Skip to content
Part 7 of 43 in the Series Kuskuren Waye? by Aisha Abdullahi Yabo

Yanzu ta gama fahimtar dalilin da yasa Yaya Hafiz ya daina kiranta ya daina nemanta dama ba sonta ya ke ba yana da wacce ya ke so son ma so wani ne take, a ɗaya ɓangaren tana tuna abinda Hajiya Turai ta yi gaba ɗaya sai ta ji auren ya fitar mata a rai ji take ko da son shi zai zama ajalinta ta haƙura da shi, tana cikin wannan yanayin Mama ta shigo ɗakin zama ta yi kusa da Zhara tana kiran sunanta,

“Zhara tashi muyi Magana.” Tashi Zhara ta yi tana sharɓar majina Mama ta dafa kafaɗarta kafin daga bisani ta ce, “Tun farkon fara maganar auren-nan waɗan-nan matsalolin na ke ma ki gudu shi ya sa naƙi amincewa da maganar ɓacin ran da mahaifin ku ya nuna ya sa dole na haƙura ba dan raina ya so ba, na kuma fahimci kina son shi hakan ya sa kawai na haƙura na bar komai.”

Ta numfasa kafin ta ci gaba da faɗin, “Wannan tijarar kaɗai da ta zo ta yi na tabbatar zuwa yanzu kin fahimci me na ke ma ki tsoro.” Cikin kuka ta ce, “Mama tabbas ina son shi amma ko son shi ne zai zama ajalina ba zan aure shi ba, ba zan taɓa auren wanda baya sona ba mahaifiyarsa kuma bata son mahaifiyata ba.” Murmushi Mama ta yi kafin daga bisani ta ce, “Ai Zhara mai afkuwa ta riga da ta afku tunda har iyayen ku suka ƙulla babu makawa Allah kaɗai ne zai hana yin auren nan, idan har ki ka ce ba za ki aure shi ba tabbas ta yi nasara dama abinda take so kenan matsalar ta fito daga garemu kinga mu ne ba mu yi biyayya ba su ne ma su biyayya, dan haka karma ki suma cewa za ki nuna rashin amincewar ki, kar kuma ki faɗa wa mahaifin ku abinda ya faru har Hassana na kwaɓeta mu ci gaba da addu’a ba abinda addu’a ta bari duk abinda ya fi zama Alkhairi Allah ya tabbatar mana da shi” saurarin mahaifiyarta take tabbas gaskiya ta faɗa amma Allah ya gani auren sam ya fice mata a rai, sai dai za ta yi biyayya wa mahaifinta In Sha Allah duk rintsi za ta jure.

*****
Suna hanyar dawowa Islamiyya ta ba Halima labarin abinda ya faru jiya bayan rabuwarsu cikin ɓacin rai Halima ta ce, “gaskiya na ji haushi da a kayi ban kusa wallahi da sai na shuka mata rashin mutunci ita har wasu kuɗi ne da su da za ta zo tana yi wa mutane rashin mutunci an faɗa mata rasa mijin aure ki ka yi ne da har take tunanin ɗan nata wata tsiyar ne ke ni wallahi da za ki bi ta tawa da kin koyawa zuciyar ki rashin sonsa ki bar banza ya gani idan zai sami irin ki.” Ta ƙarasa maganar tana ƙwafa.

Dariyar ƙarfin hali Zhara ta yi kafin ta ce, “Ki kwantar da hankalin ki kar ma ki ce za ki sa wannan aranki komai ya riga da ya wuce, sannan ni kaina na yi tunanin zan faɗawa Abbana ba zan aure shi ba, amma Mama ta hana ta ce dama abinda su ke so kenan matsalar ta fito daga wajanmu kar na bari su samu wannan damar.”

