Hannu tasa tana share hawayen fuskarta tana ƙoƙarin haɗiye kukan da ƙyar ta iya danni kukan da take ta tura ƙofa cikin sa’a ta samu ƙofar a buɗe, kutsa kanta ta yi ciki ta tarar da Zhara na bacci tausayinta ya cika ma ta zuciya da sauri ta juya tana tushe bakinta ta fito ɗakin tana kuka. Ɗakinta ta koma ta kira wayar Anwar tana kuka ta faɗa masa abin da yake faruwa ta ƙara da cewa “ba zan iya faɗa ma ta ba don Allah ka zo da kan ka” cikin kaɗuwa ya ce. “gani nan zuwa yanzun nan zan zo.” Jifar da wayar ta yi a kan gado ta zauna diɓis a kan gado “Wayyo Allana Abba ya rasu shi kenan ba za mu sake ganin shi ko jin muryarsa ba bawan Allah mutum mai haƙuri da faran-faran da jama’a.”
A waje ya yi pakeng ɗin mota ya tura ƙaramar ƙofar ya ji ta a rufe ƙwankwasa ƙofar ya yi da sauri mai-gadi ya buɗe ƙofar yana faɗin “waye ne?” Turus ya yi a bakin ƙofar yana kallon Anwar “a she kai ne sannu da zuwa.”
“Yawwa, ba ni hanya zan shiga ciki.”
“Ka yi haƙuri ranka ya daɗi wallahi Hajiya Mahaifiyar Maigida ta yi mini umurnin kar na barka ka shiga gidan nan.”
“Ita Momyn ce ta faɗa ma hakan?”
“Eh ranka ya dade”
“Mtsw! Ba ni hanya don Allah”
“Ka yi haƙur… “Wai za ka ba ni hanya na wuce ko kuma so kake na rufe idanuna na daina ganin wannan furfurar kan na ka na yi ma rashin mutunci!” Babu shiri ya kauce ya ba shi hanya da sauri Anwar ya wuce shi yana yin tsaki. “Ya Allah ka fitar da ni wannan cakwakiyar” mai-gadi ya yi maganar yana rufe ƙofa. Jin motsin buɗe ƙofa ne ya fito da Halima “ina Zharan take ne?”
“Tana ɗaki bacci take”
“Kira ta, amma don Allah kar ki yi abin da zai sa ta gane abin da ya faru” kanta kawai ta gyaɗa. Har yanzu tana inda ta sameta a kwance tana bacci. Buga ƙafafunta ta yi tana faɗin “Zhara, Zhara” buɗe idanunta ta yi cikin mamakin dalilin shigowar Halima ɗakinta in dai ba wata kuma fitinar ce ta kawo ta da uwar safiyar nan ba. Tashi ta yi ta zauna tana faɗin “mene ne?”
Kanta a sunkuyi ta ce. “Anwar ne ya zo yana falo yana jiran ki”
“To” ta amsa mata da mamakin yadda Halima take magana cikin sanyin murya. Hijab tasa ta fito ta samu dukan su suna a tsaye da murmushi a fuskar ta ta ce. “Yayana kai ne da safen nan, ina kwana” cikin ƙoƙarin ɓoye damuwa ya amsa mata gaisuwar yana faɗin “Hafiz ne ya turo ni ya ce na ɗauke ko zan kai ko duba wani abokin mu da bai da lafiya”
“To bari na yi sauri na yi wanka”
“Da dai kin zo mun tafi dan so nake mu dawo da wuri ina da aiki da yawa a office” cikin sanyin jiki ta ce. “To bari ko kaya ne na canja” ta shiga ciki Halima ma ta je ta sauya kaya kusan a tare suka fito Mai-gadi ganin sun fito tare yasa bai ce da su komai bayan addu’ar Allah ya tsare hanya. Sun kama hanya ta ce. “Don Allah Yayana ka kashi AC nan sanyi nake ji sosai tun jiya ko fanka sai da na kashi” komai bai ce da ita ba sai kashewar da ya yi. Duk da taga sunyi tafiya mai nisa hakan baisa ta yi magana ba sai da taga garinsu fa aka nufa ta kalle Halima da ta ɓoye fuskarta cikin Hijab mai fasmat ta mayar da kallonta ga Anwar da yake tuƙi “wai Yaya na ga kamar kafancan za mu tafi”
“Eh can za mu a can yake, ai kin san Nuraddin ko?”
