Skip to content

Mace Mutum 1

Part 1 of 4 in the Series Mace Mutum by Haidar Ali Maganda

Da sunan Allah mai rahama mai jin k’ai.

Gargadi

Ban yarda wani ko wata ya juya min labari ba tare da izini ba yin hakan kuskure ne, A kiyaye.

Wannan labarin k’irk’iraren labari ne duk abin da kuka gani ko kukaci karo da shi a cikin labarin anyi shine kawai don nishadi wa’azi ga al’umma.

Zamuyi wata tafiya tare da ku a wannan labari bansani ba ko zai yi dai-dai da yadda_ _kuke so, kawai abu guda nasani ba zaku yi danasanin tafiyar nan ba. Ku shirya sosai sannan ku tanadi abin goge hawaye.

Don wasu hawayen zuwa suka babu shiri._

Babi na daya

Litinin
7  march 2005
Zaria

Kamar kowanne lokaci,  abinda take gudu daya ne kuma tana tsoron faruwar shi a yau bata shirya ma hakan ba, Duk da tasan ko wane sati na duniya sai hakan ya faru. Bata kammala karatun kurman da take ba ya fado dakin kaman an jeshi , kallon fuskar shi kawai tayi ta fita daga duk wani sukuni da yai mata saura bugun zuciyar ta na nun kuwa fiye da tunani.

“Baki kammala ba har yanzu? Bansan sai yaushe zaki soma yin abu kamar mutum ba. Kullum tunanin ki da lissafin ki yana karanci maimakon yayi gaba.”

Bata furta komai ba don tasan idan tayi magana yanzun nan cibi zai zama kari, ga dukkan alamu ranshi abace yake ko wacce irin kalma zatai amfani dashi wajen lallashi bazai taba amfani ba sai dai ya kara dagula komai .

“Saboda kin maidani dan iska ina magana kin yi banza dani, wai kike takama da shine.”

Yanzun ma batai magan shurun tayi, daki ta shiga ta dauko ma amira hijabi dan suyi sauri su tafi, sai da ta tabbatar ta kamalla da yaran sun tafi tukun na ta ce da shi.

“Kayi hakuri wallahi sauri nake naga na kammala shirya yaran nan sun tafi makaranta don kar su makara.”

Sosai yake kallon ta yanajin wani irin tiriri a cikin ranshi kafin ya ce

“Hidimar yaran ki tafi tawa kenan? Sai yaushe zaki fahimci zaman kike.”

A iya nazarin ta har hanzu ta kasa hango laifin da tai masa ba, shin so yake ya tynatar da da ita tayi kuskure da ta amince da batun auren shi ko kuma so yake ya tunatar da ita mahaifin ta yayi kuskure da ya bata umarni kuma tabi. Kullum sakon batin shi guda daya ne sai dai salon ne yakan bambam ta da na kowa ne lokaci .

Maganar shi ce ta katsa ta daga tafiyar tunanin wucin gadin da tayi.

“Bama wannan ba , Habiba ina na fada miki kar ki sake tura yarannan makaranta mai yasa kike da kunnen kashi ne.”

“Kayi hakuri karatun shine abu mafi girma da daraja da yakamata muba su, saboda amanar Allah ce a garemu.”

Ta kare batun cikin sanyin murya

“Karatun shine har da “ya mace.”

“Kayi hakuri shi karatu bashi da bambanci tsakanin jinsin mace ko namiji, duk ya halasta mu nema. Ba kuskure bane don mun ba iyalin mu ilimin zamani hakan abu ne mai kyau, ko ba komai mu bamu da ilimin yakamata ace su “ya “yan mu sun samu ko ya yale. Amma kayi hakuri idan na fada maka abin da bai maka dadi ba”.

Tayi amfani da kalmar hakuri me a farkon maganar da karshe don tasan halin shi yanzu zai ce ta mai rashin kunya.

” to naji nidai bana so , su mazan da ya zama dole sai sun yi ilimin zasu yi zan dauki faruk da abba zan kaisu can kano wajen da ni nayi karatu dan shoma yayi, wannan karatun na banza ai sai yaron ka ya lalace, suma matan dan babu yadda zanyi ne”.

“Kayi hakuri ai suna zuwa islamiyya dukan su, ba sai ka kai su wani waje ba “.

” nifa kwata-kwata karatun bokon ne bana so saboda a can tarbiyar yara ke lalacewa”.

“Allah ya kyauta.”

