Skip to content
Part 3 of 10 in the Series Ma'aurata by Aisha Abdullahi Yabo

Muhusin ya shigo office ɗin Habib hannunsa riƙe da wasu takardu kallon mamaki yake bin Habib da shi.

Habib ya ɗago yana kallonsa kafin ya ce; “lafiya malam kashigo kayi man tsaye aka kana kallona kamar naci bashinka zan gudu?”

kujera Muhusin yaja ya zauna kafin daga bisani ya ce; “ba dole ba magidanci dakai kabar gidanka kazo waje kana cin abinci.”

“Mts! bata jin daɗi ne shiyasa” ya bashi amsa a taƙaice,

“Ah mutumin ko kagama aiki ne?”

Yayi maganar cikin tsokana “kana da matsala daga nace bata da lafiya sai ka kai zancen nawa wani gun.”

“Yo ba alkhairi bane?”  “to abunda kake zato ba shi bane yanzu dai mai yake tafe da kai?”

Ya sako wata maganar dan kaucewa maganar Muhusin miƙa masa takardun yayi tare da yimasa bayani sun ɗan taɓa fira kafin yabar office ɗin ya koma nasa.

Yau da wuri ya bar office hadari ya haɗu ya game sararin samaniya alamu sun nuna ko yaushe ruwan sama zasu iya saukowa.

Ya wuce wajan aikin nasa kaɗan aka sako ruwa kamar da bakin ƙwarya.

Wata dattijuwa ya gani tsaye agefen hanya ruwa na dukanta sosai ta bashi tausayi har ya wuce ta yaji bazai iya barinta ba ya dawo baya dai-dai gurin da take tsaye yayi paking fitowa motar yayi ya ƙarasa wajanta cikin ladabi ya ce,

“Sannu Iya meyasa zaki fito cikin ruwannan?”

“Yawwa sannu yaro wallahi jikanyata ce ta fito ganin hadari ya haɗu bata dawo ba ya sa na fito duba ta har yanzu ban ganta ba.”

“Haba Iya kya tsaya ruwa na dukanki wata ƙiilama ta koma gidan baki sani ba yanzu ina ne gidan naku?”

“Wancan tsallaken” ta nuna masa tsallaken titi kai dubansa yayi inda take nuna masa ganin mota na shiga ya ce,

“Muje mota sai naraka ki gida.”

“Anya yaro ayi haka.”

“Iya bazan cuta maki ba bai kamata ruwannan na dukanki ba karkiyi mura.”

Hakanan taji ta natsu da shi dan haka bata sake cewa komai ba tashiga mota da kwatancinta har suka ƙarasa ƙofar gidan.

Fitowa yayi ya buɗe mata ƙofan motar ta fito suka ƙarasa ƙofar gida buga  k’ofar yayi ba ajima ba wani magidanci ya fito yana buɗe ƙofan yaganta ajiyar zuciya Baban yayi yana kallonta,  ya ce: Babaa yanzu sabida Allah sai da kika fita bayan na hanaki to ai ga ƴar gwal ɗin taki chan ta dawo.”

Murmushin jin daɗi tayi kafin daga bisani ta ce; “kai ni dan Allah bani hanya na wuce ka tare ni da shegen ƙara da baya ƙarewa.”

Ta yi maganar cikin faɗa girgiza kansa kawai yayi tare da matsawa gefe sai da tashiga soron gidan ta jiyo tana kallon Habib “sannu yaron kirki na gode Allah yayi maka albarka amma dai watarana zaka zo mu gaisa ko?”

Murmushi yayi kafin ya ce; “Amin Iya Insha Allahu zan zo.”

“Yawwa ɗan kirki sai naganka” daganan ta yi shigewarta.

“Sannu shigo daga ciki” “Aa Baba nagode zan wuce ne amma Baba adaina barin tana fita cikin ruwa saboda lafiyarta.”

“In sha Allahu yaro ko yau ma sai da na hanata ganin na shige ɗaki ne yasa ta fita ban sani ba nagode sosai ya sunanka?”

“Habibu” ya bashi amsa tare da ciro dubu biyu yace “gashi akaiwa Iya tasai goro.”

“A a ina sam kawota da kayi ya isa mun gode.”

“Dan girman Allah Baba ka karɓar mata shaiɗan ne kawai ke mayar da hannun kyauta baya.”

Ba yanda ya Iya karɓa yayi yana tasa masa albarka.

Yana zuwa gida ya faɗa toilet yacire jiƙaƙun kayansa ya watsa ruwa masu ɗumi bayan ya fito ya shafi jikinsa da mai dan kuwa sanyi yake ji sosai ganin lokacin sallah magarib  yayi kuma an tsagaita da ruwa yasa ya wuce masallaci.

Tana sharar tsakar gida ta ji sallamar Ummin Fahad da sauri ta yar da tsintsiyar tare da amsa mata sallamar cikin fara’a ta ce, “sannu da zuwa Ummy.”

“Yawwa Fatima,aiki ake?”

“Eh Ummy” ta bata amsa suna ƙarasawa falo, Fatima taje ta kawo ma Ummy ruwa da abinci sannan ta sake gaishe ta.

Ta amsa cikin fara’a tana faɗin, “Sannu da ƙoƙari Fatima daga zuwa sai kawo abinci.”

Murmushi tayi batare da tace komai ba zoɓon kawai Ummy tasha kafin ta kalli Fatima da kyau ta ce,

“Fatima, kinyi ciwo ne?” “Aa Ummy.”

“Ki na da damuwa ne ko Fahad na ƙuntata maki ne?”

