Skip to content
Part 52 of 67 in the Series Lokaci by Fareeda Abdallah

“Inna lillahi wa inna ilaihi raji’unn!”
Su ne kalmomin da Alhaji Yusuf yake ta maimaitawa cikin ƙarfin hali da sakankancewa ga Ubangijin sammai da ƙassai saboda waɗannan manya-manyan abubuwa na tashin hankali da suka afko ma ahalinsu a lokaci ɗaya, ba tare da zato ko tsammani ba.

Duk da sanyin iskar da ke kaɗawa da gudu a cikin ɗakin shi zufa yake yi, lokaci bayan lokaci yake kama gefen babbar rigarshi ya sharce zufan da ke tsattsafo mishi akai-akai kamar ana watsa mishi ruwa.

Uncle Jamilu da ya kasance mai ɗan ƙarfin halin faɗawa Yaya Yusuf ɗin kalamai na kwantar da hankali shi ma tunda suka ɗauko Mannirah bayan ganin mummunan halin da take ciki bakinsa ya mutu. Kamar an saka salatef an manne bakin, yana tsugune a gefe ɗaya ya haɗa kai da gwuiwa. Zuciyarsa cunkunshe da tunanin azzalumai marasa imanin da suka keta alfarmar Mannira mummunar ketawa irin haka.

Abun babu imani ko ɗigon tausayi a ciki, in banda kasancewar shugaban asibitin Garkuwa Aminin Alhaji Yusuf ɗin ne da farko fau-fau ma’aikatan lafiyan sun ƙi karɓarta, wai sai an sako hukuma cikin case ɗin saboda munin case ɗin.

Izuwa lokacin da ake wannan taƙaddamar, Khamis sau biyar yana suma yana farfaɗowa. Bayan Uncle Jamilu ya ɗakko shi daga gida zuwa asibiti likitoci suka rufu a kansa ko kafin Alhaji Yusuf ya ƙaraso har ya farfaɗo. Babu abinda yake fita a bakinsa sai sambatun cikakken kwatancen da aka bashi na inda zai je ya ɗauko Mannirah.

“Jamilu, tsorona shi ne tana mace ne ko tana raye? Mutanen nan sun cutar da ni….”
Da yazo nan a zancensa sai dai aga hawaye sun ɓalle masa shar-shar kamar an buɗe famfo. Duk yadda yaso Jamilu ya tuƙa mota su bar asibitin zuwa ɗauko Mannirah ƙiyawa yayi har sai da Alhaji Yusuf ya isa asibitin.

Anan kuma aka fara wata fafatawar, duk yadda suka yi da Khamis ya zauna ya cigaba da karɓar kulawar likitoci saboda kallo ɗaya za’a mishi a fahimci ba lafiya ƙalau yake ba ya ƙi.

“Don girman Allah ku barni in je… Ƴata ce fa. Tana da wanda ya fi ni ne? Idan duk ku biyun baza ku je ba ku zauna ko ni kaɗai zan je in ɗauko ta, sun tabbatar min tana gurin, idan ban isa akan kari ba wasu mugayen ne za su sake afka mata.”

Yana wannan sambatun yake tuttuge igiyar ƙarin ruwan da yake hannunsa.

Haka nan dai suka tafi da shi ba don ransu ya so ba. A gurin tafiya ɗauko ta ne Yaya Yusuf ya kawo shawarar ko za su ɗauko ƴansanda su tafi da su, saboda tsoron kar yazo tarko aka ɗana musu.

“Yaya, muryar da ta kira ni bata yi kama da ta masu garkuwa da mutane ba. Tantiran ƴan iska ne kawai suka ɗauke ƴata suka zalunce ni, kuma sun faɗa min sun barta a gurin ne… idan ban ɗauko ta ba wasu gungun ƴan iskan ne za su sake far mata saboda gurin matattarar ɓata gari ne…”

A karo na barkatai ya sake duƙar da kanshi sai hawaye shar-shar-shar…
“Allah ya isa.. Allah ya isa… Mutanennan sun cutar da mu… In Allah ya yarda sai Allah yayi mana sakayya da gaggawa…”

Hankalinshi bai ƙara mahaukacin tashi ba sai da suka isa daidai gurin, daƙyar suka gano ta yashe can bayan wani kwalbati da ruwan kwata ke wucewa. Irin yanayin da suka ganta, mummunan yanayi ne da baki bazai iya bayyanawa ba.

“Yaya… Yaya… kun ga halin da Mannira take ciki ko? Kun ga irin zaluncin da suka yi ma Ustaziyar yarinyata ko? Saboda Allah da Annabi me nayi musu suka yi min irin wannan zaluncin…?”

