DSS (Department of State Service) Headquarter, Maitama Evenue, Abuja
KULIYA POV.
Cikin takunsa mai ƙarfi yake tafiya, kansa a sama, babu ruwansa da kallon kowa, ciki kuwa harda waɗanda ke gaida shi, kuma suma da alama basu damu ba, don idan da sabo sun saba. Shi kullum haka yake rayuwarsa, babu ruwansa da kowa a wurin, idan har kai ba a tawagarsa kake ba, to fa shi babu ruwansa da kai. Elevator ya shiga, wadda ta kai shi zuwa floor ɗin office ɗinsa.
Ya fita daga ciki, kafin ya shiga office ɗinsa, kujerarsa ya ja ya zauna, sannan ya kunna desktop, ya shiga danne-danne.
Kafin bayan shuɗewar wasu lokuta, ya ɗauki wayar land line ɗin dake kan table ɗinsa ya aika kira, kuma kalamai biyu kawai ya faɗi sannan ya katse kiran.
Bayan ɗan wani lokaci, aka ƙwanƙwasa ƙofar office ɗin, gyaran murya ya musu kamar kullum, kafin ƙofar ta buɗe.
Sharon, Abubakar da Symon suka shigo, nuni ya musu da kan set ɗin wasu sofa da ke tsakiyar office ɗin, alamin su zauna a can. Zama suka yi, a sanda shi ma ya taso daga kan tasa kujerar, hannunsa riƙe da wasu takardu ya zauna a kusa da su. ya shi ga musu bayani akan abun da ya sa ya kirasu.
“Kamar yanda muka riga muka fara wannan binciken, tun farko na sanar muku da rukuni garesu… Sunan ogansu Tomes, yana da yara shida, sannan akwai mace ɗaya a cikinsu… Kuma ana zarginsu da fasaƙwaurin miyagun ƙwayoyi, kisa…”
Sai kuma ya yi shiru, yana tauna maganar da zai faɗa ta gaba, dan har wa yau kalmar na masa nauyi a bakinsa, musamman ma idan ya tuna cewa wannan hanyar ita ce silar samuwarsa, ita ce silar zuwansa duniya, ita ce silar raba mahaifiyarsu da farin cikinta.
Wannan hanyar ita ce ta sa bayan rasuwar mahaifiyarsu aka rasa wanda zai bawa rayuwarsu agaji, har ta kai ga ya rasa yayansa, ɗan uwansa, mafi soyuwa a ransa. Kafaɗarsa ya ɗaga yana ci gaba.
“…Fyaɗe, sai kuma saye da siyarwar miyagun ƙwayoyin… A halin yanzu na yi magana da Ram, ya na tricking location ɗinsu, kuma daga zarar ya gano inda suke, kai tsaye farmaki za mu kai… Ko a mutu ko a yi rai!”
Abun da bai sani ba shi ne,wasu lokutan abubuwan da mukan furta su ne ke faruwa, wasu ƙaddarorin kan faru kamar yanda muka ayyana a zukatanmu. Wannan kalaman nasa na da alaƙa da wata ƙaddara da Allah ya hukunta faruwar ta ‘yan lukuta ƙalilan da za su zo. Wata ƙaddara da za ta tarwatsa komai, sannan ta saita wasu lamura.
A yammacin wannan ranar, bayan lokacin tashinsa a aiki ya yi, yana tuƙi cikin baƙar motarsa ƙirar honda elevate. Hannunsa na dama kan sitiyari, yayin da ɗayan kuma yake kan bakinsa.
A hankali ya ɗaga kafaɗarasa ta dama, yana tsuga gudu a motar tasa, dan dama can shi haka tuƙinsa yake, ba ya tafiya a hankali, kuma hakan ne ke sawa suke raba gari idan za su yi tafiya shi da Anna, don haka take cewa; ita tabna san rayuwarta, ba ta shirya mutuwa ba.