Nan ɗinma kaɗa kanta tayi alamar A a.

“Wannan ramar taki tayi yawa Fatima ki faɗa mun gaskiyar matsalarki kinga ke amana ce a garemu nasan halin Fahad shiryayyen yaro ne komai zai iya yi.”

Cikin murmushi ta ce, “Allah Ummy karki damu ba komai lafiya ƙalau muke zaune.”

“To shikenan Allah yasa hakan.” Ummy ta dai amsa ne kawai ba dan ta gamsu ba.

“Dama Babanku ne yace nazo na duba masa amanarsa tunda kuna lafiya shikenan dama haka muke son ji. Ki dai ta haƙuri dama shi zaman aure duk inda ki ka ga yayi ƙarko to masu yin sun sa haƙuri agaba, aure kuma ibada ne daɗinsa ƙalilanne kiƙara haƙuri kinji?”

Cike da ladabi ta amsa da “to Ummy nagode sosai.”

“Ba komai ga wannan Babanku yace na kawo maki yana gaishe ki kafin ya shigo.”

“Ina amsawa nagode sosai.”

Ta bata leda guda biyu “wannan nawa ne wannan kuma mamanki ta bada saƙo jiya da Abbanku ya je ta ce a kawo maki, daga ita har Abbanki, Zainab duk sunce agaishe ki.”

Da farin ciki ta karɓa tana ta godeya Ummy bata wani jima ba tayiwa Fatima sallama Fatima ta ɗauko sabolon wanka da turare na cikin lefenta tabawa Ummy.

Ummy na tafiya ta duba ledar da Mamanta ta aiko mata kuɓewa ce sai kuka da daddawa Baba kuwa dubu ukku ne sai kayan kwalliya da Ummy ta haɗo mata, zuwa tayi ta adana kayan sannan ta fito ta cigaba da aikinta.

Ranar awaje Fahad ya kwana sai ƙarfe tara na safe ya dawo lokacin Fatima na ƙuryar gida tana wankin tufafinta, sam bata ji dawowarsa ba shikuwa tun shigowarsa yake ta kiranta jin bata fito ba yasa shi shiga ɗakinta har ban ɗaki bai ganta ba, tunaninsa ya bashi bari ya duba ƙuryar gida ai kuwa yana zuwa ya hangota tana shanya, da saurinsa ya ƙarasa wajan. Ta sunkuya ta ɗauko zane ta shanya taji saukar dundu abayanta ihu tayi tare da miƙewa tsaye ganin shi tsaye fuskarsa ba annuri yasa ta matsa baya a tsorace tana susan bayanta dan kuwa taji dukan.

“Ke uban me kika faɗawa Ummy da har suka kirani suna mun faɗa?”

Cikin rawar murya ta ce; “wallahi ni ban faɗa mata komai ba kuma ka tambayeta kaji.”

“Ƙarya kike munafuka jikinki zai faɗa maki ne” belt ɗinsa ya ciro ya dinga dukanta yana ball da ita sai da yayi mata liƙis sannan ya ƙyaleta.

“Gobe ma kikai ƙarata gun iyayena kakkarya ki zanyi a banza!”

Ya bar wajan yana ta masifa kuka takeyi gwanin tausayi tajima awajan kafin ta tashi cikin ƙarfin hali ta ƙarasa shanya kayanta.

Da dare tana kwance ta lulluɓe da bargo zazzaɓi take ji tun bayan dukanta da yayi sai kakkawar sanyi take, da ƙarfi taji an bankaɗo ƙofa ya shigo ɗakin yana tangaɗi jin shigowarsa ne yasa ta tashi daga  kwanceyar da take ta maƙure gefen gado.

Cikin muryar marar lafiya ta ce; “dan Allah dan soyayyarka da Annabi S.A.W kayi haƙuri kamun rai wallahi tallahi ba abun da na faɗamata.”

Ta ƙarasa maganar cikin kuka hannunsa yasa bakinshi sheeee!! faɗawa kan gadon yayi tare da janyota jikinsa ya rungumeta yana magana cikin maye “ke dan uwarki zaki mun shiru ko sai na mammake ki?”

Da sauri ta haɗiye kukan tare da sa hannu ta rufe bakinta.

Nikam ganin abunda yake shirinyi yasa ni saurin barin ɗakin tare da rufe masu ƙofa.

Yau Asabar ba aiki hakan yasa tun da ya dawo masallaci sallar asuba bai kwanta ba, zagewa yayi ya gyara gidan tsaf ko ina yayi tsaf Habib kenan akwai son tsabta mata mai tsabta dai Allah bai bashi ba.

Yana kitchen yana soya dankali da ƙwai Ruƙayya ta shigo cikin kayan bacci da alama yanzu ta tashi baccin.

Miƙa tayi tare da doguwar hamma “Woww Habib me kake dafa mana naji gidan ya ɗau ƙamshi?”

Wani kallo ya watsa mata kafin ya juya ya cigaba da aikinsa.

A ranta ta ce, “Kaji dashi masifaffe duk abunka sai naci girkinnan.”

Kujera ta janyo ta zauna tana faɗin, “Habib nace na  kwana biyu banje gun hajiyarka ba yau inaso naje na gaisheta.”

“Ko?” yayi maganar cikin ko oho dai dai lokacin ya ƙarasa suyan ya kashe gas ɗin sannan ya ɗauki abincinsa yabar kitchen, tashi tayi tabi bayansa.

Ku saurari babi na hudu in shaa Allah.

Ta ku Aisha A. Yabo (Fulani)

<< Ma’aurata 2Ma’aurata 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.