Skip to content

Mace Mutum 2

Part 2 of 4 in the Series Mace Mutum by Haidar Ali Maganda

Mafita

Babu abinda yafi d’agawa Habiba hanakali kamar hukuncin magaji, wani irin bahagon hukunci ya d’auka akanta wanda har yau ta kasa fahimtar komai akan hakan.  A iya saninta da al’amarin aure banda nutsuwar da kowanne b’angare na ma’auratan kan samu akwai wasu hak’k’ok’in da ya zamar wa miji dole ya sauke su wa matar da yake aure. Idan ya k’aurace mata saboda yayi aure to hukuncin ciyarwa da ya yankemata akan laifin da batayi ba na menene,  tasan Allah ne gatan kowanne bawa kuma shi zai shiga lamurran ta.

Yau kwana biyar kenan kullum sai dai tayi buga-buga don ciyar da kanta da yaran ta , wannan dalilin yasa ta yanke shawarar su daina zuwa makaranta har sai taga abin da Allah zaiyi, wata shawara ce ta haska a cikin kanta, nan take kuma wani tunani ya haska mata, lallai shawarar da ta yanke ba mafita bace sai dai zataje wajen Kuluwa don neman nata shawarar.

*****

“Tabbas Habiba kinyi tunani mai kyau sai dai kema kina da taki hujjar idan mukayi la’akari kudin da yayan ki yabaki basuje ko inaba suka rushe saboda ciyarwa.”

Habiba ta sauke wani numfashi kana ta ce,

“Meye mafita Kuluwa,  kaina ya kulle bansan ya zanyi ba, yarana suna cikin ta shin hankali da yake jefani a cikin firgici, kin san yunwa batada hankali ina jin tsoron kar yarana su fada wata hanya ta daban, bani da kowa sai ke Bayan Ubangijina bani da dangi da ko kallo na suke suna ban hak’uri akan lamari na su sharemin hawaye zan ji dad’i.”

Ta k’are batun tana sakin wani irin marayan kuka mai tab’a zuciyar duk wanda ya gani ko ya saurara,

Kuluwa ta dafa kafad’ar ta tana fad’in,

“Idan kina fad’in haka sai inji kamar baki d’auke ni yadda na d’auke ki ba, tunda kaddara ta had’e zaren rayuwar mu nake miki kallon “yar uwa ta jini wacce zanyi iya yi na don ganin ba tai kuka ba, me yasa kike ganin kamar bazan iya share maki hawayen ki ba? A kullum muna rayuwa a yau ba tare da sanin mai gobe zata zo da shiba, Allah kan b’oye sanadin kowace k’addara don samun salama a zuciyar kowanne bawa, kowane tsanani yana tare da sauk’i.”

Kalaman Kuluwa sun shigi Habiba sosai, matsowa tai kusa da ita tana fad’in,

“Kiyi hak’uri insha Allahu bazan sake yin hakan ba.”

“Hmmm kar ki damu wata rana sai labari, yanzu shawarar da zan baki shine kamar yadda ki yi tunani ki d’auki kayan ki nemi dillaliya ta saya sai ki soma yin wata sana’a, ragowar kuma sai ki saya muku kayan abinci ki aje, amma fa kujerun kawai zaki sai da ki bar gadon ki, sannan banda d’aura ma yara talla dan yanzu muna wani zamani da yazo da abubuwa kala-kala na farin ciki da akasin shi.”

Nan farin ciki ya mamaye zuciyar Habiba tana mai jin dad’in shawarar  “yar uwa kuma aminiyar ta, tana d’aukar duk shawarar da ta bata tana ajewa a inda ya dace.

*****
Cikin ikon Allah ta soma sana’ar kayan k’ulle-k’ulle irin su kuka,kubewa,daddawa,magi da sauran su. Ciniki take yi sosai yaranta sun koma makaranta, suna samun abin da zasu ci dana al’amuran yau da kullum.

Magaji kam ba sawa ba hanawa sai dai har yanzu bai shiga sabgar ta ko ta yaran ta ko gaishe shi su kai baya amsawa ita kam cewa take ” ku cigaba da gaishe shi baban ku ne wata rana zai amsa.”

*****
Ihu take tun anajinkukan ta har muryar ta dishe ga wani irin miyau da yake zuba a bakin ta, cikin ta yayi wani kumburi na bam mamaki.

Duk dubarar da Habiba za tai tayi amma babu wata mafita, tayi jik’e jik’en, ta bata amma har yanzu babu wani cigaba.

