Tsaye take abakin ƙofa sai cika take tana batsewa tana jijjiga ƙafa wani matashi ne wanda bazai haura shekara 30 zuwa da 34 ba naga ya buɗe ƙofar da take tsaye.
Da sauri ta gyara tsayuwarta da ƙara make hanya.
Kallon uku saura kwata naga yayi mata, kafin ya ce; “Ruƙayya bani hanya.”
“Idan an ƙi fa?” ta bashi amsa tana mai hararsa, murmushin takaici yayi kafin ya ce; “wallahi ranki ne zai ɓaci gara ki bani hanya na wuce tun muna shaidar juna.”
Cikin masifa ta ce; “kayi duk abunda za kayi amma wallah kaji na rantse yau ba inda zaka fita.
Ai ba mai gadi aka kawoma ba da duk safiya zakaci uban ado ka kama hanya kabar gida sai kowane namijin kirki ya dawo gidansa yana hutawa da iyalansa kai kuma kana can kana sharhulewar ka.
Ga ƴar tsarun gida, tab ai wallahi bazata sab’uba wai bindiga aruwa, ihim!”
Hannu yasa ya tureta ta faɗi gefe kamar kayan wanki ya bar gurin da sassarfa ko kafin ta gama jimamin fad’uwar harya tada mota yabar gidan.
Ihu tasa “wallahi zaka zo ka same ni ne sai kasan kayi da ƴar halak!”
Shikuwa yana fita gidan iyayensa ya nufa zaune ya tarar da hajiya cikin baranda tana saurarin redio, zame takalminsa yayi kafin ya zauna kan dardumar da hajiya take zaune.
“Hajiya ina kwana?”
“Lafiya ƙalau Habibu ya iyalin naka?”
“Lafiya ƙalau tace agaishe ki Baba fa>”
“Au bakuyi waya ba ai ya tafi Funtuwa wajan ɗauren aure munyi zai kiraka.”
“Ayya Allah ya tsare hanya zaiyu matsalar network ne amma zan kira shi.”
Key d’in motarsa yasa yana d’an sosa bayan kunninsa kafin ya ce; “Hajiya da abinci wallahi yunwa nakeji.”
Hajiya ta taɓe baki kafin ta fara faɗa “oh ni wannan aure naka Habibu ban ga amfaninsa ba ko yaushe cikin zuwa cin abinci gida kake. To wai nikam ita matar taka aikin me take da ba zata girka ma ba?”
Langwaɓa kai yayi cikin sanyi yace “Allah Hajiya yunwa nakeji ataimaka mun.”
“Mts! wannan aure naka kam badan yana sunna ba da nace Allah waddansa ke Mairo haɗawa Habibu abinci.”
“To Hajiya” Mairo mai aiki ta amsa mata daga kitchen wainar ƙwai da dankalin turawa da aka dafa da naman rago ta kawo masa “ranka ya daɗe nan za akawo ko falo?”
“Aa ajiye mun anan nagode.”
Bayan ta ajiye taje ta ɗauko ruwan zafi da kayan shayi ta ajiye masa.
Yana kammala karin kumallo yayiwa Hajiya sallama bayan ya ajiye mata kuɗi yabar gidan tana ta sa masa albarka. Daga wajan Hajiya wajan aikinsa ya nufa.
Ta share gidan yayi tsab ko ina sai k’amshi yake kichen taje ta haɗa girki tuwon samu da miyar ɗanyar kuɓewa tasha busasshin kifi bayan ta kammala girkin ta sake gyara kitchen sannan ta je tayi wanka ta shirya cikin dugowar riga ta atamfa, dai-dai lokacin da take shirin akayi kiran isha dama tayi alwala hijab tasa ta fuskanci gabas dan sauke farali.
Har ƙarfe sha biyun dare tana zaune falo tana kallo kamar yanda ta saba duk dare tana zaman jiran dawowar mijinta Fahad takan kunna kallo idan ta gaji ta d’auro alwala tayi nafila da karatun ƙur’ani mai girma tanawa mijinta addu’an shiriya.
