Yaron mai dogon ƙeyar ne ya fara sawo kai, tukun na ɗan matsakaicin balaraben ya biyo bayansa.
Ta sau baki tana kallonsu har zuwa sa’adda Bukr ya yi musu mazauni bisa doguwar kujerar dake ɗaukan mutum biyu, wacce aka aje ta a ɗakin saboda irin baƙin nan. Cikin takunta na Wadanni itama ta ƙarasa bisa gadonta ta zauna, ga mamakinta sai ta ji wani baƙon lamari na ziyartar ta sa’ilin da wata zuciyar ta bata umarni data ɗora guntuwar ƙafarta ɗaya bisa ɗaya, lalle hakan zai ja mata matsayi musamman lura da ta yi da fuskar shanun da kyakkyawan balaraben ke yi, ƙila ma shi ne mai Funduk ɗin ya zo ya mata tambayar ƙwaf, a hankali ta jawo guntuwar ƙafarta ta ɗora ta bisa ɗayar, ta ɗago da fuskarta kunshe da murmushi ta ce,
“Sannunku fa!”
Wani ruwa ne me shegen ɗumi ya ji yana kwarara a gadon bayansa, da hanzari ya waiga ɓangaren Bukr sai dai bai jin yaron ne ya yi wannan kuwwar, ya ƙara juya kansa ɗayan gefen da fatan nan ɗin ya kasance zatonsa, sai dai kafin ya idasa tantance kome ya ƙara jin kuwwar “ga ruwa Yallaɓai!”
Ta furta sa’ilin da take aje masa tambulan ruwan bisa ɗan teburin gabansa. Dariyar da ya ji an fashe da ita ne kusa dashi ta yi ƙoƙarin dawo masa da tunaninsa dake neman tserewa, “Ukhtee ba fa yajin hausar da kike ta yi masa,” sai kuma ya maida kallonsa kan Annur.
“Akhee ittfaddol moya.”
Tsawon mintina goma suka shuɗe bata ji mutumin da Bukr ya kira shi da baƙonta ba ya tanka, cikin minti goman nan tsakaninta da Bukr suke yin magana itama kan wani abun ne da bata idasa ganewa ba, tana son tace masa Bukr wai waye wannan ɗin, sai dai tana ganin kamar kar ace ta faɗo, ta yi shiru tana mamakin yadda yau take ƙoƙarin komawa ɗabi’ar wata doguwar ƙawarta Batula, na yanga.
‘Sai dai fa wallahi na fara gajiya’ Ta furta a ranta, ‘idan ma mai Otel ɗin ne shi, ai ya yi magana in cikon kuɗi yake bina ai sai na bashi haka kawai sai…’ ta ɗago da sauri sa’ilin da taji muryar balaraben yana ambaton.
“Ya Bukr…”
“Ya Bukr…”
A yadda ta kula kamar balaraben yana ma yaron magana ne cikin lallaɓi, sun daɗe suna dogon larabcin da bata fahimta, tukunna taga Bukr ya ɗago yana kallonta fuskarsa cike da alamun tsoro.
“Ukhty umm…”
Ya fara inda-inda. Ita kuma ta sake gyara zama yatsunta sarƙafe da na juna.
“Ukhteee kinga wannan yaya nane sunansa Annur, ya ce in faɗa miki yana sonki, kuma wai so yake yi kuyi aure yaumal arbi’a, kuma wai…”
Ya yi shiru ganin ta miƙe tsaye zumbur! Jikinta na rawa.
“Me ne kake cewa?” Ta furta da muryar da bata tantance tata ce ko ba ta tata ba ce.
Bukr ɗin ma ya miƙe kamar mai shirin arcewa a guje.
“Cewa ya yi aurenki zai yi nan da ranar lara…”
“Kai dillah dakata!” Ta katse shi da tsawar da sai da kofin tangaran ɗin da Annur yasha ruwa ya motsa, yaron ya sake zabura yana dubanta, yana kuma duban Annur daya ɗago ido jajur.