Shine kawai abin da ta iya fadi don in ta biye mai anan zasu kwana suna batu guda.

“Amm babu wani abu ne anan dazan karya.”

“Babu suma yaran ruwan koko kawai suka sha kasan jiya ma dari kawai kaban tun safe har dare.”

Nan da nan ya turbune fuska  cikin sauri ya soma fadin.

“Naji! naji dan Allah , wai ke ko irin dabarun nan iri na mata baki iya ba ko irin sana’ar hannu haka? Dan zama ba zai yiwu miki ba.”

“Hakane nima ina son in fara sai dai umguwar nan sai a hankali.”

*****

Zaune take  a cikin dakin ta , lissafin rayuwa take da kuma yadda kaddarar ta take da wani irin salo mai ban al’ajabi, tasan auren hadi ne akai musu amma ya nuna mata so har tanajin tafi kowa sa’a a duniya, sai dai a satikan da basu wace biyar ba zuwa shida ciki ya bayyana a jikin ta sun so wannan ciki kamar me , tun balle mahaifin shi da ya dauki burin duniya ya daura akan cikin dan bashi da burin da ya wuce autan nashi ya samu da namiji , sai dai an samu akasi  ranar da ta haihu ta haifi diya mace ba haka Magaji ya soba amma bai ce komai ba fuskar shi kadaran kadahan yaje ya fada wa mahaifin shi na take wani irin tari ne ya sarke shi wanda yazama sanadin komawar shi ga Allah bayan yayi jinya na kwana uku, tun daga wannan lokaci iyalan gidan suka juya mata baya babu inda zata saka kanta taji dadi. Sati ya zagayo yarin taci sunan mahaifiyar magaji mairo amma ana mata alkunya da amira duk wani gata da mai jego ke samu babu wanda ta samu , cikin shekara guda da rabi ta sake samum wani cikin ta wanda shima tinanin magaji da burin shi duk namijin ne,  amma sai aka samu mace, Magaji gani yake da gangan Habiba take haihuwar mai mata tun daga nan ya kara canzawa. Baya sati guda yarinya taci sunan mahaifiyar Habiba wato aisha suna kiranta Nana. Bayan ta haifi Nana ta sake haihuwa,  na farko samaila mahaifin magaji suna kiran shi Abbati sai me sunan baban ta Umar suna kiran shi Sadauki wani lokacin kuma Faruk. Wanda yanzu haka Amira nada shekara tara Nana kuma takwas sai Abbati mai shida sai sadauki mai biyar.

Dawowar yaran daga makaranta shi ya katse mta dogon tunani da takeyi, ruwan kokon da ya rage ta basu suka sha , wasa suke kamar ba abin dake damun su tana daga zaune tana kallon yaran wani irin nishadi na mamaye ranta tana yi musu fatan dorewa a haka cikin son junan su da kauna.

Har yanzu ta kasa gane meye laifin a cikin lamarin auren,  shin laifin ta ne dan ta haifi “ya ” ya mata ko kuma dan ta aure shi akan yin biyayya ko kuma kaddarar da ta jeho “yan ta’adda kauyen su dake maiduguri suka kashe mata uwa da “yan uwa daga ita sai dan uwanta sai kuma mahaifin ta suka gudu zuwa zaria wajen abokin mahaifin ta wato mahafin magaji ko kuma nutsuwa da hankalin ta da mahaifin magaji ya gani ya nemi hada su ko kuma kaddarar da ta dauke mahaifin ta bayan ya sha jinya sati guda da auren su .har yau da take zaune tana wannan lissafin bata san ya zatai da rayuwar ta ba.

Wannan kenan

*****

Ihun yaran ne ya sanya ta fito daga uwar dakin ta jin suna fadi kawu, cikin farin ciki take fadin.

“Yaushe a gari inji maki bako.”

Dariya yayi sosai kafin yace

“Wallahi jiya da daddare kuna lafiya dai ko.”

Murmushi tayi, murmushin da takan yi a lokuta irin wannan mussaman in yayi mata irin wannan tambayar.

Shine dan uwanta da take kallo taji dadi aranta, shine aboki kuma amini da take fadi ma duk sirrin ta.

“Kamar ko yaushe dai.”

