RABI’A POV.
A yau ne aka dawo makaranta, don haka ita ma ta shirya da wuri, ta kama hanyar makarantar, Kuma bayan ta je ta gama aikinta, sai ta shiga shawagin duba Mishal, amma haka ta gama shawagin nata ba tare da ta ganta ba. Wata ƙila ba ta dawo ba, haka ta faɗawa kanta tana juyawa da ga tsayuwar da ta yi a ƙofar ajin su Mishal ɗin. Daga nan kuma ta wuce ɓangaren ta wuce ɓangaren sport na makarantar, ta tsaya a wurin da ake buga ball. Tana kallon yaran da ke cikin raga suna ta buga ball ɗin. Ƙafarta har ƙai-ƙai take mata, dan ji take kamar ta shiga cikinsu su buga tare da ita.
Gani take kamar ba dai-dai suke wasan ba. Kamar idan ta shiga cikinsu za ta iya yin abinda ya fi wanda su suke yi.
“Yaya Baby, ba haka ake ba…ki tsaya na nuna miki yanda ake…”
Tunawa ta yi da wani lokaci da ya wuce a can baya, lokacin da suke buga ball ita da Baby a garden ɗin gidansu na da. Gidan da rannan Habiba ke sanar mata da cewa Babansu ya siyar da shi.
Don wasu daga cikin kadarorin mahaifiyarta da aka raba gado aka bata, ‘yan uwan mahaifyarta suka danƙa su a hannun Ɗan Lami, sauran kuma suna wurin dangin nata.
“Ke!, me ki ke a nan ?! Bar nan dallah!”
Muryar ɗaya daga cikin masu gadin makarantar ta katseta a tsawace. Shikenan kuma, da ma ta jima da sanin cewa shi talaka ba a bakin komai yake ba. Ba shi da wata kima ko dajara a idon mutane. Ba ta ce masa komai ba, ta juya ta fara tafiya.
Ko jikin store ɗin da ta sabba zama ba ta kai ba aka kaɗa ƙararrawar tashi. Hakan yasa ta fasa zuwa store ɗin, kai tsaye ta yi hanyar fita daga makaranatar. Tun da an tashi to ita ma babu abun da za ta zauna ta yi.
Tana tafiya ta na kwatanta yanda wasan da Yaya ya bata labarin za’ayi zai kasance, yace mata yau akwai wasa tsakanin arsenal da fc Barcelona. Shi yasa take ta kwatanta yanda wasan zai kansace.
Ba tare da ta an kara ba wani me mota ya iyo kanta, ƙiris ya rage bai kaɗeta ba, amma duk da haka sai da ta faɗi.
RAJA POV.
A yau suka sauƙa a garin Abuja, bayan duk wasu maganganu da suka yi da Garuje, sai yau Allah ya hukunta tahowar tasu.
Duk da ba shi kaɗai ya taho ba, ya taho ne tare da duka yaransa, Rhoda, Alandi, Zuzu da Jagwado. Dan su ɗin na amana ne, ba zai iya zuwa ko ina ba tare da su ba.
It’s something that i never, ever, ever had.
I have never needed somebody.
But i wannan spend sleepless nights, and sleepy days with you..
With you, with you, you make me speechless…
A hankali waƙar sleepless nights ta Armaan Malik ke tashi a cikin motar tasa ƙirar Jeep. Raja ne ke tuƙa motar, yayin da Rhoda ke zaune a gefensa, Alandi, Zuzu da Jagwado na gidan baya.
Rajan na sanye cikin wani blue jeans, da farar shirt dake ƙasan baƙar denim jacket ɗin da ya ɗora a saman rigar. Kuma sak kalar kayan dake jikin Rhoda ne. Don ita ce ta zame masa kamar abokiyar tagwaitakar tasa, abu ne mawuyaci su saka kaya da ban da ban. Kaya kala ɗaya suke sakawa, size ne kawai ke banbanta. Shi da Rhodan ne ke bin waƙar, Raja na yi yana murmushi, a hankali ya ɗaga kafaɗarsa ta dama. Kuma a lokacin abun ya faru.
A lokacin ƙaddarar da ke jiransa a garin Abuja ta auku, wata ƙaddara da za ta tarwatsa komai, sannan ta saita wasu lamura.
Kan motar ya juya dan shiga layin gidan da ya kama a KAURA DISTRICT.Wata yarinya ce tafe a gefen hanya, ba ya ce ya iya ganin fuskarta ba.
Sai ganin wucewar wata baƙar mota ya yi da gudu, wadda ta so ta kaɗe yarinyar, duk da bata kaɗetan ba, sai ta kaɗata gefen hanya. Ba shiri ya taka birki. A firgice ya fice da ga motar, su Rhoda suka bishi da kallo su ma suna fitowar.
Da gudu ya yi inda yarinyar take, sannan ba tare da jiran komai ba, ya kama hannun yarinyar ya ɗaga ta.
