Skip to content
Part 39 of 67 in the Series Lokaci by Fareeda Abdallah

Bai fara neman Bilkisu da niyyar ɓata wani dogon lokaci ba. Sanin mahaifinta da matsayinsa na babban malamin addini yasa kafin zuwanshi Zariya, sai da ya sami mahaifin Falalu da ya kasance dattijo ya nemi alfarmar don Allah yaja mishi gora gurin shigewa gaba zuwa gurin Malam a nema mishi izinin fara neman auren Bilkisu.

Halayen Khamis ɓoyayyu ne ga waɗanda basu cika mu’amalantarsa ba. Da wannan dalilin yasa ba tare da wani ɗar ba Alh Yahaya da rakiyar abokinsa suka je nema ma Khamis izini, kamar yadda ya nema.

“Ma sha Allah! Na gode sosai Alhaji. A wannan lokaci da muke ciki duk wanda ya ce yana son naka ya gama maka komai. Kuma na yaba da zurfin hankalin Yaron da baiyi gaban kansa ba ya fara zuwa gurin yarinya ba ba tare da neman izinin mahaifanta ba. Wannan tsari da ya biyo shi ne abinda Addini yayi umarni. Na gode ƙwarai.

Kuma ina addu’ar Allah ya tabbatar mana da alkhairi, amma kafin in bashi izinin fara zuwa gurin Nana Bilkisu ina buƙatar a bani lambar wayarsa da cikakkiyar sunansa. Zan sa a bincika min kamar yadda addini ya ba mu iyaye dama, idan na gamsu da ɗabi’u da halayensa ba tare da ɓata lokaci ba zan aura masa Nana Bilkisu. Domin a tsari na ba’a yi min dogon samartaka a gida.”

*****

Taraddadi da fargaba. Manyan abubuwa biyu da suka cika zuciyar Khamis a cikin kwanaki goma da ya shafe yana zaman jiran kira daga mahaifin Bilkisu. Kamar yadda Malam Yahaya ya sanar da shi duk yadda suka yi da mahaifinta. Wani abu da Khamis bai taɓa yi ba a iya tsawon rayuwarsa ta duniya shi ne tashi tsakiyar dare ya roƙi Allah kan wata buƙata da yasa a gaba.

A gefe guda kuma a ɓoye, yana cigaba da ragargaza zuciyar Nana Bilkisu da kalaman soyayya, wayar da basa samun damar yi sai a ƙididdigaggun lokuta idan ta fito daga gida za ta Tahfeez, ko kuma idan za ta tafi makarantar boko, ko kuma fita da ya zama dolen-dole gare ta, saboda ba kasafai suke fita barkatai ba sai da ƙwaƙƙwaran dalili.

A lokuta da dama idan suna waya har kuka yake mata, kuka na gaske ba na wasa ba. Saboda wata iriyar zazzafar soyayya da yake ji zuciyarsa tana yi mata. A kwanakin ne ya tantance soyayyar da yake ma Bilkisu ta sha ban-ban da wanda yayi ma Ziyada, zai iya rantsewa da girman Allah soyayyar Bilkisu ta ninka na Ziyada sau biyar, saboda yanayin azabar da zuciyarsa take ciki ba ɗaya ne da wanda ya ɗanɗana lokacin Ziyada ba.

Kwanaki shida ya kwashe kullum sai ya tashi tun ƙarfe uku na dare har zuwa asubah, nafilfili yake yi, sannan ya ɓuge da roƙon Allah ya mallaka masa Bilkisu. Shi babu ruwansa ko alkhairinsa ce ita, burinsa ya samu aurenta ko ta halin ƙa-ƙa. Allah ya kawar da duk wata fitina ko tashin-tashina da zai kawo tsaiko a batun soyayyarsu har zuwa sadda za’a mallaka masa ita.

A cikin kwanakin, duk wasu munanan harkokinsa ya dakatar, ya fi zama a gida. A gidan ma ya fi zama shiru-shiru a cikin ɗakinsa yana tasbihi ga Ubangijin sammai da ƙassai.

Ko da yaga hankalin yaran ya fara ɗagawa da ganinsa shiru-shiru kuma a cikin ɗaki, abinda sam ba ya daga cikin ɗabi’unsa. Abinda suka saba da shi shi ne ko da ba shi da lafiya idan ya daɗe a gida ne ya kwana biyu, ganin za su dame shi da tuhuma yasa da kanshi ya faɗa ma yaran lafiyarsa ƙalau, su taya shi da addu’a. Akwai wata buƙata da yake da ita ga Ubangiji shi yasa ya keɓance kanshi yana addu’o’i.

