Skip to content
Part 19 of 28 in the Series Mai Daki by Hafsat C. Sodangi

“Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un.” A bayyane na furta saboda firgitan da nayi. Saki kuma?

Wannan wacce irin musiba ce?

Na kalli Ahmad wanda har yanzu yake a yadda na same shi, sannan na kalli Hajiya. Kamar kullum tana zaune ne a kan dardumarta ta sallah, sanye da zurmemen hijabinta. Zan iya cewa a tsawon zaman da nayi a gidan na watanni ashirin ban taba ganin ranar da na ganta babu hijabinta ba.

Sai nayi sha’awar ace ita din mata ce mai sassauci da rangwame a kan al’amuranta, tunda kowa ya shaideta mace ce mai yawan Ibada.

To me yasa ita din halinta ya zama haka. Danta da yake matukar kokarinsa wajen ganin yayi mata biyayya ya kaucewa bacin ranta ya batawa wanda ya bata mata.

Danta da a kullum yake fadin irin alherinta da dawainiyar da tayi da shi wajen ganin bai yi maraicin uba ba.

Danta da a kullum yake fadin cewa ita ce abinda ya fi so da girmamawa a duniya shi ta ke yi wa irin wannan kuntatawar da kuma rashin sassauci?

Lallai halinta sai ita. Take na fara kokarin rarrashin zuciyata don ta samu sassaucin tsananin da zata fuskanta a gaba.

Na rinka tunanin abubuwan da zan
yi wadanda za su taimaka mun a rayuwata da zan shiga nan ba da dadewa ba. Tunda nasan babu makawa Ahmad zai aikata abinda Hajiya ta umurce shi tunda da bakinshi ya tabbatar mun cewa ita din bata taba bashi wani umurni da ya ketare ba, face ya aiwatar da shi komai tsananin shi.

*****

Ina kwance a kan shimfidaddiyar katifata da ta sha lallausan shimfidan zanin gado na yadin (American bed sheet) dan asali da bargonshi.
Na kai hannu na shafa yadin zanin gadon tare da tuna ranar da na fara
shimfida shi a kan gadona, lokacin da nake ganiyar cin amarcina a gidan Ahmad. Na runtse idanuwana da karfi saboda wasu tunane-tunane da suke ta kawowa zuciyata ziyara.

Tunanin abubuwan da suka zo suka kuma wuce tamfar a mafarki tamfar dai ace wani barci kawai nayi mai dadi na kuma farka.

A da can, ban taba tunanin haka al’amurana za su kasance ba. A matsayin shekaruna a yanzu ashirin da uku kacal a duniya. Amma har an fara kirga mun aurena. Yanmata da yawa sa’o’ina ba su ma yi auren ba, ballantana har ace ya kare.

Take kuma nayi hanzarin yin Istigfari da na tuna akwai wasu mata kuma da suke zuwa duniya su gama rayuwarsu a cikinta su koma ga mahaliccinsu ba tare da sun yi auren ba.

Don haka ba zai yiwu nayi wa Ubangijina butulci ba, a kullum zan kasance mai yawan godiya a gare shi bisa irin yawa-yawan nimomin da ya yi mun a rayuwata.

Ban kuma dauka wannan mummunan jarrabawa ba ce sai na dauka cewa ni kuma tawa kaddarar kenan ba kuma zai yiwu na tsallake wata kaddara tawa ba face kawai na roki Ubangijina da kowacce ta tashi zuwa mun, to ta zamto mai sauki.

Ya kuma ba ni ikon dauka don Imanina ya zamto cikakke tun da aan gaya mana cewa Imaninmu ba zai cika ba sai mun yarda da kaddararmu ta alkairi ko wanin alkairi.
Bai kuma jarraba ni da ciwo ba ko wanina ko kuma ya jarrabe ni da rashi na wata gaba a jikina ba.

Sannan da aurena ya mutu a farko sai ya bani wanda ya fi mun na farkon, to ina rokon shi a yanzu ma ya bani wanda ya fi mun na biyun. Sai dai tunanina yana kawowa daidai nan sai naji gabana ya yanke ya fadi ras!

Kenan na rabu da Ahmad ba zan sake komawa gidanshi ba? Ina son mijina shima kuma yana sona. Mahaifiyarshi ce matsalarmu, don kuwa idan ba don shigarta cikin lamarin ba to don ta ya’yanshi zan iya zama da su a yadda suke, tunda ina son ubansu.

Sabanin matsalata da Ishak wanda a lokacin da aka yi aurena da shi shekaruna goma sha bakwai ne a duniya.

Ba komai yasa a ka yi auren ba face rashi da mahaifina yake ciki ga kuma kwadayinshi a kaina na ganin ni din nayi karatu.

Ya dauke ni ya ba shi ni ba tare da wani dogon nema ko bincike ba, saboda jin irin alkawuran da yayi a kaina. Alkawuran da suka zamo shi ne sanadin faruwar auren da kuma rugujewarshi.

