Skip to content
Chapter 3 of 4 in the Series Mace Mutum by Haidar Ali Maganda
Bookmark

No account yet? Register

Sabon Lamari

Abuth Zaria City

Kuluwa ce ta soma lura da numfashin ta ya soma daidai ta kamar yadda likitan ya fadi masu.

Sai da tai bacci na tsayin minti talatin kafin ta soma motsi kamar yadda Dr yadi ya sanar da su cewar yau zata farka.

A hanakali ta bude idon ta tana karewa dakin kallo, tsaf ta fahimci a asibiti take.

“Kuluwa kice dani komai bai faru ba.”

Ta fadi cikin raunin murya kamar tana son fashewa da kuka, a cikin sautin muryar ta zakanfahimci akwai wani irin ciwo da yake cinta tsayin lokaci.

Kuluwa ta matso kusa da ita sosai kafin ta ce.

“Ba zance komai bai faru ba, idan nace haka zakiji kamar kina mafarki ne gwara ki fahimci yadda rayuwa take ki gane yadda kaddar ke zuwa ba zato ko tsammani”.

Nan take lamarin ya soma haskawa a cikin kanta kamar da wasa.

*****
Bayan sun gama tattauna yadda abin zai kasance na aikin da zasu soma a cikin sati mai zuwa ita da Asiya kai tsaye ta nufi gida.

Taron mutane ta gani a kofar gidan su wanda ya sanya mata wani irin faduwar gaba da fargaba, wasu irin tunanuka ne suka soma kai kawo a cikin kanta kafin ta fahimci me ke faruwa taji saukar murya magaji yana fadin.

“Kin dawo daga yawon?, tsaya ina kika je. Wato a kullum burin ki ki nuna min ban isa ba ko, ti kin huta ki duba kalla kiga.”

Nan idanunta suka sauka akan wutar dake ci bako saurarawa a dakin ta ,sai mutane dake kokarin kashe ta amma taki mutuwa.

“Habiba na tsaneki na gaji dake wallahi.”

“Magaji yanzu ba lokacin wannan zancen bane ka bari muga karshen komai in mun natsu.”

Cewar wani yayan Magajin.

Habiba jin kalaman tai a tsakiyar kanta sun sauka da wani iri duga da ya zarce bugun guduma, idanun ta ne suke yawatawa don hangen ta inda zata ga yaran ta, hannun ta taji an rike ta juyo taga Nana da Sadauki.

“Nana ina Abba yake.”

“Abbati yana cikin daki tun dazu nake son fada ma Baba amma yaki ya ji.”

Ai bata bari Nana ta kai karshen zancen taba tai wani kukan kura zata shiga cikin gidan tana kiran sunan Abba.

Wani irin gigitaccen mari taji a fuskar ta da ya sanya numfashin ta tsaya na wacin gadi tana karewa Magaji kallo da ya mare ta.

“Na rantse da wanda raina ke hannun shi idan yaro na ya mutu kema sai kin mutu.”

Yaro na jin kalmar tai tana mata wani irin amsa kuwwa a cikin kunne ” sai yaushe Magaji zai daina son kanshi sai yaushe zai kalle ta a matsayin da take kai.

“Habiba ga yaron ki, kin kashe shi da hannun ki na tsane ki, Allah ya tsine maki albarka kije nasake ki saki daya banason na sake ganin ki ko yaran ki.”

Yaro na yaron ki, kullum a kalaman shi sai ya so kanshi me yasa.

Idanunta ne suka sauka akan Abba da fatar jikin shi ta salbe tai fari, lokaci guda taji wani abu ya tokare mata a makoshi saki kalmar ta sake maimaitawa a cikin kanta, makoshin ta ne takejin ya bushe kamar zai tsage kafin komai ya dauke mata dif.

*****

“Habiba tunanin me kike kinsan fa baki da lafiya yau kwanan ki  hudu baki san inda kanki yake ba, likita ya ce jinin ki ya hau kina fama da damuwa don Allah ki rage tunani.”

