Skip to content
Part 17 of 67 in the Series Lokaci by Fareeda Abdallah

Ya ƙura ma guri ɗaya idanu yayi shiru. Kalaman da Ummanmu ta umarceshi da maimaitawa sun taimaka masa ƙwarai gurin rage ƙunci da baƙin cikin da ke danƙare a zuciyarsa. Ummee dai ta riga ta tafi, wanda ya fi shi son ta ya karɓi abarsa, sai addu’ar Allah ya gafarta mata yakai haske cikin kabarinta. Ya zama dole a gare shi ya rungumi wannan ƙatotuwar ƙaddara da ta afko masa, sai kuma tunanin yadda zai iya fuskantar rayuwar duniya ba uwa ba uba, ga yadda zumunta ya zama a wannan zamani da muke ciki.

“Yusuf? Na ce ka sanar da Khamis halin da ake ciki kuwa?”

Maganar Ummanmu ya dawo da shi cikin hayyacinsa.

A hankali ya girgiza mata kai, alamar a’a!

“Kayi haƙuri, ya kamata ka kira lambar shi Alhajin ya sanar da su. Idan da hali suyi gaggawar tahowa ayau ya samu damar ganawa da gawar Hajiya kafin a kaita gidanta na gaskiya.”

A kasalance ya lalubo wayarsa a cikin aljihu, kamar wanda aka zare ma laka. Haka yake komai a saiɓance, sau biyu yana wuce sunan Alhaji Bashir kafin Allah yasa idanunshi tsayuwa akan sunan, ya danna ma lambar kira…’

Firgigit yayi ya dawo daga nannauyan tunanin da ya afka lokacin da ƙanin mahaifinsa ya jijjiga shi da ƙarfin gaske.
A hankali ya ɗaga idanunsa da suka yi jaa sosai ya sauke akan Baba Lurwanu.

“Anya kuwa Yusufa, Anya? wannan zuzzurfan tunanin zai haifar maka da ɗa mai idanu kuwa? Ca nake mutuwar nan wajibi ne akan ko wane musulmi?”

Ya kasa amsawa, a maimakon ya amsa ma sai ya sauke kanshi ƙasa, idanunshi ciccike da ƙwalla.

Da tausayi sosai a fuskar Baba Lurwanu ya kamo hannun Yusuf guda ɗaya ya riƙe.
“Yusufa kayi haƙuri, na sani mutuwa akwai ciwo, akwai raɗaɗi musamman rabuwa da mahaifa. To amma me bawa zaiyi tunda ba shi ya halicci kansa ba? Mutuwar nan dole ce akan ko wane mai rai, muma duk ita muke jira, su da suka tafi basu yi sauri ba, mu da muke nan bamu daɗe ba. Kai da ya kamata ma ka gode ma Allah, mahaifanka duk su biyun kyakkyawar shaida suka samu a gurin ƴan’uwa da abokan arziki, kuma ka dubi yadda gawarwakinsu ya tara mutane masu ɗumbin yawa, ko daga wannan ma ai kaga ana saka ran samun rahama a gare su. Kayi haƙuri, Ubangiji Allah ya jiƙan Hauwa’u da Abubakar.”

“Ameen. Na gode Baba.”
Ya faɗa daƙyar, yana jin yadda bakinsa ke masa wani irin ɗaci.

Wani jug mai kyau Baba Lurwanu ya ɗakko a gefensa, yana buɗewa sai ga kunun gyaɗa fari tas. Ƙaramin kofin da ke ajiye ya ɗauka ya tsiyaya kunun a ciki ya miƙa ma Yusuf
“Karɓi, yi maza yanzunnan ka shanye ka bani kofin, maƙwafciyarku sarkuwar Hamisu ta aiko da shi musamman ta ce don Allah a baka. Kuma ina lura da kai yinin jiya har dare baka saka komai a cikinka ba, yi sauri ka shanye ka bani kofin.”

