Skip to content
Part 14 of 14 in the Series Kyautar Zuciya by Bilkisu H. Muhammad

*****

“Ta canza komai nata ya canza, muryarta, furucinta, kawaicinta da komai… kai komai ma ya canza, ba ta da kamun kai, ji nake yi kamar ba ita ba, ba za ta taba komawa ita ba. Ban amince da wannan din ba, akwai abin da ke shirin faruwa”.

Salim ya dora hannu kan kafadarsa.

“Calm down, yau fa ka taba dora ido a kanta, za ta iya yin komai don ta gwada ka. Ka bi ta kawai a haka zuwa wani lokaci”.

“Ka sani halayyarta su ne suka fisgo ni, idan haka ta ke me ye amfanin alaka da ita ba shi da amfani na zan sake zuwa ba, zan goge lambarta, bana sonta a rayuwa”.

Wayarsa da ke ringin ta katse shi daga abin da yake son fadi, lambar Aazeen ya gani. Bai iya dagawa ba, Salim ne ya dauka ya danna handsfree, muryar Nurat ta karade dakin.

‘Gaya min ka koma gida lafiya?”

Bai amsa ba. Ba ta damu da jin amsa ba, ta dora da fadin.

“Za ka zo gurina, ka zo a Lifan, ba ka taba ce min kana da abin hawa ba, gaya min na wa ka aro?”

Wani irin takaici ya turnuke shi, zai yi magana a zafafe da sauri Salim ya dakatar da shi gurin shafar kirjinsa.

“Eh na abokina na aro, ko laifi ne, so ki ke yi komai sai na gaya miki?”

Sai da ta dan yi dum duk jikinta ya yi sanyi.

“Nufina ko a ya ka ke ina sonka, da ma so nake yi in ce goben da karfe nawa za ka dawo?”

Shi kansa ta kashe masa jiki, duk sai ya ji bai ji dadin yadda ya dauki zafi ba.

“Kamar yadda na zo yau”.

“Okey, shi kenan, na gode”.

Ta katse wayar. Zama ta yi a bakin gado. Anya Aazeen ba ta kwafsa ba? kada fa ta nuna masa ita wayayyiya ce, in ta ci gaba da yin haka za ta rusa komai.

“Kanwata ya aka yi ne?” Aazeen ta tambaya cikin kokarin zama kusa da ita.

“Ba ni waya ta, kin kira shi ko?”

Kada mata kai kawai ta yi.

“Ya na ganki duk a sanyaye? Ko dai akwai matsala?”

Ta rasa ta yadda za ta fahimtar da ita, ta furzar da huci.

“Yayata shi din fa ba wani wayewa ya yi ba, ya kamata ki dan dinga sassauta kalamanki har ku saba”.

Aazeen ta tuntsire da dariya.

“Kawai dai cewa za ki yi dan kauye ne. Okey, kada ki damu, zan bi da shi yadda yake so, don ina matukar kaunarsa. A hankali zan maida shi yadda nake so”. Ta fada a fili, “Sai na lalata shi, sai na gigita tunaninsa.

“Na kasa fahimtarta, tana rikita ni, kalamanta sun sha bamban da na fili. Kai akwai wata a kasa, ko me zan fahimta, ko ma wace ce ta cikin waya zan gano ta. Ita din ba za ta taba zamowa waccan din ba, ina jin haka a jikina”.

Samir ya dafa kafadarshi.

“Haka nake son ji my man, ka bi komai a sannu”.

Komawa ya yi ya zauna.

“Nurat!” Ya ambata a can karkashin zuciyarsa, me ya sa ta kasa goguwa a ransa? Duk da kokarin yakice ta da yake yi amma al’amarin tamkar tiri, aibunsa ba zai taba barin cikar burin nasa ba. ya sani yana son Nurat, a jininsa yake bai taba haduwa da wata halitta da ta hana shi sukuni kamarta ba.

Salim ya tsuguna a gabansa.

Deedat ya dube shi, “Tilas ne ni din sai na zamo mai aure, me ya sa Ummita ba za ta bar ni na yi rayuwa ta ni daya ba?”

“Aure shi ne cikar kamalarka, abokina kai babban mutum  ne, aure ne ya kamace ka”.

Salim ya dinga lallashinsa, tare da janyo masa ayoyi, har sai da Deedat ya dinga jin zai yi auren ko don cika umarnin Ubangiji, zai yi aure kawai ko da ba zai so matar da zai aura ba.

Ya jinjina kai, “Zan yi aure, zan yi yadda ku ke so, zan zauna da wadda Allah ya hada mu duk da na san babu wadda zan taba so, zuciya na kamuwa da soyayyar wadda ke kyautata mata, da zaran ka samu mai kyautata maka za ka so ta komai zai zamo labari. Na sani Nabila ba za ta kyautata min ba, ita kanta waccan din na gama karaya”.

