Skip to content
Part 3 of 9 in the Series Mafarkin Deluwa by Fulani Bingel

Da sauri ta kashe motar ta sauko ta nufi ƙofar da za ta sadata da cikin Sha Ka Tafin. Tana isa masu gadi biyu dake rakuɓe a ɗan ɗakinsu suka taso suna tahowa gurinta, gudan ya sha gabanta da sauri yana cewa

DELUWA Wada ikon Allah.
DELUWA Yar baiwa.
DELUWA Hasken Kano da Zazzau.
DELUWA Aurenki sai mai sa’a 
DELUWA maƙiyinki shi ke ganin muninki.
DELUWA kome nisan zamani zaki je makkah.

Bi a hankali da taƙawa Allah Shi ne Mai Yi…

“Ba wani Shegge ba!”

Ta ƙarasa waƙen da sauri tana fashewa da dariya mai kama da an shaƙe Ɓera, cikin jin daɗin kirarin da Madu Mai Gadi ke mata duk yayin da suka haɗu ta ce,  “wallahi Madu na maka Alƙawari duk ranar naje _makkah_ kai ne na ukun da za ka biyo bayana”.

Ya yi dariya shi ma yana shafa gemunsa da furfura ta fara ratsawa, sai kuma ya sauke idonsa kan ƙafufuwanta da suka yi butu-butu cikin wani buɗaɗɗen takalmin danƙo.

“Deluwa ke nan! Allah Ya nuna mana
lokacin, da babu abinda zai sakani dawowa ƙasar nan, kai iyalina ma sai dai su yi haƙuri… Wai lafiya naganki cikin daren nan?”

“Hmm! Kai de bari Malam Madu, wallahi lalata naso yiwa Chibunzu yau ɗin nan da niyyar tura shi barzahu, amma dai abin da sauƙi yanzu, na ma fasa, sai dai fa guba na bashi, kum har yanzu tana cinsa.”
.
“Guba fa? Madu ya tambaya da mamaki.
“Eh ita fa! Ni dai yanzu ba dogon surutu ba,  ku taimaka mini ya warware ba na so na rasa shi a halin yanzu. Da Allah Inda wani ma’aikacin da zai duba shi ku kira sai muje dashi daga ciki yanzun”.

Ta furta da alamun damuwa ƙarara akan fuskarta da baƙinta yasa baka ganin hasken farin idanunta.

Madu ya dubi abokin aikinsa, zai yi magana ya yi sauri ya dakatar dashi,

“Haba Deluwa, kamar baki san doka ba, ta yaya za su karɓeshi a wannan halin ba tare dake kin baƙunci masu Gora ba, kinsan dai ba abinda zai hana a rufeki tunda ke da kanki kince ke kika bashi gubar…”

Ya ɗan numfasa,

“To amma kamar kin take sa’a, ina da wani daɗaɗɗen tsimin da idan yasha zai yi aman duk gubar da ta shiga cikinsa nan da awa uku, amma kuma…”

“Yauwa Malam Madu don Allah taimaka ka bashi zan biya ka ko nawa kake so.” Ta tari numfashinsa.

Ya dubi Abokin gadinsa  ya ce, “to kai ka jira, ka kuma san ƙaryar da zaka yiwa duk wanda ya tambaye ka inda nake, za mu je gidana na basu tsumin.”

“Sai ka dawo.” Ya furta yana mai  komawa mazauninsa.

Mintuna Goma Sha Biyar (15) ne ya kaisu gidan Madu, nan da nan suka fito da Chibunzu suka saka shi a ɗakin dake zauren gidan, cikin abinda bai fice minti Shida (6) ba ya ɗauko tsumin. Ita da kanta ta ɗaga da kan Chibunzu ta bashi yasha matuƙar sha, wanda a lokacin idanuwansa sun ida rufewa baya ganin kome ko jin kome sai dai yana numfasawa kaɗan-kaɗan.

Gun akuri-kurarta ta koma ta buɗe wurin da suke aje kuɗinsu ta ƙirgo dubu uku tazo takawowa Malam Madu.

Ya yi godiya sosai, kana ya sanar da ita dole sai dai ta zauna anan ta kula dashi zuwa lokacin da zai wartsake gabaɗaya su tafi.

Bata so hakan ba, sai dai sanin ita ce silar kome yasa dole ta haƙura tana tunanin ƙaryar da za ta sheƙawa uwarta Duduwa, duk da tun Yamma da ta fito ta sanar musu za ta cikin ƙauyensu sassaƙo wasu itatuwa, ke nan ko da bata koma gida ba za su za ci acan gurin Gwaggonta ta kwana. Abu na biyu kuma da ya sakata jin dole ma ta zauna, shi ne tafi so ta ɗauki shi Chibunzu ta kaishi gurinsu Malam Zaidu har zuwa lokacin da Alhaji Labaran zai cika mata burinta na zuwa makkah, ta tabbata a sannan ne Chibunzu zai iya ci gaba da yawonsa ba tare da asirinta ya tuno gun Alhajin ba. A cikin ranta ta manta rana dubu ce ta ɓarawo rana guda kuwa ta me kaya. Haka duk giringiɗishin kura wataran bushiya kan ba ta mamaki. Mu je zuwa dai!

