Ammi zube akan kujera tana ta faman gursheken kuka babu zato babu tsammani taga yan sanda akanta sun zagayeta daya daga ciki ya dauko ankwai ya Sanya mata kawai ta dago kai ta dubi Aazeem ida nununta taf kwallah sun soma tafiya da sauri Aazeem ta Sha gabansu ta matso daf da ita tayi kasa kasa da murya.
“zan cire araina cewar Ina da wasu iyaye zanyi rayuwata ni kadai idan har Kika tuna dani aduniyarki ta kurkuku bazan yafe mikiba .”
daga bangaren alhaji munir kuwa gaba daya sungama shigewa Kabir suna nuna masa zasu tsaya masa sune siyasa hakane ya saka Kabir ya saki jiki sosai harta kaiga kullewar zuminci a inda Alhaji munir ya nemi auren umminsa kwadayi da buri irin na Kabir baisa ya shawarce taba kawai ya Sanya aka daura auren sai goro ya kawo mata.
Tayi kuka har ta godema Allah ankya kuwa shi Kabir mutum ne kuwa.
“Ummi na kankaro Miki darajarki kin Sami aure shine cikar Kamala rashin aurenki zai iya kawoma siyasata matsala dan haka na zabi hakan Kuma ban tsaya jin ra,ayinki ba sabida kawo yanzu bazaki San meye soba kinga kenan baki da zabi,duk da cewar kin sanshi hakan bazaisa nace ki shirya tarbar shiba.”
“Kumama kinsan na zaba Miki miji Dan gaske wanda zakiyi alfahari dashi Yana da mutukar kirki.”
binshi take kawai da kallo batare da ta iya tanka mishi komiba yagama surutansa ya yi waje.
Kabir Yana ta tsara yadda yadda,a kaita gidan Alhaji munir har yanzu takasa Koda tanka masa Dan gaba daya yanzu tsoron lamarinsa takeji .
bayan daurin aure da kwana biyu aka kaita batayi mamakin ganin kayataccen gidan ba a yadda yadda kashewa Kabir kudi idan akace Yana da gidan dayafi wannan dinma bazata Musa ba.
***. ***. ***
babu abinda Alhaji munir ya boye mata game da labarinsa yar uwarta kawo dawainiyar daya dingayiwa deedat ya gaya mata Yana mutukar son deedat bayason abinda zai nisanta shi da dansa yadda ta rike masa da ta tarbiyantar dashine yasaka shi yake mutukar kaunar ta kuma zamansu tare zai Sanya dole kabir ya bari deedat ya dawo rayuwar ta Kuma Shima din deedat din zai karbeshi a matsayin uba.
yadda yake maganar yasa taji tausayinta haka Kuma zuciyar ta ta nutsu dashi, take tayi masa alkawarin fahimtar da deedat tare da alkawarin yi masa biyayya.
tana zaune akan doguwar kujera ta harde kafa tana faman tufka da warwara ko kadan bataji kewar mahaifiyar taba saima wani tsananta da tayi , sai dai tafi tsanan Nurat fiye da komi da kowa a rayuwarta acewar ta itace silar rushewar rayuwar ta mahaifinta shine ya lallata rayuwarta ya Gina ta yarsa itama tayi alkawari yadda ya rusa mata rayuwa itama sai ta dau fansa akansa tata rayuwar sai ta tarwatsa mata rayuwa sai ta Sanya karti majiya karfi sunzo sun haike mata,amman kafinnan sai ta fara cika ma zaruk burinsa.
Shima dad din tunda ya bar gidan babu alamar zai komo deedat yake ta faman nema lungu da sako har ta handset dinsa har ya fidda rai da samunsa kawai yaji an daga.
Awayar ya sanar dashi komi har kamun da yan sanda sukayiwa ammi,ya Kuma rokeshi da ya ceto Nurat Kuma muddin ya hadu da ita ya riketa da zaran ya karasa inda yakeson zuwa zai Sanya a daura musu aure zaiyi magana yaturo wakilansa cikin sirri ba Kuma ya bukatar komi shidai kawai ya kular masa da Nuratu ita kadai ya mallaka
deedat ya gama rudewa baya wani fahimtar sosai yana bukatar yi masa tambayoyin sai dai kan ya kai ga hakan wayar ta katse yayi saurin bin Kiran sai dai an kashe wayar.
