Skip to content
Part 2 of 9 in the Series Mafarkin Deluwa by Fulani Bingel

AN RUBUTA SHI TUN 2014

AN SABUNTA SHI 25 JULY 2020

Zuciyarsa ta buga, ya yi wani irin jifa da shebur ɗin hannunsa, ya yi baya a matuƙar razane yana kallon cikin kabarin. Shi fa tunda uwarshi ta kawo shi duniya, bai taɓa shiga tashin hankali irin na yanzun ba.

Gawa ce fa da furta kalmar SO… Gawa fa?

Wannan shi ne gobarar gemu! Wani irin amai ne yaji ya taso masa, kamar me son amayar da kayan cikinsa haka ya dinga sheƙa shi, nan da nan jikinsa ya ɗauki karkarwa, idanuwansa suka firfito yana kakari.

A hankali kuma idanuwan suka fara rufewa har takai ga ya daina sanin me ke guda na, daga nan ya ɓingeri kan amansa a sume.

Duk wannan abu da ya faru ga Malam Zaidu akan idon ‘Yar Wada ya faru.

Tsananin baƙin ciki da ƙunci dake zuciyarta shi ya hana ta taimakonsa, duk da ɗan tausayinsa da ta ji ya tsirga mata. ‘Lalle dole zan saka masa da mafificin alherinsa gare ni.’

Ta faɗa cikin zuciyarta tana mai maida dubanta ɓangaren kabarin da ya zubar da Malam…

A hankali ta tako zuwa bakin kabarin ta leƙa, “ba ni hannunka jarababbe wanda bai gaji arziƙi ba. Banda kana nemo mini tsiya uban me ya hanaka mutuwa? Fito! Ni nama fasa kashe kan” ta furta tana ɗan duƙawa saitinsa.

“Bazan iya ba ai kin ɗaure hannun cikin wannan farin abin da kika rufa mini, sanyin idaniyata…”

A fusace ta rarumi shebur ta niyyar ta ragargaza masa shi, kome ta tuna? Sai kuma ta aje ta miƙa hannayenta ta fara ƙoƙarin jawo shi waje. A hankali ta fara kwance ƙullin huhun goron da ta yi masa har zuwa lokacin da ta gama fiddo shi gabaɗaya.

“Ki taimaka ki kai ni asibiti hasken rayuwata, gubar nan tafara yi mini illa sosai… Ya furta da ƙyar yana kallon ƙwalelen kanta me kama da samirar aure.

“Ba ta ce uffan ba sai gaba da ta yi, da hanzari ya rarrafa ya miƙe tsaye, sai dai tafiya kaɗan ya yi ya yanke jiki ya faɗi yana yana kiran “Jesus.”

Ta juya da sauri zuwa gare shi, ta fara janshi yawa kayan wanki, shi kuma yana ta ihu jin yana ƙuƙƙujewa, a haka harta isa dashi zuwa gun akuri-kurar da tazo da ita, ta ajiye shi kujerar me zaman banza, itama ta shiga ta tashi motar cikin ƙwarewa ta harba ta kan burji.
*****

Tuƙin take, sai dai dukkan hankalinta ya koma kan rayuwarta kacakobda dalilinta nason kashe masoyinta don cikar burinta.

Maganganun Alhaji Labaran suka fara dawo mata cikin kunnuwa tamkar a sannan ya zuba mata su.

Idan har za ki kashe Chibunzu a daren yau, ki binne shi ba tare da kin damu da cewar shi masoyinki ba ne. To ni kuma na miki alƙawarin kashe shin daidai yake da cikar burinki na zuwa Makkah.

Ta kai dubanta ɓangaren da Chibunzu yake har sannan yana numfasawa kaɗan-kaɗan, numfashi irin na tsananin rabon zama duniya ko ana muzuru ana shaho. Bata san me zata masa ya mutu ba, ya faye taurin rai, ko kuma tsabar son duniya ke damunsa? Oho!