“Kuluwa ina zanje Magaji ya sake ni bayan yasan bani da kowa.”

“Ki daina fadin haka ai kina da Allah kuma yana tare dake a kowanne irin lokaci zai cigaba da baki kariya akan komai kuma shine gatan kowanne bawa”.

Tana jindadi yadda Kuluwa ke bata karfin yin komai.

“Kuluwa ina A ban yake ina son ganin shi”.

Murmushi Kuluwa tayi kafin ta ce

“Yanzu daga dakin nake bacci yake, ki bari ya farka sai muje ki ganshi. Amma dan Allah ki kwantar da hankali ki”.

Suna cikin haka su likita ya shigo, sai da ya kalli Kuluwa kafin ya kalli Habiba ya ce.

“Sannu ya jikin”.

“jiki da sauƙi likita.”

“To Allah ya ƙara sauƙi.”

Dukkan su suka amsa da amin

“Yanzu ina ke maki ciwo.”

Shuru tayi na wasu sakanni kafin ta ce

“Gaskiya babu sai dai kaina da yayi min nauyi kamar an ɗaura dutse”.

“OK baby komai zai daina ki ji, abin da nake so da shine ki daina sawa kanki damuwa hakan zai baki matsala sosai.”

“I sha Allahu zan ki yaye.”

“Yawwa hakan yayi.”

Wasu ƴan rubuce-rubuce yayi kafin ya ɗago yana ba Kuluwa yana faɗin

“A daure a sayi wannan maganin zai taimaka mata sosai.”

Karɓa sukai suna godiya shi kuma ya fita

*****

Bayan Kwana Shida

A yau ne aka sallama su daga asibiti, haɗa kaya suke hankali kwance kamar babu wani abu dake damun su kamar komai bai faru ba.

“Kuluwa wai ni kam a ina aka samu kudin aikin Amira da na sauran komai. (tana nufin da nata da kuma na Abba)

Ina ta son inyi maki magana amma Allah bai ban iko ba sai yau”.

Murmushi kadan Kuluwa tayi tana faɗin.

“Kim San hanyoyi Allah suna da yawa,masu aikin Allah bada ƙarewa a duniya. A lokacin da muka zo kawai mu kai sa’a wasu batun Allah sun zo kawo ziyara dama suna zuwa lokaci bayan lokaci shine fa likita ya sanya sunan mu a cikin masu bukatar taimako, suka biya komai wallahi.”

Dadi Habiba ke ji sosai na sauka a cikin zuciyar ta har bata san me ya kamata tayiba.

“Muje koh.”

Cewar kuluwa tana kallon Habiba.

*****

Wani irin kallo take mai tanajin kamar ta tashi ta rufe shi da duka ko zataji sauƙin abin da take ji akan shi. Kallon shi take kallo irin a girma ba hakali.

“Kai wannan ba abin kunya bane a cikin iyalan gidan nan ace ka aikata haka, marainiya amana ka barta daga ita sai kanta, to in kamanta bari in maka tuni kafin malam ya rasu amana ya barta a.

Hannun mu saboda shina amana ce hannun shi. Ashe ka manta da girma irin na zumunci, da wane ido kake so ƴan uwan ka su kalle ka. Mai son bata masu al’amura ko me, tun wuri ina Umartar ka kake ka dawo da ita.”

Ta kare batun tana aika mai da wani irin kallo.

“Amma Ita abin da tayi bai kai ace an yafe mata shi nan kusa ba, gaba daya gidan fa taso ta halaka.”

“Nasani wannan ma abin dubawa ne, amma bai kai girman amana ba idan kuma kana son nuna min iyaka ne babu komai kaje kayi yadda kake so.”

Ta faɗi tana fashewa da kuka da face ma jima.

“Shikenan kiyi haƙuri zan dawo da ita amma ina son sai na dawo daga tafiyar da sanyi”.

“Ko kai fa Allah yayi maka albarka.”