Kai tsaye gidan su Nurat ya nufa get din gidan a hangame,kokarin parking yake ya hangi Nurat ya juya akalar motar a gabanta yayi parking bataga waye ba jitayi kawai an fincikota an maida murfi an rufe zata kwallah ihu sukayi ido biyu da Didat.
“yaya adamu Ina zaka kaini?
“Yakafeta da manyan idanunsa .”
“Sunana Ahmad, deedat ya fada cikin daure fuska babu wanda yasakeyin magana wannan gidan dai data taba zuwa nan suka nufa masu gadi suka bude get din a inda aka tanada dan ajiye motoci yayi parking ya fito sai dai bata da alamar fitowa shi Kuma baice ta fitoba ya soma tafiya karnika ta hango sunata shawagi a harabar gidan da sauri ta fito har tana cakumeshi ,masu gadin get na uku suka nufoshi suna tambayar bakuwa yayi ya sanar musu da cewar matar sace har suka isa shashen da yafi mu,amala sannan ya nuna mata dakin da zata shiga.
Tana zaune Akan darduma cike da zulumi,tafi tunanin mutuminnan saceta yayi,ko Kuma garkuwa zaiyi da ita gashi gari har yafara duhu adaddafe ta mike tayi sallar isha,I deedat ya turo kofa sanye yake da jallabiya mai yankakken hannu dakin gaba daya ya kwure da kamshi wani ma aikaci biye dashi rike da trey Wanda aka shakeshi da plas plas na abinci direwa yayi ya juya deedar ya zauna agefenta.
“Gaya min Mai kike bukata yanzu?
“dan Allah ka kaini gida.”
tafada cikin sassanyar murya.
Yayi murmushi gaba daya tausayinta takeji.
“bakyason na kaiki gun adamunki ,na fakawoki nanne sabid na taimakeki akan sa”
“bana son komi
dan Allah ka kaini gida jikina yana bani wani abu na faruwa ka taimakeni kaji.
“Idan kin kwantar da hankalinkiki zan kaiki gida sai dai ba yauba.”
Kuka ta saka masa sosai tamkar karamar yarinya dan tana ganin wannan mutumin inba bore tayi mishi ba bashi da niyar barinta bazai iya jurewa ba da sauri ya bar mata dakin .
ta Yaya zai iya sanar da ita abubuwan dake faruwa yana son gyara komi baya son daga mata hankali kutso kai tayi set room din ta durkusa agabansa tana kuka.
Ya ilayi ta Yaya zai iya fahimtar da ita ,tattaki yayi ya karasa gareta ya Kai hannu ya dagota tare da zaunar da ita akan kujera.
Yayi bala,in sassauta murya.
” Nurat!
Adamu ne kawai yake kiranta irin haka shi kadaine ke iya sarrafa harshe haka wajen kiranta
“Shin kin daina son adamun kine, adamu bazai cutar dake ba,nakawo ki nanne kawai dan kiyaye amanar da dad dinki ya bani,kinsani har abada bazan cutar dake ba dad ya umarce ni da na zauna dake zuwa wani lokaci dazaran komi yayi daidai da kaina zan kaiki gida kinji.”
Yakoma mata kamar wani sabon mutum agunta ta dan kafe shi da idanunta don kara tabbatar da adamun tane,zuciyar ta ta amince dashi to amman meye daren gaminsa da dad ankya kuwa ba yaudarar ta adamu yake sonyi ba kokarin hada ido suke tayi saurin dauke kai yayi murmushi kawai.
“Kasani ina sonka amman bazan bari na sabama iyayena sabida kaiba kataimakeni zan fito in sanar da su kaine rayuwata muddin suna kaunata zasu amince da Kai
wannan karan yo yadda kakeson Dan Allah.