“Oh na gane shi”
“Shi ne to bai da lafiya” cikin sanyin jiki ta amsa masa da addu’ar Allah ya sawwaƙi, sai dai sam ta kasa jin natsuwa ji take kamar suna ɓoye ma ta wani abun “aramini wayar ka na kira Abba na faɗa masa za mu shigo” duba wayar ya yi a gaban mota bai ganta ba ya ɗan kalleta kafin daga bisani ya mayar da dubansa ga hanya yana faɗin “ina ga fa na manta wayar a gida garin sauri” ba ta sake cewa komai ba sai jingina bayanta da ta yi jikin kujera haɗi da lumshi idanunta. Cincirindon mutane ta gani tsaye a ƙofar gidan su wasu kuma suna alwala kallon Anwar ta yi firgice saurin kawar da kanshi ya yi Halima ta fashe da kuka hannunta na rawa ta buɗe ƙofa fitowa ta yi da gudu ta shiga cikin gidan da yake ciki da mara ana ta kuke-kuke durƙushewa ta yi a tsakiyar gidan tana kallon mutane ɗai-ɗai ta kasa ko da motsa ɗan yatsanta Halima da Yaya Fati suka riƙota zuwa falon Abba “sai haƙuri Zhara Abban ki lokaci ya yi” Mama da ‘yan biyu suna zaune gaban makarar da gawar take ciki “Abba Innalillahi wa Inna ilahi raji’un, allahumma ajibni fi musibati wa ajibni khairan Minha!!! Mama ta taso daga wajan da take rungumota ta yi jikin ta “kiyi haƙura Zhara yau mun rasa Abba shi kenan ya tafi ya bar mu wanda ya fi mu son shi ya ɗauke mana innalillahi wa Inna ilahi raji… Kuka ya sarƙi muryarta ta kasa ci gaba da magana “ku daina kukan nan addu’a ita ya fi buƙata a wajan ku ku yi hakuri dukan mu mu yi haƙuri” abokin Abba ya yi maganar yana mai ficewa da sauri saboda kukan da ya zo masa. Da ƙyar ta iya matsawa gaban gawar shi ta yayi mayafin da aka lulluɓe shi da shi fuskarsa da annuri kamar za ta kira shi ya amsa mata “Allah ya jiƙan ka Abba Annabi yasan da zuwan ka, Allah ya gafarta ma.”
“Bismillah ku shigo mu ɗauke shi” Baban Halima ya yi wa wasu mazan magana suka shigo a ka ɗauki makarar faɗuwa tayi a wajan tana birgima “Wayyo Allah! shi kenan wai da gaske tafiya za su yi da shi ba zan sake ganin ka ba, ba zan sake jin muryar ka ba Abba! Mama mun shiga uku Abba ya tafi ya barmu Allah me yasa ka mana haka!!” Halima ta rungumeta tana kuka “ki daina Zhara don Allah ki daina faɗar hakan.”
Bayan sallah Isha tana zaune a kan darduma gefen Mama tana jan cazbi Aunty Laila ta kawo mata shayi mai kauri tana faɗin “don Allah Zhara ki daure ki sha gaba ɗaya wunin yau babu abin da kika sa a bakin ki”
“Aunty Laila ba zan iya ba ko na sha ba zai wuce mini ba, ba na jin daɗin komai ina ma nima na mutu, rayuwa ba za ta mini daɗi ba idan babu Abba” ta kife kai jikin Mama a ka rasa mai lallashin wani. “tabbas idan a ka ce kayi haƙuri wani abu mai girma ka rasa, sai dai wannan kukan ba zai dawo mana da Alhaji ba mun riga da mun rasa shi babu abinda yake buƙata daga gare ku sama da addu’a ita ce soyayyar da za ku nuna masa. Don Allah ku yi haƙuri, karɓi ki sha Laila haɗawa Maman ta su ita ma”
“To” Laila ta faɗa tana mai ficewa ɗakin, “ungu Zhara sai ana danni zuciya, ko dan abinda yake cikin ki ki daure ki sha kin ji ko” karɓa ta yi ba tare da ta ce komai ba ta kai bakinta da ƙyar ta sha rabin cop ɗin ta ajiye. Halima ta shigo ɗakin ta zauna a gabanta idanunta na zubar da hawaye bayan hannunta tasa tana share hawayen ta ce. “Zan tafi gida, da safe zan dawo”
“Na gode”
“Na tafi Mama”
“Sannu Halima mun gode.”