Numfashin shi ne ya ƙara tsayawa cak! Ya tafi luuu zai kifa da saurin gaske Jamilu da Yaya Yusuf suka riƙo shi, a sume, haka suka kwantar da shi gefe ɗaya.

Yaya Yusuf da yake matsayin muharramin Mannirah shi ya ƙarasa inda take ya mayar mata da ragowar kayan jikinta da suke ajiye kusa da ita.

A dole sai da suka nemo wata motar ta ɗauki Khamis da Jamilu, ita kuma Mannirah suka kwantar da ita a motar da suka je gurin da ita. Yaya Yusuf yana tuƙa motar yana sharce hawaye don tsananin tausayin halin da yarinyar da bata ji ba bata gani ba take ciki.

Bayan ta-ta-ɓurzar da aka sha da likitocin kafin suka karɓi Mannirah daƙyar bayan fitowar shugaban asibitin, kai tsaye Emergency aka wuce da ita domin bata taimakon gaggawa. Shi kuwa Khamis, ɗakin da ya bari nan aka sake kwantar da shi, izuwa wannan lokacin abubuwa yake yi kamar wanda aljannu suka buge don tsananin tashin hankali da firgicin abinda idanuwansa suka gani, sambatu yake yi, surutu yake yi, yana sake tsinuwa da jaddada Allah ya isa ga ƴan iskan da duk faɗin garin kaduna su rasa yarinyar da za su lalata sai tasa, mahaddaciyar Alƙur’ani mai girma. Daga haka sai ya sake fashewa da ƙaƙƙarfan kuka kamar ba namiji ba, sai kuma ɗif! Ya sake sumewa.

A ƙarshe dai dole likita yayi masa ƙaƙƙarfan allurar barci domin a samu ƙwaƙwalwarsa ta huta sosai gudun samun babbar matsalar da ba’a fata.

Yana barcin, babu abinda yake yi sai sauke nauyayan ajiyar zuciya akai-akai, har zuwa sadda barcin ya ɗauke shi sosai, amma duk da haka kallo ɗaya za’a yi masa a gane barcin nan fa na dole yake yi.

A wannan lokacin ne Yaya Yusuf yake tsaye akan Khamis yana sharce gumi, hankalinsa a matuƙar tashe. Tun bayan rasuwar iyayensa ya daɗe bai sake shiga maɗaukakin tashin hankali da firgici irin wannan ba. Duk maganganun da Khamis yai ta janyo musu a baya, ko rantsuwa yayi babu kaffara baya jin ya taɓa shiga tashin hankali rabin wannan balle har ya kai wannan.

Tsayuwar nan da yake yi, yana jiran fitowar likitocin da suka rufu akan Mannira don ceto rayuwarta ne. Amma fiye da awa ɗaya har yanzu babu wani likita da ya fito balle har su samu labarin halin da yarinyar take ciki.

A karo na barkatai ya sake buɗe baki da niyyar tambayar Jamilu game da barin Ziyada gidan Khamis amma ya rasa waƙar farawa. Can dai yayi ƙarfin halin buɗe baki daƙyar, muryarsa a shaƙe kamar wanda mura yayi ma mugun kamu, daga can cikin maƙogwaronsa har wani ɗaci-ɗaci yake mishi ya ce,

“Jamilu, ka ce Ziyada ta fi sati biyu ba ta a gidan Khamis? Kuma duk iya tsawon kwanakinnan hatta yaran ba su da masaniyar inda ta tafi?”

“Ƙwarai da gaske Yaya. Ba ma su Nauwara kaɗai ba, shi kanshi Khamis ɗin bai san takamai-mai inda ta tafi ba. Kuma wani babban abin tashin hankali da ƙarin damuwa shi ne ko a waya ba’a samunta…”

“Assalamu alaikum”
Shigowar Nauwara a firgice da sallamar da ta doka shi ya katse ma Jamilu maganar da yake yi.

A tare duk su biyun suka ɗaga idanu suna kallonta, kamar dai ba wacce ta dawo daga ɗaukar darasi a jami’a ba. Rangaɗaɗau kwalliya ke a fuskarta duk da yadda daga yin arba da mahaifinta da irin halin da yake ciki ta takwarkwashe fuska ta fara matsar hawaye. Hankalinta a tashe ta riƙe hannun Daddy mai lafiyar tana ƙara ƙarfin kukanta, domin ita duk a tsammaninta ko da Uncle Jamilu ya ce Daddy bai da lafiya, ta zaci karayar hannunsa ne ya ƙara tashi.