Wadannan halayya nata suke kara masa kaunarta
” duk da ban taso da iyaye ba duk da ba,a sameni ta hanyar halaliba na san zafin iyaye bazanso ki saba musuba muddin kaunata dake gaskiya ce zan bari kibi iyayenki.”
duk da tana cikin rudani haka bai hanata farin cikin sake haduwa dashiba.
“Tayaya zan yadda da cewar Kaine adamu,Kuma da sanin Abba na nake tare da Kai.”
Ya dauko wayarsa ya matso kusa da ita ya lalubo lambar dad dinsu ya nuna mata
“Jinakeyi wannan shine lambar sa duba kigani
Ta karbi wayar ta tabbatar da shi dinne.
“To amman Ina ammina kagaya mini tana Ina?
“dad zai gaya Miki bara na kirashi dazu nakira wayarsa akashe yanzu bara na sake gwadawa.”
Yanzunma wayar akashe take idanunta suka cicciko da kwallah ya dubeta ya dan kada kai alamar kada tayi kuka.
“Nine adamunki bazan cutar da keba kinsan da haka ko.”
Bata ce dashi komiba kwallar dake kwance a idanunta suka karasa gangarowa kan kuncinta tausayinta yukeji matuka ya matso kusa da ita jiyakeyi kamar zai janyota jikinsa ya rarrasheta.
“Idan Kika kwantar da hankalinkiki komi zai yi daidai nayi Miki alkawarin haka kinji .”
Ta dan jinjina Kai.
” taso muje ki kwanta kinga dare ya farayi.
ta dubeshi da mankyan idanunta har sai da tsigar jikinsa ya tashi.
ba gida zaka kaini ba.?
Yau anan zaki kwana daddy ne ya bani izinin haka nace dake babu kowa agidan naku.
To amman ka gaya min Mai yasami ammina?
“ko meye gobe daddy zai sanar dake”
Tadanyi Jim kamar tanason sake magana sai dai tayi shuru,ya dubeta kawai yayi murmushi wani irin farin cikine ke faman dawai niya dashi yau gashi atakaitaccen lokaci zai mallake burin ransa yarinyar da bai tabajin wani mahaluki azuciyarsa kamar taba .
“muje ki kwanta kinji.”
Bata da zabi dan bata tason yiwa na gaba da ita gaddama .
ta mike ta rufa mishi baya wani daki ya kaita dakinda ko a kasashen turai bata tabacin karo da irin saba yayinda take kallon fina finan su .
“Zaki Sami duk abinda zaki bukata aciki kinji,ga toilet can.”
Ya juya zai fita tayi saurin fadin
da gaske Kaine adamun?
“Nine adamunki kinji.
daganan bai sake ce mata komiba ya fita
tinawa yayi bai dauko mata kayan bacci ba ya bude wani akwatu da babu komi aciki sai kayan baccin kala, kala wadanda ya tana desu domin nabila.ya juya ya nufi dakin ya murda handle din kofar tananan zaune akan darduma ajiye mata kayan yayi akan darduman yayi waje.
acan setting room ya kasa zaune ya kasa tsaye hand set dinsa ce ta shiga ruru da sauri ya Kai hannu ya dauko lambar abban su Nurat ne da sauri ya latsa Kore ya Kara a kunne .
“deedat, Nurat ta zamo mallakinka na sami wakilanka har an daura aure mahaifinka shiya bada sadaki milyan biyar.
da sauri ya katseshi.
“daddy wani irin magana kakeyi haka,dad kanka daya kuwa nifa bani da kowa daddy ka nutsu mana kagaya min Mai ke damun kane?
“Yarona ina cikin hankalina nasan komi Kuma ba Kaine ka janyo wa kanka ba kasani kowa da tasa kaddarar mahaifinka mutumin kirkine haduwata dashi cikin lokaci kankani na fahimci haka kawai dai wannan abu yazamo kaddara amman azahiri bashi da aibu.”
wadannan maganganun susuka rikitar da deedat,shin farin ciki zaiyi ko Kuma bakin ciki.