Haka yauma tayi tana cikin karatun ƙur’ani bacci yayi awun gaba da ita can cikin bacci ta dinga jin kamar ana bugun ƙofa bugu bana hankali ba. Firgice ta miƙi tsaye tana duban agogon da ke maƙale a kusurwar falon 2:30am.
Wasu hawaye masu zafi ne suka zubo a fuskarta yanzu namijin kirki ne zai kai wannan lokacin awaje?
“Ya Ilahi ka kawo man ɗauki” nufar ƙofar tayi zuciyarta na lugudi sai da tayi bisimillah sannan ta buɗe k’ofa, aikuwa kamar yanda ta zata haka ya shigo a buge. Yana shigowa tayi saurin yin baya dan tasan bazai masa wahala ba yace zai kai mata duka.
Aikuwa batayi auni ba taji ya haureta da ƙafa tayi taga-taga zata faɗi Allah ya taimaketa ta dafa kujera sai bata kai ƙasa ba, mari ya kai mata yana zaginta cikin muryar ƴan maye.
“Ke dan ubanki ni sa’anki ne da zan sa doka ki take? Ban ce karki sake rufe mun gida ba iye?
Shine dan kin raina uwarki kika rufe kika barni inata bugun gida? Ko da kuɗin ubanki na gina gidan iye dan uwarki mai ɗan wake?”
Girgiza kai ta dingayi tana yin baya-baya tare da ƙoƙarin haɗiye kukan da yazo mata.
Faɗawa yayi kan kujera da ƙarfi yana magagin ƴan maye.
Haka ta wuce ta ɗauko abinci da ruwa ta haɗa kan babban faranti, cikin tsoro ta kawo gabansa ta ajiye “ga abinci kana buƙatar wani abun?”
Ta yi maganar cikin sanyi daga ita har abincin ya hanɓarar tare da zaro bel d’in wandonsa ya dinga zuga mata yana faɗin “dan ubanki mai kwaɗayi ance maki ni ɗan yunwa ne ko irin ubanki kamun yunwa ne ni!”
Ihu ta dinga yi tana bashi haƙuri ga zafin duka ga raɗaɗin zagin iyayenta da take ji, amma yaƙi ya barta, kola yayi tuntuɓi da ita abunka da ya bugu ba ƙaarfi sai ya zame ya faɗi agurin sai amai daganan bacci mai nauyi yayi awan gaba da shi.
Fatima haka ta tashi tana share hawayen da ke zarya afuskarta ta tsabtace wajan tare da zame masa takalmin ƙafansa, sanin bazata iya janye shi wajan ba yasa ta gyara masa kwanciya ta koma gefensa ta takure tare da yin tagumi, ahaka bacci yayi awun gaba da ita.
Ruƙayya tun fitar Habib komai ba tayi ba sai kallo da chatin sallah kuwa sai da lokacinta ya fita sannan ta tashi ta haɗa azahar da la’asar, alokacin ne taji cikinta ya fara kukan yunwa sannanfa ta tashi ta dafa indome taci ta dasa aikin nata wato kallo.
Habib kuwa sai shidda ya tashi gurin aikinsa yana ƙarasowa unguwarsu yaji anfara kiran sallah magarib hakan yasa yayi parking bakin masallacin unguwar alwala yayi tare da shiga masallaci yabi jam’i. Bayan an idar da sallah ya zauna yabi jam’in wazifa sai da akayi sallah isha sannan ya fito masallaci ya shiga motarsa da niyar ya wuce gida.
Ya ji wata irin yunwa ta taso masa har zai wuce gidan hajiyarsa ya fasa dan yasan sai yasha gori kafin tabashi abincin yasan ko yaje gidansa in banda masifar Ruƙayya ba abunda zai tarar hakan yasa ya juya motarsa yabar unguwar.
Gasasshen naman rago ya saya da yoghurt mai sanyi sai da ya biya wajan su hajiya ya kai masu nasu ya ɗan taɓa hira sannan yabar gidan suna ta sa masa albarka.
Goma dai dai ya shiga gidansa bayan ya rufe motarsa ya kulle get sannan ya ƙarasa ciki hannunsa riƙi da ledojin da yayi sayayya yana sa ƙafansa falo yaji ransa ya ɓaci ko ina kaca-kaca yanda ya barshi haka ya dawo ya tarar dashi.
