Da ɓacin rai ya ɗauki Zhara a mota suka tafi tsohon gidan sa dama ba a ɗauki kayan da yake ɗakin shi ba. “wai sai mu kwana anan ɗin?” Ta masa tambayar idanunta a kan shi zama yayi gefen gado yana faɗin “hakan ta so ba sai a yi hakan ɗin ba.”
“Shi kenan ni zan kwanta a falo sai ka kwanta anan.” janyota yayi ta faɗo jikin shi “kin ma isa sai ki barni ni kaɗai” marairace wa ta yi “ba na so mu shiga haƙƙinta ne tunda ka ga fitar ce ta janyo komai” kwanciya ya yi rairan ya rungumeta a ƙarjin shi “na san abinda nake Baby, amma dai ba zan kwanta ni kaɗai ba tunda ita ce ta janyo hakan.”
Halima zuciyarta ta ƙara hawa lokacin da ta ji tashin motar su tashi ta yi ta zauna “wato ma sake fitar ya yi da ita, ya yi kyau wallahi sai sun gane kuskuren su!.” Komawa ta yi ta kwanta ranar sai bacci ɓarawo ne ya saceta.
Washe-gari tunda safe ya tafi asibiti saboda kiran gaggawan da a kai masa, ya bar mata motarsa shi ya hau acaɓa. Sai wuraren sha ɗaya ta rufe gidan ta nufi gida. Ba ta samu kowa a falon ba sai tv da take a kunne hakan yasa ta nufi ɗakinta kanta tsaye.
“Munafuka maciya amana ai dole kiyi tafiyar sussu tafiyar munafukai masu tafiya da masakin wuta a lahira tunda ba ki da gaskiya!!” Juyowa tayi tana kallon Halima da take tsaye daga bakin ƙofar ɗakinta murmushi tayi cikin tura haushi tana miƙa “ni banda lokacin ki dan yanzu a gajiye nake, bari nayi wanka na ɗan rage baccin da ban samu nayi a daren jiya ba sai muyi magana zuwa anjima.”
Tana gama faɗa ta buɗe ƙofa da sauri ta rufe ba tare da ta yarda Halima ta ƙara su wajanta ba tana dariya. Tsayawa tayi daga bakin ƙofar Zhara tana ihu “banza da ki tsaya idan ba tsoro ba, ai wallahi a kwai Allah sai kuma ya yi mini sakayya a kan abinda kuka yi mini!” Duk zage da masifar da take Zhara bata ko buɗe ƙofa ba bare har ta kulata. Haka ta wuni cikin ɓacin rai tana dakon jiran dawowar Hafiz.
Sai dare ya dawo ta same shi a ɗakin shi yana shirin shiga wanka ta zo da niyar masifa sai dai kallon da ya watsa mata yasa tayi laƙwas “amma abinda ka mini ka kyauta kenan?” Kamar ba zai ce da ita komai ba dan har zai shiga banɗaki sai kuma ya juyo fuska babu annuri ya ce da ita “tsakanin ni dake waye yayi rashin kyautatawa? Ni da gidana wai ki rufe mini ƙofa, da banda wani gidan da matsayina da komai sai dai na je hotel na kwana!”
“To amma ai kai ne ka janyo a kan me za ka ɗauke ta a ranar girkina ka fita da ita.”
“Shi zuwa gida gaida Dady shi ne laifi?”
“Idan har hakan ne meyasa ba a tafi da ni ba?”
“Saboda kinyi bacci wannan ne dalilin. Ina faɗa maki duk ranar da kika sake kwatanta yi mini irin wannan ɗanyin aikin wallahi Halima sai nayi maki hukuncin da ba ki taɓa tsammani ba!” bai jira jin me za ta ce ba ya yi shigewarsa banɗaki. Takaici ya cikata ‘wato ma adaki mutum a hanashi kuka.’
Duk yadda ya so haɗa kansu su zauna lafiya hakan ya ci tura, dole ya kawo na gani ya zuba masu, dukansu suna da kishi sai dai ita Zhara tana yin komai da hankali tana kuma gudun zuciyar Hafiz hakan yasa ba koyaushe take biyewa Halima ba, saɓanin Halima da yana gida ko bai gida sai ta tayar da rigima. Hafiz ya yi wa Momy wayo da cewar Dady ya tambaye shi dalilin rashin zuwan Zhara makaranta wanda malamin su ne ya kira ya tambayi dalilin, dan haka yake riƙonta da ta amince Zhara ta koma makaranta, ba dan ranta ya so ba ta amince dan ba za ta so Dady ya gane ita ce ta hana ba ta sani sarai ba za ta masu kyau ba a tsakanin ita da shi. tunda ya faɗawa Zhara ta dinga farin ciki kamar za ta haɗiye shi dan daɗi, Husna ta fi kowa nuna jin daɗinta na dawowar ta makaranta. Bayan ya dawo daga wajan wata jana’iza na maƙocinsu da ya rasu yana shirin fita zuwa asibiti Halima ta shigo ɗakin Zhara da mamaki ya kalleta “lafiya?”
