Skip to content
Part 8 of 43 in the Series Kuskuren Waye? by Aisha Abdullahi Yabo

Tana ɗaki tana saka kaya Hussaina ta shigo ɗakin da gudu “Aunty Zhara Abba na kiran ki.” ta juyo tana harareta ta ce, “Ban hanaki shigowa babu sallama ba?”

“Yi haƙuri Aunty Zhara mantawa na yi” tsaki kawai Zhara ta yi ta ƙarasa saka rigar, Hussaina ta fita da sauri.

Ɗakin Mama ta samu Abba da Mama, “Gani Abba” Husaina da Hassan suna rigima Hassan na faɗin “Wallahi ni wannan na ke so.”

“Allah ba ka isa ba na riga ka ɗauka ni da na karɓo ni zan fara zaɓa” cikin faɗa Abba ya ce, “idan rigima za ku yi yanzu sai na karɓesu” Mama ta ce; “ku kawo na raba maku ko komai ya zo hannunku sai kun masa rigima.”

“Ina su ka samo chacolet da yawa haka”? Zhara ta yi tambayar tana kallonsu Mama ta ce; “Hafiz ne ya kawo masu” ta yi maganar tana karɓa, Abba ya ce; “dama kiran da na ke ma ki kenan ki je yana ɗakina yana jiran ki dan ba jimawa zai yi ba.”

“To” ta amsa jiki a sanyaye, ɗaki ta koma ta ɗauki Hijab ta sanya har ƙasa, ba wai ta daina sonsa bane yanda take jin sonsa ta sani har iya numfashinta son ba zai bar zuciyarta ba, sai dai kawai auren nasa ne ya fitar mata a rai domin bata son damuwa ta kuma fahimci auren nasa ba ƙaramar damuwa zai haifar mata ba miji ba ya sonta uwar miji ba ta sonta mutum ɗaya ne a ɓangarensa ke sonta kuma ba shi ne za ta zauna da shi ba Mahaifinsa, haƙiƙa tana tausayawa rayuwar da za ta yi bayan auren, da wannan tunanin ta ƙarasa ɗakin da fara’a Anwar ya ce; “lale marhabin da Amarya Barka da fitowa” ƙasa ta yi da kanta tana murmushi ta zauna a kan kujerar da take kusa da ƙofar shigowa kanta a ƙasa ta gaishesu, suka amsa Anwar ya ce, “Ya shirye-shiryen biki lokaci na ta ƙarasuwa ko.”

“AlhamduliLlah” ta faɗa har yanzun dai kanta a ƙasa, Anwar ya ɗan zolayeta ganin ta kasa sakin jiki ya sa ya miƙe yana faɗin, “Bari na je na jira ka a mota amaryar ta ka kunyata ta ke ji.” Ta rufe fuskarta da hannayenta, bayan fitar Anwar Hafiz ya tashi daga kan kujerar da ya ke ya dawo ta kusa da ita ya zauna, gaba ɗaya sai ta ji ta a tukare duk ta maƙure waje ɗaya muryarsa ta tsinkayo yana faɗin, “Amarsu ta ango ba kya laifi ko da kin kashe ɗan masu gida, hakanne ko?” Tana murmushi ta ce, “Anya kuwa?”

“A to hakan na ji hausawa suna faɗi mana” ta yi shiru, “za ki fara halin naki na yin shiru ko?” Ta gyaɗa kai alamar A’a “Ga shi kuwa yanzun ma amsar da kai a ke bani, me ya sa idan na kira wayar ki ba kya ɗagawa?”

“Ba komai” ta ba shi amsa a taƙaici, “Anya ba komai? Ko har yanzu ba ki manta da abinda ya riga da ya faru ba?” Nan ɗin ma gyaɗa masa kai kawai ta yi ajiyar zuciya ya yi kafin daga bisani ya ce; “Zhara na tambaye ki?”
“Eh” ta amsa masa a taƙaice, gyara zamansa ya yi yana fuskantar ta kafin ya ce, “Na taɓa cewa bana sonki?” Ta gyaɗa masa kai “magana za ki yi ba wai gyaɗa kai kamar wata ƙadangaruwa ba.”

