T.O.C Douglas Crescent, Kaura District, Game Village, Abuja.
RAJA POV.
Zaune yake a ɗakinsa, ya yi tagumi da duka hannayensa biyu, abun duniya ya bi ya isheshi, musamman yau da ya ga Rabi’a ba ta zo ba, abun ba ƙaramin ɗaga masa hankali ya yi ba, shi fa burinsa shi ne ya samu ya ganta don ya mata bayani, zai gabatar mata da kansa a ainahin yanda yake, zai faɗa mata gaskiyar komai a kansa, amma yau haka ya ƙaraci tsayuwarsa a ƙofar gate ɗin ba tare da ya ga gilmawarta ba.
Ƙofar ɗakin aka buɗe, sannan Rhoda ta shigo hannunta tiƙe da wayarsa. Kansa kawai ya ɗaga ya kalleta ya na ɗaga ƙafaɗarsa ta dama.
“Alhaji Bala ne yake ta waya. Yace ya na buƙatar kayansa cikin gaggawa”
“Mtswwww!”
Ya ja tsakin ya na kawar da kansa, shi ba ta Alhaji Bala yake ba, don matsalar Alhaji Bala sifili ce a wurinsa, babba kuma shirgegiyar matsla gareshi ita ce RABI’A!.
Ganin hakan ya sa Rhoda zama kusa da shi, sannan ta dafa ƙafaɗarsa.
“Na san halin damuwa da kake ciki, amma ya kamata ace ka sameta ku yi magana, ka faɗa mata gaskiya, wata ƙila ta saurare ka”
Fuskarsa ya shafa da hannayensa.
“Yau ba ta zo ba fa” Ya faɗi cikin wata murya me sanyi.
“Wata ƙila ta zo, ta ɓoye ne kawai dan kada ka ganta”
Da sauri ya ɗago kansa ya kalleta, ƙwarai, hakan za ta iya kasancewa, amma me ya sa shi bai yi tunanin hakan ba?.
“Ki na ga zan iya shiga cikin makarantar?”
“Me zai hana?”
Sai ya gyaɗa kansa, ya na hangowa kansa mafita a cikin kalaman Rhoda.
No.181, Guzape, Abuja…
07:00 PM.
MISHAL POV.
Tsaye take a kitchen tana juya stew ɗin da take dafawa, duk da yau girkin a makare take yinsa, saboda makarar da ta yi wurin dawowa gida. Ba tare da ta san lokacin da ya shigo ba, ta ji muryarsa a bayanta.
“Ana san magana da ke!”
Da sauri ta juyo ta kalleshi, ya na tsaye daga bakin ƙofa, kallonsa da ta yi a yanzu shi ya tuna mata da shirman da ta yi masa yau da safe a school ɗinsu, don haka ta yi ta nuna shi a wurin ‘yan makarantarsu tana faɗin ga mijinta nan.
“Waye yake san maganar da ni”
Kuliya ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, dai-dai da lokacin da Mishal ta ɗaga tata kafaɗar ta dama, don kawai neman tsokana, ita ta rasa me yake ji a wannan ɗaga kafaɗar, mutum ya yi ta wani ɗaga kafaɗa?, shi ba tsuntsun ba, kuma ta lura da wancan ɗan uwan nasa ma ya na ɗaga kafaɗar.
Cike da mamaki Kuliya yake kallon Mishal, wato shi take kwaikwayo?, don ta na ga ya na ɗaga kafaɗa shi ne ita ma za ta yi?. Kuma ita ma ta lura da kamar fushi yake shirin yi, don haka ta yi saurin cewa.
“Waye yake son maganar da ni?”
Maganar tata ta tuna masa da batun da ya zo mata, sai ya share batun ɗaga kafaɗa yace.
“Yayarki Nimra”
Sai ta juya ta kashe wutar gas ɗin, sannan ta juyo ta kalle shi.
“Wayar tana ina ?”
Da hannunsa ya nuna mata falo, don shi gajiya yake da wannan surutan, ita ma kuma ba tare da ta ƙara cewa komai ba ta raɓa shi ta fice tana dariya ƙasa-ƙasa.
Ƙamshin da stew ɗin ke yi ya ci gaba da shiga hancin Kuliya, don haka ya cewa kansa de yau ya kamata ace ya ɗanɗana abincin nata, sai ya shiga bubbuɗa pots ɗin da ta yi girkin da su, farar shinkafa ce sai wannan stew ɗin dake ta tashin ƙamshi, ga kuma coslow a gefe.
Tsakani da Allah abincin ya burgeshi kamar sauran abincinta, ga kuma yunwar da yake ji, saboda rabonsa da abinci tun safe, ya kai hannu ya ɗauki plate, ya zuba abincin iya yanda ya san zai iya cinyewa.