“Sannu kin ji”
Ya faɗa yana san kallon fuskarta, kuma sai aka yi sa’a ta ɗago da fuskar tata ta kalleshi. A lokaci guda zuciyarsa ta yi wani irin tsalle a ma’ajinta. Kamar zata fito daga bakinsa.
Ba komai ne ya jawo hakan ba, face wata fuska da ya gani, fuskar sak irin ta mahaifiyarsa, fuskar sak irin ta ƙaninsa Aliyu, sannan fuskar sak irinta ce a tare da shi. Amma ta ya hakan za ta faru ?, ya aka yi yarinyar ke kama da su ?, wacece yarinyar ma ?, daga ina take ?.
Kusan ƙamewar muntuna shida Rabi ta yi, a sanda ta kalli fuskar matashin da ya temaka ya ɗago da ita bayan kifawar da ta yi. Mamaki ne bayyane a fuskarta ita ma, kamar yanda yake kwance a tasa fuskar.
Za ta iya rantsewa da Allah ta ga gilmawar mamakin a cikin idanuwansa. Ba ƙaramar kaɗuwa ba ta yi ita ma, ba dan kada ta yiwa kanta ƙarya ba, da sai ta ce wannan ya fi kama da mahaifiyarta fiye da ita. Dan ya fita farin fata, saboda ita ba wata fara ba ce sosai, ta ɗan kwaso baƙin Abbansu.
Amma Ummansu fara ce sosai, kuma farinta sak irin na wannan bawan Allan ne, kusan rabin idanuwansa a lumshe suke, sannan ya kafeta da ƙwayarsu wadda ta kasance gray color.
Ta sani cewa ko cikin ‘yan uwanta na haɗejia babu mai kaka da wannan, duk da ba za’a rasa ba, amma dai wannan ba daga can yake ba, to kenan waye shi ?, daga ina yake ?, me yake a nan ?, kuma me yasa yake kama da Ummansu ?, don sai dai ta dangana kamar tasa da ta Ummansu ba tata ba.
Mafarin komai kenan.
DSS Headquarter, Maitama Evenue, Abuja
KULIYA POV.
“Aliyu, this will be your next assignment, ina so ka yi ƙoƙarin yinsa cikin taka tsan-tsan da kula, ka sani kuma nima na sani, a halin yanzu akwai masu farautar rayuwarka… Dan haka ka kula, coz this was the most dengerous assignment ever. Dan haka sai ka kula….”
Chidera Kinsily ke koro masa wannan jawabin, yayin da yake miƙa masa wani file. Hannu bibbiyu yasa ya karɓi file ɗin.
File ɗin da zai kai rayuwarsa zuwa wani mataki, file ɗin da zai sauya rayuwarsa, file ɗin dake ɗauke da matakin farko na sauyawar ƙaddararsa. Ƙaddarar da za ta tarwatsa komai, sannan ta gyara wasu lamuran.
Chidera ya ci gaba da faɗin.
“Case ne a kan wasu manya-manyan ‘yan ta’adda da suka yi wa garin Abuja tsinke a yau ɗin nan… Ba ma so abun ya tafi da nisa, wannan file ɗin ɗauke yake da bayanin kowannensu, don haka kasan abun yi… Sannan idan kana so za ka iya neman temakon abokin Abubakar”
Kuskure mafi girma kenan da ya zama sanadiyyar faruwar wannan ƙaddarar. Wata ƙaddara mai cike da tarin abubuwa, masu daɗi da akasinsu.
A hankali Kuliya ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, sannan ya ce.
“Zan san abun yi sir”
Kuskure na biyu kenan, wani babban kuskure da zai yi nadamarsa da farko, sannan daga baya ya dawo ya yi farin cikin ɗaukarsa.
“Shigo!”
Muryar Abubakar ta faɗi daga cikin office ɗin. Bayan da aka buga ƙofar office ɗin nasa. Kuliya ya murɗa ƙofar office ɗin, sannan ya shiga ciki. A hankali Abubakar ya ɗago da kansa ya kalle shi.
Kamar kullum sanye yake cikin baƙar suit, sai dai babu suit ɗin, waist coat ce kawai a saman baƙar oxford shirt ɗin dake jikinsa. Hannunsa na dama riƙe da file ɗin dake ɗauke da ƙaddararsu. Ƙaddarar da za ta sauya LABARINSU.
“Sabon assignment ne, idan babu abun da za ka yi, sai ka taya ni…”
Wannan dakkakiyar Muryar tasa ta faɗa. Kuskure na uku kenan. Abubakar ya yi murmushi yana aje ipad ɗin hannunsa.
“Babu damuwa Dude, ai duk assignment ɗinka nawa ne… akan miye ?”
Kuskure na huɗu kenan.