Shi yasa bata wani ɗaga hankalinta ba tana tura mishi lambar Yaya Yusuf kamar yadda ya buƙata ta kashe wayar gaba ɗaya don ma kar a sake damunta. Ta cigaba da harkokinta hankali kwance har zuwa ƙarfe shida da kwata kafin tayi sallama da masoyinta bayan ya cika mata jaka da kuɗi ta kamo hanyar zuwa asibitin.

“Nauwara?”
Abba Yusuf ya kira sunanta da wani birkitaccen murya da ya saka ta juyawa ɓangarensa a hanzarce.

A ruɗe ta zube a ƙasa tana gaishe shi, domin da farko tsabar iya duniya nunawa tayi daga shi har Uncle Jamilu kamar bata san da wanzuwarsu a cikin ɗakin ba. Hankalinta yana kan mahaifinta tana risgar kuka.

“Daga ina kike by this time around?”
Ya sake jefa mata tambayar yana harhaɗe girar sama da ƙasa yayi murtuk! Kamar bai taɓa dariya ba. Ko gaisuwarta bai samu zarafin amsawa ba. Daman tun dazu duk da hankalinshi a tashe yake jira yake yaga ta inda Nauwarar za ta ɓullo. Domin Jamilu ya faɗa mishi ita Nauwarar aka kira ta tura lambar wayarsa.

‘Amma ka faɗa mata mahaifinta ba shi da lafiya?’

Tambayar da yayi ma Jamilu kenan bayan ya gama faɗa mishi yadda aka yi.

‘Eh! Na faɗa mata. Daga baya ma da na sake kiran wayarta bai shiga ba kafin isowarka na tura mata saƙon kar ta kwana na asibitin da muke da kuma ɗakin da aka kwantar da mu.’
Amsar da Jamilu ya bashi.

Shi yasa a yanzu tana shigowa bayan kallon da ya sauke mata agogo ya kallah, sai yaga ƙarfe bakwai saura minti biyar, a wasu masallatan ma har an tayar da iƙamar sallar magriba.

“Abba daga makaranta nake Wallahi. Text ne muke da su har biyu kuma duk da yamman nan, shi yasa ban dawo da wuri ba. Don Allah kayi haƙuri…”

Ta amsa a tsorace kuma a marairaice tana sake matsar ƙwalla don kawai ya yarda da ita.

A karo na uku sake kallonta yayi. Zuciya mai mugun saƙe-saƙe nan take ta fara mishi wasu miyagun saƙoƙi da yasa ba shiri ya fara a’uziyya a zuciyarshi. Ya rasa dalilin da yasa idan ya kalli Nauwarar da yanayinta ta fi yi mishi kama da wacce ta fito daga gidan biki ba wacce ta fito daga Jami’a kuma ƙaramar jarabawar da sukai ta caja mata ƙwaƙwalwa ba.

Ƙwafa yayi, irin ƙwafan nan mai ƙarfi. Ya buɗe baki zai yi magana wata ma’aikaciyar jinya ta buɗe ƙofar ɗakin ta shigo, bakinta ɗauke da siririyar sallama. Idanunta akan Yaya Yusuf ta sanar da shi saƙon likita na son ganinshi a Ofis ɗin sa.

Da saurin gaske ya fice, Uncle Jamilu ya mara mishi baya a gaggauce.

Baki buɗe Nauwara ta bi bayansu da kallo, zuciyarta cike da tunanika mabanbanta. Sai kuma ta mayar da hankalinta kan Daddynta, ta ƙure shi da kallo tana karantar yadda ya wani rame ya zabge a lokaci ɗaya. Ko yau da safe kafin ta tafi makaranta sai da ta leƙa asibitin a gurguje ta duba lafiyarsa, jikinsa yayi sauƙi sosai. Har ma ya tabbacin a ranar za’a sallame shi…

“Mannirah…”

Ta kira sunan ƙanwar nata a fili tana zazzaro idanu.

Sai a lokacin tunanin ƙanwar nata da yadda Daddy yai ta kiranta akai-akai yana tambayarta Mannira ya faɗo mata arai.
“Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Allah dai yasa ba wani abu ne ya samu Mannira ba.”

Tayi maganganun a fili. Sai kuma cikin sauri ta zaro wayarta a cikin jaka ta danna kiran lambar Mannirah.

Wani abun ban mamaki da ɗaure kai a gare ta shi ne nan gefen gadon da Daddy ke kwance, inda Abba Yusuf ke tsaye ta ji ringing ɗin wayar, da saurin gaske tasa hannu ta ɗauko wayar tana ƙare mata kallo.

