Skip to content
Part 49 of 49 in the Series Labarinsu by Salma Ahmad Isah

No.86, Garki 2, Abuja…

RABI POV.

Zaune take daga bakin gadonta tana latsa wayarta. Ta shirya tsaf dan zuwa islamiyyar da Zaid ya ambata mata, yanzu haka shi take jira. Ji ta yi zuciyarta na tashi, hakan ya sa ta aje wayar hannunta. Jin cikinta murɗawa ya sa ta miƙe tsaye, sai kuma ta ji amai, ba shiri ta nufi banɗaki da gudu.

Amai ta shiga yi kamar me shirin amayo hanjinta, duk abun da ta ci na safiyar tas ta zazzage shi. Kuma bayan ta gama aman sai ta ji kasala ta kamata, ta ji jikinta duk ba daɗi. Kafin ta fito daga banɗakin ma sai take jin juwa na ɗinbata. Da ƙyar ta iya ƙarasawa ta zauna a bakin gadonta, hannunta na dama dafe da cikinta.

A dai-dai lokacin Zaid ya shigo ɗakin yana kiranta, ba ta samu damar amsawa ba, face binsa da kallo kawai da take, ganin yanayinta ya ɗarsa masa wani zargi a ransa.

“Baki da lafiya ne?”

Kanta ta girgiza masa tana miƙewa.

“Lafiyata ƙalau”

Be yarda ba, amma ba ya so ya takura mata, sai kawai ya gyaɗa kansa ya na kama hannunta.

“Na fahimta… Kin shirya?”

Kanta ta gyaɗa tana ɗan cije baki, saboda cikinta da take jinsa babu daɗi.

“Raj!… Me muke a nan?”

Muryar Rabi ta tambaya, a sanda ta ga Zaid ya kawosu wata football academy, makarantar da ta yi ta lokacin tana yarinya, dan a sanda Ummanta ke da rai nan take kawota training ɗin ball.‘As Roma Football Academy’ haka sunan makarantar.

Zaid be amsa mata ba, sai fita da ya yi daga motar, sannan ya zagayo ta ɓangarenta, ya buɗe mata motar, mamaki ya ƙi barin kan Rabi, haka ta fito baki buɗe, sai bin wurin take da kallo, wurin da rabonta da shi kusan shekaru shida kenan.

“Zuwa yanzu ta girma… Dan haka ba daga rukunin da ta tsaya za ta ci gaba ba, za mu turata cikin rukunin sa’o’inta”

Cewar shugaban makarantar, yayinda Zaid da Rabi ke zaune a tsallaken teburin office ɗinsa. Zaid ya gyaɗa kansa, duk da ba yau ya fara faɗa masa hakan ba, tun ranar da ya fara zuwa makarantar shugaban ya sanar masa da wannan batun. Kuma ya yarda da hakan, shi ya sa ma ya kaita aka mata gwaji a asibiti, kafin ta fara buga ƙwallon da ta kasance burin rayuwarta. Juyowa ya yi ya kalleta. A dai-dai lokacin da ita ma ta kalleshi, idonta ya ciko da ƙwalla, bakinta har rawa yake, ta ma rasa abun da za ta ce da shi, sai kawai ta kafe shi da ido tana kallo.

Da haka suka bar office ɗin, aka bata kayan da zata riƙa sakawa idan ta zo makarantar, wata jar jersy ce, da wandonta, shugaban ya sanar musu da cewar zuwa gobe za su dawo, domin za su mata gwaji, idan ta ci gwajin da za su mata, za ta iya fara karɓar horo tun daga ranar.

Suna tafe a mota ledar kayan na kan cinyar Rabi, hannunta ta kai ta fito da jersyn ta ɗagata sama tana kallo. ‘ADAWIYYA’ shi ne abun da aka rubuta a bayan rigar. Ƙwallar da take ta shanyewa tun ɗazu ce ta gangaro kan kuncinta. Sai ta ga kamar tana rayuwa ne cikin mafarki, domin da ƙwallo a mafarki take ganinta, bayan hargitsin da ya ahigo rayuwarta sai ta manta da ƙwallon. Ta haƙa wani wawaken rami a zuciyarta, ta cilla burikanta na rayuwa, ta binnesu, don a lokacin gani take rayuwar tata ta zo ƙarshe, labarinta ma ya ƙare, komai ma ya ƙare.

Shigowar Zaid rayuwata ya sauya komai, ya sauya yanda take kallon kanta, ya sauya yanda take ganin rayuwa, ya cika mata burikanta na rayuwa, duk abubuwan da take ganin ba masu iyuwa ba ne sun iyu, ta rasa me zata ce da shi, tace ta gode?, a’a, godiya ta yi kaɗan ta isar da shi, addu’a ita ce kawai abun da ya kamata ta masa, sannan ta ba shi ko wace kulawa, ƙauna da soyyaya. Ganin ya nufi hanyar Kaura ya sa ta share hawayenta, don bayan wani lokaci me tsayi, yau Allah ya yi za ta haɗu da ƙanwarta.