Ta ja wani siririn tsaki tana mai rage gudun da take yi cikin a kori-kurar ta. Wataƙil ta yi hakan ne dan tana tunanin zai iya ƙarasawa kafin ta kai Asibitin da ta dosa dashi.

Wa ce ce ‘Yar Wada?

Asalinta ‘yar cikin garin Kaduna ce, Mahaifinta Malam Na Allah baya da wata sana’a data fice dukanci. Su huɗu ne a gurin iyayensu, maza uku ne a gabanta, sai ita ta huɗu da haihuwar ta tsaya akanta. Akwai Ila da Sirajo sai kuma Yusifu da ita Saratu. Ana kiranta da Deluwa ne saboda maza ukun da ta biyo, shi ya sa ma sunanta na Saratu ya ɓace sai dai Deluwa. Wani abin mamaki shi ne, ita kaɗaice ‘Yar wada a cikinsu ita kaɗaice kuma kome na halitatta ya bambanta da nasu. Sai dai fa tun tana yarinya take da wani irin farin jini gurin jama’ar unguwarsu, hakan ne yasa ta yi ƙaurin suna wajen tsokana da neman magana.

Deluwa mace ce mai jin ƙarfi. Takan ɗauki jarkar ruwa biyu a hannunta takai gidansu idan ana wahalar ruwa. Tana da son taimakon iyayenta a wancan lokacin, sau da yawa ita kan bi mahaifinta gun sana’arsa ta dukkanci tana taya shi.

Tana da son ace ita kyakkyawace duk kuwa da uban munin da take dashi. Sai dai hakan bai hana wasu jama’ar su kirata da me kyau ba musamman saurayinta Chibunzu. Tsabar gayu ne yasa bata barin gashi ko ƙwal akanta, take aske shi tun mahaifinta na bugunta uwarta na zaginta har sun sakawa Deluwa ido ba yadda za su yi.

Idan aka matsa mata takance “Baba! Ku bar ni da kaina haka, ya za ai biri nabda gashi Ni da wasu ke kwatanta ni da biranya ace ina da gashi, ai gwara na bambanta da su ko? Baba, ni a guri na duk matar da ke barin gashi a kanta ba ƙaramar tantiriyar ƙazama ba ce.” Idan ta faɗi haka uwar kan rufe ta da bugu ta ce sai dai uwar ubanki ce ƙazamar!

Deluwa tun tana shekara Sha Biyu (12) a duniya take jin wani malaminsu ɗan Agulla a islamiyyarsu na basu labarin wani shahararren guri a _MAKKAH_ me suna _HAMMAM BUKHAR_ (wai a wurin ake maida tsoho sabo, fasonka ko ya kai wanda zaka zira kwandala biyar cikinsa, idan ka shiga gurin ka fito za ka ga ya goge tas! Kamar baka taɓa taka ƙasa ba)

To fa tun daga ranar Deluwa tunaninta ya koma yadda za ta je _Makkah_, tun iyayenta na ɗaukan abin wasa har lamarin ya fara shallake tunaninsu, abin har ya fara ba su tsoro kuma.

Kullum ta duniya zancenta ke nan, “sai na je _makkah_ na shiga
_hammam bukhar_ an rage min girman kaina an ƙara mini tsayi, sai na auri balarabe na haifi kyakkyawar ɗiya da shi. Wannan shi ne _Mafarkin Deluwa_ har kuwa a cikin barcinta shi zaka ji tana faɗi.

Nan da nan kuwa ta dage da neman na kanta, ita ce zuwa kasuwar bacci saro fari tazo ta soya su da mai. Haka za ta ɗauko a kanta tun daga Badarawa sai tazo kasuwar kawo, nan da nan ɗiyan yarbawa zasu siye, ta haɗa kuɗin tayo gida.

Idan yayin fari ya ƙare sai kuma ta koma haɗa maganin shawara dana basir tayo gammo shi ma ta bi kasuwa sai ta siyar. Gata da farin jinin sana’a ko wacce ta dosa bata faɗuwa. Kuma wani abin al’ajabin muninta shi ke kawo mata kasuwa sau tari gun jama’a. ‘Yan uwanta su yi ta mata dariya suna mata shaguɓen yadda jarin fara zai kaita ƙasa mai girma irin _Saudiyya.