“Dan na shigo wajanka ne kake tambayata lafiya? To ita ce ta kawo hakan”
“Dole na tambaye ki dan dai yau ba girkin ki ba ne sannan kuma bai kamata a ce kin shigo har turakarta ba wanda na tabbatar da idan ke ce aka yi wa hakan tashin hankalin da za ki yi sai sama da ƙasa ma sun girgiza.”
Zhara da take buɗe ƙofar banɗakin ta ce Sweet Baby na haɗa ma ruwan wank… Shiru tayi tana mamakin dalilin shigo mata har uwar ɗakinta, kallon ƙasa da sama Halima tayi mata sanye take cikin rigar bacci iya guawa ƙirjinta duk a waje, tsaki tayi tana mai kawar da kanta murmushi Zhara tayi a ranta tana faɗin ‘wallahi sai nayi maki abinda gobe ko da kuɗi a ka ce ki shigo mini ɗaki kanki tsaye ba za ki yi ba.’
“Wai mene ne kin sa mu gaba da kallo me ya faru?”
“Dam… Rungumar da Zhara tayi wa Hafiz ne yasa ta kasa ƙarasa maganar sai ma sakin baki da tayi tana kallon su Zhara tana wasa da sajen fuskarsa ta ce. “Ka manta da ana jiran ka mu je na ma wankan.” kalar wasan da take masa hakan ya hanashi kuzarin yin magana har suka shiga banɗakin suna maƙali da juna, dariyar su ta dinga juyowa daga banɗakin “za ki sa na kasa fita fa Sweet Baby” abinda kunnenta ya iya juyo mata kenan ta bar ɗakin a zuciye.
Kwance ya sameta a kan gado tayi rigingini zama yayi gefenta yana gyara mata kwamciya “mai juna biyu ba a so ta yi irin wannan kwanciyar ki daina kinji ko Baby.”
Janye jikinta tayi daga gare shi tana turo baki “mene ne kuma?”
“Saboda kawai na je ina so za mu yi magana shi ne da kai da matarka za ku wulaƙanta ni.”
“Uhm! Kin fiya anyi ance Baby, tsakani da Allah bai kamata ki shiga har ɗakin baccinta ba wanda na tabbatar da idan har ke aka yi wa abinda za ki yi har sai yafi hakan. Shi kenan dai kiyi haƙuri wace magana ce kike so ki faɗa mini sauri nake ana jirana” gyara kwanciyarta tayi tana turo baki “kawai kayi tafiyar ka na fasa” miƙewa yayi tsaye bayan ya mata kiss a goshi “na tafi ki kular mini da kanki da kuma Babyna” ko kallonsa bata yi ba har ya fita.
Kiran waya ne ya tashe shi daga bacci sanda yaga mai kiran gabansa ya bada dum! Ɗaga kiran yayi idanunsa a kan agogon da yake manne a kusurwar ɗakin ƙarfe biyun dare “lafiya?”
“Cikina ke ciwo mutuwa zanyi Baby!” Ta ƙarasa maganar cikin kuka da sauri ya sauka daga kan gado Zhara ta buɗe idanunta cikin bacci ta tambaye shi me ya faru yana tafiya ya bata amsa da sauri ta sauko daga kan gado ta biyu bayan shi. A tsakiyar falonta suka sameta tana riƙi da ciki tana muƙurƙusa riƙota yayi ta kwanta a jikin shi tana kuka “sannu za ki iya tashi ki sauya kaya mu tafi asibiti?”
“A’a ni ba zan iya tafiya ko ina ba, ka bari zuwa safe dai mu ga ni”
“Ba zaiyu ki zauna da ciwo a gida ba, Zhara taimaka ki ɗauko mata kayanta” ta amsa masa da to, ta tafi ɗauko kayan, ƙara bajewa tayi a jikin shi tana mayar da numfashi shafa bayanta yake yana yi mata sannu cikin nuna kulawa da tausayi. “Sannu Halima, ga kayan.”
“Don Allah ka ƙyaleni zuwa gobe yanzu ya fara lafawa da na motsa ciwon zai iya tashi.”
