"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'unn!"Su ne kalmomin da Alhaji Yusuf yake ta maimaitawa cikin ƙarfin hali da sakankancewa ga Ubangijin sammai da ƙassai saboda waɗannan manya-manyan abubuwa na tashin hankali da suka afko ma ahalinsu a lokaci ɗaya, ba tare da zato ko tsammani ba.
Duk da sanyin iskar da ke kaɗawa da gudu a cikin ɗakin shi zufa yake yi, lokaci bayan lokaci yake kama gefen babbar rigarshi ya sharce zufan da ke tsattsafo mishi akai-akai kamar ana watsa mishi ruwa.
Uncle Jamilu da ya kasance mai ɗan ƙarfin halin faɗawa. . .
Mun gode da wannan update din.
I like the idea