Sannan ya fara ci, bai taɓa zaton ƙaramar yarinya kamar Mishal za ta iya yin girki haka ba, a da duk ɗaukan zancen girkin nata yake a matsayin shirme, amma yanzu da ya ɗan-ɗana sai ya ji kamar irin wannan abincin yake buƙata a kullum domin ci.
Mishal na fita ta hangi wayar tasa aje a kan coffe table, da sauri ta ƙarasa wurin ta ɗauki wayar, gaisawa suka yi, kafin Nimran ta tambayeta yanayin zaman nasu, kana ta ƙara mata da nasiha, ita kuma Mishal ɗin babu abun da ta tambayeta sama da Daala, don ita kaɗai ta yi kewa.
Sai da suka gama wayar, sannan ta tashi ta nufi kitchen ɗin, zuciyarta ɗaya ta tura ƙofar kitchen ɗin, kuma abu na farko da idonta ya fara gane mata shi ne.
Kuliya tsaye a kusa da stove, hannunsa na hagu riƙe da plate, wanda yake cike da shinkafa da miyar da ta dafa, harda coslow a gefe, hannunsa na dama kuma riƙe da cokali, ya kai shi setin bakinsa ya na shirin kai loma.
Ba ƙaramar dariya ya bata ba, mutumin da a kullum yake gudun cin abincinta, yau shi ne ta kama ya na cin abincinta a ɓoye, amma sai ta riƙe dariyar, ba tare da ta ce masa komai ba, ta tsaya a kusa da shi, ta sauƙe tukunyar stew ɗin daga kan stove.
Kuliya ya ci gaba da binta da kallo, ya zaci za ta ce wani abun, amma sai ya ji ta yi shiru, har ta gama kwashe abincin duka, ta zubawa Ayra, sannan ta ɗauki nata ta zauna a kan kujerar island.
Ganin ya kasa ƙarasa cinye abincin nasa ya sa Mishal faɗin.
“Ka zauna ka ƙarasa ci”
Kuliya ya ɗan sosa ƙeyarsa, sannan ido ba kunya ya ƙaraso ya zauna a tsallakenta ya na ci gaba da cin abincin. Ita dai Mishal sai ƙunshe dariyarta take, duk da daga can ƙasan zuciyarta akwai wani abu ɗan ƙanƙani me kama da damuwa, kuma abun ya samo asali ne saboda rashin zuwan Adawiyya makaranta!, abu ne wanda tun bayan da suka ɗinke bai taɓa faruwa ba, ko a da can ba ta ganinta tana fashi bare yanzu, amma har can ƙasan zuciyarta take fatan kada Allah ya sa wani abu mara kyau ne ya faruwa da Adawiyyan.
Washe gari…
Brickhall School, Kaura District, Game Village, Abuja.
RAJA POV.
Cike da mamaki principal ɗin makarantar yake kallon mutumin dake zaune a tsallaken teburinsa, kamar ba shi ba ne jiya ya zo ya na tambaya a kan Rabi’a, yau kuma sai ga shi ya dawo da wani yanayi da ban, saɓanin wanda ya zo da shi jiya, stil kuma ya na sake tambayarsa a kan Rabi’an.
“Ka yi shiru, ko akwai matsala ne?”
Rajan ya tambaya, ganin yanda mutumin yake kallonsa, principal ya girgiza kansa.
“Ba haka ba ne, kawai dai yau kwana biyu kenan bat ta zo ba!”
Wani irin shiru ne ya ratsa office ɗin, kuma a cikin shirun, banda bugu cikin sauri babu abun da zuciyar Raja ke yi, wannan abun da yake ji a jikinsa ya fi ƙarfin tsoro, ji yake kamar ma ya haukace ne, me ya sa Rabi’an ba ta zuwa?, saboda shi ne?, amma me ya sa?, ko wani abu ne ya sameta?.
Da waɗanan tambayoyin fal a ransa ya bar office ɗin.
“Yayana!”
Ya ji an kira sunan a bayansa, amma bai tsaya ba, saboda halin da yake ciki ba zai barshi ya tantance da shi ake ko ba da shi ake ba.
“Ɗan uwa!”
Aka kuma kiran sunan, hakan ya sa ya tsaya sannan ya juyo, wannan yarinyar ce, wadda ta ce masa ya na kama da cousin ɗinta.
“Dama a nan kake ?”
Mishal ta tambaya a sanda take isowa gabansa, mamaki fal kanta, na son sanin me ya zo yi a makarantarsu.
“Na… Na zo neman wani ne”
Sai ta gyaɗa kanta.
“Ka same shi?”
Ta tambaya, sai ya girgiza kansa.
“A’a, ban same shi ba”
Ya faɗi yabna ɗaga kafaɗarsa ta dama, Mishal ta jinjina girman Allah a cikin ranta, sak Kuliya,duk da akawai ‘yan banbance banbancea tsakaninsu.