“Uhum! Shi kenan Allah ya ƙara sauki bari na kai ki ɗaki” ƙara shigewa tayi jikinsa tana magana cikin muryar marar lafiya “ni dai a’a ka barni a hakan ban so na motsa ko kaɗan sai ciwon ya ƙaru” zuba mata idanu tayi tana zancen zuci ‘dama jikina ya bani ciwon nan na ƙarya ne wato ni za ta nunawa kissa, ai kuwa na fita iya iskanci wallahi’ maganar Hafiz ta dawo da ita daga zancen zucin da take “idan ba damuwa na kwana anan tunda kinga uzuri ne na ciwo” murmushi tayi kafin daga bisani ta ce. “Haba ba komai wallahi ai ciwo ya share komai” sai da safe tayi masu ta tafi ɗakinta.
Washegari har ta haɗa masu karin kumallo basu fito ba, ta kira wayar shi bai ɗaga ba ga shi ƙarfe tara za ta shiga aji duba agogon da yake manne a kusurwar ɗakin tayi 8:25 gyaɗa kanta kawai tayi taje ta shirya ranta a matuƙar ɓaci har kusan tara basu fito ba hakan yasa ta ɗauki mukullin motarta da ya saya mata wacce bata taɓa fita da ita ba sai shi ne wani lokacin ya kan fita da ita ta bar gidan ko karin kumallo bata yi ba. Buɗe idanunsa ya yi yana miƙa Halima da take zaune gaban madubi tana kwalliya ta kalleshi ta madubi “Sannu da tashi My Heart” tashi ya yi yana sauko da ƙafafunsa ƙasan gado idanunsa a kan agogo “kai har 11 ta wuce me yasa ba ki tashe ni ba?”
“Yi haƙuri ba na so kanka ne ya yi ciwo shiyasa ban katse ma baccin ba” “Innalillahi wa Inna ilahi raji’un!” Ya yi maganar yana riƙi kansa tare da miƙewa da sauri, da sauri ta sha gabansa “lafiya me ya faru?”
“Zhara ce za ta tafi makaranta ta faɗa mini 9 za ta tafi” tsaki tayi ciki-ciki a zuciyarta tana faɗin ‘kawai ya wani tsoratani a banza.’ bayan ya fita ta koma ta zauna tana ƙarasa shirinta tana jin zuciyarta fis ko ba komai yau ta san ta baƙanta ran Zhara, shiyasa asuba nayi ta dinga murƙusun ciwo sai a ɗakin yayi sallah asuba da hakan ta dinga jan shi har bacci ɓarawo yayi awon gaba da shi. Dawowa yayi ɗakin jiki a sanyaye ya duba wayarsa yaga ta masa kira kusan biyar ajiyar zuciya yayi “ki dinga tashina bacci matuƙar kin san ranar ina da fita aiki, ko Dr Mansur ya mini kira ya kai uku kuma a maimakon ki ɗaga sai kika ƙi.”
Bayansa ta dawo ta tsaya ta kwantar da kanta a bayan shi tana marairace fuska “ba fa laifina ba ne kasa wayar slin ne fa, amma dai zan kiyaye kayi haƙuri” kansa kawai ya gyaɗa mata ya shiga banɗaki. A gurguje ya shirya yana sanya agogo a hannunshi ta ce. “Wai tafiya za kayi ba ka karya ba?”
“Jirana ake yi, tunda kin shirya ki zo mu tafi tare asibitin.”
“A’a kawai ka tafi ai na ji sauƙi sosai ciwon ya lafa” idanunsa a kanta ya ce. “Kin tabbatar” gyaɗa masa kai ta yi alamar eh, “shi kenan Allah ya ƙara sauki.” Rakashi tayi mota bayan ya fita ta dawo tana rawa zuciyarta fal da farin ciki.
Kai tsaye makarantar su Zhara ya fara tafiya ya samu tana cikin aji suna karatu ga shi tun a gida yake ta kiran wayarta amma bata ɗauka ba. Hakan ya juya zuwa asibiti dole saboda kiran da ake tayi masa a asibiti. Suna tashi makaranta tabi Aunty Husna gidanta sai bayan da aka yi la’asar sannan ta bar gidan. A falo ta samu Halima kwance jikin Hafiz “My Heart ni dai zan bika idan za ka taf” sallama kawai tayi ta wuce ta gaban su har za ta shiga ɗaki ya jeho mata tambaya “ina kika fito? Dan na je lokacin tashin ku ba kya makaranta.”
“Gidan Aunty Husna na biya” ta ba shi amsa ba tare da ta juyo ba tare da shigewa ɗaki da sauri. Janye Halima yayi daga jikin shi yabi bayan Zhara, Halima ta je wajan ƙofa ta kara kunnenta. Tsayawa yayi gaban Zhara da take ƙoƙarin cire kayan jikinta fuskarsa babu annuri, “da izinin wa kika tafi gidan Husna?”