“Me kake faɗa mini ne wai kamar kana magana da abokinka na wasa, kamar tsohuwarka na maka tatsuniya, yaro idan fa kana kallona guntuwa, to wallahi na haife ka da haihuwar zan yi, shi wanene yayan naka a ina ya ganni, yaro wane ya ce maka aure na zo yi garin nan ma? Wai wane irin so kake faɗi, kai a shekarunka har yaushe kasan so, to ko a garin mahaukata nake ne kai wai ka tabbatar saudiyya ce nan din? Banda hauka bansan mutumin ba kawai ka zo kana maganar aure, anya?”
Ta yi shiru tana maida numfashi, tana jin tunda uwarta Ladiyo ta kawota duniya ba a taɓa cin mutuncinta irin yau ba. Yaron ya juya yana kallon Annur kamar zai fashe da kuka, a hankali ya ƙara maida kallonsa ɓangaren Deluwa.
“Wallahil Azim Ukhtee haka ya ce mini yana sonki, kuma wai so mai tsanani. Ni bansan inda ya ganki ba, tun jiya dana ganshi cemin ya yi ya sanki fa, uqusum billahil azim ana ma bi kazzib alaiki…”
“Kazib ɗin ta ci ubanta, na ce ka ci ubanka Yaro, so me tsanani ko? Shi tsananin ya ci gwafar ubansa!” Sai kwalla sharrr! Ta koma gadonta ta zauna daɓas ta maida ƙafafuwanta yadda suke da, ji take kamar ba a taɓa ma yaudararta da kalamai masu daɗi da suka ba irin yanzun da gaske ta fara tunanin mahaukaci ne wannan mutumin, to ina ya santa?”
Bukr ya matso kusa da ita ya sunkuya yana kallonta.
“Ki saurare shi ki ji inda ya sanki Ukhtee, da gaske yake sonki fa. Ya rantse fa da Allansa, wallahi ba mahaukaci ba ne.”
A hankali ta sauke ƙafar data ɗora bisa ɗayar tana duban yaron na tsayin mintuna, ta sani idan Allah ya yi nufinsa sai kaga falwaya ta yi ganye, amma itan ta gaza gane ta inda lamarin nan zai zama gaske, wai fa balarabe ke sont ko? Ta saje yin tsuru, can kuma ta nisa tana mamakin jin ta fara yarda da batun, ta yi duba ga ɗan Balaraben a fakaice, taga ya sunkuyar da kansa kamar yana cikin damuwar kar ta ƙi amsar tayinsa, kai ita fa sai taga kamar har irin ramar nan ta masu ciwon so ya yi, ‘Allah sarki, ko tun dirata ƙasar ma yake dakon so na?
Oh Allah! Ƙila tun a cikin Airport na fara sace masa zuciya’. Ita kaɗai ta fara jin wani irin sanyi yana ratsa ta, ta ɗan mintsini kanta, “kai anya ina da rai kuwa?” ta furta a zahiri sa’ilin data kai kallonta gefen gadonta ta yi arba da tabaronta, “Eh lalle ina da rai, tunda a lahira kam ai bazan ga tabarau na ba, amman me ke faruwa haka wai? Ni, ni Deluwa Yar Badukku?” Ta wage wargajejen bakinta sa’ilin da takai hannu bisa baratolinta ta shafo a nutse don ƙara tabbatarwa, bata san sa’adda bakin ya idasa wagewa da alamun murmushi ba, Bukr dake bin ta da kallo ya yi saurin sunkuyar da kansa a zatonsa hamma take.
‘To amma shi kuwa mai ya gani gare ni, kai wai ma…?”
‘Shi Chibunzu mai ya gani gareki da ya nace miki?’
‘A jininki ne, baiwar A jikinki take!’
Ta ji wata zuciyar tata na ba ta amsa, ta kuwa miƙe da sauri, sai kuma ta ƙara komawa dabas tana zare ido.
Ki zama mai Amana a duk inda kika samu kanki.
Nasihar tsohonta ta farko ta faɗo mata tana gabda amsar tayin balarabenta. Ta runtse ido da sauri tana hango lokacin da shi kanshi Chibunzun ke jaddada mata riƙon amanar, ga mamakinta sai ta ji duk wani ɗoki na sakinta, lalle riƙon Amana abune mai wahala, amman kam idan har kayi shi daɗinsa baya taɓa gushewa.