Mama na ji matuƙar tausayin Zhara, mutuwar nan ta girgiza ni, na ji tsoron rayuwar nan rai ba a bakin komai ya ke ba” ajiye fitilar hannun da take gyarawa ta yi tana faɗin “dama ba mu ne muke ta hauka ba Halima mene ne rayuwa yanzu a kwai ka anjima a ji babu kai. Shi fa ya dawo ne da niyar cin abinci rana ahanyar ce babbar mota ta taka shi, ko da a ka tafi asibiti rai a hannun Allah, wallahi da yamma muka tafi duba shi abin tausayi gaba ɗaya fuskarsa ta dame bai san waye a kansa ba, cikin dare ya amsa kiran Mahalacci. An kira Zhara an kira ki ba a samu ba, babu rabun za ta gan shi a rayen sai dai ta tarar da namansa. Ga sirikin na ku har shi Hafiz ɗin an kasa samun su a waya”
“Innalillahi wa Inna ilahi raji’un! Nayi da-na-sanin abin da na aikatawa Zhara, tayi iya ƙoƙarin ta wajan ganin ba mu samu saɓani ba amma sam na kasa fahimtarta na biyewa zuciya da shaiɗan. Ko jiyan ni ce na yi sanadin da a ka kasa samunta” ta faɗawa Mama abin da ya faru Aunty Laila da ta idar da Sallah Isha ta juyo tana kallonta da takaici “wallahi kin ji haushi ni ko wani ne ya zo ya ce za ki yi wa Zhara hakan anan take zan ƙaryata shi, amincin da a ka gina tun yarinta har za ki bari kishi ya yi silar ruguza wannan kyakyawar alaƙar taku. Kina jinta fa Yaya.”
“Humm ni ai Laila na ma rasa me zan ce, kowa dai yayi da kyau kansa, in kin bi duniya a sannu ta zo maki a sannu idan kin zo ma ta da garaje ahakan dai za ta zo maki. Nayi faɗa nayi nasiha amma abanza dan haka ni na kawo na gani na zuba ma ki duk abin da kike ji ko ganin shi ne daidai sai kisa himma kiyi!”
“Ku yi haƙuri wallahi na gane kuskurena zan kuma neme gafararta da yardar Allah ba zan sake ƙuntata ma ta ba, ba zan sake neman ta da fitina ba.”
“Da dai kin taimaki kan ki wallahi, Allah na tuba mene ne kishi a ma ka kishiyar da ba ka san halinta ba shi ne tashin hankali, amma wacce kuka fi kowa sanin juna me za ta yi mene ne ba za ta yi ba duk kin sani to me zai sa ki ɗaga hankalinki ki dinga yi mata bita da ƙulli” aikuwa da mijin Aunty Laila ya yi ta fito ya katse masu maganar ta masu sai da safe. Bayan tafiyarta ne ta je ɗaki ta duba jakarta dan ɗauko waya babu waya ta fito tana faɗin “Mama ba ni aron wayar ki na yi wa Hafiz magana na manta wayata a gida”
“Wayar ba ta da caji tun safe take a kashe ina ga ma ki ce nayi wayar ƙarshe da ke ta kashe kanta, kwana biyun nan muna fama da rashin wuta” komawa ta yi ta zauna tana tunanin ta ya za ta samu ta yi waya da Hafiz.
Zhara da take kwance a jikin Mama ta ce. “Mama an faɗawa su Dady?”
“An kasa samun wayarsa, amma Anwar da yamman nan ya zo ya ce ya bar wayarsa a gida dan haka zai koma Kano dan ya faɗa masu susan abin da ake ciki”
“Ni tunda muka zo ma ban sake saka shi a idanuna ba”
“Ko da ya zo kina daƙi kina sallah. Uhm! Jiya kamar wannan lokacin yana gama cin abinci yake maganar ki ya ce ya yi kewar Mamansa dole zai shirya ya je ya duba ki har nake yi masa tsiyar ba ya kunyar ki kina ‘yar farin, ya ce a’a shi Mamansa zai je ya ga ni kar na wani kawo masa wani karatu can, har wayar ki ya yi ta kira ya kasa samun ki” kamar ta faɗa mata abin da ya faru sai dai tunanin kar ta ƙara mata wata damuwar bayan wacce take ciki yasa ta ce. “babu ntwrk ne shi yasa, ashe babu rabon zan ji muryarsa ko ƙara ganin shi, zan yi kewar Abba” ta fashe da kuka. Kasa bacci tayi hakan yasa ta ɗauro alwala ta fuskanci gabas.
Ranar da a ka yi addu’a uku da yamma Halima ta shiga ɗakin Zhara ta samu tana zaune a kan darduma tana jan cazbi zama ta yi kusa da ita idanunta a kasa “ya ƙarin haƙurin mu”
“Da godiya”
“Allah ya jajjada rahamar sa a gare shi”
“Amin na gode” daga hakan babu wanda ya sake yin magana sai can ta ɗan gyara zamanta tana faɗin “ina mai ba ki haƙuri a kan kuskuren da na yi ma ki a baya tabbas nayi da-na-sani don Allah ki yafe mini.”