“Uhm! Maganar Mama gaskiya ne, Ubangiji Allah ya kawo maki mafita, amma gaskiya bana yi maki fatan auren shi domin gara a ce mace ce bata son aure a kan a ce namiji ne baya so, bayan haka kuma ga matsalar uwar miji ƙawata Allah ya warware maki komai cikin sauƙi alfarmar Annabi Muhammad (S.A.W)”

“Amin ya rabbi ƙawata.”

So take ta ƙarfe ta hana zuciyarta tunanin Yaya Hafiz sai dai sam hakan ya gagareta sai daɗa hauhawa son nasa ya ke babu bugun numfashinta da za ta yi ba tare da Yaya Hafiz ba, sai dai tana ƙoƙarin ɓoye damuwarta dan bata son Mama da Halima su shiga damuwa silar damuwarta, wani lokacin hakan za ta killaci kanta ta yi kukanta mai isarta har sai ta gaji ta lallashi kanta, kwance take a kan katifa sai juye take bacci take so ta yi sai dai tunani ya sa bacci ya mata ƙaura, tun bayan faruwar lamarin bacci ya mata ƙaranci, kiran waya ne ya shigo wayarta a hankali ta kai hannunta bayan filo ta janyo wayar Yaya Hafiz ne duba agogon wayar ta yi ƙarfe 12:30 am kamar ba za ta ɗauka ba sai kuma ta ɗaga dab da za ta tsinke, tana jin ajiyar zuciyarsa, shiru ta yi bata ce da shi komai ba, cikin sanyin murya ya ce,

“Kin tashi hankalina Zhara kwana biyu kenan ina kiran wayar ki amma ba kya ɗagawa kuma na tabbatar da kinga kiran ɗagawar ne dai ba za ki yi ba.” Shiru ta masa murmushi ya yi kafin ya ce, “Ki yi haƙuri kar laifin Momy ya shafeni har ga Allah ban san Momy za ta zo gidan ku ba sai bayan ta dawo ta faɗa min ta zo da abinda ta yi, ki yi haƙuri kuma zan zo har gida na ba su Mama haƙuri.”

“Yaya Hafiz kenan ai zuwan Momy ba laifi bane kuma duk abinda ta faɗa gaskiya ne dama ina haɗin kefe da kaska, ku ɗin ma su kuɗi ne irina ‘yar talaka sam ba sa’ar auren ka bace ban tantanci zama matarka ba.” Ta ƙarasa maganar idanunta na zubar da hawaye, ɗaure fuska ya yi kamar tana gabansa ya ce, “Dani da ke a kwai wani banbanci ne? Karki manta mahaifina da mahaifinki uwa ɗaya uba ɗaya su ke kenan dai duk abinda muka mallaka naku ne domin abu ɗaya ne, dan haka kima daina kawo wannan a ranki, na sani ba a kyauta ma ku ba amma ina mai baki haƙuri a madadina da kuma Momy sannan na roƙi ki ki baiwa Mama haƙuri In Sha Allah ranar asabar zan zo na bata haƙuri.”

“Komai ya wuce ba ma sai ka zo ba dan Mama ta ma manta da abin.” “Ba kya son ganina ko ba ki yi missing nawa ba?” Murmushin gefen baki ta yi a ranta tana faɗin wannan ya raina mata wayo yana nuna kamar sonta ya ke kamar ya wani damu da ita, “Kinyi shiru”

“Humm Yaya Hafiz me ya sa ba za ka fito ka faɗan gaskiya ba? Na sani ba sona kake ba kawai dai biyayya ka ke yi wa su Daddy.”

