A zuciye Zhara ta ƙarasa gabanta tana faɗin “wai ke wace irin zuciya ce da ke? Mun yi rashi ba ki zo kin mana ta’aziya ba, a lokacin da muke cikin jimami sai ki zo ki neme ƙara mana wata damuwar saboda ba zuciyar musulunci ne da ke ba ko me!?”
“Kar na sake jin bakin ki Zhara” ɗagawa mama hannu tayi tana faɗin.
“A’a barta ta nuna mini kalar tarbiyar da kika yi mata. Wato ni uwar mijin na ki za ki yi wa rashin mutunci saboda ba a ba ki tarbiyar ƙwarai ba ko, to daga yanzu ni uwar Hafiz na sa almakashi na datsi igiyar auren ki da Hafiz, gida kuma dole sai kun bar shi yanzun nan ba sai anjima ba!”
“Innalillahi wa Inna ilahi raji’un! Na roƙe ki da ki barmu mu ji da abin da ya same mu Turai kar ki ce za ki ƙara ɗora mana wani nauyin bayan wanda yake tukare da zuciyar mu, ki bari Maigidan na ki ya dawo sai a yi magana” juyawa ta yi ba tare da ta ce da ita komai ba ta fice. “Ni na rasa wace irin kalar ƙiyayya ce matar nan take yi mana koyaushe burunta taga mun tozarta.”
“Humm ni me zan ce Zhara ita ta ta kalar zuciyar kenan, tunda ni dai tun zamana da ita babu wani abu na rashin kyautata wa da nake yi mata kawai dai kishi ne na matan sauri da yadda Inna mahaifiyar su Abban ku ta nuna mini so da ita har ‘ya’yanta saboda irin yadda nake kula da ita tamkar wacce ta haifini bayan wannan babu wani dalili na ta na ƙiyayyar da take mini wacce ta shaf… Kasa ƙarasa maganar ta yi ganin Hajiya Turai da wasu zaratan gabza-gabzan maza su huɗu sun biyu bayanta “yawwa duk wani abu da yake gidan nan ku kwashe kusa mota, idan suka kawo ma ku tsaiko a aikin ku ni na ce kuyi masu abin da kuka ga dama!”
“An gama Hajjaju makkatu” ɗaya daga cikin mazan ya yi maganar. Zhara ta tari ƙofa tana faɗin “babu gardin da ya isa ya shigo mana gida har ɗakin baccin mu wallahi!” Bangajeta ya yi ta faɗi ƙasa riƙi mararta tayi “Wayyo cikina Mama!” Ɗagota ta yi tana yi mata sannu “ba na ce ki yi shiru ba, kin ga ba ke kaɗai kike ba don Allah kar ki sake yin magana, tayi duk abinda take jin shi ne daidai a duniya ba matabbata ba ce za ta tafi in da ya je ɗin” ‘yan biyu suka rungume su suna kuka ganin yadda ake ta fito masu da kaya a wulaƙanci.
Maƙota suka fito suna tambayar ba’asi Momy ta watsa masu kallon banza tana “faɗin masu gida ne suka zo karɓe gidansu ko da akwai abin da za ku yi?”
“Amma dai gaskiya ba ki da imani duka kwana nawa da rasuwar Alhaji ai ko za ki karɓe gida kya barsu su su kimtsa a nitsi ba wai ki zo ki wulaƙanta su hakan ba” Iya ta yi maganar ranta a ɓaci “yi haƙuri Iya don Allah kar ki sake cewa da ita komai, ta tabbata a cikin duniyar idan har ta isa!” Mama ta yi maganar tana janye Iya daga gaban Hajiya Turai “ki barta ta tsaya yanzu jikinta ya gaya ma ta, ko me za ku faɗa sai dai ku faɗa amma gida ne sai an bar shi!”