Tunanin hakan yasa shi yin murmushi a cikin ransa, a fili kuwa babu komai a kan fuskar tasa, ba fushi yake ba, ba fara’a yake ba, haka kuma ba ƙunci yake ba.
Duk ƙwaƙwaffin mutum ba zai iya tsintar abun da ke kwance a kan fuskar tasa ba. Kamar daga sama wata motar ɗiban yashi, ta daki motar tasa daga gefe. Motar tasa ta yi ta dungurawa tana sakewa a kan titin, hakan ya sa ta yi kwatsa-kwatsa tun kafin ta tsaya da dunguwarawar da take.
No.234, Efab Estate, Gwarinfa, Abuja
MISHAL POV.
Tsaye take a cikin kitchen, sanye cikin uniform, a hankali hannayenta ke jera kayan abincin da ta gama girkawa a cikin lunch box ɗinta.
Ƙofar kitchen ɗin ta buɗe, Hajjara ta shigo tana mata murmushi kamar wancan karon, kuma a yanzun ma sai da ta tsorata, dan ba ta san da me ta zo ba wannan karon. Ƙarasowa ta yi gabanta ta tsaya tana mata wani irin kallo.
“Ya akabyi Tsaka?!”
Mishal ɗin ta tambaya, tana maida dubanta kan kayan da take jerawar. Sunan ya daki gangar zuciyar Hajjara, amma da ta tuna abin da ya kawota sai kawai ta basar.
“Tsaka ba?, za kuwa ki ga ma’anar tsaka”
“Ai babu kalar tsakar da ban ga ba… Me haɗa mutum da mutum ai tsaka ne Hajjara!… ko babu wanda ya taɓa baki labari cewar kaf tarihi babu wanda ya kai tsaka iya munafirci?”
Ta kira sunanta kai tsaye, kuma tana kallon cikin idonta. Dan ba ta shakkarta ko tsoronta, tsoron sharrinta kawai take.
“Yaro man kaza… Ke a tunanin ki za ki iya raba ni da mijina kuma na zauna ina kallonki ?”
Mishal ta ɗan yi murmushi tana harɗe hannayenta a ƙirji.
“Hajjara… Ke ce kika ɗauke ni a matsayin kishiya, ko da wasa ba na kishi da ke, saboda ban ga dalilin yin hakan ba, na ga kamar jahilcinki na san taɓa miki ƙwaƙwalwa, babu aure tsakanina da mijinki… Kuma kafin ya fara saninki ni ya fara sani… Amma ba zan yi mamaki ba dan kina kishi da ni, tun da ‘yar da kika haifa ma kin ƙita saboda tana da nakasa… Me zai sa na ji haushi dan ni kin ƙini?”
A wasu lokutan duk da ƙarancin shekarun Mishal da kuma yarintarta tana da hankali, dan wani zubin takan yi magana ta hankali.
“Wata ƙila daga yau ba za ki ƙara ɗaga yatsarki a fuskata ba…”
Hajjara ta faɗa tana kallonta. Mishal ba ta fahimci abin da take nufi ba, sai da ta ga ta shiga waige-waige a cikin kitchen ɗin, sannan ta gane me take nufi. Kuma ba ta ƙara tabbatar da abin da kanta ke gaya mata ba, sai da ta ga Hajjaran ta rarumo wuƙa.
Abubakar na zaune a falo yanawa Daala wasa, sai ji ya yi an ƙwalla wata razannaniyar ƙara, wadda yake jin tana fitowa daga kitchen. Tsabar tsoratar da ya yi, ya kasa gane ƙarar waye.
Ba shiri ya miƙe, ya nufi kitchen ɗin gadan-gadan. Ba ƙaramin tashi hankalinsa ya yi ba, a sanda ya yi arba da abinda ke aukuwa a kitchen ɗin.