*****

Tabbas duniya juyi-juyi ce, rayuwa ta yi wa Habiba kyau na bam mamaki, idan ka ga ta a ƴan kwana kin nan sai da ƙyar zaka shaida ta daga ita har yaran ta komai sai son barka yanzu aiki take tare da Asiya tana samun rufin asiri sosai har ƴa ƴanta sun koma makaranta. Kuluwa ce ta bata ɗaki falle guda tana zaune da yaran ta kafin a ga mai ubangiji zai yi.

Yanzu bata da damuwar komai a ranta don har makaranta ta shiga da ake koya musu karatun addini dama boko. Hankalin ta ya ƙara kwanciya tana ƙoƙarin tura yaran suje gaida mahaifin su kamar yadda Kuluwa ta ce mata da uba ake ado riga ko a kasuwa a sayo, uba bane shi yasa take yin hakan bawai don tana so ba, tun da yaran suke zuwa basu taɓa ganin uban ba sai dai Hanne ta ce masu baya nan amma bata fasa tura su ba.

Damuwar Habiba guda daya ce amma ta rasa ta yadda zata fada mata.

*****

Yau tun safe bata zauna ba saboda zazzabin da Abbati ya kwana da shi, ta kai shi kemis an bata maganin malaria ta bashi amma shuru bai sauka ba kawai sai ta yanke hukuncin ta kai shi asibiti. Haka ta goya shi ta rungumi Sadauki ta tafi asibiti Almadina.

Gidan ta janyo ta kulle don dama ita kaɗai ce a ciki yaran duk suna makaranta ta Kuluwa kuma taje gidan su gaida iyayen ta, makullin gidan ta ba wani mai shago dake kallon gidan kamar yadda suka saba idan zasu fita wani zai riga dawowa ko yara in sun dawo daga makaranta.

*****

An duba Abbati an tabbatar mata malaria ce tai mai mugun kamu an rubuta mata magungunna ta biya pharmacy ta saya ta hau abin hawa zuwa gida.

Hankalin ta kwance taje gum mai shago don a san makullin ya bata ga mamakin ta sai taga gidan a buɗe ba tare da tunani komai ba ta kutsa kai cikin ɗakin da yake a matsayin nata.

Abba ta sauke dake bayan ta yana bacci shi kuma Sadauki ya zauna buta ta dauka don shiga bayi, ta fito daga bayi sai taga ɗakin kuluwa a buɗe cikin hanzari ta nufi ɗakin don taki ya ta bari su sai taga takalmin mai gidan kuluwa kawai sai ta juya. Taso bakin ɗakin ta kenan sai taji ankirata har zata basar sai ta amsa.

“Nine kizo”.

Da kamar baza ta je ba sai kuma ta tafi a bakin ɗakin ta tsaya ta ce

“Baban Isah gani.”

“Ki shigo man sai kace zan cinyeki.”

Ji tai gaban ta ya buga da wani irin sauri sai ta kawar da tunani da ke son bijiro mata a zuciya kawai ta shiga.

Tana shiga shi kuma yana daga bayan ƙofa, kawai ji tai an rufe kofar da wani irin karfi, ƙarar bugun ƙofar ne ya haifar mata da wani irin faduwa gaba mai ban mamaki

*****

“Allah dai ya shige mana gaba akan dukkan komai.”

Cewar wata farar dattijuwa

Kuluwa ce ta amsa da

“Amin goggo.”

Tsohuwar ce ta kalli  kuluwa cikin alamun ta tuna wani abu kafin ta ce

“Yawwa wai ni kam ina Habiba ne kwana biyu ban sanya ta a idanuna ba”.

Murmushi ne ya faɗaɗa a fuskar Kuluwa kafin ta ce

“Aiki tana nan”

Dattijuwar ta ce

“Allah dai ya saka maku da alkairi juyi ta haƙuri da juna, wani abin dole sai ana kau da kai”.

“Amin goggo, I sha Allahu zamu kiyaye. Bari in tafi naga yamma na gabatowa”.

“To ki gaida yaran.”