Ko da ya karɓi kunun, ya daɗe riƙe da kofin a hannunsa, shi bai sha ba, shi bai ajiye ba. Har sai da Baba Lurwanu ya sake cewa
“Yusufa sha mana.”

A hankali ya ɗaga kofin yakai bakinsa ya kurɓa, duk da bakin babu daɗi, kunun na ratsa maƙogwaronsa zuwa cikinsa ya tabbatar yana jin yunwa.

Da zafi-zafi yai ta kurɓa a hankali har ya kusa shanyewa, tambayar da Baba Lurwanu yayi masa kan Khamis na dalilin da ya hana shi zuwa tun jiya yasa shi yin shiru cikin tunani.
‘Awa uku cif aka ƙara bayan tabbatar da rasuwar Ummee kafin aka yi jana’izarta. A cikin awa ukun nan ya tsammaci ganin Khamis ya iso afujajan, amma har aka bizne ta babu Khamis babu Alhaji Bashir, babu kuma kiran waya daga Alhajin don bayar da uzurin ko go-slow ne ya hana su isowa akan lokaci.

Bayan an dawo daga maƙabarta ma bai cire ran ganin tilon ƙanin nasa ba, yana zaune a ƙofar gida cikin taron ƴan’uwa da abokan arziki hankalinsa rabi da rabi yana kallon hanyar shigowa cikin layin ne. Duk motar da ta ƙaraso ta faka a tsammaninsa Khamis da Baba Bashir zai gani, amma har aka shafe tsawon yinin gaba ɗaya bai ga ko mai kama da su ba. A tunaninsa, wannan muhimmin rashi ne da duk wanda zai ji a jikinsa bayan su biyun nan ne, ya so Khamis ya iso akan lokaci, su rungume juna suyi kuka, su jajanta ma juna kan wannan rashi da suka yi, su shafe tsawon lokaci suna yi ma iyayensu addu’a, sannan ya raka Khamis har kabarin Ummee ya ziyarceta, yayi mata addu’o’i. Idan sun dawo gida sai ya ba shi labarin yadda har a gargarar mutuwa Ummee bata daina ambaton sunansa ba.

Ladan yana ƙwalla kiran sallar magrib ya cire rai da ganin Khamis. Hannu yasa ya ɗauke ƙwallar da ta cika masa idanu, ya tattara tunanin ƙanin nasa ya ajiye a gefe ɗaya…’

“Alhaji? Kuzo da sauri don Allah, su Khamis ne suka iso, ga shi can ya yanke jiki ya faɗi a tsakar gida.”
Muryar Inna Balaraba matar Baba Lurwanu ya katse mishi tunanin da yake yi.

Da saurin gaske Baba Lurwanu ya miƙe yana faɗin
“Subhanallahi, Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un!”

Ko kafin Yusuf ya yunƙura don miƙewa, har Baba Lurwanu ya fice daga ɗakin Inna Balaraba ta bi bayansa. Shi kam har ya miƙe, sai ya koma ya zauna jaɓar, yana jin yadda wani ƙunci da damuwa ya sake lulluɓe zuciyarsa. Wani dunƙulallen abu da bai san ko menene ba ya tsaya mishi a maƙoshi, a jere sau biyu yana haɗiye kakkauran miyau ko abun zai wuce amma bai wuce ba.

A hankali yaja da baya ya jingina da jikin kujera, idanunsa ya lumshe. Sannu-sannu yake jin yadda bugawar zuciyarsa ke sauyawa, daga sannu a hankali zuwa sauri sauri. Addu’o’i yake ta maimaitawa a zuciyarsa don samun sauƙin halin da yake ciki.

“Bismillah, ku shigo da shi, kuyi a hankali Malam. Alhaji sannunku da zuwa.”
Ire-iren kalaman da ke fita daga bakin Baba Lurwanu kenan har aka ƙarasa shigo da Khamis ranga-ranga cikin falon. Kan doguwar kujera aka kwantar da shi.

