Skip to content
Part 4 of 9 in the Series Mafarkin Deluwa by Fulani Bingel

Ba ga su Malam Idi da suka sandare a wurin ba, har wasu yara da ke wasa a ƙofar gidan firgitaccen ihun kukan ganinta suka fara musamman jin yadda Malam Tsalha ya fara faɗin “gata nan jama’a!” Yana ƙoƙarin tashi zai ranta ana kare, sai dai tafiya tare gagare shi sai rarrafe ya kama yi ya shige zauren gidan Malam Zaidu.

Malam Idi da Malam Lawal suka rufa masa baya yayin da suka yi fatali da kwanon abincin dake gabansu, suka bar Malam Zaidu zaune ya zuba mata ido da alamun mamaki a fuskarsa.

Abun ya bawa Deluwa wani irin mamaki na ganin yadda jama’a ke ta ɗibar gudu akanta.

Wani irin baƙin ciki take ji na shigarta, duk farin jininta duk ɗaukakarta a unguwarsu wai ita ce yau jama’a ke gudu akan ganin halittatta har ana ƙin yarda da rantsuwar da tayi na cewa ita ba fatalwa ba ce? Tunaninta ya tafi da nisa…

Ta tuna sa’adda aka saka ta primary yadda yara ke ƙin zama kusa da ita, da yadda ba a karɓar ko abin hannunta, a sannan ba ta damuwa, yaro ma ya faye kallonta fashewa take da kuka ta yi ta jibgarsa sai malamai sun raba, ta tuna a cikin ajinsu akwai yaro me ido ɗaya, babu mai takura masa, akwai wani me jan gindi, malamin ajinsu har sweet yake ba shi, to ita shin menene aibunta da ake gudan halittar, halittarta ta zama abin dariya ga wasu jama’ar.

Menene aibun ƙasancewarta a ‘Yar Wada?

Me ya sa ake muzantamu da aibantamu haka? A cikin ranta ta ce,

Lalle yanzu lokaci ne da mu wadanni za mu tashi tsaye mu gyara duniyarmu.

Ban taɓa jin wada sarki ba.

Bantaɓa jin wada gwamna ba.

Bantaba jin wada ya zama wani babban mai faɗa aji ba a duniya.

kullum mune a ƙasƙance abin dariya da zunɗe ga wasu jama’ar.

‘Ni Deluwa ‘Yarbadukku daga yau na sha alwashin sai na zama wata a duniya, sai na ɗaukaka ‘yan uwana wadanni, sai mun mamaye duniya da irin tamu baiwar da Allah yaba mu…’

Ta goge zafafan hawayen dake bin tiƙa-tiƙan kumatukanta tana fatan wataran ta goge irinsu na farin cikin ɗaukakarta a rayuwa. Ta juya da sauri za ta koma motar ta ji an riƙe hannunta. Ta ɗago kai tana kallonsa, girgiza mata kai ya yi, yana mai nuna mata ɓangaren da Malam Zaidu ke tsaye yana kallonta, a hankali Malam Zaidun ya ƙaraso gareta.

“Deluwa? Allahu Akbar kabeeran!…” Cike da mamaki a fuskarsa ya ci gaba. Yanzu dama ke ce kika zo maƙabartarmu jiya?

“Eh nice Malam, ta furta da rarraunar murya.”

Wani tausayinta ya ji ya tsirga masa, tabbas an tafka abin kunya, ɗiyar abokinsa suka riƙa kira a matsayin fatalw, shi kwata-kwata bai gane taba duba da ya shafe shekaru huɗu rabon da yaje gidansu, iyakarsa da babanta su haɗu a kasuwa duk sati.

Amma me ta zo yi da gawa a wannan daren? Ya tambayi kanshi, kana ya riƙo hannunta yana faɗin zo mu shiga daga ciki. Duka suka ɗuru ciki har da Chibunzu, anan suka tadda su Malam Tsalha sun rufe ƙofar daga ciki… Sai da ya yi magana tukunnu suka buɗe suna rarraba ido. Babu ɓata lokaci Malam Zaidu ya larabta musu matsayinta gurinsa, duk kunya ta kama su musamman Malam Tsalha, shi ne ya yi ƙarfin halin tambayar abinda za ta yi to da gawa a wannan daren.