Can ya hango Ruƙayya kwance kan doguwar kujera tun kayan da yabarta dasu da safe sune ajikinta da alama ko wanka batayi ba.
Mts! tsaki ya shige ɗakinsa cikin da takaicin halin matarsa, motsin rufe ƙofar ne ya tasheta daga bacci da sauri ta miƙe zaune tana murzar ido kafin daga bisani ta tashi tabi bayansa Riga ta tarar yana cirewa bayan ya cire rigar ya ce; “malama lafiya zaki shigo man ɗaki ba sallama?”
Cikin masifa ta ce; “ita takawo haka yunwa nakeji me kasayo?”
“Abunda kika aike ni” daga haka bai sake cewa da ita komaiba ya janyo ledar ya bud’e ya fara cin naman yana kurba yogurt.
“Kan ubanan! wai me kake nufi zaka sayo abu ka hanani saboda rashin adalci irin naka kabarni da yunwa kasayo daɗi kana ci, wa ya san iya abunda kaci kafin kadawo gida.”
“Ya Salam! wai Ruƙayya miye matsalarki ne rashin adalcin na miye na maki miye ban saya na ajiye maki ba? Ke kika so ki zauna da yunwa, akwai ba babu ba baƙin halinki ne dai ya hanaki ki girka. Wannan kuma ga naki nan aleda ki ɗauka ban iya tauye haƙƙi ba, dan haka dan Allah ki shafa mun lafiya kibar ɗakinan” ya faɗa yana mai nuna mata wajan da ya ajiye.
Figar ledar tayi ta wuce tana faɗn “oho dai dole abani tunda nagani wanda kuma akaci awaje Allah ya isa ban yafe ba.”
Kaɗa kansa kawai yayi ba tare da yace da ita komaiba yana kamallawa yayi brush tare da watsa ruwa ya ɗauro alwala.
Bayan ya fito ya shirya cikin kayan bacci kwanciya yayi kan gado yana juyayi buƙatar matarsa yake sai dai yasan idan zaiyi me ba bashi haƙƙinsa zatayi ba sai randa tata buƙatar ta kuɗi ta tashi zata neme shi, tsaki ya sake yi karu na ba adadi, ganin ba zai iya jurewa ba kamar yanda yake abaya yasa ya miƙe tsaye. Ɗakinta ya nufa ransa ne ya sosu ganin ɗakin nata duk ƙazanta haka ya jure ya ƙarasa ciki. Har yanzu dai tufafin da ya barta da su ne ajikinta gaskiya ba dan yana hannu ba da bazai iya kusantar ta ahakan ba.
Ruƙayya da take barccinta mai daɗi taji ana taɓata zaburi tayi ta miƙe zaune ganinsa kusa da ita yasa ta fara masifa, “malam wani iskanci ne wannan ina baccina zaka zo ka tashe ni da salon maitarka!”
Duk da maganar ta ɓata masa rai bai nuna mata ba tunda buƙata gare shi.
Murmushi yayi kafin ya ce; “neman haƙƙin nawa ne iskanci Ruƙayya? To koma dai miye ina buƙatar haƙƙina.”
“Tab ashe kuwa zaka bushe ni dan Allah ka ƙyaleni bacci nakeji.”
Cikin lallashi ya ce; “haba Ruƙ’ayya me yasa dan Allah kike man haka? Wallahi idan wani yaji zai ɗauka ba auren soyayya mukayi ba. Ki tuna Habib ɗinki ne fa ki tallafi masoyinki ki kawar masa da ƙishin ruwa.”
Yamutsa fuska tayi kafin ta ce: “Na ji nawa zaka biya.”
“Yanzu Ruk’ayya haƙƙ’in nawa da sadakina da komai za kice sai na biya?”
Juya masa baya tayi tana murguɗa baki ta ce; “oho kai kasan wannan sannan baka tashi ba ni mts!”
“Ki jiƙ’a kisha bana so kuma wallahi zan baki mamaki Ruƙayya”! Yabar ɗakin afusaci, ita kuwa ko ajikinta saima gyara kwanciyarta da tayi.
Inajin dadin kasancewar d wannan littafin sbd inasamun karuwa