Sai da suka fara zuwa suka ga Rhoda, kafin ta fice ita ɗaya, bayan ta da faɗa musu cewar za ta je ta ga ƙanwarta, Zaid be hanata ba, don shi ma ya na so su tattauna da Rhoda kan case ɗinsu, saboda suna kyatata zaton zuwa gobe za’a shiga kotu.

Kanta tsaye Rabi ta shiga makarantar, masu gadi sai tambayarta suke, kan dalilin dena zuwanta makarantar, ita kuma tana amsa musu da rashin lafiya ta yi, kuma su ma sai suka yarda, saboda ganin tabon dake kwance a gefen fuskarta. Duk da sun ga sauyi sosai a tare da ita.

Kafin ta kai ss3 har ta fara hawaye, saboda ba ƙaramin farin ciki take ciki ba, ta ƙagu ta haɗu da Mishal, don ta bata labarin abubuwan da suka faru bayan rabuwarsu.

Cikin wata irin sa’a, tana isa ƙofar ajin ana kaɗa ƙararrawar break, hakan ya sa ta tsaya cike da zumuɗi tana san ganin fitowar Mishal. Sai da ko wani ɗalibi ya fice daga ajin, kafin Mishal ta miƙe tana muzurai, sai ciza baki take don tafiyar ma da ƙyar take, haka ta shiga taku cikin ƙarfin hali, har ta kai waje.

Ba tare da ta lura da wanda ke tsaye a bakin ƙofar ajinsu ba ta fara tafiya ta na nufar playground. Rabi’a ta lura da yanayin tafiyarta, amma kuma ɗaukin ganinta ya sa ta ture komai tace.

“Mishal!”

Cak Mishal ta tsaya da tafiyar da take, sakamakon sauƙar sautin muryar yayarta da ta ji, yayarta mafi soyiwa a ranta, yayarta da take ji da ita, yayarta da take cikin halin damuwa na rashin ganinta.

“… Kin ji abun da ya faru da ni!”

Cewar Rabi, a sa’ilin da ta ɗiga aya a ƙarashen labarin da take bawa Mishal, suna zaune ne kan kujerun da suka saba zama a da, Mishal wadda idonta ya cika da ƙwalla ta kalli yayarta. Duk da Yazid bai samu damar ci mata zarafi ba, amma ta san yaya zafin abun yake, ta san irin baƙin ciki da ƙuncin da ake shiga, ta san zafi da tabon da abun kan barwa ‘ya macen da ta fuskance shi. Ita ba ta da wani wayo sosai, amma ta san irin ƙasƙancin da mata ‘yan uwanta kan fuskanta, idan har basu kai budurcinsu ɗakin mazajensu ba. Duk da ita Adawiyyan ta tsallake wannan ramin.

“Yaya ina so na faɗa miki wani abu”

Rabi ta share hawayenta tana kallon Mishal.

“Kina kama da Aliyu, kuma na san ke ma kin san hakan, kina da danganta da shi?”

Rabi ta yi murmushi tana ɗauke kai.

“Wata ƙila idan na faɗa miki ba za ki yarda ba. Amma mijinki cousin brother ɗina ne, sannan kuma shi ne ƙanin mijina. Ɗan biyunsa ne, amma abun da ya shiga tsakaninsu ya rabasu ne… ban sani ba”

Wani irin shiru ya gifta a wurin, ba ka jin komai sai sautin wucewar iska. A cikin wannan shirun, Mishal ta kunce ta kuma saƙa ya fi sau a ƙirga. Kenan wannan wanda take gani a tsallaken makarantarsu shi ne Zaid ɗin da Adawiyya ta aura?.

“Da… Da ma Raja shi ne Zaid ɗin?”

Mamaki ya kama Rabi.

”Kin san shi ne?”

Mishal ta gyaɗa kanta da sauri ta na share ƙwalla.

“Na sanshi…”

Rabi ta yi ajiyar zuciya tana ɗaga kanta sama.

“Ya kamata mu san abun da ke faruwa a tsakaninsu”

Rabi ta faɗi tana sauƙe kanta ƙasa. Mishal ma kai ta gyaɗa mata cike da gamsuwa.

“Yau idan muka koma gida zan tambayi Aliyu”

Rabi ta yi murmushi.

“Ni kuma zan tambayi Zaid”

Sai kuma suka yi dariya a tare, ashe soyyayar da sukewa juna ba za ta faɗi ƙasa ba, ashe Allah ya hukunta zamowarsu facalolin juna. Dariyar da Mishal ta yi ce ta sa jikinta jijjiga, hakan ya sa ta yi famu, sai ta ɗan cije lips ɗinta cikin jin zafi. Sai a lokacin Rabi ta lura da abun da yake faruwa da ƙanwar tata.