Babu wanda ya sake yin magana sai zuba masu idanu da a ka yi ana yin ƙus-kus sai da suka kwashe komai ta ce. “Sai ku bisu ku faɗa masu inda za su kai ko ina laifi ai nayi ma ku nasiha ma” janyo hannun yaranta tayi suka fito a waje suka haɗe da Maman Halima da ta zo da sauri tana faɗin “Maman Zhara me ya faru ne yanzu nake dawowa daga unguwa ake faɗa mini ana kwasar kayan ku” a gajirce tayi mata bayanin komai cikin zubar da hawaye ta ce. “Innalillahi wa Inna ilahi raji’un yanzu to ina za ku tafi?” Ingizar da Momy ta ta yi wa Mama ne ya hanata ba ta amsa “ina da abin yi ba wai ku tsaya surutu ba maza ku shiga mota rufe gida zan yi”
Zhara ta riƙo Mama tana yi wa Momy kallon tsana gaba ɗaya ta sure mata a rai “ko za ki rama mata ne!?” Zhara ba na so kar ki kulata, ji ki ki ɗauko mana akwatin kayan mu har na ‘yan biyu” da ƙyar ta iya zaƙulo kayan ta fito da su ta roƙi wasu da su taimaka su kama mata suka kawo wajan Mama “ni ba zan shiga motar ki ba domin duk wanda ya iya yi ma wannan tozarcin tabbas har halakar da rayuwar ka zai iya, ki je da sauran kayan kiyi duk yadda kika so da su. Zhara mu je mu samu a-dai-daita-sahu mu shiga” murmushi Momy tayi tana faɗin “daɗi na da ke a kawai tunanin, kinyi kyan kai. Kai Ajingo idan kuna da yadda za ku yi da kayan ku je da su kun samu ganima.”
“Ku zo mu tafi gida don Allah kafin Malam ya dawo mu ji yadda za a yi.”
“A’a Maman Halima ba za mu ɗora ma ku nauyi ba, za mu tafi mun gode Allah ya bar zumunci” duk yadda ta so lallaɓa ta taƙi zama har wasu maƙota sun neme su zauna a wajansu suka ƙi dole suka haƙura. Sai bayan da taga tafiyar su sannan ta rufi gidan ta shiga motar da ta ɗauko haya daga filin jirgi. Ta bar mutanen unguwa da zaginta.
Ko minti talatin ba su yi da tafiya ba sai ga motar Dady da Yaya Hafiz sun ƙarasu tare da Khadija. Hafiz ya fara isa ƙofar gidan Khadija na bayan shi kallon-kallo a ka shiga yi tsakanin shi da Khadija “Yaya ya na ga gidan a rufe?”
“Ni ma mamakin da nake kenan” Dady ya ƙarasu yana faɗin “ya kuka tsaya”
“A rufe yake da kwaɗo” wani dattijo da ya fito gidansa ya ƙarasu wajan yana faɗin “sannun ku da zuwa, ai masu gidan ba su jima da tafiya ba.”
“Ina suka tafi?”
“Eh to gaskiya tafiyar ba ta hankali ba ce babu wanda zai ce da ku ga in da suka nufa” ya faɗa masu abin da ya faru ya ƙara da cewa “na ji dai ana faɗin matar Yayan shi mamacin ne ta aikata masu hakan” faɗuwa ya yi a wajan yana kuka kamar ƙaramin yaro “innalillahi wa Inna ilahi raji’un! Turai waci irin masifa kika janyo mini, na zo ina kukan na rasa gudan jinina sai na tarar da wannan abin takaicin ina zan gan su ina suka nufa?” Hafiz ya goge hawayen da suke zubo masa a fuska ya rusuna gefen Dady zai yi magana kuka ya kufce masa yana jin wani irin ciwo a zuciyarsa a ce mahaifiyarsa ce ta aikata wannan rashin imanin. Cikin kuka Khadija ta tafi gidan su Halima da sassarfa tana zuwa ta samu Baba da Mama suna mayar da ba’asin abun, “Khadija” Mama ta kira sunanta da sauri “don Allah Mama ina su Aunty Zhara suka tafi?”
“Wallahi ba wanda yasan ina suka tafi dan ba yadda ban yi Maman Zhara ta faɗa mana ba taƙi faɗa kawai sun shiga a-dai-daita-sahu suka yi tafiyar su.”
“Tare muka zo da su Dady” tashi Baba ya yi yana faɗin mu je na gansu.”
Ko da suka ƙarasa suka samu maƙota ana ta ba shi haƙuri shimfiɗa tabarmar da ya zo da ita ya yi ya na roƙonsu da su zauna, bayan sun zauna “a yi haƙuri haƙiƙa abubuwan basu yi daɗi ba, ina mai yi ma ta’aziya Allah ya jikan shi da rahama Allah yasa ya huta.”