“dan haka Nurat matar kace nabaka amanarta gaba daya ni nagama nadama ni ba mutumin kirki bane tin asalina nasan zakaso kaji labarina kafin na mika kaina ga hukuma zanso kuzo kaida Nurat kusameni a inda nake daganan zan gabatar maka da mahaifinka kaji zan turo maka da kwatancen inda zaku sameni yanzu.ina son ko so daya na sake ganin Nurat dina .”
duf wayar ta katse yadinga zagaye dakin yanajin komi tamkar amafarki.
hakan na nufin kenan Nurat zata zamo bata da kowa ya,ilahi wannan wacca iriyar mosiface Kuma wai mahaifina.
Wayar sace tafidda wani sauti alamar shigowar sako da sauri ya bude wayar kwatancen yaturo masa hadi da jaddada cewar ya rike Nurat amana.
Yanzu ya fara gaskanta lamarin,to amman shin waye mahaifina aina yake idan suka hadu da wani idon zai dubeshi.
Bathroom ya shiga ya watsa ruwa kamar yadda ya Saba kafin ya kwanta sai ya yi wanka ka,idane ya Sanya kayan bacci,wadanda sukayi mutukar yi masa kyau acan karkashin zuciyarsa wani irin farin ciki ne ke hudashi, yanufi shashin da Nurat take Yana son sake ganinta kafin ya iya kwanciya.
tagama saka kayan baccin kenan tana gyara ma daurin tare da tunanin ankya bazata cireba kuwa riga ne mai wani wawakeken wuya kusan saman bra dinta a bude ga wani wando Wanda iya kacinsa cinya gata dama da cinyeyi gaba daya sun Kara ma cinyar girma kayan shanunta sunyi das a kirjinta ga babu bra ajikinta daman bawani sawa takeba amminta tace yanayin bra dinta basu bukatar rigar bra ,ta kada kai
bazata iyaba cirewa zatayi idan tana bacci ya shigo ya gantafa,wata zuciyar tace,to ke maiya kaiki yin bacci ashema kina cikin kwanciyar hankali kenan kibar shi kawai jitayi gaba daya an bude kofar gaba daya ta daskare agun shi kam ya kasa dauke idanunsa daga kanta tarasama abinyi sabida rikicewa ta Kai hannu ta rarumo zanin gado ta kudundune jiki aciki,
dakyar ya lalubo nutsuwarsa.
“Kiyi hakuri daddy ne ya Kira waya shine nazo na kawo miki.”
Tana bukatar jin gaskiyar lamari Mika hannu tayi ta karbi wayar.
“Ki kirashi wayarsa a kunne take.
ta shiga kokarin kiransa ringing daya ya daga muryarsa ta rasa dodon kunnen ta.
daddy na Kaine ?
“Nine Nuratu na,yanzu ina cikin farin ciki na cika Miki burinki yanzu kin zamo matar deedat,Ina nufin adamu”.
.da sauri tago Kai ta dubeshi,ta sake Mai da Kai,
“To dad ina ammina?
amminki zata dawo ki kwantar da hankalinkiki komi zaiyi daidai kafinnan Ina son kiyi mini alkawari Zaki yi biyayya ga deedat nayi bincike sosai mutumin kirkine bantaba ganin mutum kamar Saba,ina tayaki murna tare da fatan alkhairi,Kuma kada kibani kunya kiyi biyayya inaji ajikina bazai taba cutar dakeba,na yadda da tsantsar sonda yakeyi Miki don haka rashin biyayya shine zaisa ki sire a zuciyarsa kinji Nuratu na.”
Ta dinga kada kai kamar tana gabansa.
“daddy nayi maka alkawarin haka,zanyi,dad zanyi haka taita maimaitawa cikin muryar kuka har wayar ta katse batare da ta sani ba deedat ya karasa gareta tare da zame wayar daga kunnenta juyawa yayi ya fita babu walwala,hakan yasaka ta tsargu .
daddy,nayiwa daddy alkawari naga yafita fuskarsa babu annuri ko dai wani abin nayi masa ta koma ta kwanta ta janyo bargo ta rufa.
