Da sauri ta kashe motar ta sauko ta nufi ƙofar da za ta sadata da cikin Sha Ka Tafin. Tana isa masu gadi biyu dake rakuɓe a ɗan ɗakinsu suka taso suna tahowa gurinta, gudan ya sha gabanta da sauri yana cewa
DELUWA Wada ikon Allah.DELUWA Yar baiwa.DELUWA Hasken Kano da Zazzau.DELUWA Aurenki sai mai sa'a DELUWA maƙiyinki shi ke ganin muninki.DELUWA kome nisan zamani zaki je makkah.
Bi a hankali da taƙawa Allah Shi ne Mai Yi...