Anan ne ta larabta musu kome da ƙudirinta na son su riƙe Chibunzu gunsu zuwa lokacin da zasu ji labarinta cikin jirgi su sake shi…

Shi ma ta ƙara jaddada masa da ya yi hankali da Alh. Labaran bata san me ke tsakaninsu ba, amma ransa yake so ba kome ba…

Nan dai duk ta faɗa musu kome, ƙarshe kuma ta yiwa Chibunzu alƙawarin aurensa bayan ta dawo daga Makkah.

Anan suma suka amsa mata akan za su tsare shi har zuwa bayan tafiyarta, suka kuma yi mata faɗa akan ƙudurin da ta yi a baya na kashe Chibunzu domin cikar burinta… Nan dai suka rabu da alƙawarin idan ya zamana saura kwana ɗaya ta tafi za ta zo gun Chibunzu su yi sallama…

Shi dai ɗan kyakkyawan saurayin daba

wadatacciyar lafiya ta ishe shi ba lokacin baice uffam ba sai kallonta da yake ta yi kwalla na cika masa ido yana tunanin rabuwarsa da masoyiyarsa Deluwa.

Deluwa A Gidan Alhaji Labaran

Bayan Deluwa tabar wajensu Malam Zaidu, kai tsaye gidan Alhaji Labaran ta yiwa tsinke. Tana zuwa ta ci sa a kuwa Alhajin na gida, ba ɓata lokaci matar Alhaji ta sauke ta a babban falonsu.

“Ah! Deluwa ke ce da daren nan”

Cewar Alh. Labaran.

“Eh! Yallaɓai, kasan da zafi-zafi akan bugi ƙarfe.”

“To ɗan ba mu guri Hajiya,” ya faɗi yana kallon Matarsa da ta kame kan kujera, ba ta ce kome ba, ta miƙe ta shige ɗakin dake kusa da ita.

Ya kai kallonsa kan Deluwa , “fatan sai da kika kammala aikina sannan kika zo nan ɗin?”

Ta yi wani ɗan bushashshen murmushi tana kallonsa ta ce,

“Alhaji komai fa ya kammala, yanzu haka Chibunzu ya daɗe da garzaya wa barzahu.”

Ya washe jajayen hakoransa yana murmushi.

“Ho! Deluwa aikinki ya yi kyau, lallai yau na ƙara tabbatarwa kina son zuwa Saudiyya, tunda har kika iya kashe babban masoyinki.”

“Hmm! Alhaji ke nan, Masoyi ai bai da amfani in har babu cikar buri!”…

“Sai dai akwai wani abu da nike son sani daga gareka, wai dan Allah Alhaji me ya…”

“Dakata Deluwa!” Yai saurin katse ta idanuwansa na nuna alamun gargaɗi.

“Idan na saka ki aiki, bai zama lalle sai kinsan dalilina na yin hakan ba, tunda ko har kika gama yin abin da na saka ki, to ki sha kuruminki alƙawarin da na ɗaukar miki dole zan cika shi yanzu, tunda kika biyan buƙata ba tare da wata matsala ba, to tabbas ni ma zan cika maki dukkan zancena, ke kima ƙaddara cewa _Makka_ kaman kin tafi ne, waɗanda ke can kawai suka riga ki zuwa, kinga ma an kusa buɗe Hajji, dole gobe zan tura ki da Shaddadu Direba, kuje ku yi fasfot, da yardar Allah nan da sati uku an gama kome. Wane suna Hajiyar za ta saka ne a can?” Ya dan numfasa yana mata dariya.

Ta washe wargajejen bakinta, wanda ƙila a zaton ta murmushin da zai kashe Alhajin ta yi.

“Deluwa Malam Na Allah, yallaɓai, ai shi ne sunan da a kafi sanina da shi”.