Mishal ce zaune a kan marbles, hannaunta na dama riƙe da na hagu. Yayin da tsintsiyar hannunta na hagun ke zubar da jini, sai kuka take tana hawaye. Dubansa ya kai kan Hajjara dake tsaye a kanta, hannunta riƙe da wuƙa.
A tsorace Hajjara ta kalli Mishal sannan ta kalleshi, sai kuma ta cillar da wuƙar, idanta ya cika da ƙwalla, ta ci gaba da kallon Abubakar tana girgiza masa kai, alamun a’a.
“Innallilahi wa inna ilaihi raji’un, Hajjara, kashemin ƙanwa kike san yi?”
Abubakar ya tambaya a kiɗime, yayin da ya ƙarasa gaban Mishal yana duba hannun nata. Hajjara ta shiga girgiza masa kai, tana san ganar da shi gaskiyar abin da ya faru. Ita fa ba ta yi komai ba, ba ta san ya aka yi komai ya auku ba. Cikin muryar kuka ta shiga faɗin.
“Abubakar Wallahi… Walahi ban mata kom…”
“Ki min shiru!, Kada ki sake min magana. Na ɗauka tsanarta kawai kika yi, ahse har kasheta ma za ki iya yi!”
Abubakar ya katseta a zafafe, bayan da ya ɗago daga duba Mushal ɗin da yake. Ya ƙara tsugannawa kan Mushal da ke ta kuka kamar zata fasa gidan.
Yasan ƙanwarsa da dauriya, ba komai takewa kuka ba tun tana ƙarama, tana iya jure komai duk zafinsa, dan haka tun da take kuka, dole ciwon nata ba ƙarami ba ne.
Kamata ya yi, sannan ya miƙar da ita yana shirin fita da ita daga kitchen ɗin. Sai da suka zo wucewa ta kusa da Hajjara, Mishal ta kalleta, kamar ba ita ceke yin gunjin kuka yanzu ba. Sai da ta faki idon Abubakar, sannan ta ƙiftawa Hajjara ido ɗaya, tana murmushin da ke nuna ita ta yi winning gasar.
“You lose!”
Ta furta hakan a iyaka kan leɓenta kawai, wanda Hajjaran dake ganinta ce kaɗai za ta iya gane me ta faɗa. A sanda Hajjara ta zube a ƙasa tana runzar kuka.
A lokacin Mishal ta dawo da nata sabon kukan, tana riƙe hannunta. Hakan yasa Abubakar ƙara ruɗewa, don bai ko Hajjara bai waiwaya ba.
Nizamiye Hospital, Sector S. Cadestral zone, Life Camp, Abuja
“Kamar yanda na faɗa maka ne, yanka ba wani sosai ya shigeta ba, dan haka ba wata damuwa, za ku iya tafiya…”
Likitan da ya duba Mishal ne ke korowa Abubakar bayani, wanda gaba ɗaya hankalinsa ya gama ta shi.
Daga can wata kujera dake gefe a office ɗin kuma, Mishal ce zaune, daga ita sai long sleeve Oxford shirt ɗin uniform ɗinta, suit ɗina na aje a gefen kujerar da take kai. Kanta a ƙasa tana tuna abun da ya faru ɗazu.
A ɗazun bayan da Hajjara ta rarumo wuƙa, sai ta ɗorata a tsintiyar hannunta sannan tace.
“Zan yanka kaina, dan na rabaki da Abubakar, zan zubar da jini na fansa, dan na shiga tsakaninku, zan yanka kai na yanzu, sannan na kira shi na ce kece kika yanka ni…”
Kuma tun kafin ta gama faɗin abun da za ta faɗa, Mishal tai wuf ta ƙwace wuƙar daga hannunta, sannan ta ɗora a nata hannun ta yanka kanta. Ta kuma yi sauri ta danƙawa Hajjaran wuƙar, kafin ta faɗi ƙasa, shi ne ta kurma wannan ihun tare da saka kuka.