Dariya yayi kadan wacce a iya fuska kadai ta bayyan kana ya ce,

“Aure dai kalmar ita kadai ce wato bauta ga allah da raya sunnar manzon sa, zaman ne kawai yake da bambanci wata in kika ji nata matsalar sai kiga ke a aljanna kike wata kuma takaici zata baki kiji me yasa take zaune a irin wannan rayuwa, to duk ba zabin su bane daga Allah ne ki zama mai godiya a gareshi sai ya nin ka miki. A bayan komai kuma kalmar daya ce na fada miki ba daya ba ba biyu ba yanzu ma ita zan fadi hakuri.”

Kalaman shi sun yi tasiri sosai a ranta shi ne mutumin da yakan sa taji ita din mace ce kamar ko wacce.

“Hakane, ina godiya da tuni.”

Dariya kawai yayi ya soma fito da kayan da yazo mata da su na tsaraba garin rogo sai manja, kana ya dauki wasu kudi masu yawa ya bata don ta ja jari.

“Tafiya zanyi Habiba, ba lallai in dawo nan kusa ba shiya sa nazo , ga kudi nan kija jari ki soma wata sana’a dan zama haka bazai yiwu miki ba.”

“Amma kace jiya ka dawo.”

“Eh jiya na dawo yau kuma zan juya kiyi hakuri.”

“Yaya na gode kai ne ke sawa inji har yanzu ni “yar gata ce a yanzu kaine uwa kaine uba a gareni tunda kazama silar farin ciki na har nakanji bana maraicin komai.”

Har bakin gida ta raka shi tana jin wani iri a ranta kamar kar ya tafi.

*****

Inama bawa nada ikon hangen wata kaddarar, da habiba ta iya yinta don kange kanta akan akasin kaddara.

Yau tsayin sati biyar kenan da tafiyar dan uwan ta bai dawo ba, bai saba irin wannan dadewar ba shi yasa duk tabi ta damu,. abu guda ne ke kawo mata sauqin damuwar ta yadda taga magaji ya canza bawai akanta ba, sai ma abinda ya cigaba wajen ci mata mutunci. Yanzu kam yana kokarin kawo masu abinci musamman yanzu da ya samu amfanin gonar shi, wanda ya baiwa kowa mamaki dan hatsi ne aka kwaso sosai,  har mashin jincheng wanda ake yayi a cikin shekarar 2005 sai da ya saya sabo fil.

*****

Kamar kullum yau ma zaune take bayan ta kwantar da yaran ta sunyi bacci, batasan asalin sunan abin da take ji acikin ruhinta ba.

Magaji ne ya shi go da sallama ta amsa abinci ta dauko mai,  wani kallon walakanci yayi mata ita da abincin kafin ya ce.

“Banajin yunwa.”

Kwashe kayanta tayi sabida tasan ba zai ciba tunda ya fadi haka nan ya soma yi mata wani fada na rashin dalili kafin ya kwanta.

Washe Gari

Tagama duk abinda zatai har yaranta ta sallama sun tafi makaranta.

Har yanzu tsaki yake yi ta lura tunda ya tashi yau kamar da baccin rai ya farka.

“Habiba wai kina da hankali kuwa, har yanzu kin kasa maida kanki mace ita mace fa da sanin gyaran kai aka santa.”

Kallon shi take, kallo irin wanda yake nuna bata fahimci inda ya dosa ba kawai abin da ta lura da shi guda ne a cikin kwanakin nan kullum cikin zagi da hantarar ta yake takasa sanin mafarin wannan abu.

“Ni nagaji da halin ki Habiba,  daga yau ki kwashe duk tarkacen ki ki maida dakin yara , dan ina tunani aure zanyi a cikin satin nan.”

Kalmar auren ce ta sauka a cikin kirjin ta da wani irin duka fiye da tunanin ta nan take ta nemi duk wani dan shi na bakin ta tarasa, neman wani abu takeyi ko yaya yake dan ta fahimci ta inda ta gaza amma tarasa duk wani kokarin ta akan shi takeyi da kuma yaran ta mai yasa zai mat hakan, dakin take kare wa kallo dan taga a inda yakamata ace sun zauna har su biyu,  duk dakunan ba wada tattatu bane, falo ne guda sai dakuna biyu sai bayi sai wani karamin daki dake tsakar gida.

*****

Babu abin da yake bata mamaki kamar yadda yake gyaran gidan amma ko da wasa bai waiwayi dakin da take ba balle yaci arzikin ko fenti ne.

Ana gobe daurin auren yazo yace mata.

“Habiba ina miki gargadi da babbar murya akan matata, wannan falon nata ne , ansa “

Ya mika mata  dan makulli.