“Shi kike sakawa a Makaranta?” Alhajin ya ƙara tambayarta.

“A’a, da Saratu Idriss nake amfani” ta faɗa a gaggauce.

“Hajiya Deluwa, in kun je can, ki yi amfani da sunan Makarantarki.”

Ta ƙara faɗaɗa murmushinta, “Haba Alhaji kadaina fasamun kai mana, “Hajiya Deluwa!”, ta ƙara maimaitawa, “Wallahi baka ji yadda sunan ya yi dadi ba.” “A’a, Hajiya Sarah za a CE.” Sai kawai ta ƙara fashewa da dariyar da ta firgita jinjinrin Alhaji da ke barci a d’akin da Mamansa ta shiga.

“Tashi haka Deluwa na sallameki sai kinjin tashi.” Alhaji ya fad’a kagauce yana duban k’ofar d’akin.

Bayan ta koma gida ta shaidawa Mahaifanta dukkan abunda ke faruwa.

“Ke Deluwa ki rufawa kanki asiri, muna zamanmu lafiya kije ki dauko mana fitina” cewar mahaifinta,

“Haba baba Wallahi babu abunda zai faru da yardar Allah, kudai ku tayani addu’a kuma ku kama bakinku, kaman ma bakusan meke faruwa ba, ta kara da cewa,shi dai Idan takamarsa zalunci to yau yagamu da gamonsa”

Hakan dai badan sunso ba suka rabu da ita.

Bayan kwana goma sha biyar, Alhaji hafizu yasa akai masa kiran Deluwa,ya shaidamata cewa ya kammala komi na vizar ta, Harma zata fito washegari, yanzu kawai ta je ta had’a dukkan shirinta, don ako wane lokaci zai iya kiranta ta tafi.

DELUWA A FILIN JIRGI

9.

“Ki zama mai Amana a duk inda kika sami kanki.

karki zama mai daukan kanki fiye da kowa wannan na cikin dabi’a A bar k’i.

Ki zama mai bin na gaba dake koda kuwa ya miki rashin kyautawa.

Ta hakane kurum dukkan wani burikanki zasu cika.

karki zam mai mugunta, kibi komi a sannu, sai ki ga komi ya zame miki sau’kau’ka. Ba a samun duniya da garaje Deluwa, komi ga yadda ka daukeshi a hakan yake zo maka. Ki guji k’arya domin ita ke saurin ruguza rayuwar bawa, tafi abinki Deluwa Allah ya cikamiki burinki !”

Wannan itace nasihar da Tsohon Deluwa ya mata a lokacin da ya zamana saura

kwana d’aya ta tafi, tayi sallama da iyayenta da zummar zata wuce kano gidan wata ‘kanwar mahaifiyarta takwan, wanshegari kuma ta tafi zuwa filin jirgin Malam Aminu Kano.

Kai tsaye data fito daga gidansu bayan tayi sallama da mutanen Unguwarsu,

wasu dayawa suna kukan rabuwa da Deluwa, musamman yayanta Ila da kyar ya

rabu da ita lokacin, haka nan dai zuciya ba dadi ta rabu dasu, sai ta yiwa MARABA

tsinke gidansu Malam Zaidu, su kansu sunyi jimamin tafiyar karshe dai sukayi mata fatan Alheri. Malam Tsalha keda karfin halin yi mata sautun Jallabiyya mai fiffike in zata komo.

Tsaye take ita da Masoyin ta Chibunzu kuka yake kamar ‘karamin yaro koda dai bai

cika shekara Ashirin da biyar ba, amma soyayyar Deluwa ta maidashi yaron gaske, Sai ga Chibunzu harda sharce majina, gwiwowinsa a kasa yadda tsayin nasu zai

zama daya, yana rokon Deluwa da ta ri’ke amanarsa karta gujeshi.

Ranar farko da Deluwa taji ‘kaunar Chibunzu marar Algus ta tsirgamata har zuciya, lokacin tai duba zuwa kyan da Allah ya bashi tamkar yayi kansa, tana mamakin Abinda Chibunzu ke nema gareta, duk wadannan dogayen kyawawan ‘yammatan dake bibiyarsa, kamar ta manta Allah shike sallad’a dukkan al’amura cikin karfin ikonsa da buwayarsa.