Da wannan tunanin ta lumshe miitsi-mitsin idanuwanta masu kama da an soya gero, a hankali tunaninta ya haska mata  kanta a cikin jirgi tana ta gaisawa da turawa da labawa tana da kurɓar shayi bil baskawit(Biscuit)…

*****

Tun lokacin dasu Malam Tsalha suka arce gida, a tsammaninsu na ganin  fatalwa suke ta kokawa kawunansu na kaiwa dare a maƙabartarsu. Lalle da suna bin shawarar matansu da magabatansu sun tabbata da zai yi wahala su ga fatalwa irin wacce suka gani a daren, sai dai hakan ya zame musu darasi, musamman Malam Tsalha da ya kwana yana gudawa, musamman yake ganin gizon da kwalelen kan Deluwa ke masa, shi yafi kome ma ɗaga masa hankali. Dan zai iya rantsuwa da Allah ko inuwarsa ya kalla sai yaga ta zame masa ɗan ƙaramin halitta irin tata.

Don haka washegari basu fito ba sai wurin ƙarfe 10:30am, shi ma Malam Lawal ne ya yi karfin bibiyar gidajensu suka fito, abinda ya razana su sun je gidan Malam Zaidu Mai ɗakinsa taba su tabbacin bai kwana gida ba, sau biyu tana tura yara nemansa ko a masallaci ya kwana sunce basu ganshi ba, Malam Shitu shi ya yi ƙarfin halin kwantar mata da hankalin za’a ganshi, tukunna suka fito duk jikinsu a sanyaye…

“Ta tafi dashi!” Malam Tsalha ya furta bayan sun fito yana dafe cikinsa da har lokacin murda masa yake yi. “A’a Malam mu dai je maƙabartar mu gani tukun, idan ba mu ganshi ba sannan za mu samu tabbacin ta tafi dashi ɗin, Malam Shitu ya faɗa. “Amma kai za ka fara zuwa duba shin ko?” Inji Malam Tsalha yana nuna Malam Shitu da baki.

“A’a fa, dukanmu za mu yi shahadar ƙuda mu je, Zaidu ai haƙƙinsa na wuyanmu, banda wannan ma shi zaman duniya na mai rabo ne, mu je Malam kar bata lokacin da muke yi ya jawo wani abin.” Cewar Malam Lawal.

A ɗarare suka doshi maƙabartar kowannensu da irin addu’ar da yake ambato a zuciyarsa, har zuwa lokacin da suka isa hanyar shiga cikin maƙabartar. Kai tsaye  Malam Shitu da Malam Lawal  suka shige ciki, yayin da Malam Tsalha ya ɗan tsaya daga baya yana leƙensu haɗe da ƙifta idanuwa kamar ambashi ajiyar kunama.

Wani ƙadangare daya yanko a guje yabi takan ƙafar Malam Tsalha shi ya saka shi kwaɗa ihun wayyo! Gami da hantsilawa cikin maƙabartar yana faɗin “shi ke nan burinku ya cika! Ta riƙe mini ƙafa”.

Da hanzari suka jiyo, basu san sa’adda suka tuntsire da dariya ba ganin yadda ya baza babbar riga a ƙasa, Malam Shitu ya ce, “gaskiya na ba ka sarautar matsorata a…”

Bai idasa ƙarasawa ba idanuwansu suka kai kan Malam Zaidu dake can yashe a ƙasa duk kura ta lullɓeshi, za  ka ma iya ɗaukan shi a matsayin gawa duba da yadda babu wani alamun numfashi a tare da shi…

Da hanzari suka ƙarasa gurinsa, cikin zafin nama Malam Lawal ya kinkime shi ya sa a bayansa suka fito dashi zuwa gida. Nan fa aka nemo wani Mai Kemis  ya fara duba shi, shi ya bada tabbacin da ransa, dogon suma ne ya yi…

Anan ya yi masa abinda zai masa tukunna ya jona masa ƙarin ruwa.

Matarsa dai ba abinda take sai kuka da Allah wadai da wannan aiki nasa na kaiwa dare a maƙabarta. To haka gasu Malam Tsalha duk jikinsu ya daɗa yin sanyi tsoronsu ya ƙara girmama.

Haka suka zauna jugum har dai zuwa lokacin da Malam Zaidu ya farfaɗo sosai ya gane a inda yake…

Nan fa bayan ya ƙara shanye wata ledar ruwan ya wattsake tas! Har ya samu damar larabtawa su Malam Shitu yadda ta kaya, ya basu tabbacin gawar da zai binne da kunnensa yaji tana ambaton kalaman soyayya ga fatalwar da ta kira kanta Yar Wada.

Daga lokacin fa suka yi alwashin magaribar fari za su dinga barin maƙabarta… Duk da, da ƙyar suka shawo kan Malam Tsalha ya ce zai koma, amma da ya rantse da mutuwarsa ya bar aikin maƙabarta har abada. Cikin wannan jimamin bayan sun dawo daga sallar la’asar suna zaune kofar gidan malam zaidu suna cin abinci…wata mota kirar akuri kura ta doso inda suke dukkansu suka bita da kallo har zuwa lokacin da motar ta tsaya kusa da su mamallakin motar ya buɗe murfinta.

‘Yan guntayen ƙafafuwantane suka fara sauka kafin lailayayyen kanta ya biyo baya…

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mafarkin Deluwa 2Mafarkin Deluwa 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×