Zuciyarsa ta bada dum ya a ka yi ta fahimci hakan? Tambayar da ya yi wa kansa kenan a zuciyarsa a fili kuwa cikin dakiya ya ce, “Wannan tunaninki ne kawai Zhara amma ba hakan bane.” Ccikin jin haushi ta ce, “Yaya Hafiz Momy ce ta faɗa da kanta kana da wacce ka ke so kuma ka sani na sani ba za ta taɓa yi ma ƙarya ba, k… muryarta ta fara rawa hakan ya sa ta yi shiru tana ƙoƙarin haɗiye kukan da ya zo mata, cikin sanyin jiki ya ce,

“Ki yi haƙuri Zhara gaskiya ne ina da wacce nake so amma kuma hakan ba zai sa na ce ba zan aure ki ba ko bana sonki, ban taɓa ƙin ki a zuciyata ba Zhara, kuma babu abinda zai sauya aurenmu, ina neman alfarmar ki da kar ki bar hakan ya zauna a zuciyar ki bare har ya sa dam… tsinki kiran ta yi tare da jefar da wayar tasa kanta cikin filo tana wani irin kuka mai cin rai da sanya tausayi a zuciyar mai saurare. Ya sani ko ya sake kira ba ɗaga kiran za ta yi ba hakan ya a jiye wayar zuciyarsa a takure ya kwanta, sam bai ji daɗin abinda Momy ta ma sa ba, Zhara ‘yar’uwarsa ce ba zai so a ce ta sanadinsa ta shiga damuwa ba, duk da duk abinda ya faru KUSKUREN TA NE domin ita ce ta ba da damar da wata ta shiga zuciyarsa da ta ba shi kulawar da ta dace da hakan bata faru ba.

*****
Duka ɓangarorin biyu shirye-shiryen biki su ke, idan ya zo ta kan je su yi fira a mutunci kamar yanda ta saba tarbarsa, kamar yadda Mama ta faɗa mata kar ta sake nuna masa damuwarta ta bi maganar bata sake yarda ta nuna damuwarta a kan yarinyar da ya ke so ba, shi ma kuma yana ƙoƙarin nuna kulawarsa a gareta, sai dai fa ba abinda ya sauya daga soyayyarsa da sabowar budurwarsa Sadi baby, zai yi wa Dady biyayya ya aure zaɓinsa daga baya shi kuma ya aure zaɓen zuciyarsa. Tafi ya ke zuciyarsa ciki da tunanini da tarin mamaki har ya isa gidan da ta masa kwantance wanda ya gane gidan ta hanyar tambaya kiran wayarta ya yi ya faɗa mata yana ƙofar gidan ta turo ƙanenta ya masa isu ɗakin da ya ke suro. Cikin abinda a ka kawo ruwa kawai ya iya sha, daga bakin ƙofa ta tsaya tana sallama amsa sallamar ya yi tare da zubawa ƙofar idanu kyakyawar matashiya ce ta shigo tana sanyi da riga da siket na a tamfa sai ƙaramin mayafi da ya tsaya iya kafaɗanta duk da fuskarta babu wani kwalliya sosai hakan bai hana sirrin kyanta fitowa ba da kuma kyan dirinta, murmushi suka sakarwa juna zama ta yi a gabansa tare da tanƙwashi ƙafafunta cikin tausasa murya ta ce; “Barka da zuwa ya hanya?”

“Hanya AlhamduliLlah” bayan sun gaisa taga babu alamar ya ci abinci ta ce, “Me ya sa ba ka ci abincin ba.” cikin murmushi ya ce, “Jira na ke ki fito muci tare” murmushi ta yi tana faɗin “kai ko shi kenan ko abaki ka ke so ai sai na baka.”

“Da gaske kike za ki bani a baki”? Rufe fuskarta ta yi tana dariya ƙasa-ƙasa kafin daga bisani ta ce; “A’a wasa na ke, da dai a ce za mu yi aure da sai na ce sai lokacin ya zo zan ciyar da kai da hannuna.”

“Kamar ya da aure za mu yi, to idan ba aure za mu yi ba me za mu yi ko kuma na ce me ye ma’anar soyayyar tamu”? Ya yi tambayar cikin mamaki, ƙasa ta yi da idanunta da su ka fara sauya kala daga fari zuwa ja hawaye sun ciko idanunta “ba komai ka ci abincin kaga ka yi tafiya mai ɗan tsayi.”