“Amin. Don Allah ina iyalan nasa suka tafi?”
“Wallahi ba mu sani ba, dawowata kenan a ke sanar da ni abin da ya faru.”
“Innalillahi wa Inna ilahi raji’un! Ban ji rasuwar ba sai shekaranjiya da dare labarin ya same ni, ko Kano ba mu je ba muka zo nan sai ga labari marar daɗi mun tarar. Hafiz kira wayar Zhara.”
“Dady ka manta na faɗama tun d1,@a na bar gida ban sake samunta ba ko na kira ba ta shiga.”
“Kira ta Maman ta su” da sauri ya lalubu number ya kira sai dai a kashe take, da sanyin jiki ya faɗa masa. Haka suka shiga motar da suka ɗauko shata daga filin jirgi suka bi gidajen ‘yan’uwa suna duba su ba su je ba. A bakin hanya suka samu masallaci suka yi sallah Magarib Khadija ta yi ta ta a gefen hanya kusa da mota, bayan sun fito masallaci Hafiz ya ce. “Ko mu gwada zuwa tashar mota ko Allah zai sa a dace?”
“Eh shawarar tayi” ya kalle Baban Halima yana faɗin “idan har ba za mu takura ma ba ko za ka raka mu har can ɗin?”
“Haba takura kuma a’a wallahi, su ɗin fa sun zama ahalina anyi zama na amana da ɗan’uwan ka, da ina a wajan ma abin ya faru ba zan taɓa bari su tafi ba. Dan haka sai inda ƙarfina ya ƙare wajan nemo in da suke.” Suna ta yawo har bayan isha babu labari sun kasa samun su dole suka haƙura bayan sun a jiye Baba gida suka tafi masauki. Bayan ruwa babu abinda suka iya ci. Khadija ta ɗora kanta a kan cinyoyin Dady cikin muryar kuka ta ce. “yanzu shi kenan ba za a gansu ba.”
“Ba a cire rai da rahamar Ubangiji za mu yi ta addu’a Allah ya bayyana mana su, ya kuma sa suna waje mai aminci.”
“Amin” Hafiz tashi ya yi ba tare da ya ce komai ba ya shiga ɗaya ɗakin dukan su suka bi shi da kallo Khadija tayi karfin halin tashi ta bishi ta same shi zaune a ƙasan kafet ya dunƙule kansa a tsakanin guawoyinsa zama tayi kusa da shi tana faɗin “ka yi haƙuri Yaya na tabbatar da za a gansu ba mamaki sun tafi gidan wasu ‘yan’uwan Mamanta ne da mu ba mu san su ba” ɗago kansa ya yi yana kallonta da idanunsa da suka yi ja ya ce. “Ban san a wani hali take ba a wannan lokacin, ta rasa uba a lokacin da take matuƙar buƙatar mai nuna tausayi da bata haƙuri Momy ta zo ta ƙarasa saka su cikin damuwa, ga ƙaramin ciki a tare da ita ina zan sa kaina, nayi da-na-sanin tafiyar nan da nayi, da ina nan da duk hakan ba ta faru ba.”
Kasa tsayar da kukan da ya zo ma tayi “kunya nake ji idan ina ganin abinda Momy take yi na rashin kyautawa, ina jin tsoron hukuncin Dady a kanta a yadda nake hango fushi a idanunsa.”
“Ko me ya yi ita ce ta janyo Khadija ba za mu iya hana shi ba kamar yadda muke tausar sa a baya, kawai dai dan uwa na uwa ne amma wallahi da mtsw! Shiru yayi yana yin ƙwafa.
Da sassafe suka sake fita gidan Yaya Fati suka koma bayan sun gaisa Dady ya ce.
Sun kuwa kira ki?”
“Wallahi Alhaji har yanzu ba su kira ni ba, na ta kiran su kuma wayar a kashe, sannan duk wani ɗan’uwa ko abokan arziƙin da na san suna hulɗa na bincika ba su tafi ba.
Tsoro nake ji idan har lafiya dan ban tunanin ana lafiya su kasa kira na” jiki a sanyaye ya ce da ita “mun gode, yanzu za mu tafi idan har kun ji wani labari na su kar a yi jinkiri wajan sanar da mu, nasa sanarwa na ba ‘yan-sanda rahoton neman su, sai mu yi ta addu’a Allah ya bayyana su.”