“Humm ni ban taɓa riƙon ki a raina ba, kawai idan da abin da ya mini ciwo nake kuma jin ba zan iya mantawa ba sawa da kika yi aka karɓe mini wayata sanadin hakan na kasa jin muryar Abbana har ya tafi inda ba zan sake ji ko ganinsa ba, sai dai na haƙaitu baya a cikin ƙwaƙwalwa ta”
“Wallahi ba ni ce nasa Momy ta karɓe wayar ki ba hasalima ban san dalilin zuwan na ta ba har sai bayan da ta karɓe, wallahi nayi nadama ki yafe mini” share hawayen da suka zubo mata a fuska tayi tana faɗin “Allah ya yafe mana gaba ɗaya.”
“Na gode, Anwar ya kira wayar Baba ya ce na ba ki haƙuri na rashin dawowar sa, ko da ya koma ya samu Mamansa ciwonta ya tashi yanzu haka suna asibiti” cikin jimantawa ta ce. “ayya ba komai Allah ya ba ta lafiya.”
“Wai kuwa kun samu Hafiz, ni dai na kira shi da wayar Baba ba tayi na masa magana wtspp baya online” gyaɗa kanta ta yi tana faɗin “har yanzu ba mu same su ba daga shi har Dady, har na fara jin tsoro ma.”
“To Allah yasa lafiya, shi ma Anwar hakan ya ce, amma ya ce a kwai wani abokin Hafiz da ya sani da yake zaune a can zai neme shi ya ji” komai ba ta ce da ita ba baya da gyaɗa kan da tayi. Tashi tayi tana faɗin “gobe da safe zan tafi Kano saboda jibi zan je asibiti wajan awo”
“Allah ya tsare hanya, na gode.”
Washegari da yamma suna zaune tsakar gida Husaina na wanke-wanke Mama ta dubi Zhara da take gyara wa Hasan maɓallin rigarsa “wai yaushe za ki koma gida ne?”
“Sai Yaya Hafiz ya dawo”
“Wai ki zauna anan ɗin har tsawon wata uku? Ina ba zai yu ba mijin ki bai sani ba ki zauna idan kin san hakan za ki yi me yasa baki faɗa masa tun kan ya tafi ba. Ki shirya jibi ki koma ɗakin ki” juyowa ta yi tana kallon Mama “don Allah kar ki ce dole sai na koma Mama kar kuma ki tambayeni dalili, idan har kika tilastani komawa zan koma amma ba mamaki labarin mutuwata ya riskeki a sanda ba ki yi tsammani ba” tana ƙarasa maganar ta shige ɗaki. Shiru tayi tana nazarin maganar Zhara tabbas a kwai abin da take ɓoye mata, tana cikin tunanin kamar daga sama ta shigo gidan kallonta Mama ta yi har ga Allah ba ta yi tsammanin ganinta ba, “sannu da zuwa Hajiya Turai ga wuri ki zauna”
“Ba shi ya kawo ni ba, ya dai hasahi Allah ya gafarta masa”
“Humm to Amin mun gode Allah ya ba da lada” kallon gidan ta shiga yi tana yatsinar fuska kafin ta dawo da kallonta ga Mama tana faɗin gida na zo a ba ni”
“Gida za a ba ki kamar ya ban fahimta ba”
“To bari na yi ma ki gwari-gwari wannan gidan kin san dai ba na ku ba ne gidan Alhaji ne ko?” Miƙewa Mama tayi Zhara da ta jiyo muryarta ta fito da sauri ta tsaya daga bakin ƙofa, “tabbas gida a da na Alhajin ki ne ya ce mu zauna a ciki Abba ya so ya sai gidan Alhaji yayi faɗa a cewar sa komai nasa na Abba ne babu cinikayya a tsakaninsu a gaban ki a gabana a ka yi komai Alhaji ya ɗauko takardun gida ya mallaka mana a matsayin gida ya zama mallakin Abba, kinga kenan ba ki da hurumin karɓe mana gida”
“Ni kuwa nake da wannan hurumin domin kin sa ni sai dai idan kin ƙi gaskiya aro ya ba ku ba kyauta ba, dan haka nasiha ɗaya zan ma ku ga mota can na zo da ita za ta kwashe duka komatsan tsumukaran kayan ku ta kaiku duk in da kuke so amma wannan gidan dai ko awa ba za ku ƙara a cikinsa ba!”