A sadda yake maganar Ziyada tana zaune can gefe ɗaya tana daddanna wayarta. Akan idanunsa ta taɓe baki, taja tsaki ƙasa-ƙasa, daga ƙarshe ma ta tashi daga gurin fuuu ta shige ɗakinta lokacin da ta ji yaran gaba ɗaya sun ruɗe suna masa addu’ar Allah ya biya masa buƙata.

Kiran gaggawa da Sanata Ɗanjuma yayi masa bayan ya kwana biyu bai neme shi ba, da buƙatarsa na saffa-saffan ƴanmata yara ƙananu masu jini a jika guda uku shi ya katse mishi duk wani hanzari. Kamar bazai amsa kiran ba, amma sanin irin asaran maƙudan kuɗaɗen da zai tafka idan bai amsa kiran ba yasa shi katse duk wani hanzari nashi ya amsa wayar. Kamar yadda ya zata, ƴanmata ne Sanatan yake so da gaggawa, za’a kai mishi su Abuja a ranar.

Haka nan ya amsa da
“To Ranka ya daɗe. An gama! Za’a same su kamar yadda ake so!!”

Cikin ƙanƙanin lokaci yana daga zaune nan cikin falonsu ya tsara ƴanmatan da zaiyi tafiyar da su, saboda ƙananun karuwai masu ƙanƙanan shekaru da manya waɗanda suka daɗe a harkar suna nan zube da yawa, shi kanshi bazai iya iyakance ƴanmatan da yake harka da su ba, saboda a kullum ƙara samun sabbin shiga ake yi.

Awa huɗu tsakani yayi duk shirin da zaiyi, a lokacin yaran sun dawo daga makaranta yayi sallama da su, ya kalli ɓangaren da Ziyada ke zaune ko kallon tsiya bai samu ba balle ya samu arzikin Allah ya tsare daga bakinta ba, ya san kuma hakan bai rasa nasaba da yadda ta ji shi yana amsa wayar cewa za’a taho da su a ranar. Ta san kawalcin ƴanmata zai je, shi a karan kanshi ya san Ziyada ta yi mishi ƙwaƙƙwaran sanin da ko motsi idan yayi ko da bakinsa bai furta ba za ta iya fassara abinda zai aikata.

Haka ya fice daga gidan jikinsa a saɓule, zuciyarsa cike da damuwar yadda kullum al’amarin zamantakewarsu ke ƙara taɓarɓarewa. Gani yake kamar a hankali Ziyada take rikeɗewa daga wacce take tsananin ƙaunarshi zuwa wacce take zaune da shi na dole, a yadda take nuna mishi kamar ma ba ta da wani zaɓi ne a zama tare da shi. A dole take zaune da shi, lallai ya kamata bayan auren Bilkisu ya nemi daidaito da Uwar ƴaƴansa. Saboda soyayya ce ta haɗa su ba ƙiyayya ba.

Daga gida, kai tsaye ya wuce zuwa inda ya umarci ƴanmatan suyi mahaɗa, ya kwashesu a sirrance suka nufi Abuja. A yadda ya tsara, kwanaki biyu kacal zai yi a Abuja ya karɓi sallamarsa ya juyo Kaduna.

Amma cikin hukuncin Allah Kwananshi ɗaya ya samu kiran da ya daɗe yana tsammani daga mahaifinta. Bayan amsa wayar a ladabce, jiki da bakinsa na rawa kamar yana gaban Sheik ɗin. A fujajan ya juyo zuwa kaduna ba tare da yayi sallama da Ƴan matan da ya tafi da su ba ballantana Sanata Ɗanjuma, ko ta kan sallamarshi bai bi ba ya tattara ina-shi ina-shi ya kamo hanyar zuwa Kaduna. Tsakaninsa da Allah ya ma manta da al’amarinsu gaba ɗaya.

Kamar dai shi ke da washe gari, tun a hanya ya gama tsara duk abinda zai faru a gobe lahadi da zai amsa kiran babban malamin kuma mai shirin zama sirikinsa. Cikin motarsa ya ɗan waiga ya kalli gefe da gefe, babu laifi, motarsa babbar mota ce da in dai ba ƙarya zai saka ma kansa ba babu inda bazai shiga da ita ayi mishi kallon daraja ba.