Ila ya sha gaya mata, “Deluwa, ko filin jirgi kika je koro ki za’a yi _makkah_ ba ta irin mu ba ce, _makkah_ ta masu kuɗi ce, ke kuwa na tabbata ko da kuɗin, to billahilazi duk ranar da jirgi ya haɗa ido dake tarwatsewa zai yi, kina wahalar da kanki ne a banza! Babu balaraben da zai iya aurenki a duniyar nan ko shi ne muzuru saurin aure!” Takan ji baƙin cikin maganar Ila, wani zubin har kuka take yi, kafin kuma ta ji fatawar _Makkah_ ta mai rabo ce, idan Allah Ya yi ko akan jaki aje. Nan fa ta ƙara jin ƙwarin gwiwa. Akwai fa tauhidin _makkah_ kiran Allah ne, dan har a allo ta rubuta wannan da tawada ta shanye dan kar wataran imaninta ya ruguje, ta fara jin ba za ta iya zuwa ba.

To, a irin zuwa tallan tane ta haɗu da Chibunzu sai dai, shi Addinin kiristanci yake bi.

Chibunzu kyakkyawa ne son kowa ƙin wanda ya rasa. Shi ya fara ɗaukarta ta dinga taya shi tuƙin akori-kura, sukan ɗauko kaya daga wannan kasuwa su kai wancan kasuwa. Anan ma tana samu dashi sosai, dan ta wannan hanyar ta fara tunanin lalle burinta zai cika, ga wani abin mamaki, yadda ƙafar Deluwa ke kaiwa gun burki, takance wannan duk wata alama ce, na ita ɗin ‘Yar baiwa ce.

Chibunzu yana tsananin son Deluwa, shi ba abinda ke burge shi irin tsinin mazaunanta da mini-minin ƙirgar danginta masu kamar an mulmula hura. Ya sha yi mata alƙawarin zai siyar da Akuri-kurarsa ya bata kuɗin ta tafi _makkah_, ba shida burin da ya fi ya auri Deluwa duk kuwa da ‘yammatan dake sonsa yan uwansa arnaku, ya kwance musu ba su san sirrin da ke cikin auren wadanni ba ne. Shi fa kullum zancensa akan ta amince su yi aure ne, shi kuma zai kaita _makkah_ko ta halin ƙaƙa, sai dai ta ƙi yarda da zancensa har zuwa lokacin da Alhaji Labaran ya kira ta da ƙudurin shi na son ta kashe mishi shi.

Shi kuma zai saka mata da zuwa _makkah_ ba tare da sanin dalilinsa ba ta amince har ta yaudari Chibunzu ta bashi wata guba ya yi dogan suma ta ɗauko shi zuwa maƙabartarsu Malam Tsalha.

A sannu ta sake maida kanta ɓangaren da Chibunzu yake numfashinsa sama-sama. Sai taji wani tausayinsa ya tsirga mata a zuciya. Tabbas ko babu soyayyarsa a ranta to fa akwai shaƙuwa mai girma.

ALLAH Sarki masoyina_… Ta furta tana mai ɗora guntun hannu gefen fuskarsa. “Duk ranar da naje Makkah na auri balarabe na maka alƙawarin zan gudu da cikin ɗiya ta, bayan na haife ta sai ka dawo addinina mu yi aurenmu. Kai kaɗai ne masoyina na gaskiya, bazan kashe kaba, lalle babu me ɓoye mini kai sai wancan Malamin. Zan maida kai gare shi ya aje mini kai har zuwa sa’adda zan dawo. Ka yi haƙuri ba laifina bane, laifin zuciya tane…”

Ta furta tana mai ƙoƙarin tsayawa a kofar wani ɗan ƙaramin Sha Ka Tafi…

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mafarkin Deluwa 1Mafarkin Deluwa 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×