Cikin daren nan ban runtsa ba. Idona biyu har aka yi assalatu. Duk sa’adda na yi juyi sai na ji wani irin dunƙule kamar curin fura ya taso daga tumburƙuma ta ya tokare kafofin shaƙar numfashi na. Sai na ji na rasa walwala ina tuna irin cin zarafin da tsamurmurin mutumin nan ya yi min. A ganina ko da baƙaƙen maganganun da ya farfaɗa min sun isa su fusata ni. Maganganun suka riƙa diro min kamar dirar harsashi kamar ta amsa kuwwa.
“Ɗan tsuguni da kai. Yaushe ka isa aure? An gaya maka aure abin wasa ne ko ƙiriniya? Wacce sana’a gare ka? Mene ne matsayin iliminka? Kada ka ƙara zuwa gidan nan idan kana son kiyaye mutuncinka, kodayake ba ka san shi ba da tuni ka daina damunmu da zuwa wajen ‘yarmu da sunan zance ba tunda aniyarka ba ta alheri ba ce. Mutumin kawai!”
Maganganun suka yi ta dawurwura a ƙwaƙwalwa ta kamar amsa kuwwa.
Na yarda ban isa aure ba saboda ban mallaki ko daya daga sharaɗan da aka gindaya na yin aure ba. In ban da shekarun munzali ban mallaki wani abu ba daga sharuɗɗan da suka gindaya min. Karewar ta ma, ‘yar sana’ar da nake yi ta rini an rushe rumfar kan cewa ta hau kan titi. Yanzu dai bani da aikin fari balle na baƙi, ina kuwa zan samu tsububin kuɗi har dubu ɗari da sunan kuɗin gaisuwar aure? Da na mallaki wannan adadin ma ai ba zan kashe su haka ziƙau ba, sai na ware waɗanda zan ɗinka sutura ta kece raini, hakan zai sa ƙila na huta da gorin tsohon nan wai shi kakanta, idan zai kore ni yayin da na je gidansa zance.
“Kana yawo da riga kamar ta ƙaninka wa zai ba ka auren ɗiyarsa? Tafi ka koyi saka suturar kirki. Kar na ƙara ganinka ƙofar gidana.” Ya sha maimaita min wannan maganar. Ni kuwa da naci kamar makahon kare, ba na iya daurewa sai na je na yi ido huɗu da sahibata Bahijja. Danginta duka sun nuna a zahiri ba sa tare da ni. Yau dai ta faru ta ƙare, an yi wa mai dami ɗaya sata.
Na ji gaba ɗaya raina dubu ya ɓaci musamman idan na tuna irin naushin tashi ka sha garin da wani gwabjejen ƙato ya yi min bisa umarnin kawunta da kakanta waɗanda suka yi min dirar mikiya a inda nake rakaɓe da ‘yarsu. Su bisa tilas suke nufin na daina kula jininsu tunda bani da ƙumbar susa. Da sun kwantar da hankalinsu ma, tuni na fita daga tarkon kaunar Bahijja tunda na fahimci ba irin takunmu ɗaya ba. Ni na fi son rayuwar raɓi-ka-wuce, ita kuma da danginta sun fi son a yi ta ta ƙare.
Na yi ta juyi bisa katifata mai cike da tsummokara da shirgin suturana masu dauɗa. Duk juyi ɗaya sai na yi ƙwafa ina mai tunanin hanyar da zan bi na rama irin wulaƙancin da suka yi min a daren jiya. Wata zuciyar na ƙarfafa min gwiwar dole sai na ɗauki fansa. Idan ma bani da ƙarfin rama dukan, bai kamata na bar zagin da suka yi min ya wuce a banza ba. Babu shakka sai na rama zagin nan ko da kuwa zan rasa ragowar ƙarfin nawa. Zuciyoyina duka suka ƙarfafe ni kan wannan aniyar.