“Wannan da shi zaki rufe dakin can na tsakar gida da aka mai da miki da tarkacen ki, dake da yaran ki banason ko da wasa ku shiga sabgarta ko abin da zai bata mata rai , idan har ki ka yi kuskuren haka to wallahi ki kuka da kanki kina jina.”

Da kai ta iya amsa mai ita dai tasan bawani jin shi take a rai ba balle har auren shi ya dameta to amma abin da takeji a kirjin ta yayi mata tsaye shi bai fito ba shi bai shige ba menene shi bata sani ba.

*****

“Kulu kinji abinda ke faruwa, bansan ya zanyi ba.”

Kulu ta ce,

“Ai baki da abinyi da ya wuce hakuri Habibi, kin ganni nann ni kadai nasan irin gwagwarmayar da nake a cikin gidana , rayuwar aure sai hakuri sabida mazan suna mana kallon wasu hallittu daban basu dauke mu a matsayi mitane ba , duk wata mace da kika sani tanada nata matsalar sai dai ciki badan abinci kadai akayi shi ba. Habiba ki bude kunnen ki da kyau in fada miki sirrin da ban taba fadama kowa ba , saboda rayuwa sirri ce zaman aure kuma dan hakuri ne. Habiba.”

Ta sake kiran sunan ta a kari na biyu kafin ta dora da,

“Tunda nai aure har yau bansan me ake kira farin ciki ko kwanciyar hankali ba, tun da nai aure kullum cikin bakin ciki nake kwana nake ta shi, bari in baki labrin a takaice lefen da yayi min ahi ya kwashe abin shi ya saida samiru na tas ya kwashe su ke yanzu haka da kike gani na da tsohon cikin nan uwata ce take bamu abin da zamu ci muda yara ta ce min ko da wasa kar in yarda na bashi abincin ta amma bazan iya ba.”

Cikin kakkaurar murya tace,

“Habiba aure a yau dan hakuri ne ki je kiyi hakuri , ki daga hannu ki roqi ubangiji sauki akan komai ya baku zamn lafiya, ki roqi Allah yasa ba mai raba tsakanin ki da yaran ki bane wannan itace shawar dazan baki.”

*****

Bayan biki

Yau tsawon wata guda da sati biyu kenan.

Habiba kam maganar da magaji yai mata ta shiga kanta daram ta zauna tanayin iya yinta don ganin wani abu bai shiga tsakanin ta da amaryar shiba mai suna hanne , duk da taga kan amaryar yana rawa bata da kunya ko kadan kawai hakuri takeyi dan a zaune lafiya, wani sabon walakanci da magaji ya dauka shine ya mika mata gaba daya ragamar gidan sai abin da tace girki ma ita take yi sai abin da taso take tsammata ita da yaranta , tana amfani da kaeatun da Kuluwa tai mata sosai.

Zaune take ita kadai a cikin daki kamar yadda ta saba idan yaran sun tafi makaranta sai dai tai zaman ta har sai lokacin sallah tukunna ko kuma Hanne tai mata kira na gadara da walakanci don tai mata wani aikin.

Wani irin kuka daji mai han firgici da taahin hankali wanda ya sanya hanjin cikin wani irin yamutsawa, tabbas kunnuwanta ba gizo sule mata ba ihun Sadauki takeji to”yaushe ya fita.”

Take tambayar kanta kaitsaye ta fito falon hanne ta da gani wayar wuta tana dukan shi da duk iya karfin ta, batayi wata wataba taje ta kwace shi daga hannun ta yana wani irin kuka kamar ranshi zai fita , jikin shi duk ya baci da jini sabida saida ta cire mai riga ta soma dukan shi.

Cikin salama Habiba tace,

“Hanne miyayi miki haka? Wannan dukan ai yayi yawa.”

Wani kallon kaskanci tai mata kafin tace.

“Yanzu na gane inda ya koyi rashin tarbiya, saboda uwar tashi bata da ita balle har ta bashi.”

“Hanne ki dubi Saduki da kyau karamin yaro ne bai kamata kiyi mai irin wannan dukan ba , ko da zagin ki yayi , ko ni mahaifiyar shi bana mai dukan nan.”

Habiba ta danne bacin ranta sosai kafin tace,

“Dama ta ina zaki mai tun da kin lalatashi , to wallahi ba yaron ki ba koke ce kikai min haka u**r ki zanci balle, kuma ko yanzu ban huce ba sai na hukun ta shi dai-dai da laifin shi.”