‘To amma ai ina da damar da zan auri wannan ɗin tunda shi ya ce yana sona, idan ya so daga baya ba sai na koma na auri masoyina Chibunzu ba, shi ke nan ma ina haihuwa da balaraben sai na gudu da abinda na haifa, nasan dole zai yi kyawun shi, idan na koma kaduna dashi ƙila har ya’yan Gwamnamu zasu na zuwa kallonsa saboda kyawu, ni kuma da haka sai na tara abinda zan cika burina kan Wadanni’ ta faɗi a zuciyarta tana mai ɗora hannunta bisa haɓarta, da alama tunanin nata na mugun mata daɗi.
‘To kuma idan kika haifi mai kama dake fa? Ta yi saurin gintse fuska kamar tana magana da wani. Haba dai, ai a gidanmu ma ni kaɗaice Wada, kai Allah Ma ya kiyaye ko da nike Wada ai bazan…’
“Ukhtee kin yi shiru,” Ta yi firgigit tana kallon yaron, sai kuma ta yi saurin yin murmushi.
Cikin nutsuwa ta maida kallonta kan ɗan balaraben da har yanzu kansa ke sunkuye kamar baya jin ciwon hakan, sai kuma ta wulƙila mitsi-mitsin idanuwanta da alamun fari take masa.
“Ba kome Bukr, ka gaya masa zan yi tunani kawai, duk yadda ake ciki zuwa ƙarshen watan nan za ku ji ni”. Yaron ya zaro ido yana kallonta da wani irin mugun mamaki.
“Ukhtee tunani kuma? Shifa yaumul Arbi’ah yake so a ɗaura muku aure.”
“Da yake na yi maka kama da dajajah? Na ce da kaza na maka kama da daga zuwan mutum zan aure shi ba tare da kowa nawa ya sani ba? Na ce maka ka ce masa zan yi tunani kawai, ai ban ce na amshi tayin ku ba.”
Ta furta tana mamakin yadda yau ta ji kamar tana kashe murya tana rangwada da karya harshe cikin zancenta.
*****
“Tirƙashi! Wai ni wannan abun zai jama aji? Wallahi Abuya ga Bukr ka tambaye shi, cewa ta yi wai sai ta yi tunani nan da (nihayil shahar) sannan za ta neme mu fa.” Annur ya furta muryarsa na karkarwa tsabar ɓacin rai.
“To na faɗa maka ba haihuwa ba, ko duniya za ta kawo mini ba na ƙara komawa wannan Abun.” Ya mula ya ƙara mulawa kafin ya sunkwi da kai a hankali hawaye ke sauka bisa kuncinsa na tsananin tozarta da ya ji ya yi, tunda yake a rayuwarsa bai taɓa shiga wannan musibar ba sai da ya haɗu da Abuya. Wai shi ne yau don yana son haihuwa gun abinda bai fi ya latse da motarsa ba, ke ja masa rai? “Sai na kasheta!”
“Ashsha!” Abuya ya furta fuskarsa cike da murmushi mai shaƙarwa.
“Kana son ɓata ƙaddararka in har ka ce zaka yi wani mugun abu kan abinda aka riga aka rubuta maka. Ban taɓa gaya maka ba, amman yau zan faɗa maka. Wannan matar taka da kake cewa Abu, ko da baka aureta ba, lalle sai jininka ya fita daga jikinta ta kowacce irin saɗara, don haka bazan daina baka haƙuri ba, daga nan har zuwa ranar da zaka ga ɗanka, ka yi haƙuri lamarin mata haka yake, kar kuma ka manta itace uwar da za ta sama ma dukkan farin cikinka…”
Ya ɗago cikin zafin rai yana duban tsohon, “Farinciki fa ? Farinciki gun abun nan, wai to…?
Kuka ya ƙara ƙwace masa, Bukr da hanzari ya tashi ya yi waje, shi yarintarsa sam bata bari ya gane dukkan zancensu ba, “Me yasa Akhee ke kuka?” Ya furta sa’ilin da yake share nashi hawayen da baisan dalilin zubowarsu ba, kila na ganin dan uwansa nayi ne.