A cikin tsadaddun suturun da yake da har ya gama tsara dakakkiyar shadda getzner da zai saka a goben, hula da takalmi da agogo duk ya gama zaɓin waɗanda za su shiga da kayansa. Tun a hanyarsa ta dawowa ya kira wani abokinsa da yake canjin sabbin kuɗi ƴan dubu-dubu ya umarci ya aje masa canjin dubu ɗari. A yadda ya tsara, waɗannan kuɗaɗen gaba ɗaya zai ƙarar da su ne gurin yi ma ƙannen Bilkisu da iyayenta mata alkhairi, domin gidansu babban gida ne da ya tara iyalai da yawa. A tunaninsa yayyafin kuɗi da zaiyi musu ba ƙaramin girma da daraja zai sake kankaro ma kansa ba.

A goben tare da Yaya Yusuf yake so su tafi zaria. Da wannan dalilin yasa yana shiga cikin garin kaduna kai tsaye gidan Yayan ya wuce. Abu ne da bai taɓa tsammani ba yadda Yaya ya iya baɗawa idanunsa toka yace bazai je nema mishi aure ba, duk da kuwa ya ji a babban ahalin da ya nemo auren.’
Wannan mamakin da ɓacin ran bai sake shi ba har ya ƙarasa gidansa, a lokacin ana ta kiraye-kirayen sallar isha’i a masallatan unguwar.

Daram! Ƙirjin Nauwara ya buga lokacin da ta ji muryar ƙannenta sun ruɗe da murna suna faɗin.
“Oyoyo! Daddy! Oyoyo! Daddy!”
Runtse idanu tayi tana jan duk wata addu’a da ta zo cikin zuciyarta. Shaf! Ta ma manta a cikin bayi take ba’a addu’a a ciki.

A gaggauce hankalinta a tashe ta fice daga cikin bahon ruwan zafin da take zaune dirshan tana gasa jikinta kamar yadda Mummy ta umarceta akai-akai. Ruwan ta zubar, ta sake tara wani ruwan, ta saɓa soso a jikin sabulu ta fara wanka, jikinta babu inda ba ya rawa.

Ko da ta fito daga bayin, ta kasa yin hanzari wajen shiryawa, duk da kuwa a ɗokance take da son zuwa yiwa Daddynta sannu da zuwa. A zuciyarta take ta addu’ar Allah ya taushi zuciyar Mummy kar ta faɗa ma Daddy irin daɗewar da tayi a waje. Duk da ta san mawuyacin abu ne hakan ya faru, ko don saboda rashin jituwar da ke tsakaninsu. Amma da tayi tunanin irin yadda wani lokacin iyayen nasu ke kamar wahainiya wajen sauya yanayin zamantakewa yanzu daɗi anjima ba daɗi sai zuciyarta ya ƙara ɗugunzuma.

‘Bayan dawowarta a ƙurarren lokaci ta sha faɗa kamar Mummyn za ta aro baki. Da ace Mummyn mai saurin hannu ne ta tabbata yau da ta sha mari ba ɗaya ba ba biyu ba. Don sau uku tana ɗaga hannu sai kuma ta sauke ta cigaba da zazzaga bala’i. Kiran wayar Mummyn da Aunty Ruƙayya tayi shi ya kawo ƙarshen faɗan ta samu sulalewa zuwa ɗakinsu jikinta a saɓule.

“Aunty Nauwara tun safe sai yanzu after magrib, don Allah ina kika je…?”

“In da kika aike ni. Sa’idawa masu barci da ido ɗaya ina ruwanki da harka ta?”
Ta katse Mannirah a tsawace, da salo irinna neman wanda za ta sauke ƙuncin da ke zuciyarta a kanta.

Ƙasa-ƙasa Mannirah ta harari yayar nata. Sum-sum ta fice daga ɗakin zuwa gurin ƙannenta. Harara Nauwara ta raka ta da shi har ta ɓace ma ganinta, a fili ta ja tsaki sannan ta cire hijabi ta fara kwaɓe kayan jikinta don yin wanka da alwala. Tana cikin bayin ne ta ji yara na murnar dawowar Daddy.’

“Aunty Nauwara wai ki je inji Daddy.”
Ta ji muryar Hafiz kamar saukar aradu ya dira a kunnuwanta. Ko kaɗan bata ji buɗe ƙofar ɗakinsu da yayi ba balle shigarsa cikin ɗakin saboda nisan da tayi a tunani.

Ko kafin ta juya ta bashi amsa har ya fice daga ɗakin da gudu. Doguwar rigarta ta sallah ta yayimo ta zumbula a jikinta. Ta zura hijabi ta fice zuwa falon, ga mai hankali kallo ɗaya za’a yi mata a fahimci rashin nutsuwa a tattare da ita.

“Nauwara? Lafiya kike kuwa?”
Daddy ya tambayeta yana sake ƙura ta da kallo.

