Skip to content
Part 5 of 43 in the Series Kuskuren Waye? by Aisha Abdullahi Yabo

Maganar shi ta jiyo yana faɗin, “Kina jina kuwa? Zhara” ƙit ta tsinki kiran tare da kashi wayar gaba ɗaya komawa ta yi ta kwanta a ranta tana faɗin ‘Yaya Hafiz neman rigimar shi ta yi yawa gaba ɗaya zama a cikin ma su jajayen kunne ya sa ya zama wani iri, ita gaskiya tana jin kunyar yin hakan duk da tana masa kyakyawan zato bai yi hakan da wata manufar ba amma ita kam sam ba za ta iya yin hakan ba, gara ta kashe gobe sa yi Magana.’ Daga hakan ta juya ta yi kwanciyarta zuciyarta fal da tunanin shi har bacci ya yi awon gaba da ita.

*****
Jin kiran ya tsinki ya kashi data ya kira numberta ya ji wayar a kashi sosai ya ji ranshi ya ɓaci ya sani da gangan ta tsinki kiran mirginawa ya yi ya gyara kwanciyar shi, sosai ya ji haushinta har ga Allah ba ya nemi hotonta ne dan wata mummunan manufar ba amma shi ta mayar da shi wani ɗan iska ta kashi waya.

Danna kiran number da a ke turo ma shi saƙo ya yi ba dan ya sa ran za a ɗaga ba cikin sa’a kuwa kiran bai jima da shiga ba ya jiyo wata murya mai daɗi da sanyi ta ɗaga tana masa sallama, lumshi idanusa ya yi sosai murya ta ratsa zuciyarsa da jikinsa, bayan ya amsa mata sallama ya ce; “Yau dai na cire tuta tunda har a ka ɗaga kirana ko” tana murmushi ta ce; “Dama ai ko yaushe tutar ta ka a ɗagi take My Noor”
“Hmm na gode, da fatan kina lafiya?”

“Lafiya lau, kamar yanda jikina ya ke bani kana cikin ƙoshin lafiya.”

“Ni kuwa na tambaye ki mana?”
“Ka yi tambayar ka idan har na sani ba da jinkiri ba zan baka amsa.” Gyara kwanciyar shi ya yi kafin daga bisani ya ce; “dan Allah a ina ki ka sanni kuma ta ya ki ka samu nimberna?”

Shiru ta yi na ɗan daƙiƙo bai katse mata shirun ba ya dai kasa kunne yana jiran amsa, ajiyar zuciya ta yi marar sauti kafin ta ce; “ban tsammani tambayar da sauri haka ba, amma hakan ba zai hana na baka amsa ba, ranar na zo asibitin ku na kawo mamana da ba ta da lafiya, to kaini likitan da ka dubata, tundaga ranar da idona ya ganka, zuciyata ta faɗa sonka.”

Ta yi shiru “uhum ke nake saurare.”

“Uhum ka yi haƙuri kar ka ga kamar bani da kunya ba hakan bane gaskiya ni mace ce da bana iya ɓoye abu a raina, da yawa hausawanmu musamman hausa Fulani suna kallon macen da ta fara faɗawa namiji kalmar so mace ce marar ta ido ma’ana marar kunya kuma wacce ba ta da kamun kai, to ban sani ba ko kaima hakan kake kallon lamarin, ni dai abinda kawai na sani bana ɓoye abinda ya ke raina, kuma na ɗauka rashin faɗa kamar na cutar da kaina ne da kuma zuciyata” har a cikin ran shi bai ɗauki hakan wata damuwa ba hasalima burge shi ta yi wannan ita ce irin macen da ya ke mafarkin samu wayayyar mace marar duhun kai, murmushi ya yi kafin daga bisani ya ce; “karki damu, ni ban ɗauki hakan wata matsala ba, mace ma tana da damar faɗar abinda ya ke ranta a inda ya dace ko a musulunci hakan ba laifi bane matuƙar hakan ɗin anyi shi ne bisa gaskiya da kyakyawan yaƙini.”