“Faɗamin sunansa, na san kowa a makarantar nan, zan nemo maka shi”
Duk da halin da yake ciki sai da ya ɗan murmusa.
“Ba lalle ki san shi ba. Zan koma, na gode ƙanwata, ki kula da kanki!”
Haka kawai ya samu bakinsa da furta sunan, kuma bai jira cewarta ba, ya juya ya ci gaba da tafiya.
Mishal ta ci gaba da kallon bayansa, abubuwa da dama na mata kai kawo a cikin kai, tana son ta san me ya sa Anti Adawiyya ba ta zuwa, kuma ta na son sanin me ya sa Kuliya babya tare da ɗan uwansa, tabna son ta san me ya sa su duka suka zo makarantarsu, don ta san ko Kuliyan ma jiya ba wurinta ya zo ba.
No.189, Radeemer Estate, Lugbe, Abuja.
Siyama da Karima Yayarta da kuma yaran Kariman ne zaune a falo suna karin kummalo. Kowacce a cikinsu jikinta ɗauke yake da rauni, raunin da suka samu a zuwansu gidan Kuliya.
“Salamu Alaikum!”
Suka ji sallamar Anna, a yayin da take turo ƙofar falon, da sauri Karima ta miƙe tsaye, hakan ya sa Siyama ma ta miƙe, saboda sun san ba su da gaskiya.
Ɗaya bayan ɗaya yaran Kariman su uku suka riƙa gaida Anna, ta na amsa musu.
“Abdul ku je ɗakinku ku ƙarasa karin a can”
Babban ɗan nata ya amsata ya na haɗa kan ƙannensa wuri ɗaya, tare da ɗiban kayan abincin nasu suka yi ɗaki.
Kamar da Annan take jira, ta samu guri ta zauna tana musu kallon tuhuma, ganin yadda ko waccensu ta kafa inda-inda ne ya tabbatar mata da gaskiyar abun da suka aikata, duk kuwa da ta san Kuliya ba zai mata ƙarya ba.
“Yanzu ke Karima a matsayinki na babba, ya kamata a ce kin aikata abun da kika aikata?, Ko za’a kira abun da Siyama ta yi a matsayin yarinta naki ba za a ce yarinta ba ce, saboda kin fita shekaru da sanin ya kamata. Amma saboda ke babbar kwabo ce, kika wanki ƙafa kuka je gidan matar mutane kuka rufa mata duka ko?!”
Da sauri Siyama ta girgiza kanta, hawaye na ciko mata ido, musamman da ta tuna abun da ya faru a wacan ranar.
“Anna Wallahi. Wallahi ba mu…”
“Ƙarya kuke!, Idan ba ku ne kuka daketa ba za ta buga kanta da kanta a jikin bango ne, ta zo tace ku ne kuka mata dan kawai ta muku ƙazafi?”
Da sauri Karima ta gyaɗa kai.
“Wallahi Anna ba mu daketa ba, hasalima ita ce ta dake mu, duba ki gani…”
Ta ƙarashe tana nunnuna mata tabon raunikan jikinta. Anna ta yi dariya, irin kun rena min hankalin nan.
“Karima ko ƙur’ani za ki dafa kan wannan maganar taki ba zan yarda ba, jibe ki fa, yadda kike rusheshiyar nan da ke sai na yarda waccan ‘yar fingilar yarinyar ita tai miki wannan raunin?, saboda ga Annan mahaukata ko?, to ni ba ma wannan ne ya kawo ni ba, zuwa na yi na ja muku kunne, babu ku babu gidan Aliyu, sannan babu ruwanku da sabgar matarsa, idan kuma ba ku ji ba ku je ku yi, Wallahi ni da kai na zan sa Aliyun ya hukunta ko waccenku, har ke Karima, tun da ba wani fikon arziƙi kika masa ba, in kun ce bakwa ji sai ku gwada mu gani!”
Tana ƙarashewa ta miƙe ta fita, don da ma abin da ya kawota kenan, Siyama ta zube a kan kejera tana fashewa da kuka.
“Kin ga inda kika kai mu ko Anti, yanzu ga shi bayan dukan da muka sha Anna ma ta ƙara mana da nata kashedin”
Karima ta matse ƙwalla, tunawa da irin dukan da suka sha da ta yi.
“Da ma ni sam soyyayar Kuliya ba ta karɓeni ba, ban da wahala babu abun da nake sha”
Ta ƙarshe tana miƙewa, tare da nufar ɗakinta da gudu. Karima ta yi tagumi tana jinjina sharri da kissa irin na wannan ‘yar mitsitsiyar yarinyar da suka rena, ko dan ai an ce ɗan hakin da ka rena.