Tana gyaɗa kai ta ce; “A’a baka taɓa faɗa ba, amma kuma bakin da ba zai ma ƙarya ko sharri ba ya faɗa mahaifiyar ka.” Ya ja numfashi ya furzar a hankali kafin daga bisani ya ce; “Na yarda da maganar da ta faɗa amma kuma ba ki ji a bakina ba ko? Dan haka na roƙe ki da ki manta da wannan zancen mu yi shirye-shryen biki cikin kwanciyar hankali abu ne da ba za a fasa ba kinga kenan wata jayayya ko ka ce na ce duk bai tasu ba kawai mu yi abinda ya ke gabanmu” hawaye ne taji sun ciko mata idanu zuciyarta ta mata wani irin nauyi ‘wato da gasken ba ya sonta kawai zai aureta ne saboda babu yanda zai yi tunda ya san ba zaiyu a fasa ba’ “Kinyi shiru” ya katse mata tunani murmushi ta yi kafin ta ce; “Yaya Hafiz dama ai ban ce na ɗauki hakan wani abun ba, ni na karɓi ƙadarata a duk yanayin da ta zo min, dan haka ba ka da matsala dani.”

“Uhm! Allah Ya iya mana, yanzu wani shiri ki ke?”

“Na me fa?”

“Na biki mana an buga katin ɗauren aure su ne ma na kawowa Abba, so na ke na ji dame-dame za ku yi muna zuwa sai na bayar a buga katin ko da ban zo ba Anwar ya kawo ma ki.”

“Walima ce kawai za mu yi, sai Musaffa.” Ya zuba mata idanu yana faɗin “bayan shi fa, ba za ku yi kamu ba da dai sauran bukukuwa irin na ku na mata?” Tana gyaɗa kai ta ce; “A’a gaskiya walima ita ce sunnar da Manzon Allah (S.A.W) ya koyar da dukan ma’aurata da su yi domin samun albarka a cikin aure, Musaffa kuma maganar Allah ce za a tafru a karanta, sauran bukukuwan kuma ra’ayi ne idan mutum ya so ni kuma hakan bai taɓa burgeni ba.”

“Oh ashe fa amaryar tawa uztaziya ce, shi kenan Allah ya nuna mana ni zan tafi.” Ya cire kuɗi masu yawa ya bata taƙi karɓa “Me ya sa ba za ki karɓa ba”? “Ba komai” ya ɓata rai yana faɗin “To ki karɓa bana son musu” ta karɓa da hannu biyu tana masa godiya, ya ma ta sallama.

Ɗakin Mama ta je Abba ya fita ya su yi sallama, ta ba Mama kuɗi Mama ta tambayeta na me ye ta faɗa mata ya ba ta ne kawai “Kin san bana son yawan karɓar kuɗi ko”?

“Mama shi ne ya matsa sai na karɓa fa”

“To ki dai kiyaye karɓar abinsu gara idan anyi aure duk abinda ya ba ki wannan matarsa ce ke, amma yanzun mu kiyaye mutuncinmu ya fi” Abba da ya ke shigowa ɗakin ya ce; “me ye abin faɗa dan ya bata kuɗi ko ba maganar aure a tsakaninsu ai Yayanta ne zai iya yi ma ta komai, na fahimci har yanzu a kwai wani abun a ranki gami da aurennan” Mama ta yi shiru Zhara ta fita, bayan fitar Zhara Mama ta ce, “Ni ba komai a raina kawai dai naga kamar yawan karɓar kuɗi a hannun namiji ba mutuncin ‘ya mace bane, amma tunda ka faɗi hakan shi kenan Allah ya taimaka.”

“Amin, ya dai fi ɗin” ya faɗa yana zama kusa da ita, ta bashi kuɗin ya ce; “A’a ki bata abinta mana, yawwa akwai maganar da nake so mu yi da ke dama” ya gyara zamansa kafin daga bisani ya ce, “Munyi magana da Yaya ya ce shi ne zai yi komai, duk da na so ya bari ko wani abunne a ce mun saya mata amma sai ya hau faɗa dan haka me ki ke ganin ya kamata a ce mun saya mata a matsayinmu na iyayenta dan sauke hakƙinta da ya ke kanmu”?

“To Abbansu abinda duk kaga ya dace a yi, tunda shi Yayan ya dage shi ne zai yi komai dole a bar masa komai ɗin.”

“Hakanne, am ni tunanin da na ke ko zan bata kuɗinne sai ta yi sana’a da su idan har mijin nata zai amince”?

“Gaskiya wannan shawarar ta yi, sai dai to idan bai zai yarda ba fa”? Shiru ya yi yana nazari kafin ya ce; “mu dai bari bayan auren idan ya ce bai amince ba sai muga abinda ya kamata a yi ɗin.”

“Allah ya nuna mana”

“Amin, ni zan fita a kwai abinda ku ke buƙata?”