“Na ji daɗi sosai da har ka fahimcini, yawwa sai maganar a ina na samu number ka, gaskiya na sha wahala sosai kafin na samu Number ka ciki harda bibiyar ka shafukan sada zumunci har dai Allah ya sa na samu Number ka, ina fatan da amsoshin nawa sun gamsar da kai”? Ta yi maganar tana murmushi.
“Sosai kuwa na gamsu, amma fa tambayar ba ƙarewa ta yi ba.”
“To a shirye na ke da ba ka ko wace amsar tambayar ka My Noor” haka ya yi ta yi mata tambayoyi gami da wajan zamanta da kuma matakin karatunta, bai san sun ɗauki dogon lokaci suna magana ba har sai da idanun shi suka kai kan agogon da ya ke manni a kusurwar ɗakin ƙarfe biyun dare, daga nan ya mata sallama ba dan ranshi ya so hakan ba domin ji ya ke kamar su kwana a hakan yana jin daddaɗar muryarta. Ya jima yana juyi da tunanin yanda zaiyi da Dady dan shi kam yanzu ya ga matar aure, cikin tunanin mafita bacci ya yi awon gaba da shi.

*****
Zhara ta je gidansu Halima suna zaune gindin famfo tana taya Halima wanki-wanki, Zhara ta kalle Halima ta ce, “wai ni kam Halima ya maganar nan ne har yanzu baki ce dani komai ba.” tana harararta ta ce; “kin manta munyi alƙawarin babu tambaya?” saurin rufe bakinta ta yi da hannunta tana dariya ta ce, “Uu na manta, kin san me wallahi ji nake na ƙagu na ji komai shi ya sa har na kasa haƙuri na tambaya.”

“Ai kuwa ki ƙara ɗaura ɗamarar haƙuri dan komai ba za ki ji a yanzu ba, idan kuma ki ka sa garaje sai na daina.” ta yi maganar tana mai ɗaukar kwandon da su ka rafka kwanukan a ciki, Zhara ta ce, “Na daina rigimammiyata.”

“A to da dai ya fi maki.” Tsintsiya Zhara ta ɗauka ta share wajan sannan su ka dawo ɗakin Halima za su fara karatun hardar su Zhara ta ce; “Kin san me?”
“Aa sai kin faɗa”
“Anfi sati Yaya Hafiz bai kirani ba fa, har na fara jin tsoron anya lafiya.”

“Kuma bai ɗaga kiran ki?”

“Tab nan fa ɗai an cewa guguwa ji ki ɗebo ruwa rafi. Kema kin san ba zan iya kiran shi ba.” Tana harararta ta ce, “To ki daina cewa kin damu, dan da kin damu tabbas za ki kira shi, kuma Allah dole akwai dalilin rashin kiran ba mamaki ma wani abun ki ka masa dan na san halinki bagidajiya ce ke da a ƙauye a ka haifi ki Allah da ban san ya za ki zama ba.”

Duka Zhara ta kai mata tana faɗin “Ni ki ke kira da bagidajiya ko, za ki sani wallahi.” Halima na dariya ta ce; “To idan ba gidadanci ba ta ya kana son abu kuma kana halin ko oho da shi, shi kaɗai ne ya ke nuna ma ki damuwar shi kinga kuwa dole ya ji wani abun a ranshi ko tunanin ba kya son shi tunda ita zuciya ba ta da ƙashi sannan an halicci zuciya da son abinda ya ke kyautata mata kin san haka, ya kamata ki gyara gaskiya, sannan ba mamaki a kwai abinda ki ka masa.”

Cikin ajiyar zuciya Zhara ta ce; “Wallahi na rasa me ya sa nake matuƙar jin kunyarsa, sam bana iya sakewa da shi, ni idan dai ba ranar da na faɗa maki ya ce na turo masa hotona na kashi waya ba ban san na yi masa wani abun ba bayan haka gaskiya, kuma daga sannan ne ya sauya mun.”

“Allah ba mamaki shi fushin da ya ke kenan, ki a jiye wannan kunyar tuni an dainata ta zama tsohon yayi ki sake da shi ki nuna masa kulawa da soyayya kar kunyar ki ta zama KUSKURE na farko da za ki rusa zuciyarki damar da ki ke da ita ki rasata, ki tuna fa shi ba tashin nan bane, tashi a ƙasar masu jajayen kunne ya riga ya yi rayuwa cikin wayayyen mata sai kinyi da gaske wajan iya masa yanda ya ke so.”