Sai kawai ta yi murmushi a fili, yanzu da ace ba ta yi hakan ba, da yanzu ita ce a ciki, ta rasa me ta tsarewa Hajjara da ta tsaneta haka, ba ta san me ta yi mata ba.
Hannunta na hagu ta ɗago, ta kalli plastern da aka saka mata yanzu, sannan ta ɗaga kai ta kalli Abubakar da ya zo ya tsaya a kanta yana kallonta cike da tausayawa.
“Sannu Hafsat, tashi mu je”
Sai ta miƙe tsaye, tare da kai hannunta na dama ta ɗauki suit ɗin.
Wayar Abubakar ta yi ƙara a sanda suka fito daga office ɗin, hannunsa ya sa a aljihu ya ɗauko sannan ya amsa.
“Hello Sharon, howdey?!”
Daga cikin wayar Sharon tace.
“Fine sir… Kuliya ne ya yi hatsari jiya, sannan an kwantar da shi a asibiti…”
“What?!, hatsari?!, a ina?, wani asibiti yake?”
Ya katseta tare da jero mata tambayoyin. A lokaci guda kuma ya dakata da tafiyar da yake, hakan yasa Mishal ma dakatawa tana kallonsa.
“Nizamiye hospital”
Sai ya yi shiru.
“Yanzu haka ina cikin Nizamiye hospital ɗin, wani ɗaki yake ?”
“Room No.18”
”Nagode Sharon”
Kuma daga haka ya sauƙe wayar.
“Ukti abokina ba shi da lafiya, muje mu duba shi”
Mishal ba ta damu da san sanin waye abokin nasa ba, dan haka kawai ta bi bayansa.
Room No.18, Nizamaye hospital
KULIYA POV.
“Yanzu miye amfanin irin wanna?!, Ka daba abun da ya sameka ka gani da idonka, kullum ina cikin maka nasiha a kan yawan gudun da kake da mota, amma sam baka kulawa, yanzu ga irinta nan!…”
Anna ce ke ta balbale shi da faɗa, yayin da take tsaye a kansa, kusa da gadon marasa lafiyar da yake zaune a kai. Ya jingina bayansa da gadon, gefen fuskartsa na manne da plaster, hannunsa da kuma wuyansa gaba ɗaya rauni ne.
Allah ne ma ya kawo masa abun da sauƙi, dan a sanda wannan babbar motar ta daki tasa sai Allah yasa ya fita ta wundo, sanda motar ta tashi sama.
Bayan ya faɗo sai ya gangara bakin titi, hakan ne ma yasa ya ji raunikan jikinsa. Kuma a sanda jama’a suka kawo masa ɗauki ya suma, don haka bai farka ba sai cikin daren, shi ne ya tsinci kansa a asibiti.
“Yanzu idan ka ga motar taka ba za’a ce ɗan adam ya fita daga cikinta ba, saboda yanda ta kwankwatse!…”
Anna ta ci gaba da faɗi cikin faɗan da take, a hankali ya ɗaga kansa ya kalleta, sannan ya ce.
“Ki yi haƙuri Anna, amma ni ban san daga inda motar take ba, kawai da…”
“Ina za ka sani?, ai ba za ka sani ba!”
Kuma tana kaiwa nan ta figi jakarta ta fita, dan ba za ta iya jurewa ba, Aliyu kaɗai ya rage mata a duniya, duk da ba ita ta haife shi ba, amma ta na sansa, tana masa so irin na ɗa da uwa. Gawara ta nuna masa fushinta a kan abinda ya yi, wata ƙila ya fahimci kuskurensa ya gyara.
A hankali Kuliya ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, sannan ya shafa kansa. Duk yan da aka yi wannan haɗarin shiryyaye ne, dole ne ma wani ne ya shirya shi. Kuma ko kokonto ba ya yi, imma dai waɗan da ya taɓa sakawa ciki matsala ne, ko kuma waɗanda yake tunkara a yanzu.