“No, Ubangiji na iya juya al’amarinsa”.

Ya dora hannunsa a kan na Deedat cikin kokarin kwarara masa gwiwa.

*** *** ***

Ta lumshe ido, Deedat kawai ta ke tunawa, fuskarshi kawai ta ke gani, mafarkinta ya dinga dawo mata, wani irin nishadi ta dinga ji. Ta yi murmushi duk me ye wannan? Me ke faruwa da ita? Kenan wannan shi ake kira so? Tabbas in haka ne so na da dadi.

Tab lallai Yaya Aazeen ba ta taba sanin so ba, duk wannan girman nata. Soyayyar kudi kawai ta sani, ina ma Allah zai jarrabe ta da soyayyar Adamu haka?

Ta yi murmushi, lokaci daya kuma ta ji kunyar kanta.

“Anya ni ce kuwa?” Ta tambayi kanta.

Ta dinga Allah-Allah litinin ta yi ta koma makaranta, kila ta ga abokin principal. Humm da alama wannan mafarki tafe yake da guguwar sonsa a zuciyar Nurat.

“Mrs. Zaruk gaya min tunanin me ake yi haka?”

Ras! Gabanta ya buga don gaba daya ta mance da batun wani Zaruk.

“Me ye na ga kin wani yi kicin-kicin ko kin mance alkawarinmu?”

“Yaya ta ina sani”. Ta ce da ita don ba ta son tuna zancen. Sai a lokacin ta daga kai tana kallon Aazeen, shigar da ta yi har gwara ta jiya.

“Yaya Aazeen amma za ki dora after dress a kan kayan ko?”

“Kamar ya? Akwai aibu tattare da kayan ne? Ke ni fa dadina da ke kauyanci, kuma ki shirya yau za ku gaisa da shi”.

Jinjina kai kawai ta yi, ta sani muddin za ta ci gaba da nuna wayewarta Adamu zai iya guduwa.

“Kina ji ina yi miki magana, budirin me ake yi? Ni ma ga ni a yi da ni”. Hajiya Rahma ta fada lokacin da ta shigo dakin.

“Ammi bakona ne nake cewa ta shirya za su gaisa”.

Hajiya Rahma ta dinga murmushi a can karkashin zuciyarta addu’a ta ke yi Allah ya sa karshen zaman Aazeen ne a gida ya zo, ta ga alama a kwana biyun nan suna cikin farin ciki.

A fili ta ce, “Ai ba ma Nurat ba, har da ni ma za mu gaisa”.

“Kai-kai-kai Amminmu, lallai mutumin nan ya taki sa’a, ina ma ya zo a yadda nake so? Ina ma mai kudi ne?”

Ta dawo bayan Ammi ta tsaya tare da rungumo ta, ta dora kai a bayanta.

“Ammi shi din talaka ne, sai dai in kin ganshi sai ki zaci wani shege ne, amma ba shi da kyau ma sai tsabar kyau shi ya sa nake jin cewar zan iya maleji da shi. Ammi kullum kuna cewa na yi aure kila wannan karon na yi don ina sonsa, zan san yadda zan yi ya yi kudi ta kowacce hanya zan bi ya yi kudi”.

Ba Ammi ba, hatta Nurat ta yi mamakin kalamanta.

“Ki yi fatan Allah ya sa ya zamo alkhairi a gare ki, sai ki ga ya zamo mai kudin kin ji”.

“Ammi dole ne fa ya yi kudi, alheri ai in dai maikudi ne ka da ma ya zamo alkhairi”.

Wayarta ta hau kara.

“Ammi, ina jin ya karaso, Allah ya sa ‘yan iskan yaran nan sun gama shirya komai”.

Ta yi waje a sukwane.

“Ammi kin ga fa a yadda za ta je gurinsu?”

“To ya za a yi? Sai addu’a, komai zai zamo labari. Ammi shi din fa ba kamar yadda ta ke so yake ba”.

“Kada ki damu, ina fatan nan gaba zai iya sauya ta muddin tana sonsa. Ban taba jin Aazeen ta ce tana son wani ba, ko ba komai an samu ci gaba”.

Nurat ta yi murmushi cike da farin ciki, ta ce, “Haka ne Ammina”.

Zaune yake hannunsa rike da waya yana chat da abokan kasuwancinsa, sanye yake da kananan kaya, sun yi matukar yi masa kyau, ta sawo kai babu ko sallama, hakan ne ya sanya bai san da shigowarta ba.