Dr. Nura da yake ƙofar gida lokacin da mata suka fasa kururuwar faɗuwar Khamis ɗin da saurin gaske shi da wasu maza suka shiga cikin gidan don ganin abinda yake faruwa. Ko da yaga halin da ake ciki da sauri ya fice zuwa gidansa don ɗauko kayan aikin gaggawa, bayan ya hana a tafi da Khamis ɗin asibiti, tunda anyi ta shafa mishi ruwa a tsakar gida bai farfaɗo ba.

Duk da yake safiya ce, cikin gidan da ƙofar gida mutane ne sosai. Da yawan ƴan’uwa na jiki-jiki a gidan suka kwana. Babban falon Hajiya Hajiya Hauwa’u cike yake da mata. Can cikin uwarɗakin Ummee aka shigar da Ziyada da take lulluɓe ruf, har da niƙafi a fuskarta. Hajiya ma sanye take da zumbulelen hijabi mai kauri, ta rungume ƴar laɓuɓuwar jaririyar da aka yi mata shiri sosai cikin kayan sanyi, sannan aka naɗe ta a cikin tawul mai kauri, aka rufe ta a cikin hijabi, duk domin kar ta shaƙi iskar hanya, ga tafiyar ba kusa ba. A cikin ɗakin suka tarar da Ummanmu, ƙannen Hajiya Hauwa’u da wasu ƴan’uwa na kusa sosai. Ganin Ziyada da Babyn da ta haifa sai lamarin ya haɗe musu biyu, ga jimami, ga murnar ƙaruwar da aka samu. Ita dai Ziyada kanta ta kwantar a ƙafafun Ummanmu tana sharɓen hawaye.

Ƙaramin falon Alhaji Abubakar inda Yusuf ke zaune aka shigar da Khamis. Kallo ɗaya Yusuf yayi ma Khamis ya kawar da kansa da sauri, ganin yadda ƙanin nasa yayi wani irin rama sosai, yayi baƙi, kamar ba Khamis ɗan ƙwalisan matashinnan da ƴanmata ke rububinsa ba.

Dafa kafaɗarsa da aka yi yasa shi ɗaga idanunsa ya kalli wanda ya dafa shi, sai yaga Baba Bashir ne. A hankali ya zame zai durƙusa ƙasa da sauri Baba Bashir ya riƙo shi, tsaye ya miƙar da shi ya rungume shi a jikinsa yana ɗan bubbuga bayansa alamar rarrashi, sun ɗauki daƙiƙu cikin shiru zukatansu cike da jimami, kafin Baba Bashir yayi ƙarfin halin ɗago Yusuf daga jikinsa suka kalli juna cikin ido.

Yusuf ne ya fara saukar da ƙwayoyin idanunsa ƙasa. Hawaye ne ya cicciko a idanunsa, lokacin da Baba Bashir yayi ƙarfin halin fara mishi gaisuwa da addu’ar Allah ya jiƙan mahaifiyarsa, da mahaifinsa da bai jima da rasuwa ba. A taƙaice ya ƙara da faɗin irin kyawawan halayensu da ya sani, ya cigaba da addu’ar halayensu na gari ya bi su har cikin kabarinsu.

“Ameen ya Allah”
Mazauna cikin falon suka amsa gaba ɗaya.

Hannun Yusuf ɗin ya ja suka zauna kan kujera suna kallon irin kulawar da Dr. Nura yake ba Khamis. Mai abu da abinsa, cikin ƙanƙanin lokaci Khamis ya farfaɗo, ya dawo cikin hayyacinsa. Kamar ba shi ne aka shigar da shi falon ranga-ranga ba ya numfashi ba.

Duk yadda ake jera mishi sannu ya kasa amsawa, duƙar da kanshi ƙasa yayi ya dinga rusa kuka. Can da ya ɗaga kai yayi ido biyu da Yusuf da rarrafe ya sauka daga kan kujerar da yake ya ƙarasa kusa Yayan nasa ya rungumeshi. Kuka yake yi sosai, gwanin ban tausayi, mazauna falon sai share hawayen suke yi, mutuwar ta dawo musu sabo.