“To Amin ya Allah Ubangiji Allah ya kawo mana mafita.”
Zaune suka sameta ta cake cikin tsadaddin Les tana kallo tana cin dumbun na ma, “ikon Allah ku ne tafe yanzu kai Hafiz Khadija ya haka ba ku tafi ba ne?” Tayi maganar cikin nuna rashin gaskiya dan ba tayi tsammanin ganin nasu a yanzu ba. Kallon da suke yi mata ne yasa ta tsalgu sai rarraba idanu take Khadija tayi hanyar sama za ta wuce maganar Dady ce tasa ta tsayawa cak zuciyarta na bugawa fat! Fat!! Fat!!! “Ba su ki ka tozarta ba Turai ni ne nan kika tozarta na kuma gode Allah ya saka da alkhairi, ki je kuma na sake ki saki ɗaya!” Buga gaba tayi tana miƙewa tsaye “saki! Alhaji kan ka ɗaya ni ce fa, anya kunnena daidai ya jiye mini?” “Eh sakin fa, wace ce ke da ba zan iya rabuwa da ke ba! Sannan kin ci albarkar ‘ya’ya wallahi da yau sai dai ki kwana a hannun hukuma!”
Ya kai duban sa ga Khadija da take kuka yana faɗin “maza ki ɗauko ma ta mayafinta!” Da gudu ta ƙarasa haurawa sama. “Wallahi babu inda zan tafi ko ka sake ni zama daram dan na girmi zawarci a gida, sai dai kai ka tafi wani wajan ni kuma nayi zaman ‘ya’yana!”
“Ga dukan alama so kike hukuma su yi ram dake matuƙar ki ka ce za ki zauna mini a gida” Hafiz ya fice da sauri zuciyarsa a ƙuntace. Khadija na kawo mayafin ta bashi ta haura sama, “ga shi maza ki bar mini gida ko tsinki ba za ki ɗauka ba dan babu abin da kika zo da shi” ya ƙarasa maganar yana warci wayar hannunta “saboda wadancan banzayen za ka wulaƙanta ni a gaban ‘ya’yana, shi kenan zan tafi amma wallahi sai kayi da-na-sanin tozarta ni da ka yi!!” Tasa ƙiyarta ya yi har zuwa haraba yana faɗin “ki tabbatar da idan har wani abun ya samu iyalan ɗan’uwana hukuma ce za ta raba ni da ke!” Masu aikin gidan suka yi cirko-cirko suna kallon baƙun yanayin da suka gani.
Mai mashin ya ajiye shi kofar gida bayan ya biya shi ya buga ƙofa mai-gadi ya buɗe yana tambayar waye ganin Hafiz yasa shi fito da idanu “yallaɓai kai ne tafi ikon Allah, sannu da zuwa.”
“Yawwa Malam Idi sannu” ƙarasa shigowa ya yi ya biyu bayan shi yana faɗin “ai ban san za ka dawo ba, ya haƙurin rashin da a ka yi, Allah ya jikansa da rahama.”
“Amin Ya Allah na gode” ganin Hafiz na shirin shiga gida yasa ya kira shi “yallaɓai”
“Na’am ko a kwai wani abun ne?”
“Eh to a kwai maganar da nake so na faɗama ne na abinda ya faru bayan tafiyar ka”
“Ina sauraren ka” ya yi maganar yana mai mayar da hankalin sa kan shi. Ya faɗa masa duk abin da ya faru ɓacin rai yasa ya kasa cewa komai ya wuce mai-gadi, “Allah dai ya taƙaita ran maza ya ɓaci, dole kuma na faɗa dan tsira da aikina.”
“Halima Halima Kina ina ne!!?” Halima da take kichen tana aiki gabanta ya ba da ras! “Kamar Muryar Hafiz nake ji?” A tsoraci ta fito ta samu ya nufi ɗakinta “Baby” a fusace ya juyo ya cakumo wuyanta “me kuka yi wa Zhara!!?” Hannu tasa tana ƙoƙarin janye hannunsa dan sosai ya shaƙita idanunta suka fito da ƙyar ta iya cewa “don Allah ka caka ni zan faɗa ma gaskiya.”