Dariyar yaƙe ta lalubo ta makawa fuskarta, sai kuma tayi takwa-takwa da fuskar ta ƙarasa da sassarfa zuwa gare shi ta zauna a ƙasa kusa da ƙafafunsa. Kanta ta ɗora akan cinyarsa, da sanyin murya ta ce
“Gajiya ce kawai Daddy, na gaji, kaina har ciwo yake min. Ba zato ba tsammani kwatsam wani lecturer ya tsiro mana da text ba tare da mun shirya ba. Ƙwaƙwalwarmu ta wajigu shi yasa ka ganni sai a hankali. Barka da zuwa. Ya hanya Daddyna? Ina fatan ka dawo lafiya?”

“Lafiya ƙalau Nauwara. Kar ki damu. Karatu musamman na jami’a ya gaji haka. Ke dai ki cigaba da jajurcewa kina bitar duk darussan da ake muku akai-akai ba tare da jiran lokacin text ko jarabawa ba.”

“To Daddy.”
Ta amsa a ladabce. Tana jin ƙaunar uban har zuciyarta.

“Allah ya muku albarka gaba ɗaya.”

“Amin Daddy.”
Suka haɗa baki gurin amsawa.

Babbar ledar tsarabarsu ta ice cream da kalolin biskit da har ya kusa gida ya tsaya a wani babban shoppin mall ya siyo musu ya damƙa ma Nauwara da cewar ta rarraba musu.

Ƴar ƙaramar jakarsa ta matafiya, wayoyinsa biyu, makullin motarsa ya kwasa ya nufi ciki bayan ya basu uzurin zai je yayi wanka.

“Daddy a shirya maka abinci ko akwai wani abu da kake so a dafa maka?”
Manneerah ta tambaye shi a ladabce.

“A’a Mannee, na gode. Anjima idan na fito tea kawai zan sha.”

“A fito lafiya Daddy.”
Manyan yaran suka haɗa baki gurin faɗin haka.

Har ya kama hannun ƙofarsa zai buɗe, sai kuma ya fasa. Kai tsaye ya nufi ɗakin Ziyadah da tun shigowarsa cikin falon ta tashi da gaggawa kamar ta ga dodo ta wuce cikin ɗakinta.

“Mummyn Nauwara, barka da hutawa.”
Abinda ya fara faɗa kenan a tausashe bayan ya buɗe ƙofar ɗakin ya sa kansa a ciki. Kuma aka yi arashi karaf idanunsa suka faɗa cikin nata.

“Wa’alaikumussalam”
Ta faɗa a wulaƙance. Fuskarta a ɗaure tamau kamar wacce tayi arba da wani babban maƙiyinta.

Ya san baƙa ta yaɓa mishi, saboda shigarshi ba tare da sallama ba. Don haka ya ɗan koma da baya ba tare da ya rufe ƙofar ba yayi sallama cikakkiya, bai jira amsawarta ba ya sake shigowa cikin ɗakin a karo na biyu.

“Ziyaaaa… Kin canza min gaba ɗaya. Saboda Allah da Annabi yanzu har mun kai matsayin da ko sannu da zuwa ba ni da arzikin da za kiyi min…?”

“Mace ta gari tana sannu da zuwa ga mijin da ta san ya tafi nemo musu halas ne. Ga mijin da bashi da aiki sai cin haram, shan haram, sutura da haram ko a gurin Allah bai cancanci wata kulawa ba balle girmamawa…”

Garam! Ya buga mata ƙofa da ƙarfi, ba tare da ya tsaya jin ƙarshen baƙaƙen maganganunta ba.

Da kallo ta bi ƙofar da ya buga mata, sai kuma ta ja dogon tsaki kamar bakinta zai taɓa ƙasa. Ta galla ma ƙofar harara kamar shi ke tsaye a gurin sannan ta juya ta cigaba da sabgogin da suke gabanta.

Bai bari maganganun Ziyada sun tsaya mishi a zuciya ba, nan bakin ƙofarta ya watsar mata da kalamanta sannan ya wuce zuwa ɗakinsa. Bayan ya ajiye duk kayayyakin hannunsa wanka ya shiga, ya daɗe a cikin bayin kafin ya fito bayan ya ɗauro alwala.

Ba tare da kunyar Ubangiji ba ya rama sallolin la’asar, magrib, isha’i da suka kuɓuce masa. Addu’a yayi mai tsawo kan Allah yasa duk abinda zai ji gobe daga bakin mahaifin Firdausi ya zama alkhairi. Kafin ya shafa addu’ar, ya miƙe ya naɗe daddumar ya ajiye a mazauninta.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Lokaci 38Lokaci 40 >>

1 thought on “Lokaci 39”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×