‘Jiya tunda ya fita daga gida, bai koma ba sai misalin ƙarfe goma saura minti biyar na dare. Da kallon fuskarsa za’a gane a firgice yake, hankalinsa a tashe, da wannan yanayin nasa da su Hajiya suka gani yasa suka yi tsammanin ko ya samu labarin rasuwar Ummee ne.

Ko da ya musu sannu da gida, yayi tsammanin zai samu tukwuicin faɗa kan daɗewar da yayi a waje, abinda bai saba faruwa ba ko a lokacin da yake karatu. Da yaji Alhaji bai ce mishi komai ba sai bin shi da yake yi da wani irin kallo sai yayi tsammanin laifin da yayi ya girmama ne, har Alhajin ya rasa da wasu irin kalamai zaiyi amfani gurin yi masa faɗa.

Don haka ya zauna dirshan a ƙasa ya sunkuyar da kanshi, ya haɗe hannaye biyu ya fara bayar da haƙuri kan daɗewar da yayi, tare da alƙawarin hakan bazai sake faruwa ba in Allah ya yarda.

Maganar da suka ji yana fita a bakinsa yasa suka tabbatar ba shi da labarin babban rashin da yayi. Haɗa idanu suka yi, sannan Baba Bashir ya ɗan muskuta yana sake karantar yanayinsa, tunda an ce labarin zuciya a tambayi fuska. Har lokacin wannan firgici da tashin hankalin kwance yake ƙarara a fuskar Khamis. Ya kamata ya tambaye shi ina ya tafi tsayin yini gaba ɗaya? Ya kamata ya tambaye shi me yake damunsa? Mecece matsalar da yake gani kwance a fuskarsa? Amma bazai iya ba, saboda shi kanshi yana cikin wani irin yanayi ne na kewa da juyayi. Tun bayan da suka dawo daga asibiti bayan fargabar ina Khamis ya shiga? da addu’ar Allah yasa yana lafiya ƙalau. Babu abinda yake yawan tunani sai marigayi Amininsa Abubakar da matarsa Hauwa’u. Aminin da nisan gari baisa sunyi wasa-rere da amintakarsu ba. Haka ya kwaso hotunansu masu yawa yana kallo yana sharar ƙwalla, sai kuma ya musu addu’ar Allah ya gafarta musu.

Maimakon ya fara faɗa masa rasuwar Ummee, sai ya ɓuge da faɗa masa matarsa ta sauka.

“Ta haihu Baba? Laa’ila… Alhamdilillah.! Kaaai… Allah na gode maka. Me ta haifa Hajiya? Yanzu haka ina Ziyadar? Allah yasa dai ita da Babyn lafiya lau suke?”
Ya jero maganganun a ruɗe, da fara’a sosai a fuskarsa, bakinnan a wage kamar gonar auduga.

“Ƴa mace ta haifa Khamis, ita da Baby lafiya ƙalau, suna cikin ƙoshin lafiya. Yanzu haka ma suna cikin ɗaki suna barci.”
Hajiya ta amsa mishi da ɗan taƙaitaccen murmushin yaƙe, amma saboda murnar da ya shiga sanadiyyar jin ƙaruwar da ya samu ko kaɗan bai lura ba.

“Bari in leƙa in duba lafiyarsu.”
Ya faɗa a ɗokance sannan ya yunƙura da nufin miƙewa tsaye.

“Khamis?”
Baba Bashir ya kira sunanshi.
“Ziyada ta galabaita sosai gurin haihuwarnan. Likita ya so ya riƙeta ta kwana a asibiti amma sai muka roƙi alfarmar a bamu ita mu dawo gida, bayan munyi alƙawarin za mu barta ta huta sosai. Don haka tun ɗazu barci take yi, ka zauna anan, bari Hajiya ta shiga ciki ta ɗauko maka jaririyar, idan Allah ya kaimu gobe da asubah sai ku gana da Ziyada.”