“A’a Allah ya tsare a dawo lafiya”

“Amin.” ‘Har cikin ranta bata so a ce Yaya ne zaiyi komai ba da ya bari sun yi wa ‘yarsu kayan ɗaki iya zarafinsu shi ne mutuncinsu amma ta tabbatar gori da shagwaɓi sai sun sha shi a wajan Hajiya Turai, kawai dai faɗan da ya fi ƙarfinka ka mayar da shi wasa.

*****
A mota faɗa ne ya kure tsakanin Anwar da Hafiz, Anwar ya ce; “wai Hafiz me ya sa ka ke yin abu da rashin lissafi ne saboda Allah, ni ba inda zan je daga nan Kano kawai za mu In Sha Allah.”

“Wai kai me ye matsalarka da ita ne?” Hafiz ya yi tambayar ransa a ɓaci, “Saboda cin amana ne bana so wannan abun da ku ke daga kai har ita cin amana ne kuma wallahi ba ku yi wa Zhara adalci ba, ni banga me tafi Zhara da shi ba da har za ka sota ka nemi cin duduniyar ‘yar’uwarka wacce ku ke shirin aure.”

“Kana bani Mamaki Anwar me ye cin amana anan ɗin na ce ne ba zan aure Zhara ba ita wacce na ke so zan aure? Ko kuma haɗasu duka na aura shi ne cin amana? Allah fa bai haramta aurena da ita ba dan ina auren Zhara” Anwar ya ɗan kalleshi kafin daga bisani ya mayar da dubansa ga tuƙin da ya ke yana faɗin “na yarda babu haramci amma kuma hausawa sunce ana barin halak ko dan kunya ko?” “Ni ba ruwana da wata magana ta hausawa ba zan haramta wa kaina abinda Allah bai haramta min ba, ba kuma zan shigo garin-nan na wuce ban ganta ba” parking Anwar ya yi gefen hanya ya kalle gefen da Hafiz ya ke zaune ya ce’ “Shi kenan ba zan hanaka tafiya ba, a sauka lafiya” ya buɗe motar ya fita ya nufi bakin titi ya tsaya Hafiz ya fito motar ya dawo ɓangaren direba ya zauna ya rufe ya ja motar a fusace ya bar wajan, Anwar ko kallon ƙurar motar bai yi ba yana tarar mota har Allah ya sa ya samu motar da za ta Kano ya shiga.

Tsaye ya ke ƙofar gidan nasu ya ta gwada kiran number kamar koyaushe bata shiga, da ƙyar ya samu yaro ya aika a kira masa ita jim kaɗan yaron ya fito ya ce; “wai ance waye?”

“Ka ce baƙo ne” yaron ya juya ya shiga jim kaɗan ya fito ya faɗa masa tana fitowa, ya yi wa yaron godiya, sam bata so fitowa ba Hajiya ce ta matsa mata hakan ya sa dole ta fito ganin shi a tsaye ya sa ta yi turus tana kallonsa a tsorace, ƙarasawa ya yi gabanta ya tsaya yana kallonta ta juya da sauri ta shiga suro ya biyota za ta shiga cikin gidan da zafin nama ya riƙo hannunta suka tsaya cikin suro cikin sanyin murya ya ce; “me ye haka Baby me ya sa ki ke so ki wahalar da zuciyar da take tsananin sonki”? Lumshi idanunta ta yi zuciyarta na dukan uku-uku ta kasa cewa komai ta kuma kasa janye hannunta, “Halima” ya kira sunanta cikin wani irin yanayi da har sai da taji a jikinta, ya ci-gaba da magana ba tare da ya damu da ta amsa masa ba “dukanmu mun yarda da zukatanmu a sarƙi su ke da ƙaunar juna bai kamata ki tilasta ni santa zuciyarki da tawa zuciyar ba wanda kin san yin hakan ba ƙaramin illata mu zai yi ba” muryarta na rawa ta ce, “na sani Love amma bani da ƙarfin zuciya ko idon da zan iya kallon Zhara na faɗa mata ina son mijin da za ta aure har kuma wai muna so mu yi aure, gaskiya ba zan iya ba! Kawai kamar yanda na faɗama a baya mu haƙura shi ya fi” fuskarsa babu Annuri ya ce, “a wajanki ne ki ke ganin shi ya fi amma ni a wajena hakan sam ba mafita bane, ki bar komai ahannuna na san me zanyi” ta zuba masa idanu ta kasa cewa komai ya gyaɗa mata kai cikin nuna tabbaci ya ce, “ki yarda dani na sani kina tsoron kar amince ku da Zhara ya samu matsala ba zan bar hakan ya faru ba, amma ki sani aurenki dani ba fashi.”