Inama wuta Hanne tajefa Habiba, jin zagin tai kamar ta watsa mata ruwan zafi , tana daukan komai amma ban da cin zarafin iyayen ta bata jure wannan duk yadda take mutum kuwa aiko bata wata-wata ba ta dauke ta mari nan take fada ya kaure a tsakanin su ai ko Habiba tai mata lilis , kafin taja Saduki suka shige daki.

Zaune take kan abin sallah tana addu’a bayan ta idar da sallah, su Amira ne suka shigo, ko kayan makarantar basu cire ba sukayi kwano da aka aje musu abinci wanda kason su dukkan su har da Habiba suka soma ci.

“Mama ki tashi Sadauki yaci abinci.”
Amira ta fadi tana kokarin mikewa don tashinshi

Cikin hanzari Habiba tace,

“Kyale shi bai jin dadi ne.”

Idon Amira ne ya sauka a jikin shi

“Mama miye wannan a jikin shi , bulala me yayi? duka fa mama.”

Habiba bata kai ga bata amsa ba suka ji muryar magaji yana mata wani irin kira kamar yaki.

Da sauri ta fita ta same shi a falo dama ya daina shiga dakin ta tun lokacin da yayi amarya.

A falo ta same shi Hanne zaune a gefen shi da bakin ta a kumbure kamar shantu

“Gani “

Abinda tace kenan tana zama a gefen shi

Kallon ta yayi irin na kaskanci kafin yace,

“Kinsan wacece wannan a wajena?”

Bata ce komai ba saboda ba matsalarta bace,

“Diyar inna Baraka ce.”

Sai yanzu ta fahimci dalilin da yasa yake mata cin kashi saboda yana auren “yar uwar shi saboda ubanta ya bashi kyautar gona yana noma , gaba daya gidan su ita kadai ce bare dukkan su auren zumunci sukeyi kadan daga aikin zuri’ar su suzo yi mata walakanci wata magana ya fadi da ya sanya ta dawo hayyacin ta cikin kaduwa da mamaki.

“Tambayar ki nake yi ke dawa kuka yi mata wannan dukan ?  matar tawa zaki wa haka.”

Kalmar matar da ya fadi ne ya bata mamaki to ita a wane mataki ya dauke ta

“Ke kin san Hanne ” yar dangi ce gaba da baya , ko bance komai kin san akwai wanda zasu zo har gidan nan su rama mata.

“Amma kamata yayi ka tambayi meyafaru, bawai kazo kana fada ba.”

“Dan iyayen ki ni kike fadama haka rashin kunya zaki min, ko kin manta ne in tuna miki darajar mahaifina kike ci wallahi badan shiba da tuni na dade da sakin ki saki irin na wulakanci, bagidajiya kawai.”

Wasu iri hawaye ne suke ke towa tun daga cikin kirjin ta suna sauka akan kumatun ta

“Wannan ba adalci bane magaji , hakan da kake bai kamata ba.”

Mari ya dauke ta da shi yana fadin .

“Ni zaki ma rashin kunya, karya kawai dabba.”

Nan take ya rufe ta da wani irin duka kamar ya samu namiji dan uwan shi, ai Hanne ta samu abin da take so itama tazo suka dunga dukan ta.

Tunda suka soma haniya yaran sukaji kuma suka fahimci da maman su ake yi suna tsaye akan idon su ake dukan ta kuka kawai suke.

Hannu yakai zai mata wani irin duka sai yaji an rike hannun duba wan da zaiyi sai yaga Abbati ne yarike hannun gam ga kuma Hanne can ya ture ta fadi.

“Tun dazu kuke dukan ta , kuma ta mutu amma baku tsaya ba , mu dawa zamu zauna tunda ta mutu. Anti Amira shikenan itama ta tafi inda kawu ya tafi ba zamu sake ganin ta ba koh.”

Ya fadi yana mai kallon Amira da take kuka iya karfin ta.

“Kuyi hakuri magaji bazan sake ba na tuba , ka yafe min.”

Kashi ashirin na bacin ran Abbati ya ragu saboda yaga bata mutu ba.

Wani mugun tsaki Magaji yayi kafin yace

“Mtswww! Dole sai na hukunta ki akan laifin ki wallahi sai kin dandani kudar ki”.

Mafarin kenan

Ku tanadi abin goge hawaye a kusa da ku dan labarin zai tabaku sosai

Wane irin hukunci kuke tunani magaji zai dauka akan Habiba

Pls share and comment

Bookmark

No account yet? Register

Mace Mutum 2 >>
Share |

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.