Tana ɗaki tana saka kaya Hussaina ta shigo ɗakin da gudu "Aunty Zhara Abba na kiran ki." ta juyo tana harareta ta ce, "Ban hanaki shigowa babu sallama ba?”
"Yi haƙuri Aunty Zhara mantawa na yi" tsaki kawai Zhara ta yi ta ƙarasa saka rigar, Hussaina ta fita da sauri.
Ɗakin Mama ta samu Abba da Mama, "Gani Abba" Husaina da Hassan suna rigima Hassan na faɗin "Wallahi ni wannan na ke so."
"Allah ba ka isa ba na riga ka ɗauka ni da na karɓo ni zan fara zaɓa" cikin faɗa Abba ya ce. . .
Masha,Allah Allah ya kara basira
Ma sha allah