“Me yake damunki Ƙanwata?”

Nan da nan ƙwalla ta cika idon Mishal, ta turo bakinta gaba tana shirin fashewa da kuka.

“Wallahi Anti Adawiyya Abu Aswad mugu ne, kuma zuciyarsa ma baƙa ce kamar kayansa, da ma ai na faɗa masa cewar sai na faɗa miki idan muka haɗu…”

Nan take Rabi ta gane inda zancen ya dosa, amma kuma sai sunan da ta kira mijin nata da shi ya bata dariya.

“Abu Aswad kuma Mishal?”

Mishal ta share ƙwallar da ta zubo mata.

“Abu Aswad mana, ba shi ne ba kullum cikin saka baƙaƙen kaya, shi ya sa na saka masa sunan…”

“Na ji kin ce kin gaya masa cewar za ki gayamin abun da ya miki, da ma ya sanni ne?”

Mishal ta kuma goge ƙwalla.

“Ya sanki mana. Sanda kika ɓata shi na sa ya yi ta nemanki, kuma na san cewa shi ma ya gano cewar an saceki , amma shi ne ya ƙi faɗa min”

Haƙuri Rabi ta shiga bata, kafin ta ƙarashe da bata shawarwari kan yadda za ta kula da kanta, da kuma gyara jikinta. Basu rabu ba sai da suka yiwa juna alƙawarin sanin dalilin rabuwar waɗanan ‘yan uwan biyu.

No.86, Garki 2, Abuja…

07:30pm

ZAID POV.

Gama wayarsa da shugabansu ke da wuya, ya ji wayar ta sa na ringing. Hakan ya sa ya duba screen ɗin wayar, don ganin me kiran. Ganin Kawu Abdullahi ne ya sa shi yin murmushi, ya na ɗaga kiran.

Gaisawa suka yi cike da girmamawa, kafin dalilin kiran ya taso.

“Ɗazu muke jin wani zance a gida. Wai ka kai Rabi’a makarantar ƙwallon ƙafa!”

Zaid dake tsaye a ƙofar ɗakinsa ya sosa kansa cikin jin nauyi, kafin yace.

“Eh haka ne”

“To tun wuri, ka yi gaggawar janye wannan ƙudirin naka… Ka bar ganin ita matarka ce, mu iyayenku ne, tun farko ya kamata ace ka shawarce mu kafin ka yanke hukunci a kanta. Ko a sanda take yarinya da mahaifiyarta ta kaita makarantar ba so muke ba, dan de muna ga yarinya ce, shi ya sa muka yi shiru. Amma a yanzu ta girma, tun da har mun mata aure, dan haka ba zamu ɗauki wannan shashancin ba. Tana mace me ya haɗata da wata ƙwallo?, zaman gida da kula da tarbiyyar yara shi ne ya dace da ita, ba gudu da gajeren wando a kan idon tarin mutane ba!…”

Haka Zaid ya ja bakinsa ya yi shiru, har Kawun ya kai ƙarshe a faɗan nasa bai ce masa ƙala ba, sai da ya tabbatar da Kawun ya kai ƙarshe a wajen amayar da abun da ke bakinsa kafin ya seta kamillalliyar muryarsa, ya shiga koro bayani a natse, kuma cikin da girmamawa.

“Na fahimce ka Kawu, kuma duk abun da ka faɗi gaskiya ne. Amma kuma ita ma Adawiyya tana da gaskiya. Ka san a ina ta yi gaskiya?”

Kawu Abdullahi dake zaune a kusa da su Baba ya juya ya kallesu, dan kuwa suma suna jin duk maganar da Zaid ɗin yake, sai kuma ya girgiza kansa cikin faɗin.

“A’a, sai ka faɗa”

“Lokacin da ta farfaɗo a asbiti, ta kalli idona tace min maza ba su da adalci, kansu kawai suka sani; kuma kasan dalili?”

Ya tambaya ba dan ya na buƙatar amsa ba, dan kafin ya amsa masa ya ci gaba da cewa.

