa yana sake jajjada masa lallai ya ƙara godiwa Allah. Wata kyakyawar ƙaramar akwati da take a gefen shi ya janyo ya ajiye gaban Zhara “ga tsarabar ki nan.”

“Oh Allah Dady duk ni kaɗai na gode sosai Allah Ubangiji ya ƙara lafiya da nisan kwana, Allah ya ƙara buɗi” ta yi maganar tana shafa a ƙwatin. “bari na buɗe maki ba yadda ban yi a bani ko dubawa ne nayi ba a ka ce ba z… Tsakn da Momy tayi ne yasa ta haɗiye sauran zancen dukan su suka zuba mata idanu “tun ɗazun kun damu mutane da magana a kan mutum ɗaya sai ka ce wata ‘yar gwal, sannan Alhaji in banda taya ɓera ɓari saboda Allah duka yaushe ne a ka yi mata kayan auren wanda na tabbatar da wasu kayan sai ta yi shekara ma kafin ta kai garesu bare har ta sa su” zuba mata idanu Dady ya yi kafin daga bisani ya ce. “Kuɗin ki ne ko kuɗina ne? Turai ba na son rigima fa.”

MIƙewa ta yi tsaye “kuɗin ka ne ba nawa ba ne kam, amma ɗa dai ai nawa ne ba kai kaɗai kake da haƙƙi a kansa ba ko? Sannan idan da adalci ai ba ita kaɗai ba ce matarsa bare har ka ba ta ita kaɗai” barin wajan ta yi tana ƙwafa har ta fita ta dawo tana faɗin “kai kuma ina jiran ka a ɗaki, da kai nake Hafiz” cikin sanyin jiki ya amsa mata da “to” girgiza kai Dady ya yi kafin daga bisani ya ce. “Ni ban san me yake damun Maman ku ba sam ba ta son gaskiya, duk yadda nake haƙuri da halayyar ta tana shirin ta kaini bango wallahi”

“Kayi haƙuri Dady za ta daina ne In sha Allah”

“Mtsw! Za ta daina yaushe kenan? Mutum yana girma amma yana cin ƙasa haba!”

Zhara ta kasa cewa uffan har a ranta ba ta ji daɗin hakan ba ina ma ba ta zo ba, ga shi zuwan nata ya haddasa ɓacin rai sai suka bata tausayi yadda suke ba shi haƙuri. Cikin ƙoƙarin kawar da zancen ya ce. “Ina ita Halimar ne da ba ku zo tare ba?”

“Da tare za mu taho ko da na dawo ta yi bacci.”

“Ba komai Allah ya yi albarka, ga ta ta tsarabar. Khadija ɗauko ledar da take a kan gado” da sauri ta ɗauko ta kawo wa Hafiz karɓa yayi yana godiya “to amma ni na ga tsarabar kowa banga tawa ba.”

“Goɗai-goɗai da kai ne za a yi wa tsaraba, a’a na riga da na yayeka ai ka barwa ƙannenka” shagwaɓi fuska ya yi “gaskiya ni dai ana nuna mini wariyar launin fata haba shi kenan ni an mayar da ni saniyar ware”

“Ai fa sai kayi idan kuma kana son wata jallabiyar ɗaya tal buɗe wadrop ka ɗauke ɗaya” nufar wadrop ɗin ya yi yana faɗin “wa a ke yi wa kyauta ya ƙi ai da babu gwada kaɗan duk dai ba hakan a ka so ba” dariya suka yi gaba ɗayan su. Sun jima suna fira a wajan Dady kafin suka yi masa sallama.

“Jirani a mota bari na yi wa Momy sai da safe.”

“Ni ma ban ma ta sallama ba ai” yana tafiya ya ce. “Tawa ta isar ma ki” ya ƙarasa maganar yana barin wajan dan gujewa wata fitinar yasa ya hanata zuwa, itama taji daɗin hanatan da ya yi. “Bari na tsaya na taya ki fira kafin ya fito” kallonta Zhara tayi tana faɗin “kin kyauta ai, wai ko sau ɗaya ba ki taɓa tunanin ki ce bari ki je ki ga gidana ba ko” dafa kafaɗarta tayi “kiyi haƙuri na so na zo ko da da satar hanya ne amma Momy tayi rantsuwar ba za ni ba, wannan ne yasa dole na haƙura amma dama ina so idan Dady ya dawo sai na yi masa magana, za ki ganni koyaushe ina sha Allah ”

“Ayya ba komai Allah ya kyauta”

“Amin, ni sai jiya nake jin wai Halima ta dawo gidan ki da zama a wajan Momy ma na ji “

“Eh ai tun kwana biyu da zuwana ne ta dawo”

“Sakarci wannan yarinyar sam ba ta san kanta ba wallahi, kuma ke wai sai ki ka ƙyaleta, da ni ce ke wallahi uban kuturu ma ya yi kaɗan” murmushi Zhara tayi tana faɗin “kai Khadija mene abin rigima, ai ba wani abun ba ne dan ta dawo, ni kaina na fi so mu zauna a waje ɗaya ai” za ta yi magana Hafiz ya ƙarasu fuskarsa a haɗe sai da safe suka yi mata ta juya zuwa cikin gidan tana jin ba daɗi a ranta na halin mahaifiyarta ta sani sarai ita ce ta ɓatawa Yaya Hafiz rai. A mota tana so ta tambaye shi meya faru sai dai tunanin bai kamata ta sa kanta a tsakiyar uwa da ɗanta ba kawai ta ja bakinta ta yi shiru, ta dai san gatanar gizo ba ta wuce ta ƙoƙi.

Tsaye suki a bakin ƙofar babban falon da mamaki ya kalleta ya na faɗin “ke ce kika rufe ƙofar nan?”
“A’a ni ko ɗakina ban sawa key ba bare wannan da take ta kowa da kowa” gyaɗa kansa ya yi yana buga ƙofar ko Allah zai sa Halima ta juyo su ta zo ta buɗe shiru Zhara ma ta buga amma ko motsi ba su juyo ba. “Ba a kwai key a wajan ka ba?”
“Duk suna ciki na bar su, waya kawai na fito da ita”

“To ya za mu yi yanzu tunda Halimar da alama baccinta ya yi nauyi?” Wayarsa ya ɗaga ya kira number Halima “bari na kira wayarta ko Allah zai sa ta ji” sai da kiran ya kusa tsinkewa sannan ta ɗaga tana meta “wai mene ne ne kun dameni da bugun ƙofa da kiran waya kawai ka hanani bacci cikin salama” cikin takaici ya ce. “Kenan dama kina ji ƙyale mu kawai kika yi kin kyauta ai, sai ki ta su ki buɗe mana.”

“Idan har zan buɗe to meye amfanin na rufe kenan.”

“Kenan ke kika rufe ƙofar?” Ya yi tambayar da mamaki a fuskar shi tsinki kiran tayi ransa ya matuƙar ɓaci sake kira ya yi sai dai ta kashe wayar, ba ta buƙatar ya faɗa mata ko me ya faru dan komai ta ji duba agogon wayarsa ya yi sha biyu har ta wuce “shi yasa na ji tsoro na dai san ba zai wuce fitar da muka yi a ranar girkinta ne ya janyo hakan ba. Komai bai ce ba ya ma rasa me zai yi.

<< Kuskuren Waye? 33Kuskuren Waye? 35 >>

1 thought on “Kuskuren Waye? 34”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×