“Hum! Kayi haƙuri na kira ka kafin na fita ba ka ɗaga ba, kuma na bar wayar a gida shi yasa” nuna ta ya yi da ɗan yatsa “karki kuskura ki sake zuwa wani wajan ba tare da kin faɗa mini ba, idan kuma ba hakan ba ranki in yayi dubu sai ya ɓaci!” Sarkafi dogowar rigarta da ta cire tayi tana faɗin “In sha Allah ba za a sake ba” daga hakan ta shige banɗaki. Halima ta bar ƙofar ɗakin cikin jin haushi dan ba hakan ta so abin ya tsaya ba.
Ta fito wanka ta same shi a zaune bakin gado ta tsaya gaban madubi tana sharci ruwan jikinta da ƙaramin tawol rungumeta yayi ta baya yana shinshinar ƙamshin jikinta kasancewar da turaren wanka take wanka, “kiyi haƙuri bacci ne ya mini nauyi shiyasa ban fito da wuri ba, kuma wayata na barta a silent shiyasa ban ji kiran naki ba.”
Murmushin haƙori tayi da yafi kuka ciwo “ni ka daina ba ni haƙuri ai ba na ce ka yi laifi ba ne” juyo da ita yayi suna kallon juna “nima ba na ce kin ce ba ne ai, sai dai na san wacece Zharana. Kiyi haƙuri kin ji Sweet Babyna” shigewa tayi jikin shi ta kwantar da kanta a ƙirjin shi ba tare da ta ce komai ba, murmushin jin daɗi yayi ko ba komai hakan da tayi ya tabbatar masa da ta haƙura.
Ranar asabar kasancewar ba ranar girkinta ba ne bayan ta gama lazumanta na safe ta koma ta kwanta bacci, har Hafiz ya shigo ya fita bata sani ba. Sai wuraren sha biyun rana ta tashi, wanka ta fara yi bayan ta shirya ta fito falo kai tsaye dinning ta nufa wayam babu komai juyowa tayi zuwa falo ta kalle Halima da take kallo ta ce. “Ya banga komai a dinning ba.”
“Iya cikina da na mijina na dafa, dan ba baiwa ce ni ba da za ki kwanta kina bacci na girka miki abinci ba.”
“Shi kenan bari Yaya Hafiz ɗin ya dawo zan faɗa masa dan na gaji da wannan halin naki da kike mini duk ranar girkin ki in dai ba shi ne a gidan nan ba ba za ki bani abinci ba, sannan kuma an hanani shiga kichin sai dai nayi ta ɗirkar kayan fulawa da lemo a ɗaki. To na gaji wallahi bari ya dawo a san yadda za a yi dan ba zan yarda amini kisan mummuƙe ba!”
“Ko uban Hafiz za ki faɗawa ki je ki faɗa masa wallahi nafi ƙarfin ki” ido buɗe take kallonta da tsananin mamaki “kika ce me?”
“Ba buƙatar sai na maimaita dan ba kurma ce ke ba sarai kin ji me na faɗa” cakumar wuyan rigarta Zhara tayi “ke iskanci naki ya shallake kan kowa har ya dawo kan ubana!” Cire hannun Zhara tayi daga wuyanta tana dariya “oh ni Halimatu yau naga yadda kuɗi suke sa ake ado da uban wasu, ko da yake ba abin mamaki ba ne kuɗi ai ba abinda basa sawa a duniyar nan dan kin manta tsohon ki da yake faƙiri kin riƙi uban w… Marin da tayi mata ne ya sa ta haɗiye sauran zance kallonta take da tsananin mamaki a fuskarta “bala’i! Kika mareni, wallahi kuwa sai kin sani dan ba za ki mari banza ba!!” Ta kai hannu za ta rama Zhara ta kauce ta kamata da kokuwa ingijeta tayi ta faɗi gefe tana faɗin “kin san babu abinda za ki iya ɗauka a jikina, kawai ba zan biye maki ba ne saboda abinda yake jikin ki.”
Ta riƙi kwalar rigarta tana faɗin “ina mai ja ma ki kunne da ki iya bakin ki zan iya jurar komai amma banda taɓa mini martabar iyayena. Ina faɗa maki da babban murya ki iya bakin ki!”
“Yanzu na dawo gida za mu yi waya anjima ko kuma mu haɗu asibiti da yamma” tana jin muryar shi ta sa ihu tana riƙi cikinta firgice ya ƙarasa shigowa ya samu Zhara tana ƙoƙarin janye hannunta jikin Halima.
Fulani