“Ban sani ba, dan ban duba ba”
Ya amsa shi a taƙaice, duk kuwa da yasani ɗin.
MISHAL POV.
Shekaran jiya suka dawo daga Maiduguri. Kuma a jiya ne Abubakar ya kaita aka cire mata braces ɗin dake haƙwaranta.
Ba ƙaramin daɗi ta ji ba a sanda aka rabata da su, don Allah ya sani, ba ta san su, ga shi dai ita ta ce a saka mata su, amma daga baya sai suka gundureta.
Zaune take a comound ɗin gidan, suna hira ita da Shatu, yayin da Daala ke zaune a gabanta. Akasarinta hirar tasu a kan Maiduguri ne.
Daga can saman benin gidan kuwa, Hajjara ce ke leƙowa ta window tana kallon Mishal ɗin. Cike da tsana da kuma alwashi.
Ta ɗaukawa kanta alƙawarin ganin bayan Mishal, ba za ta huta ba sai ta ga tabbatuwar hakan. Ko da za ta ƙarar da duka abun da ta mallaka ne sai ta aikata hakan.
Abun da ba ta sani ba shi ne; ƙaddarar da Allah ya hukunta faruwarta ta kusa afkuwa, kuma tun kafin abun da ta tsara ya kai ga gaci komai yake wargajewa.
Unguwar Rafin Cinnaka, Suleja, Niger state
“Yanzu miye abun yi ?”
Muryar Habiba ta tambaya, yayin da take zaune a falon gidan yayarta hajiya Inno. Hajjiya Inno ta yi murmushi.
“Yanzu abun da ya kamata shi ne kawai ki kawo wani abun, a kai masa a matsayin kafin alƙalami… A fara aiki a kan Saratun, na faɗa miki aikinsa ba ƙaramin ci yake ba… Da zarar ya yi aikin ina mai tabbatar miki da ko sati ba za’a yi ba za ki ga samari sun fara sintiri a ƙofar gidanki…”
Habiba ta ɗan yi dariya.
“Haka nake san ji, dan Wallahi har ga Allah na gaji da ganinta a gidan nan haka… Ita ma idan ta ɗan samu ta yi auren nan ai yafi ko?”
“Hakane”
“To sai batun Mama, yarinyar nan so take ta fara fin ƙarfina, wai rannan dan na mata magana kan ta ɗan yafita min wani abu sai ta hauni da faɗa?!”
“Mtswwww!, Wallahi kuwa Habiba da kin bada mata, har ita ta isa dan ubnta ?, Idon ki za ki murje ki nuna nata cewar ke ce uwrta, ba ita ta haifeki ba!”
Habiba tace“Hummm!” cikin taɓe baki.
“Gaakiya ba zan iya takurata ba, dan baki san yanda nake san Mama ba ne, sam ba na so ranta ya ɓaci Wallahi, ke dai kawai kawo wata shawarar”
Cike da mamaki Inno take kallonta. Can kuma sai ta taɓe baki tace.
“To ai ita ma nata lamarin mai sauƙi ne, sai amata na kasuwar samarin, alhajan nan na abuja su yi ta kai kawo a kanta, sannan a rufe mata baki, duk sanda za ki mata maganar kuɗi ta miƙo miki kawai…”
Habiba ta saka dariya har da shewa, tana jin wani abu na washewa daga ranta.
“Wallahi Yaya Inno abun ne da yawa, kin ga na Zainab ma abun yaƙi daɗi, kar ki ga yanda bawan Allahn nan ke gasa mata aya a hannu”
Inno ta kuma yin dariya.
“Shi ma nata mai sauƙi ne… Habiba idan fa da kuɗin ki shikenan, duk wata matsala taki ta kau, in dai za ki bada shikenan…”
Ta sauƙe ajiyar zuciya.
“Sai kuma na wannan shegyar yarinyar, kinbga fa duk dan na tagayyara rayuwarta na sa Ɗan Lami ya dawo da ita nan garin, toh!, ta taggayar ɗin, amma ni ba haka na so ba….Na fi so ta ƙare da cikin shge, shi ne fa yasa ma na aikata akatau, amma dai har yanzu shiru ki ke ji…”
Dariyar da Inno ta saka ce ta sata yin shiru.
“Wai ni Habiba yaushe kika yi sanyi ne ?, ina Habibar da na sani ta da ?, wai duk kin yi sanyi kin zubar da makaman yaƙinki ?, yo in ba haka ba ai wannan ba wata matsala ba ce, ke dai zo ki ji”
Ta ƙarashe tana matsawa kusa da Habiban, Habiba ta miƙa mata kunne.
A take Habiba ta saka shewa tana tafa hannu, bayan da ta gama sauraron abinda Innon ta raɗa mata.
“Ai kuwa ko miliyan nawa zan sadaukar a kan wannan aikin, in dai har… Zan ga bayan jinin Maryam a duniyar nan!”