“Dalilin shi ne; mu maza a kullum gani muke mune a gaba, dan haka dole duk abun da muke so shi za’a ayi, hakan ba wai kuskure ba ne, saboda mu Allah ya bawa girma, amma kuma su ma suna da nasu ‘yancin. Domin ko addini ya basu ‘yanci, daraja da kima, sai de ni kuma a yau ba ma duba hakan, sai namiji ya auri mace, ya zaunar da ita a gida, ya hanata rawar gaban hantsi, ya sa ƙafa ya take mata burinta da kuma ‘yancinta, ga shi de ba ta son abun da yake mata, amma saboda ganin ita macace sai ta haƙura ta ja bakinta ta yi shiru. Kawu a mafiya yawan lokuta muna dannewa mata hakkinsu, suna da baiwa kamar mu, suna da shauƙi kamar mu, suna da zuciya kamar mu, duk abun da zai fusata mu suma zai iya fusata su, banbanci mu da su shi ne, su sukan iya jurewa abun su shanye a cikinsu, wata dan ‘ya’yanta, wata dan iyayenta, wata ma dan mijin shi kansa, haka za ta jure rintsi da wuya. Kawu, Adawiyya ta shiga taskun rayuwa kala-kala, taga iftila’i da ban da ban, yanzu ne ya kamata ace ta samu jin daɗi da hutu, a yanzu ya kamata ace burukanta sun cika. Ni kuma ina son ta yi farin ciki, kuma na yi alƙawarin sama mata duk wani abu da zai dawwamar da murmushi a fuskarta. Ƙwallo mafarkinta ne, lefi ne dan na temaka wurin ganin ya zama gaskiya?!”

Shiruuu, har bayan shuɗewar wani lokaci, a cikin wannan shirun Baba dake kishingiɗe ya miƙe zaune da kyau, cikin alfaharin kasancewar Zaid jika a gareshi, Kawu Abdullahi kuma nadamar kiransa da masa wannan kashedin yake. Kasa cewa komai ya yi, ya kashe wayar. Jin wayar ta katse ya sa shi sauƙe wayar.

Sannan ya fita daga ɗakin, dan da ma niyyar fita yake, kiran shugaban nasa ya same shi. Shi ya sa ya tsaya ya amsa saboda muhimmanci kiran. Kitchen ya nufa, dan ya san ba za ta wuce can ba.

Damm, zuciyarsa ta harba bindiga, lokacin da ya saka ƙafarsa a cikin kitchen ɗin, abu na farko da ya fara arba da shi shi ne, Wutar gas a kunne tana ci. Irin waɗanan dalilan ya sa baya san shiga kitchen, ko da magana yake san yi da Rhoda idan har tana kitchen sai de ya haƙura. Ba shiri ya ji kansa na juyawa, duniyar ta fara masa duhu, numfashinsa ya shiga kokawar ɗaukewa.

Rabi dake wanke nama a sink ta juyo da sauri jin fitar wani kalar numfashi.

“Ga ruwa”

Cewar Rabi tana miƙa masa ruwa a cikin wani glass cup, Zaid da ke zaune kan kujera a falo ya ɗago da kansa ya kalleta. Kafaɗarsa ya daga ya na miƙa hannunsa tare da karɓar glass ɗin. Rabi ta zauna a gefensa tana shafa kafaɗarsa a sanda yake shan ruwan. Ita ta karɓi cup ɗin ta aje, bayan da ya kammala shan ruwan.

Gefen fuskarsa take kallo cike da damuwa. Har zuwa lokacin tana shafa kafaɗarsa a hankali.

“Na zubo maka abinci?”

Zaid da ya cilla duniyar tunani ya girgiza mata kai, ya na jingina da bayan kujera, hakan ya sa Rabi ta ɗauke hannunta daga bayansa, ta dawo da shi ƙirjinsa tana masa tausa. Ganin har zuwa lokacin be dawo dai-dai ba ya sa tace.

“Me yake damunka wai?”

Kallon fuskarta ya yi na wasu ‘yan sakkani, sai kuma ya kama hannunta dake kan ƙirjinsa, ya kwantar da ita akan ƙirjin nasa, ta yanda har tana iya jiyo sautin bugun zuciyarsa dake shirin ɓalla allon ƙirjinsa ta fito.

“Na san komai a kanki, ya kamata a ce kema kin san komai akaina!…”

Tun kafin ya kai ƙarshen labarin nasa Rabi ta fara hawaye, tunawa da ta yi cewar ɗan uwansa da yake so, kuma yake tunani ya mace yana raye.

“Zaid!”

Ta kira sunansa tana sharar ƙwalla. Kanta Zaid ya shafa yana amsawa.

“Aliyu ya na raye!”

Wani irin bugu da ta ji zuciyarsa ta yi ya sa ta yi saurin tashi daga jikinsa, dan a tunaninta ko zuciyar tasa ta buga ne gaba ɗaya. Amma kuma sai taga har lokacin yana da rai, sai de kuma kamar ya mace, dan kallonta kawai yake, amma jikinsa a ƙame. Wai me take faɗi ne?, Aliyu yana raye?, Aliyunsa bai mutu ba?. A’a, wata ƙila dai kunnensa ne ke haihuwa, ko kuma Rabi’a tana faɗin hakkan ne dan ta kwantar masa da hankali. Aliyu na raye?.

<< Labarinsu 48

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×