“Kinga ɗago kan ki ki kalleni ki faɗa min abinda ya ke zuciyar ki ba abinda zan iya ci a yanda maganar nan taki ta suki zuciyata.”

A ɗan zaman da su ka yi ta fahimci Hafiz kaifi ɗaya ne tabbas ba zai ci komai ɗin ba, jan numfashi ta yi ta furzar ahankali kafin ta ce; “ba ka yi mamakin cewar ina son ganinka a gidan iyayena ba saɓanin haɗuwar da mu ke yi a gidan Yayata? Na sani ganin a inda na ke ma zai saka ka tunani ko na ce mamaki.”

Gyara zamansa ya yi kafin ya ce; “Dan kin neme na zo gidan iyayen ki ba zanyi mamaki ba dan abu ne da ko baki ce ba dole ne ni na nemi hakan tunda soyayya ce mu ke da mu ke fatan ta kaimu ga aure kinga kenan hakan abu ne da ya zama dole, kawai idan ma da abinda na yi mamaki ganin inda ki ke ne wannan ma ba wai wani dogon mamaki bane duk da dai na ɗan sha jinin jikina da maganar ki wanda duk mai hankali da tunani ya san dole a kwai wani abu.”

Kallonta ya yi cikin tashin hankali ya ce; “Baby hawaye na ke gani a fuskar ki mene ne me ya faru? Faɗa mun” fashewa ta yi da kuka da ƙyar ya iya lallashinta ta masa bayanin komai zuba mata idanu ya yi ya shiga ruɗu sosai da jin abinda ya ke zuciyarta har ma ya rasa abin faɗa muryarta da ta shaƙi dan kuka ya jiyo tana faɗin “Zan bar ka ba dan bana sonka ba sai dan hakan ya zama dole na sani zanyi matuƙar kewar ka ba kuma zan hana zuciyata ci-gaba da sonka ba har abada zan yi matuƙar jinyar rashin ka.” Ta kifa kanta a kan cinyoyinta tana cigaba da yin kuka har cikin ransa ya ke jin ciyon wannan kukan nata baya son kukan mace bare kuma wacce ya ke so tamkar ransa, ya kai hannu zai taɓa ta sai kuma ya janyi hannu tuna hakan ba abinda ya dace bane, ajiyar zuciya ya yi kafin daga bisani ya ce,

“Ki min alfarma ki daina kukan-nan da ki ke yana matuƙar ɗaga min hankali, sannan ki bani hankalin ki ki ji abin da zan faɗa” ahankali ta ɗago tana kallonsa idanunta ba su daina zubar da hawaye ba sai dai saitin kukanne baya fita, sanya idanunsa ya yi a cikin nata ta yi ƙasa da idanunta da take jin sun mata nauyi ba za ta iya jurar idanunsa a cikin nata ba, bai damu ba bai kuma kawar da idanunsa daga kanta ba ya ce; “Baby na ji duk abinda ki ka faɗa sai dai abinda na ke so ki sani wannan ba hujja ba ce da za ta yanki soyayyarmu ba ko ta hanamu cikar burinmu na yin aure ba, ina sonki babban burina kuma ki kasance matata uwar ‘ya’yana babu abinda ya isa ya sauya hakan da yardar Allah.” Cikin kaɗuwa ta ce,

“Ta ya hakan za ta faru Hafiz wai ko baka fahimci abinda na faɗa maka bane?”

“Na fahimci ki sarai, amma ki sani ba abinda zai sauya.”

“Ka yi haƙuri ni ba zan iya yin hakan ba sam ba san iya ba!” Ta faɗa cikin ƙaraje tare da tashi tsaye za ta fita cikin zafin nama ya miƙe tsaye tare da shan gabanta fuskarsa babu Annuri ya ce,

“Za ki iya Baby dole za ki iya, wasa ki ke so ki yi da zuciyata me ya sa za ki bari na faɗa sonki in har kin san ba da gaske ki ke ba? Dole za a yi aurenmu ki sa wannan a zuciyarki.” Ya zura ƙafarsa a cikin takalmi ya fita ransa a ɓaci durƙushewa ta yi wajan tana wani irin kuka a ranta tana ji ina ma za ta mutu me ya sa so zai mata haka me ya sa ƙaddarar rayuwarta ta zo mata a hakan?