Kare masa kallo ta keyi, wani irin sonsa da kwarjininsa duk sukatarar mata. Ita kam ko a cikin shugadaddi da samarin da ta ke mu’amala wadanda suka ci sukatada kai, ba ta ga wanda yake mata wani irin kwarjini irin Deedat ba, ga wani shakkarsa da ta ke yi. Kai wannan mutumin na daban ne, to ko don shi din mai kyau ne?

Murmushi ta yi hade da gyaran murya. Da sauri ya daga kai idanunsa suka gauraya, ta sake sakar mishi murmushi, fararen hakoranta masu dauke da wushirya suka bayyana. Ya dauke kai, tana son ta shige masa sai dai ina! Ba ta san dalilin da ya sa ta kasa yin hakan ba, ta dan bada tazara tsakaninsu ta zauna.

“Ka gaji da jira ko?”

“No, kada ki damu”.

Suka dan yi shiru zuwa wani lokaci ta numfasa.

“Na ga kamar ka canza”.

Ya dan dago kai cikin zuba mata manyan idanuwansa. Gaba daya ta dinga jin kasala na saukar mata, tana jin kamar ta je ta rungume shi.

“Me ya sa ki ka ce haka?”

“Kawai dai”. Ta ce.

“Bai sake bi ta kanta ba, ya hau sabga da wayarsa.

“Wayyo Allah, yau na hadu da gamona, talaka sai shegen girman kai.

“Bismillah, ya kamata ka ci wani abu ko?”

Ta shiga kiciniyar tsiyaya masa lemo a cup.

“Ga shi”. Ta ce da shi.

Ya karba ya ajiye.

“Am… da ma ina son tambayar aikin da ka ke yi”.

“Kina bukatar maimaici kenan?”

Duk ta dabarbarce.

“Ji nake yi na dade da shaida miki?”

“Okey haka ne”.

Ya sake tabbatar da zarginsa.

“Ba ni da takamaiman aiki, duk abin da ya samo so nake yi, tuntuni na gaya miki”.

“Adam babu abin da ba zan iya yi maka ba, za ka zamo duk yadda ka ke so, za ka taka duk wani matsayi”.

“Me ya sa ba za ki bar ni a matsayina ba, ina jin dadin rayuwa ta a haka, ina ci ina sha, shi ya sa bana hangen sama. Kullum kasa nake hanga, haka ne ke sa wa na dinga gode wa Allah”.

“Amma Adam kowa na son ci gaba, inda ba ka bukatar ci gaba da samun guri za ka yi ka kwanta”.

Ya yi murmushi.

“Da alama kina gaba da talauci”.

Ta jinjina kai.

“Sosai kuwa”.

“Kintaba dandanar shi talaucin ne?”

“No, ko kadan ban taba ba, kuma ba zan taba ba”.

“Babu mamaki nan ngaba  ki taba tunda kin shirya rayuwa da talaka, amma kuma ai bai kanata ki daura gaba da talauci ba, tunda ba ki taba dandanarsa ba”.

“Ko ban dandana ba, ina jin yadda duk wani talaka ke neman tsari da shi talaucin”.

“Haka ne, amma ba ki sani ba, shi wannan talakan ya fi ku inganci da komai”.

“Tab! Ina da aiki da alama wannan ya gama rika a talaucin”. Ta ayyana a zuciyarta.

“Ya kamata mu bar wannan zancen, don ba za ka fahimta ba, amma ka bari da sannu kai da kanka za ka dinga gudar wa talauci”.

Ya kalle ta a sakarce.

“Yaushe kenan?”

Ta mike tsaye ta dan yi tattaki ta komo gabansa ta tsaya, lokacin da na sauya ka, lokacin da na koya maka hawa manyan motoci, na koyar da kai cin abinci mai dadi. Lokacin da na koya maka shigar tsadaddun kaya”.

“Oh haba?” Ya ce da ita.

Dan zaman da ya yi da ita ya gama sanin wace ce ita, dabi’unta gaba daya irin wadanda yake kyama ne, shi kam dariya ma ta soma ba shi. Gani ya yi ta mike.

“Kanwata za ta gaishe ka”.

“Da kin kyale ta, don lokacin tafiyata ya yi”.

Yana magana cikin duba agogon da ke daure a tsintsiyar hannunsa.

“Ai kuwa ba za ka sanya kanwata ta yi fushi ba, yadda ta dokanta da ganinka”.

Ba ta tsaya jin wata magana ba ta yi waje.

“Ammi ki ga uban hijabin da ta yafa? Gaskiya ba za ki je da wannan abin ba, haba kamar mai takaba? Ki cire wannan tsummani”.

Ta make kafada, “Au ko to shi kenan, ki kyale ta kawai”.

