Bai fara neman Bilkisu da niyyar ɓata wani dogon lokaci ba. Sanin mahaifinta da matsayinsa na babban malamin addini yasa kafin zuwanshi Zariya, sai da ya sami mahaifin Falalu da ya kasance dattijo ya nemi alfarmar don Allah yaja mishi gora gurin shigewa gaba zuwa gurin Malam a nema mishi izinin fara neman auren Bilkisu.
Halayen Khamis ɓoyayyu ne ga waɗanda basu cika mu'amalantarsa ba. Da wannan dalilin yasa ba tare da wani ɗar ba Alh Yahaya da rakiyar abokinsa suka je nema ma Khamis izini, kamar yadda ya nema.
"Ma sha Allah! Na gode sosai Alhaji. A. . .
Dan Allah a kara mana update🥹