Haka kuluwa ta taho zuwa gida tana jin jikin ta yayi wani irin sanyi, san bata jin kuzari ko kaɗan.

*****

Sai da rai dariya mai isar ta kafin ta ce

“Ai ko dai gaskiya ne don garin ya karɓe ka kaga yadda kayi kyau da ƙiba kuwa”.

Shima dariya yayi kafin ya ce

“Ni ko ban ga wata ƙiba da nayi ba ko haske.”

Haka suka ci gaba da hira cikin farin ciki kafin Iya ta ce

“Yawwa Magaji tun da ka dawo a ina maganar mu ta kwana.”

Tsaf ya fahimci inda ta dosa amma sai ya nuna kamar bai fahimta ba

“wacce magana kenan?”

Ya faɗi yana kallon ta don neman ƙarin bayani

“Iyaka ta zaka nuna min kenan,shi yasa baka ɗauki zance na da muhimmanci ba har ka manta?”

Ta ƙare batun da sigar tambaya

“Kiyi haƙuri Iya, hirar da muke ce ta ɗauke min hankali, amma daga nan can zanje. Ba ance tana gidan su Kuluwa ba?”

“Eh tana can, Allah sarki itama Kuluwa ba dai kirki, haka tsohuwa ta take itama yanzu kai maza kaje”

*****
Idanunta ta runtse iya yadda zata iya koda, wasa ba taɓa hango hakan daga cikin al’amuran ƙaddarar ta ba.

Ƙara matsowa yayi jikin ta sosai yana faɗin

“Haba karki min haka Habiba kin san yadda nake son ki kuwa, ke wlh ni har aure ki ma zanyi kawai ki amince zan maida ki tankar sarauniya a cikin mata. Zaki zama mai kallon kanki a matsayin mace mai iko da kuma karfin…”

Bai kai ga faɗin abin da ke bakin shi ba ta tari numfashi shi da faɗin

“Kaji tsoro Allah Baban Isah, ni ba mazinaciya bace na faɗi maka tun ba yau ba mai yasa kake son yi min haka ba hali na bane ban taɓa aika ta hakan ba.”

“Masami Nima ba Halima bane ban taɓa yi ba amma ke ɗin ce ta daban wallahi, kiyi haƙuri ki buɗe idon ki ki kalle ni ko zan ji sanyi.”

Ko da wasa baza ta iya buɗe ido ba, kallon da tai mai ma a lokacin da ta shigo bata san tsirara yake ba.

Ƙoƙari take ta kwatanta halin irin na wasu mazan ita dai ta san ba tai dace ba to ashe kuluwa ma hakan take.

Saukar hannun shi taki a wani ɓangare na jikin ta cikin zafin nama tai Ƙoƙari ture shi ba tare da ta buɗe idonta ba

*****
“Sannu”

Ita ce kamar da ta fito daga bakin magaji a lokacin da yaga kuluwa zata shiga gidan.

“Yawwa sannu.”

Abin da ta ce da shi kenan

Sai ya cigaba da faɗin

“Dama nazo wajen Habiba ne na maida ta, don ta koma ɗakin ta.”

Wani ɓangare na zuciyar ta yaji daɗin hakan sai dai wani sashen na son sanar da shi wani abu dake ranta amma ta kudurce sai sun dawo da Habiba zatai masa maganar.

“To Allah ya tabbatar da alkairi bari na kira ta.”

Tsakanin mata da miji sai Allah abin da tace a ranta kenan

*Abou Farouq ne*

*****

Me kuke tunani zai faru ga kuluwa zata shigo ga magaji a ƙofar gida ya zo biko
Ga Habiba da Baban Isah a ɗaki

Ina buƙatar kowa ya faɗi abin da yake hasashen zai faru

Ina godiya sosai ga masu Ƙoƙari tambayar wannan labari da kuma masu sharhi alheri Allah ya kai musu a duk inda suka

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

<< Mace Mutum 2Mace Mutum 4 >>
Subscribe
Notify of
guest

0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments
You cannot copy content of this page.