Aazeen ta yi kwafa hadi da rankwashinta a ka.

“Yar kauye na ga sanda za ki waye”.

Da sauri Nurat ta yi waje cike da dokin son ganin Adamu, ga farin cikin Aazeen ta yi na’am burinta na gaba Aazeen ta amince da aurensa, malaminsu ya ce duk mutumin da ya yi sanadiyyar hada aure yana da lada mai girma.

Ta yi sallama cikin dasasshiyar muryar da yakejin ita kadai ce da shi, gabansa ya buga da karfi. Ya yi saurin dago kai idanunsu suka gauraya, ita kam ji ta yi kafafunta sun kasa daukarta. Ta shiga rudu sosai tana jin komai tamkar a mafarki.

Zamowa ta yi kasa ta zauna, cikin rawar murya.

“Sannu da zuwa”.

Da kyar ya budi baki, “Yauwa”.

Jikinsa ya yi la’asar, me ke shirin faruwa da shi? Ya zamo mara sa’a a duniya.

“Ya Allah na rasa komai, ka bar ni da Nurat”. Ya fada a ransa.

Kamar ya sani, ya ji a jikinsa wannan kaddara ce mummuna. Ya jinjina kai, dole wannan karon kaddarar ta sauya, ya sani ba a sauya ta.

“Tana nan tana yi maka kauyancin nata da ta saba ko?” Aazeen ta fada lokacin da ta shigo.

“Adam kanwata ce, sunanta Nurat”.

Da kyar ya daidaita kansa yana yake.

“Na ga kama ai”.

Mikewa ya yi, “Zan wuce”.

“Yau dai na ga duk kana sauri, ina son mu samu lokaci sosai don sake fahimtar juna”.

“Kada ki damu, a hankali komai zai daidaita”.

Ya dan dubi Nurat wadda ta kasa dago kanta.

“Kanwata, babu sallama?”

Ta yi murmushi, “A sauka lafiya”.

Kwance ta ke a saman gadota yi ruf-da-ciki, ta kasa saisaita hawayen da ke faman tsinkowa a idanunta, muryar Aazeen ta ji, da sauri ta sa gefen hijabi ta goge fuskarta, ta maida ido ta rufe.

Aazeen ta shiga jijjiga ta, wani irin haushin yayar tata ta dinga ji. Wata irin tsanarta ta dirar mata, abin da ba ta taba ji game da ita ba.

“Ai ko dole ki farka a baccin nan”.

Ta dago ido, ba ta son Aazeen ta ga kwallar shi ya sa ta ke kokarin maida shi. Aazeen ta kafe ta da ido.

“Gaya min lafiya ki ke kuwa?”

“Kaina ne ke ciwo”.

“Ai ko daurewa za ki yi, za ki kira Adamu a waya”.

“Na ga bai dade da barin gidan nan ba?”

“Ba za ki gane ba, kawai muryarsa nake son ji, ina kewarsa sosai”.

“Yaya Aazeen kina sonsa sosai?”

Aazeen ta jinjina kai, “Sosai da sosai, bana gajiya da tunaninsa”.

“Amma Yayata kada ki manta, kin yi wa kanki alkawarin auren wani”.

“Na sani, amma bana ji nzan so wani kamar Adam”.

“Kenan kin fasa auren wancan din?”

“Duka su biyun zan iya aurensu, ina nufin in na auri daya sannan daya”.

“A ina ki ka taba jin haka?”

Ta kama kumatunta ta ja.

“Sarkin tambaya. A takaice dai zan kare rayuwa ta da Adamu, lokacin da na maida shi yadda nake so”.

Nurat kawai sanya mata ido ta yi cikin kasa fahimtar inda Aazeen ta dosa.

Karar wayar Aazeen ta katse mata tunani.

“Zee ta kira ni”. Aazeen ta ce, tana amsa kiran ta sanya ta handfree.

“Na kira in ji labarin mutumin, ya bada kai?”

“No bana tunanin irin mutanenmu ne, da alama sai ya shiga aji, kuma kin san wani abu? Duk lokacin da nake tare da shi bana iya rike kaina”.

“Wow! Amma zan so in ga gayen nan”.

“Hmm, ke dai bari. Wallahi gayen gaye ne”.

Mikewa Nurat ta yi, ba za ta iya jure jin wadannan kalaman daga bakin Aazeen ba. Ficewa ta yi ta sitroom ta koma. Kwanciya ta yi a doguwar kujera ta yi lamo, tana jin wani abu a zuciyarta wanda ba ta taba ji ba, tana jiyo dariyar Aazeen, ta lumshe ido, wani irin zazzafan hawaye ya silalo kuncinta.

<< Kyautar Zuciya 13

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.