“Assalamu alaikum”

Cewar Kuluwa tana shigowa dakin, da yake a farkon gidan yake, yana daga cikin abubuwan da Hanne ta sanya shi yayi cewar bata buk’atar su a sashin ta shi yasa ya toshe k’ofar ta cikin falon akai mata wata k’ofar ta tsakar gida.

Cikin tashin hankali Habiba ta ce

“Kuluwa kin ga har maganin da kika ban na bata amma har yanzu kamar zata mutu”.

Cikin tausayawa Kuluwa ta kalle ta ce

“Kiyi hak’uri, komai zai zo da sauk’i, amma anya yarinyar nan ba wani abu taci ba”.

Kallon ban fahimta ba Habiba taimata

Cikin idonta Kuluwa ta kalla kafin ta ce

“Eh ina nufin taci wani abu ko lalatacce ko kuma guba “.

Kalmar guba ce ta daki zuciyar ta da wani irin bugu na ban mamaki .

Tabbas d’azu tana cikin d’aki taji lokacin da Hanne take cewa Magaji ya siyo mata maganin k’wari

“Kuluwa ya zanyi mu kai ta asibiti.”

Cikin tausasa murya da tausayawa kuluwa ta ce

“Hakane amma yana da kyau ki fadi wa mahaifin ta don ya sani…”

“Mahaifi dai! A d’auri kashi ko a b’ata igiya, ai nice nan ubanta kuma nice uwarta, mutumin da bai damu da yasan ya muke rayuwa ba.”

“Ko menene Habiba yana da hak’k’i akan ta sabida shi ubane, kin san ba’a canzawa tuwo suna.”

Ba zata iya yin musu da ita ba,cikin hawaye wani na bin wani ta ce.

“To mu fara kaita asibitin tukunna, kar ta mutu dan Allah.”

“Babu matsala zamu kaita ,ba kin ce yana nan ba.”

Girgiza kai kawai Habiba tayi alamar eh

“To kije ki fad’a mai Amira bata da lafiya zamu kaita asibiti, kiyi sauri”.

Cikin sauri ta mik’e tana gwama k’afa ta shiga falon, kiran shi take da alamun rauni a muryar ta.

Fitowa yayi daga dakin yana bin ta da wani kallon takaici.

“Lafiya kike min wannan kiran kamar yak’i.”

Cikin kasalalliyar muryar ta da rauni ya bayyana a ciki take fad’in

“Dama Amira ce bata da lafiya ina son kaita asibiti.”

“Sabida wannan banzan zancen ne zaki katse min uzuri na, wai sai yaushe zaki koyi hankali ne, ni banida ko asi dan haka ki san nayi ke “yar taki.”

Kwata-kwata bata fahimtar zancen shi sabida hankalin ta ba a wajen shi yake ba, tunanin ta yana can wajen d’iyar ta.

“To me kike jira da bazaki tafi ba.”

*****

“Ya amince.”

Abinda ta iya fad’ama Kuluwa kenan tana daukar Amira

Kai tsaye asibiti Abuth suka nufa dan anan ne zasu samu sauqin wasu abubuwan, emmargency aka kaita nan wasu nurse suka soma bata taimakon farko da d’aura mata drip . anyi mata duk wasu gwajejen da suka kamata

Yanzu ma zaune suke a ofishin wani likita yana yi musu bayani

“Wane irin sakaci ne wannan? Yarinya k’arama kamar wannan ace taci guba har ta kai lokaci mai tsayi haka baku kawo ta asibiti, har sai da abin yaci jikin ta sosai”.

Kallon kallo ake tsakanin Habiba da Kuluwa ko wacce bakin ta ya rufe suna rasa da wace irin kalma ya kamata suyi amfani wajen fahimtar da shi.

Kuluwa ce tai k’arfin halin fad’in

“Likita yanzu meye abin yi? A wane hali take?”

Ta jero mai tambayoyi

“Yanzu dai dole za ai mata aiki saboda abin ya tab’a cikin ta sosai”.

Ya maida hankalin shi akan wata “yar takadda yana rubutu kafin ya d’ago yana miko musu.

“Ga wannan sai kuje can wajen da ake biyan kud’i ku biya za su baku wata takarda sai ku kawo min, dan Allah kuyi saurin biya don ayi mata aikin nan cikin gaggawa”.

Amsan takardar Kuluwa tayi saboda ta lura babu wani kuzari a jikin Habiba,kana suka mik’e don zuwa wajen biyan k’udin kamar yadda aka kwatanta musu.