Jin wannan maganar yasa jikinsa yayi sanyi, a hankali ya koma ya zauna, zuciyarsa cike da tunani mabanbanta. Kamar bazai sake cewa komai ba sai kuma ya ce
“Baba da gaske lafiyarta ƙalau?”

“Zanyi maka ƙarya ne?”
Baban ya mayar masa da tambayar bayan ya ɗan harhaɗe girar sama da ƙasa.

Yana nan zaune Hajiya ta shiga ta fito masa da jaririyar da kallonta kawai ya mantar da shi duk wani firgici da tashin hankali da ya koma da shi cikin gidan. Haka ya dinga kallonta fuskarsa a washe, zuciyarsa cike da matsananciyar ƙaunarta. Shi fa bai taɓa sanin yana da son yara ba sai ranar da aka nuna masa Nauwara a matsayin ƴarshi ta cikinshi.

Yanzu kuma ga wata kyakkyawar zinariyar Ziyada ta sake suntulo mishi, shi kam me zai ce ma Ziyada? Tsakaninsu sai sakayyar soyayya mai tsanani haɗe da tsaftatacciyar ƙauna mai tafe da tausayawa haɗe da girmamawa. Minti ɗaya biyu sai ya tofa ma jaririyar duk addu’ar da ta zo bakinsa.

Ita dai barcinta take hankali kwance, duk juya ta da yake yi bata san halin da ake ciki ba. Ta fi minti talatin a hannunsa kafin Hajiya ta katse masa hanzari ta hanyar cewa ya kawo yarinyar ta mayar da ita ɗaki.

“Ayya mana Hajiya, ko mu ɗan ƙara minti kaɗan? Bata gama jin ɗumin Daddy ba…”

“Khamis ungo naka”
Baba Bashir yayi masa daƙuwa.
“Maza miƙa mata ita a mayar da ita cikin ɗaki. Na zaci gobe ma rana ce? in dai ƴa ce har sai ka gaji da riƙe ta tunda taka ce.”

Haka nan ba don ransa na so ba ya miƙa ma Hajiya ita. Bai ƙara daɗewa a zaune ba yayi musu sai da safe ya shige ɗakinsa, bayan Hajiya ta sake yi mishi tayin abinci ya ce ya ƙoshi.

“Alhaji? Yanzu sai yaushe kenan za ka sanar da shi rasuwar?”

“Gobe da asubah in sha Allahu. Tunda aka shafe yinin yau bai sani ba, idan na faɗa mishi a yanzu tabbas na rusa mishi darennan kenan, bazai taɓa iya barci ba. Gobe muna idar da sallah zan tari liman ya taya ni yi mishi nasiha sannan mu sanar da shi.”
Da haka iyalan suka rabu.

Da asubah kamar yadda Baba ya tsara haka ce ta kasance, tun a masallaci yake kuka. Duk yadda Liman yayi sharar fage da nasiha mai ratsa zuciya ya kasa riƙe kansa. Rasuwar Ummee duk da ba ta da lafiya abu ne da bai taɓa tsammani nan kusa ba.

Daƙyar suka isa gida, babu ɓata lokaci kuma suka hau shirin tafiya kaduna. A lokacin har direban Alhaji Bashir ya isa gidan. Khamis bai ƙara tabbatar da rasuwar Ummee da gasken gaske bane, sai da suka isa ƙofar gidansu yaga maza da yawa a wajen, ga rumfuna an kafa a ƙofar gidan. Suna shiga cikin gidan ne zuciyarsa tayi rauni, duk yadda yake daurewa a dole ya yanke jiki ya faɗi ƙasa war-was.’

<< Lokaci 16Lokaci 18 >>

1 thought on “Lokaci 17”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.