Kan nasa ya sauƙe shafawa, sannan ya kalli side drawer, inda wayarsa da sauran kayan da ke jikinsa a jiyan suke aje. Hannu ya kai ya ɗauki wayarsa da ya buɗeta tun jiya ya ga yanda ta farfashe.
Bai damu da fashewarta ba, ya shiga daddanawa, duk da bata dannuwa da daɗin rai. Lambar Ram ya nemo, wani ma’aikacinsu wanda ya san kan computer, kuma ɗan baiwa wanda yake aikin ɓadda kama.
“Easy…”
Ya amsa gaisuwar da Ram ɗin ke masa bayan ya ɗaga kiran. Ya ɗaga kafaɗarasa a hankali,sannan yace.
“Me ka gano ?”
“Sir na samo location ɗin, sun sauƙa ne a wani gida dake Abacha road”
Muryar Ram ɗin ta faɗa daga cikin wayar. A hankali Kuliya ya gyaɗa kansa, sannan ya kashe wayar ba tare da yace komai ba. Ya kai hannu ya aje wayar tasa, kuma a dai-dai lokacin ne, ƙofar ɗakin ta buɗe.
Abubakar ya fara shigowa, biye da shi wata yarinya ce, mai kama da Abubakar ɗin, sai dai kuma ita yafinyar ta fi Abubakar ɗin hasken fata da kuma kyau. Zuciyarsa ta faɗa masa cewar yarinyar na da kyau, wani irin sihirtaccen kyau, wanda a kallo ɗaya za ka tabbatar da cewa ƙwarai, tana da kyau.
Amma kuma shi ba ya san raini, shi yasa bai ciki shiga sabgar mata ba, musamman wannan da ya gane cewa ita ce ƙanwar Abubakar ɗin da yake yawan masa zancenta. Kansa ya kawar yayin da Abubakar ɗin ya miƙo masa hannu alamun su gaisa. Gaisawar suka yi yana wani basarwa.
Kallo ɗaya Mishal ta masa ta sheƙar, dan ta ga alamun wannan mutumin ɗan raini ne, amma duk da haka sai wani ɓari na cikin zuciyarta wanda yake me hankali ya ce mata; ko ba komai ai abokin Akinta ne, kuma da gani ya girme mata, dan haka ya kamata ta gaida shi. Ciki-ciki kamar me ciwon baki tace.
“Ina kwana…”
Wani abu me kama da igiya ya ɗaure zuciyar Kuliya a ma’ajinta, ya ji kamar zuciyarsa ta gaza, ya ji yana san ya sake kallonta, amma dan kada ta raina shi, sai kai wai ya ƙi ya kalleta ma bare ya amsa gaisuwar.
Abun ya bawa Mishal haushi, duk da ba da ƙarfi ta yi maganar ba ai yaci a ce ya ji gaisuwar, bata iya ɓoye-ɓoye ko riƙe fushi ba, don haka ta kalle shi tace.
“Ba ka ji ina gaida ka ba ne ?!…”
Sai a lokacin ta kalli abinda ba ta lura da shi ba a kallo na farko da ta masa, kammanin fuskarsa, kammace sak irinta Antinta ADAWIYYA!, kenan yayanta ne?, ko ɗan uwanta ne ?…. Haka tunanin ya ci gaba da yawo a cikin kanta.
Ba Kuliya kawai ba, hatta da Abubakar kallonta ya yi, abun ya bashi mamaki, a cikin shekarunsa za’a iya kwasar nata, kuma a bar sauran da zai isa a bawa wani mai hankalin. Amma ko tsoro babu a idonta ta kalleshi take masa magana a tsaye. Idonta da ya kalla ne yasa gabannsa wani irin bugu, wanda sai da ya ji ƙaran bugun zuciyarsa a kunnuwansa. Ƙwayar idonta na da kyau kamar fuskarta, wasu irin olive green colour eyes gareta…