***

Kwance ya ke a kan gado idanunsa a rufe kamar mai bacci sai dai ba baccin ya ke ba tunani ne kawai ya yi wa ƙwaƙwalwarsa yawa har tana shirin bugawa saboda abubuwa sun masa zafi har ya ma rasa ta ina zai suma domin warware matsalar da take gabansa cikin sauƙi, Anwar ya shigo ya same shi cikin wannan yanayin “Amma mutumin nan ka ma raina mutane wallahi, yanzu ko shiryawa ba ka yi ba kasani fitowa ka hanani baccin safe kai kuma kana nan kana more bacci abun ka.” Juye ya yi tare da buɗe idanunsa ya saukar a kan Anwar yana faɗin “Wa ya faɗama bacci na ke, na yi wanka tufafi kawai zan sanya mu tafi ni kaina Dady ne ya azalzaleni a kan na je na kaiwa Abba katin ɗauren aure” Zuba masa idanu Anwar ya yi yana nazarin yanayinsa kafin daga bisani ya ce, “Ba bacci ka ke ba kenan tunani ka ke ko? To kai da likita ne ba zan faɗama illar da tunani ya ke haifarwa ba sai dai ma kai kafaɗawa wani” ajiyar zuciya Hafiz ya yi yana mai saukowa daga kan gado ya ce; “Na rasa yanda zanyi ne Anwar kaina ya ƙulle na rasa gano mafita Anwar.”

“Hafiz koma me ye wallahi laifin ka ne Allah fa baya ɗorawa bawa abinda ba zai iya ɗauka ba, koma me ye kai ne ka so sanya kanka a cikin damuwa” tsaki Hafiz ya yi kafin ya ce, “Matsalata da kai kenan in dai a kan Zhara ne komai na yi a wajanka ba daidai bane sam ba ka fahimtana.”

“Kai ne ba ka kyautawa shi ya sa ka ke ganin kamar fahimtar ka ne bana yi, amma wallahi kai kanka ka san abinda ka ke shirin yi ba abu ne da zai ɓullar da kai hanya mai kyau ba, a shawarci ka yi haƙuri ka karɓi ƙaddarar ka da hannu bibbiyu.” Yana sa hula ya ce, “Dama na faɗama ban karɓa bane, ko na ce ba zan aureta ba, amma nima ai ina da damar auren zaɓina ko itama ƙaddarata ce?” “Allah ya baka damar auren mace sama da ɗaya amma abinda ka ke shirin yi sam bai dace ba.”

“A addini ne ya hana?” Ya masa tambayar tare da juyowa ya zuba masa idanu, yana gyaɗa kai ya ce, “A’a addini bai hana ba, amma dai Hausawa sun ce ana barin halak ko dan kunya.” Wajan adana takalmi ya je ya ɗauki kalar kayan jikinsa yana zura ƙafafunsa ya ce; “kaga Malam tashi mu tafi in dai wannan ne sai mu kwana mu wuni ba za mu taɓa fahimtar juna ba” Tashi Anwar ya yi yana faɗin “ina dai jiye ma ka yin aikin dana-sani, amma tunda ka ce ka ji ka gani Allah ya bada sa’a, duk wanda ya ce yana iya haɗiye gatari sai ka sakar masa ɓota” komai Hafiz bai ce da shi ba ya buɗe ƙofa ya fita Anwar ya girgiza kai aransa yana jinjina taurin kai irin na Hafiz bin bayansa ya yi da sauri.

Fulani

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 2.8 / 5. Rating: 10

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Kuskuren Waye? 6Kuskuren Waye? 8 >>

6 thoughts on “Kuskuren Waye? 7”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×