Da mamaki sosai take ƙare ma fuskar wayar kallo. Gilashin fuskarta wayar tayi ratsa-ratsa, kamar dai wayar ta yi mugun faɗuwa akan tiles ko kuma an yi ma wayar mugun taku cikin rashin sani.

Zuciyarta ne ta sake cika ta tumbatsa da tunanika mabanbanta.

“To ina Mannirah?”

Ta sake tambayar kanta a fili.

Ko kafin ta sake yunƙurin aikata wani abu ko cewa wani abu Abba Yusuf da Uncle Jamilu sun buɗe ƙofar ɗakin sun shigo. Matsanancin tsoro ne ya lulluɓeta da ganin yanayin idanun su biyun. Sun kaɗa sunyi jajur, kamar ma sunyi kuka bayan fitarsu.

“Abba? Me yake faruwa ne don Allah? Ina Mannirah?”

Ta jera musu tambayar tashin hankali na gasken- gaske na bayyana aka fuskarta. Idanunta ciccike da hawaye.

Kamar bazai amsa mata ba, ɗaƙiƙu arba’in ya ɓata yana kallon Khamis, sai kuma ya kawar da fuskarshi da sauri yana kallon gefe ɗaya ya ce,

“Ki harhaɗa tarkacenki, ga direba nan zai zo ya ɗauke ki. Ku je can gidanku ki haɗo min kayan Daddynku da na Mannira, ita ma tana Emergency ba ta da lafiya. Sannan ki haɗa duk wasu kayayyaki naki da za ki buƙata za ki koma can gida na da zama…”

Bugawar da ƙirjinta yayi yasa da sauri ta ɗaga idanu tana kallonshi. Sai kuma ta saukar da idanunta ƙasa da sauri, domin ta san Abban no nonsense ne. Ba su da suke ƴaƴan Khamis ba, ko Khamis ɗin ne idan Abba ya yanke hukunci ko zai mutu sai ya bi abinda Abban ya ce.

Da alamun tun kafin shigowarsa cikin ɗakin ya kira direban, domin ba’a ƙara mintuna goma cikakku ba Direban ya iso. Ɗauke da Hajiya Zainab da Ƙanwarta Aunty Ikilima, wacce a mafiyawancin lokuta take zaune a gidan Yusuf ɗin saboda karatun da take yi a KadPoly.

Matashiyar mace ce mai shekaru talatin da takwas, mijinta mutuwa yayi ya barta da ƴaƴa biyu. Bayan mutuwarsa ta yi aure har sau biyu amma ba’a dace ba, daga ƙarshe dai ta tattara auren ta ajiye gefe ɗaya ta koma makaranta.

Ita Alhaji Yusuf ya buƙaci a taho da ita tayi jinyar Mannirah, saboda a lokacin ita tana hutu. Shi kuma da kanshi zaiyi jinyar Khamis.

Ba tare da ɓata lokaci ba Nauwara ta bi bayan direban zuwa gida, harhaɗa kayayyakinsu tayi kamar yadda Abba ya umarceta sannan ta sake shiga motar suka koma asibiti. Daga can kuma basu sake ɓata lokaci ba direba ya kwashe su zuwa gidan Abba Yusuf, hankalinta tashe da rashin ganin Mannirah. Har sai da ta daure ta tambayi Abba, ko za ta iya ganin Mannirah?

“Har yanzu likita bai bayar da umarnin za’a iya ganinta ba.”

Wannan amsar da ya bata, shi ya ƙara girmama tashin hankalin da zuciyarta ke ciki.

*****

A karo na barkatai ta shiga cikin ɗakin, bakinta ɗauke da siririyar sallama. Sai dai wani abun ban mamaki da yasa ta ɗan tsaya tayi jim a tsaye guri ɗaya bakinta buɗe shi ne ganin har lokacin yadda ta fita ta barta a ɗazu yanzu ma haka take.

Kuma idanunta a buɗe, ta ƙura ma guri ɗaya idanu kamar dai yadda take a ɗazu. Kayan abinci abin sha da komai da aka jera mata suna nan yadda suke ajiye. Ko taɓawa bata yi ba.

“A’a Auta ba lafiya… bari in ɗauko makullin mota mu tafi asibiti. A yanzu kam idan za ki rantse sau dubu bazan yarda lafiyarki ƙalau ba.”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Lokaci 51Lokaci 53 >>

2 thoughts on “Lokaci 52”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×