Tuni ta dade da farkawa ta takure a bakin gado kuka take faman yi kewar iyayenta take yi tunda take bata taba kwana a wani guba kukan tane ya farkar dashi da gudu ya mike tare da matsowa kusa da ita.
Nurat Mai ke faruwa?
"Ammina.
ya rike hannunta Yana wasa da yatsunta
"Kiyi hakuri muyi sallah zan kaiki gun su kinji,tashi muje kiyi alwala kinga za,a tada sallah "
ya kamo hannunta bai saketaba har sai da ya danganata ga toilet sannan ya rufe ya barta aciki Shima ya nufi toilet din dakinsa ya daura tasa alwalar. . .