Tunda ya koma daki i komi ya kunce masa,tabbas wannan abinda yakeji shi ake Kira da Sha,awa ayadda ya ganta hoton sai dawo masa yakeyi tsananin so da Sha,awa ya sanyashi mance duk damuwar da yake ciki zuciyarsa ta dinga raya masa yanzufa halalin sace tayaya zai dinga cutar da kansa ya ture bargonsa gefe ya fito daga daki Kai tsaye ya kutsa dakin.
da sauri ta rufe idanunta ga bargon data lullube jiki ya yaye idan Kuma ta janyo zai gane ba bacci takeyiba to amman Mai ya dawo dashi, ko dai wani abin yake bukata daddy fa ya gargadeta a hankali ta bude ido yadda ya kafe ta da idanune yasa ta saurin janyo bargon .
Ya shafa keya.
“Kinyi addu,a kuwa?
Jinjina masa Kai kawai tayi .
ya juya ya fita ya kafe abakin kofa Yana faman sakar zuci shifa yanaji bazai iya rayuwa ba muddin bai hada shinfida da itaba .
Kamance da cewar kace tayi kankanta sai ka raineta ,zuciyarsa ta gaya masa haka,murmushi yayi ya Kai hannu ya murda handle din kofar ya shiga tananan zaune a tsakiyar gado ya kasa ce mata komiba idanunnan sunyi jajir.
“Yaya deedat kana bukatar wani abinne?
Ya gama rudewa yama rasa Mai zaice bai San sa,ar da ya furta
“dakin nawa sauro yayi yawa.
Azuciyarsa ya dinga addu,a Allah yasa tace yadawo nan.
“To ni sai in koma can din sai na lilliba.”
Wayyo Allah yarinyar nan bazata gane ba.
Kokarin mikewa takeyi ya dakatar da ita.
“bazaki iyaba kawai idan kin amince sai mu kwana tare.”
To tace tana kokarin komowa kasa .
“a,a kiyi kwanciyarki ai inaga gadon ya ishemu ko.”
ta kada Kai kawai.
ko ajikinsa ya haye godo ,zo kaga idanun Nurat gaba daya sunyo waje ta koma ta kwanta ta takure jikinta gu daya.
Nurat,kince nine burinki kin Sha gaya min kina Sona,to amman Mai yasa kike tsorona haka?
“babu komi.
Kin mance nifa abokinkine Kuma Mai sonki,ko ke kin daina Sona?
“a,a Ina sonka mana.”
“To amman naga kina tsorona.”
Tayi shuru,
haushin kansa ne ya kamashi ya yakeyin abu kamar wani ba na mijiba karamar yarinya yanawa wani raragefe akanta kamar wani soko.
“Nurat kina son baby na na cikinki yayi kwari?
Kunyar kalaminsa taji har ta dan rufe ido ya Kai hannu Yana shafa gashin kanta.
Aiko ta Kara kamkame jiki gabanta ya dinga faduwa har sai da ya dinga Jin bugun yaja tsaki aciki bai San sa,arda ya janyo ta jikin Saba,kamshin jikinsu suka gwuraya.
Jikinta ya dinga rawa tausayinta da haushinta suka rufeshi.
“Nurat adamunki ne fa bazan cutar dake ba kin sani ada banyi miki hakaba yanzun kin halatta agareni kidaina Jin tsorona kinji bacci kawai nakeson kiyi babu abinda zanyi miki kinji .”
Ta jinjina kai.
yasake kamkameta ajikinsa yana shafa mata baya kamar yarinyar goye. ahaka bacci yadebeta ko kwakkwarar motsi baya son yi sabida kada ta farka acan cikin zuciyarsa yana faman godema Allah ko yanzu burinsa ya gama cika wani irin sonta Allah ya dora masa yayi alkawarin riketa da Amana bazai taba cutar da itaba wani bacci mai dadi ya daukeshi.