“Gaskiya ba zan iya tura masa hotona a yanda ya ke so ba.”

“Nima bance ki yi hakan ba, amma dai ki daina tura masa hoton da ki ke sanyi da Hijab, ki kuma kirashi ki bashi haƙuri.”

”Uhm! Shi kenan zanyi ƙoƙarin yin hakan.” Ta yi maganar ba dan a ranta ta ji za ta iya yin hakan ba.” Daga nan su ka fara karatu zuciyarta ciki da tunani.

*****
Yana cikin duba wani dattijo marar lafiya Anwar ya buɗe ƙofa ya shigo, da sallama, Hafiz ya ɗago ya dube shi yana amsa Sallamar, kafin daga bisani ya mayar da duban shi ga marar lafiyar, Anwar ya samu kujera ya janyo ya zauna, “Baba zan rubuta ma ka magani ka dinga sha a kan lokaci ka kuma ragi tunani hakanne zai sa jininka ya daina hauhawa” ya kalle wanda ya kawo marar lafiya ya ce, “akwai maganin bacci ya dinga samun bacci isasshi, sannan an samu guri da babu hayaniya ya kwanta hakan zai sa ya samu bacci cikin natsuwa yin bacci ku dinga hana shi saka abu a ranshi domin wannan karon jinin na shi ya hau sosai.”

“In sha Allah likita za mu kiyaye mun gode sosai.”

“Allah ya bashi lafiya.”

“Amin” ya rubuta mashi magani su ka fita suna ma sa godeya, Anwar ya ce; “bokan Turai ya a ka yi ne ka dameni da kira dole na bar aikina na zo” tasuwa ya yi kafin ya ce; “ina zuwa bari naga idan babu mutane sosai.”

Wata ce ta shigo ya riƙi kanshi nuna mata wajan zama ya yi kafin ya buɗe ƙofa ya ce da Nus ta tura sauran wajan Dr Mahabub ko Dr Balkisu, yana gama faɗa ya dawo ciki ya duba matar bayan ya sallameta ya sawa ƙofar key ya dawo ya janyo ɗaya kujerar ya zauna suna fuskantar juna da Anwar kafin ya ce, “Abokina ina cikin damuwa fa.”
“To me ya faru?”

Ya yi tambayar cikin mamaki, ya ja numfashi ya furzar a hankali kafin daga bisaniya ce; “A kan maganar aurena ne, ka dai san inda tani ne sam ba zan ɗauko maganar aure yanzu ba, to Daddy ne ba yanda na iya dole na yi yanda ya ke so, sai dai a kwai matsala gaskiya gami da zaɓin da ya mun.”

“Wace irin matsala kuma Hafiz naga dai yarinyar nan ‘yar’uwar ka ce, dan haka bana tunanin wata matsala tunda abun na gida ne.”

“Mtsw, hakanne amma ni dai a wajena gaskiya da matsala, ba zan ce bana son Zhara ba, amma ni son da nake mata so ne na zumunci matsayinta na ƙanwata, na yi zaton kafin auren mu zan iya sonta har mu fahimci juna amma na fahimci sam hakan ba mai yi bane, domin ita wata irin bagidajiya ce ko kuma ma na ce ga dukan alamu itama ba sona take ba kawai biyayya take yi.”

Anwar ya zuba ma shi ido yana kallon shi ya kasa cewa uffan, “Malam ba kallona na ce ka zo ka yi ba magana za ka yi.” Ya yi maganar yana hararshi,
“to ni me ka ke so na ce ma Hafiz”?
“Shawara za ka bani yanda zan ɓullowa Daddy a fasa auren ba tare da na samu matsala da shi ba, danne yanzu haka na samu wacce nake so kuma tsarinta ya yi daidai da nawa tsarin.”

“Hafiz magana ta gaskiya ba zan taɓa ba ka shawarar ka bijirewa zaɓin Mahaifin ka ba, kuma ni banga matsalar yarinyar nan ba Hafiz, samun mace mai hali irin nata da kuma kunya abu ne mai matuƙar wahala a wannan zamanin, kar ka bari ka rasa wannan kyakyawan zaɓin dan Allah Hafiz.”