“A’a Hafiz sam hakan bai dace ba mu dai yi haƙurin kawai”

“Mu yi haƙuri mu yi haƙuri ki ke ta faɗa to ni na faɗa maki ba zan iya haƙura da ke ba, idan har kuma ki ka na ce da lallai-lallai sai mun rabu tabbas zan je yanzu ba sai anjima ba na faɗa mata komai na faɗa mata ke na ke so ba ita ba, duk abinda zai faru ya faru!” Ya yi maganar a fusace ta kalleshi da matuƙar tsoro tabbas zai iya, ‘ita kam ta shiga uku me yasa zuciyarta za ta mata wannan rashin adalcin da ta sani tun farko kar ta suma yin abinda ta san ba za ta iya hana zuciyarta soyayyarsa ba’ ta yi ƙasa da kanta tana kuka mai sauti ya sunkuya gabanta ya sa gwiwoyinsa a ƙasa cikin sigar lallashi ya ce “don Allah Halima kar ki hana zukatanmu sukuni na tabbata kina sona karki hanamu cikar burinmu saboda wata alaƙar da take tsakaninki da Zhara” sunkuyawa ta yi gabansa tana kuka tana faɗin “ina sonka Hafiz na sani ba zan iya raba zuciyata da sonka ba har abada, haka rabuwarmu tamkar raba rayuwata ne da duk wani farin ciki amma r… Yasa hannu ya rufe mata baki yana gyaɗa kai ya ce; “bana son jin wannan kalmar Baby Ina sonki babban burina ki kasance matata kuma In Sha Allah sai hakan ta faru ni dai fatana kawai ki bani haɗin kai” ta kasa cewa komai ya miƙa tsaye yana duba agogon hannunsa kafin daga bisani ya mayar da dubansa gareta yana faɗin “zan tafi kar na yi tafiyar dare ki kular min da kanki” ya ciro kuɗi masu yawa ya bata da ƙyar yasa ta karɓa ya tafi tana tsaye cikin suro har taji tashin motarsa ajiyar zuciya ta yi ta koma ciki.

*****
Ke da ki ka ce ba za ki fita ba ya a kayi ki ka daɗi”? Hajiya ta mata tambayar tana mai zuba mata idanu Murmushin ƙarfin hali ta yi ta faɗa ɗaki da sauri, “shiryayya ai dana-sani na ƙyaleki ɗin kar ki tafi” Hajiya na rufe baki Zhara ta shigo gidan bayan sun gaisa da Hajiya ta shiga ɗaki ta samu Halima tana kwance rub da ciki idanunta a rufe, ta kai mata duka tana faɗin “ba dai bacci ki ke ba?”

Juye Halima ta yi tare da tashi zaune tana faɗin “baccin lafiya yanzu da yamma kawai dai na kwanta ne” Zhara ta zuba mata idanu kafin ta ce; “me ya same idanunki sunyi ja kamar ma kuka ki ke” shafa fuskarta Halima ta yi tana gyaɗa kai ta ce, “kuka kuma a’a kawai dai yau na tashi da ciyon ido ne.”

“Ayya sannu Allah ya ba ki lafiya, dama zuwa na yi mu yi magana tunda ba kya jin daɗi shi kenan bari kawai daga baya ma yi maganar.”

“Haba faɗa min me ye”? “Yaya Hafiz ne ya zo ya ke tambayata wai dame-dame za mu yi”
“To me ki ka ce masa?”

“Walima da Musaffa kawai na ce za mu yi” Halima ta kai mata duka tana faɗin “amma yarinyar nan mugun ‘yar rainin wayo ce kina nufin ba za mu yi kamo da dena da sauran bukukuwa ba?”

“Kema dai kin san duk bana ra’ayinsu.”

“Wallahi ba ki isa ba ko ba kya so mu muna so ba za mu yi bikin lami ba dole ne sai mun raƙarƙashe kiransa ma zanyi ya bamu kuɗaɗi ya kuma mana shirin gaske” Zhara ta harareta ta ce; “hum-um ashe kuwa ana shirin biki babu amarya” tsaki Halima ta yi tana faɗin “gaskiya ke banza na sani tsab za ki ƙi zuwa wannan ƙarami ne a cikin halinki, Allah ya kyauta ma ki” ta ƙarasa maganar cikin jin haushi murmushi Zhara ta yi.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 2.2 / 5. Rating: 13

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Kuskuren Waye? 7Kuskuren Waye? 9 >>

2 thoughts on “Kuskuren Waye? 8”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×