Haka na kwana na hantse cike da ɓacin rai da kuma burin ɗaukar fansa ko ta wanne hali. Abu ɗaya zuciyoyina suka fi ƙarfafa min domin fashe fushina shi ne na samu aji garau domin na samu kuzarin kantafi da garin Kano yadda zan iya juye duk wani abu da ke cikin raina kan waɗannan da nake kira ‘ƙadangarun wofi’.
Na yi hanzari na kintsa ba tare da na yi karin kumallo ba, na yi tsinke wajen Girbas Mai-Aji Garau. Na yi sa’a yana gida bai fita ba. A gurguje ya bani ‘yan ƙwayoyi guda shida masu launin rawaya da ja, ya ce na kora da ruwa.
“Ka ga wannan rawayar sunanta a Zunguri Duniya. Idan ka sha za ka iya ɗaukar duniyar nan duka a kafaɗarka ba tare da ka ji komai ba. Wannan jar kuma danjaros kenan. Ita amfaninta duk abin da ka tuno a ranka shi za ka aikata. Idan ka sha ka yi tunanin kuka, to shi za ka yi ta yi, in dariya ce ma za ka yi ta ƙyalƙyalawa. Don haka in zagi kake son yi da zarar ka sha, sai ka daina tunanin komai sai zagi. Na tabbata za ka dawo ka ban labari.”
Na tafi gida cike da murna gida da kuma soma shirin zuwa gidan kakan Bahijja na juye musu kwandon zagi da sassafe. A raina ina cewa, ‘yau za ku gamu da gamonku a wajena’.
Zuwana gida ba jimawa na yi karin kumallo a gaggauce. Babban burina na garzaya inda zan sauke kwandon zagin da na soma tarawa cikin ma’ajiyar kwanyata.
Babu jimawa sai na ji kwanyar tawa ta soma lodin manya – manyan ashar irin na tsofaffin maguzawan asali da rinjawan kauye ɗin nan da kuma irin zagin ‘yan zangero, waɗanda zan ƙundumawa tsofaffin tare da yanko ba’a ‘yar asali na lafta musu. Na riƙa ji a raina cewar farar ƙwayar nan, za ta ninka min ƙarfina zuwa kamar ninki ɗari biyu ko fiye da haka yadda zan kama wuyan Uzairu, watau yayan Bahijja da ya naushe ni na faɗi. Kawunta kuma zan yi masa kamun kare ga zomo na watsar gefe ɗaya. Shi kuwa kakanta nata da yake ya manyanta, kwaf ɗaya kurum zan yi masa bayan na kare masa zagin tsame nama.
Ina cikin wannan tunanin sai na ji cikina ya murɗa, yana wani irin ƙugi kamar tashin tsohon babur mara salansa. Na ƙaddara cewa bayan gida ne ke ƙwarzaba ta. Na shiga domin biyawa jiki buƙata na samu sauƙin rugugin da cikin ke yi.
A cikin banɗakin sai na ga wasu ‘yan ƙwari ƙanana-ƙanana suna wani irin kumburi suna ƙara girma kamar ana buga musu famfo. Na ga wani kyankyaso yana kallona yana dariya. Bakinsa har da haƙora. Haushi ya kama ni, nan take na soma maimaita haddar ashar ɗin da na iya tunowa na shiga zazzagawa kyankyason nan. Shi kuwa bai ma san ina yi ba sai dariya yake min. Sai na lura kusan dukkan ƙwarin nan dariya suke min a lokaci guda kuma sai na ga suna ƙara girma kuma yana motsewa su koma ‘yan ƙanana har ba a iya ganin su idan sun motse.
Ban koma ta kansu na fito na shiga ɗakina domin na ɗauki sandar da zan jibgi mutanen nan da suka yi min ƙanƙanci watau Kakan Bahijjja da ‘ya’yansa. Ina shiga ɗakin sai na ga fankar sama na juyawa da ƙarfi tana shillo zuwa ƙasa tana qkawo min cafka kamar za ta fille min wuya. Na yi wuf cikin hanzari na kwanta rub da ciki. Ba don haka ba gani nake da tuni kan nawa ya jima da barin gangar jikina.