Ya ƙarasa maganar cikin magiya, tsaki Hafiz ya yi karo na biyu kafin ya ce; “Na ce da kai ba ta da hali ne, kawai ra’ayinmu ne bai zo ɗaya ba, ta ya zan aure macen da ban san ya ainahinta ya ke ba, ko musulunci fa ya yarda na yi wa matar da zan aure kallon tsab, amma malam na je na aure mace ban san a ya take ba, na sani ko kura ce da fatar a kuya a ke so a min.”

Kallon ka sha ƙwaya ne Anwar ya yi wa Hafiz kafin daga bisani ya ce; “Yanzu Daddy ne zai ma ka zaɓin tumun dare, shi ne za a haɗa baki da shi a maka rufa-rufa?”
“kai matsalata yi wa mutum bahaguwar fahimta, yaushe na faɗama hakan, kawai dai na san Daddy yana son yarinyar sosai komai zai iya yi a kanta” tagumi Anwar ya yi yana kallon Hafiz shi harma ya rasa me zai ce, jan numfashi ya yi ya furzar kafin ya ce; “ka santa ne da wata nakasa”?
Yana girgiza kai ya ce; “sam-sam lafiya ƙalau na santa sanin yarinta kafin na tafi karatu, amma ai rayuwa ba tabbas ne da ita ba, ba mamaki wani abun ya sameta bayan tafiyata, idan har ba hakan ba, babu dalilin da zai sa ta dinga ɓoyon kanta a cikin Hijab.”
“Ka kyautata zato Hafiz, Ina da tabbacin Daddy ba zai maka zaɓin da zai cutar da kai ba.”
“Kaga Anwar kawai ka bani shawarar yanda zanyi da Daddy mu rabu lafiya, dan maganar nan da nake ma mun kai ƙarshe da wata yarinya har mun haɗu da ita kuma ta min, ita nake son aure a matsayin uwar ‘ya’yana.”
“Gaskiya ni ban san me zan ce da kai ba, bayan kayiwa mahaifinka biyayya ka rabu da ƙyale-ƙyalen matan nan ka rungumi Zhara ba abinda mace za ta nuna mata ko fuskarta kaɗai ka kalla ka san ita ɗin kyakyawa ce” cikin jin haushi ya ce; “Malam riƙi shawararka bana so.”
“Da ka san ba ka son uwar me ya sa ka nemi na zo na baka shawarar.” ya yi maganar yana dalla masa harara, ”na ji koma me ye ka faɗa ni na nemo ka yanzu kuma na ce ka tafiyar ka”
“Ka faɗi duk abinda kake so ka faɗa amma gaskiya ɗaya ce dole na faɗa ma ka kar ka bi ruɗun zuciya ka saɓawa mahaifinka kar ka gujewa ‘yar’uwar ka saboda wata bare, wallahi samun irin Zhara a wannan lokacin yana da matuƙar wahala.” cikin masifa ya ce, “Sai faɗi kake mai irin halin Zhara yana da wahala, a wajan ka ne ya ke da wahala, na ma gama fahimtar son nata kake shi ya sa motsi kaɗan ka yaba halinta to ka je na bar maka ka aureta!”

Murmushin takaici Anwar ya yi kafin ya ce, “Ni ka ke faɗawa magana Hafiz, shi kenan ka je duk wanda ya ɗebo da zafi bakinsa, Allah ya bada sa’a.” haka su ka rabu zuciyar kowa ba daɗi. Hafiz ya tattara inasa-inasa ya bar asibitin, tuƙi ya ke tunani ya ke, ga Haushin Anwar, ga kuma tunanin yanda zai shawo kan Daddy, in dan ta Mommy ne sam baya jinta dama ba so take ba, Daddy shirye-shiryen auren kawai ya ke, ko zama yayi bai da magana sai ta auren, shi har ya ma rasa wani irin so Daddy ya ke wa Zhara ne, shi dai duk wacce za a yi a yi amma auren nan ba zai yi ba ya riga ya samu zaɓin zuciyar shi, yau tunkarar Daddy zai yi da maganar.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 2.7 / 5. Rating: 21

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Kuskuren Waye? 4Kuskuren Waye? 6 >>

8 thoughts on “Kuskuren Waye? 5”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×