Lalle soyayyar Chibunzu gareta daga Allah ne, duk da ya kasance Arne marar Addini. Ta sami kanta tana mai share mai hawaye da ‘yan guntayen hannuwanta…

Zuciyarta ta karye wani irin shaukin son Chibunzu ke shigarta, fashewa tayi da kukan itama hade da d’ora faskeken kanta kan kafadar Chibunzu.

Masoyan biyu an rasa mai rarrashin wani cikinsu, sai da Malam Zaidu

dake tsaye gefe yana sharar kwallar tausayi, gami da wani tunani na daban a zuciyarsa, tabbas akwai alamun Chibunzu zai iya zama mai Addini d’aya da Deluwa, ya matso ya janye Chibunzu da alamun su wuce gida haka ya tafi yanata waiwayen Deluwa itama tana wai wayensa har suka shige cikin gidan.

DELUWA A?

Tunda dan Takzi ya aje Deluwa

filin jirgin Malam Aminu kano mutane keta kallonta suna mata dariya ba komi

ya jawo haka ba sai irin shigar data yiwa jikinta, riga da wando na atamfa ta saka ta

dauko wani bakin tabarau ta rufe idanuwanta, haka takalminta sandal ta tasaka irin

wanda mata da maza na sakawa ta dauko wani dan siririn mayafi ta rataya a

wuyan ta kalar atamfar. Kanta da yasha Askin baratolli ta shafeshi da mai sai kyalli

yake da walkiya.tana ta taunar chingam abinta had’i da jan troly na kayanta.

Bata wani damu da dariyar mutanen ba don ta saba itama, layin tantancewa tabi, haka dai taita

kwaikwayen mutanen dake gabanta har zuwa lokacin da ta gama komi itama ta

shiga wurin jiran sanarwar tashi.

Karfe 9:30

jirgin yazo karfe 10:00 Deluwa na cikin jirgi zaune kan kujerar tana ta lissafin

kujerun ciki a zuciyarta, har lokacin da akayi sanarwar a kimtsa a daura belt jirgi zai

tashi a kashe waya banda kunna taba dai-dai sauran sanarwar da akayi cikin

harshen turanci da Larabci, ga Deluwa ba tajin ko Alif daga ingilishin har larabcin, barta dai da wayewa irin ta rayuwa.

Don haka takara kishingid’a tana jin sanyin A.C na shigarta. Cikin hakan wata ‘yar yaloliyar budurwa mai fantin ‘yar tsana a fuskarta dake aiki cikin jirgin tazo wucewa kusa da kujerar Deluwa data lura barci kamar take sai ta matsa tana fadin

“YA WALAD INTA DAYR TANOUM ?”(yaro barci zakayi ne ?)

Deluwa tai sororo tana dubanta…

Deluwa tai sororo tana duban yar balarabiyar da bata san yarenta ba

don haka tai shiru.

Yar balarabiyar ta saka hannunta ta jawo belt ta daurawa

Deluwa gami da dan shafa faskakareren kanta tana murmushi.

Deluwa wani dadi ya kasheta, ta tuna lokacin da take mafarki tana gaisawa da turawa yau gashi har balarabiya na shafa kanta takai hannunta dai-dai inda balarabiyar ta ta6a, ta shinshina hannunta hadi da ambaton kanshin larabawa daban yake a ranta.

Lokacin jirgi ya fara jangwal-jangwal ta rike hannun kujerar sosai hadi da

runtse ido tanason tuno addu’ar zama cikin jirgi ta gaza, sai dai ta hango kanta

tamkar balarabiya lokacin da ta fito daga HAMMAM BUKHAR, harta fara lissafa

mazan da zata yaudara ciki kuwa Harda SHRUKHAN na kasar India…

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mafarkin Deluwa 3Mafarkin Deluwa 5 >>

2 thoughts on “Mafarkin Deluwa 4”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×