*****
A hanyar su ta zuwa gida don dauko dan abin da suke da shi idon Kuluwa ya sauka akan takardar dake hannun ta.

Firgici tashin hankali sune suka bayyana kwance akan fuskokin su ganin irin kud’in da zasu biya.

Cikin sabon tashin hankali da fargaba Habiba take fad’in

“Kuluwa a ina zan samo irin wannan k’udin masu masifar yawa, ni ko a zahiri ban tab’a ganin su ba, ya zanyi ina mafita? “.

Ckin tsanani tausayawa Kuluwa ke fadin.

“Allah yasan damu shi zai bamu mafita, saboda a gareshi muka dogara kuma muke neman taimako”.

Zuciyar ta tuni ta tafi wani wajen daban tana sake bud’e k’wak’walwarta ko zata samu mafita nan take ko ta hango mafita a dai-dai lokacin tunanin ta da zuciyar ta suka haska mata komai tar kamar hasken lantarki.

Kuluwa ji tai kawai an damk’i hannun ta, a hankali ta d’ago tana kallon Habiba da take wani irin murmushi, murmuahin da kallo guda zakai mata ka fahimci akwai wani ciwo a k’asan zuciyar mai murmushin.

Murmuahi take don taba Kuluwa k’arfin gwiwa.

“Kuluwa muje na samo mafita, muje gida.”

A dai-dai bakin gate din suka tsaya don neman mashin, Habiba idan don son ranta ne to a kasa zasu tafi sai ta lura kamar ciwon kafafun Kuluwan ya motsa saboda zirga-zirga shi ya sa.

Basu sha wahala ba suka samu abin hawa har cikin Tudun/Jukun a bakin layin su Kuluwa aka sauke su suna shirin bashi kudi sukaji magana a bayan su.

“Haba Kuluwa ina kikaje ne?,tun dazu ina jiran ki.”

Wani kyakkyawan murmushi ne ya bayyana a saman fuskar Kuluwa tana fadin

‘Wallahi mun je asibiti.”

“Toh fa waye ba lafiya.”
Cewar waccan.

“Diyar habiba ce”
Ta fadi tana nina Habiba

“Habiba wannan itace Asiya kanwata da nake baki labari”.

“Oh nagane ita ce wadda ke harkar abinci ko.”

“Eh ita ce, ashe baki manta ta ba.”

“Asiya wannan ita ce Habiba da nake yawan baki labari.”

Murmushi sukeyi dukkan su, Asiya murmushi take hade da takaicin yadda rayuwa taiwa Habiba , gata mace har mace amma an daure zuciyar ta da sarka. Shiyasa har yanzu takejin lokacin ta baiyi na tai aure har sai ta kafa kanta da sana’ar ta sabuda bazata yadda da wannan zamantakew ba babu sakewa namiji ya nuna miki ba kikai ba yai ta maki walakanci tu balle in yagan shi da sabuwar. Har gobe tana kallon kanta a matsayin madubi, madubin da zata kalli kanta kana taba wasu su kalli kansu do su san kai kuma zasu iya.

Sai da ta dan matso kadan kafin ta dafa Habiba ta ce.

“Kar ki karaya a cikin kowace tafiya akwai gargada,cikin kowace rayuwa akwai kaddara me ko akasin ta ki karfafa kanki komai zai zama kamar bai faru ba, zaki ce na fada maki wata rana zai zama labari.”

Kallon ta Habiba tayi da murmushi kwance a fuskarta.

“Nagode Asiya hakika kina karamci kukan sa inji ni kamar kowa ta hanyar karfafa min gwiwa da kuke ina godiya Allah ne kadai zai iya biyan ku.”

“Yiwa kaine.”

Cewar kuluwa

“Anty Kulu idan babu damuwa me zai hana idan na samu aiki tazo munayi, ko ba komai zata samu abin dogaro da kanta ko ba yawa.”

“Zanyi.” Cewar Habiba idanunta suna haskawa da wani irin farin ciki da dadi, amma duk da haka bata daina jin faduwar gaban da takejiba tun dazu

*****

Mafitar da zata zame mata farin ciki na wani lokaci, kafin ta zama sila kuma sanadin wata kaddarar da zaji ina numfashin ta ya tsaya cak.

Wata mafitar zuwa take ba tare da kayi zato ko tsammani ba.

Inama inama, inama Habiba tana duba da ta duba ko zata samu wata mafitar ba wannan ba, inama tasan mai zata tara a gidan da ta juya akalar ta zuwa wani wajen daban ba wannan ba.

Bookmark

No account yet? Register

<< Mace Mutum 1Mace Mutum 3 >>
Share |

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.