Sai kuma na ga fankar ta cilla sama can ƙololi, ta yi min nisa fiye da yadda na saba ganinta. Sai na lura ashe ma komai na ɗakin gaba ɗaya ƙara tsawo yake yi, dandaryar sumintin kuma na ga tana ƙara yin ƙasa, can ƙasa. Na ga ina lumewa ƙasa abubuwa na ƙara tsawo. Sai na ganni tamkar ina cikin injin hawa bene yana yin ƙasa da ni, na ga garun ɗakin nawa yana ƙara tsawo da sauri. Hakan ya fusata ni na shiga antayawa bangon nan zagi irin na asalin maguzawan ƙauye.
Da dai na ga bangon ba zai daina miƙewa ba, sai na rabu da shirmensa na fito na daddagara na fita waje. Ba domin na fita ba, da ɗakin ba zai daina miƙewa sama yana ƙara tsawo ba. Haka na ƙaddara a raina.
Sandar da na riƙo zan yi duka da ita sai na ga tana motsi. Ba jimawa ta rikiɗe zuwa wata shirgegiyar macijiya. Sai na jefar da ita a tsorace na shara da gudu. Ina cikin tafiya sai na lura duk gidajen da na wuce suna biyo ni a baya. Idan na tafi su tafi, idan na tsaya su tsaya. Da na ga haka sai na faki idonsu na shara a guje, su ma gidajen gaba ɗaya suka runtumo da gudu suna biye da ni. Na kara fallewa da gudu suna biye da ni ƙafa da ƙafa.
Na zo daidai wani katafaren kogi, ga gidaje na biye da ni za su hallaka ni. A sanina dai kogin nan wata kwalbati ne da ya ratsa unguwar mu. Yau kuma sai na ga ta rikiɗe zuwa wani katafaren kogi, ruwa na toroƙo. Na hangi wani kwale-kwale a tsakiyar kogin. Zuciya ta raya min da na bari gidajen nan su hallaka ni, gara na shiga kogin na hau kwale-kwalen na gudu. Ba tare da wani tunanin ba na tattakura na daka tsalle na yi daken cikin kogin nan.
***** ***** *****
Sannu a hankali na buɗe idanuna, hayaniyar da nake jiyowa sama-sama da maganganu ƙasa-ƙasa ya sa na yi wur da idanuna, sai na fahimci cewar kwance nake a wani matsakaicin gado, hannuna sagale a jikin wani ƙarfe. Ƙafata na gan ta harɗe da wani irin ƙarfe. Na yi yunƙurin miƙewa zaune sai na ji na kasa. Na ji muryar yayata tana kiran Innata tana cewa, “Umma ya farka.” Umma ta rugo da gudu zuwa kaina. Idanunta cike da hawaye.
“Sannu ɗan nan. Allah ya ba ka lafiya. Ya sa kaffara ne.” Na wulƙita idanuna, na ga ‘yanuwa da abokan arziki ne tsaitsaye kaina. Sai na haƙiƙance cewar asibiti aka kawo ni.
Sannu a hankali ƙwaƙwalwa ta ta riƙa tunano min abin da ya faru da ni. Duk da har a lokacin ina jin tasirin miyagun ƙwayoyin nan tare da ni amma zuciyata cike take da nadama. Na yi ta roƙon Allah gafara tare da ƙudirin cewar ni da ƙwaya har yaumut tana. Gefe ɗaya kuma na yi ta fatan kada likita ya gano musabbabin da ya jawo mini karaya gami da raunuka. Ina ta maimaitawa a raina cewar tushen kowacce tsiya da asara yana tattare da shan miyagun ƙwayoyi.