Idan kuma da ace zaman da yayi da ni akwai adalci a ciki ko kuma sassauci ko tausayawa wadannan abubuwa sune suka hadu suka zamo soyayya da kauna to duk da da sauki.
Idan har akwai abinda nake tunawa da Ishak da ke sake sani kin shi to bai wuce dukan rashin tausayi da yake yi mun ba.

To sai na auri Ahmad, mutumin da ya ban yanci na walwala. Nayi rayuwar aure irin wacce ban taba mafarkin ana yin irinta ba a gidan aure.

Saboda irin sona da tattalina da mijina yake yi. Ya nuna mun cewa ni din ina da matukar muhimmanci a wurinshi.

Ya kuma so ni so na hakika, ya mutunta iyayena da yan uwana, ya guje mun bacin raina, ya tattali farin cikina.

Amma sai gashi ‘ya’yanshi da mahaifiyarshi sun ki yarda su bar ni na zauna da shi duk da hakuri da halinsu da nake yi.

Idan har ina da laifi ko kuma wani ganganci da na aikata a lokacin da aurena na fari ya mutu, to a wannan karon kam nasan ba ni da wani laifi.

Sai dai na kasa hakura, fatana bai wuce da ni da shi mu samu maslaha kan al’amarin aurenmu ba. Tunda dai an yi sa’a saki daya ne a tsakaninmu.

An kwaso kayana tas daga gidan Ahmad, ba wai don na hakura da zama da shi ba. Sai dai kawai don jiran shawarar da shi da kanshi zai zartar a kan maganar.

Sakon da ya turo mun kenan a waya daren da na dawo gida. Cewa na saurare shi kan shawarar da zai yanke na neman mana mafita nan da kwanaki uku.

Sai kuma kudi da suka shigo account dina masu auki. Ta bangaren Babana dai abin ba a cewa komai, don kuwa bakin cikinshi ba ya’ misaltuwa.

Umma kam har a wannan karon ba ta ce komai ba, harkokinta take yi. Nayi matukar kokarin ganin ban takura kaina da tunane-tunane ba, ta hanyar shiga duk wani hidima na gida da ake yi. Har girki na karba ni nake yi da sassafe kan bakwai zuwa bakwai da rabi na kammala abin karyawa. Idan na gama kumana zauna taya Umma saye da sayarwanta, muna kulla na kullawa. Babbar matsalata ba ta wuce na rashin barciba. Sai nayi matukar sa’a ne kwarai nake samu na dan runtsa.

Al’amurana ne kawai za su yi ta dawo mun rayuwar da nayi da Ahmad mu’amallarshi da kuma yadda yake harkokinshi a cikin gidanshi.
Daga manya zuwa yara da kuma masu yi mishi hidima bisa sassauci da ganin mutuncin kowa.
Ranar shi da farin cikinshi dakuma fushin shi da kuma wasu abubuwa masu dama. Me yasa mutane ba su da tausayi ne, babu sassauci a cikin al’amura amma kuma mu sai muce muna neman sassauci a wurin Ubangijinmu.

Bayan mun san shi ne ya yi umurni da mu yi wa na kasa damu sassauci da adalci. Duk da abin da Hajiya tasa danta ya yi mun zama dashi bai fita a kaina ba, har yanzu kuma jiran shi nake yi naji abinda zai ce.

Satina uku cif a gida Ahmad yazo sai da ya gaisa da Babana da Umma sannan na same shi a zauren gidanmu, bayan Babana ya aiko Tasi’u cewa naje na same shi.

Cikin kyakkyawar shiga na dogon hijabi da na dora akan kayan dake jikina dinkin atamfa riga da zani na same shi.

Nayi matukar kokarin daurewa ta ganin bai fahimci wani abu game da halin da na shiga ba.

Kaina na sunkuye na gaishe shi bayan na zauna akan shimfidar tabarmar da aka yi mishi. Ya amsa cikin yanayin shi kadaran kadahan. Ban kalle shi ba na ce, “Ya su Hajiya?”

Ya dan yi jim bai amsa ba kafin ya ce, “Suna nan kalau.” Abinda a sani kuma shi ne kallona yake yi duk da kin yarda mu hada ido da nayi ta hanyar kallon ‘yan yatsun hannuna da na yi wa lalle a safiyar yau.

“Nayi tafiya ne Hauwa’u, shi ne abinda yasa ba ki ganni ba, tafiyar ta dauke ni tsawon kwanaki goma sha takwas, sai a daren jiya na dawo. Don haka kiyi hakuri.”

Shi dai mai yawan bada hakuri ne, abinda zuciyata ta ke fada mun kenan. To amma hakurin da ya bani a yanzu menene ma’anarshi?

Nayi hakuri ne a kan sakin da ya ya mun, ba zai iya sake zama da ni ba ko kuwa nayi hakuri ne na koma dakina?

A yanzu ne nasan na daga kaina na kalle shi muka hada ido alamar ya dade yana kallona hakan bai sa na daina kallon shi ba babu abinda ya canza a tare da shi.

Komai nashi yadda yake illa idanunshi da launin su ya dan surka. “Kiyi hakuri Hauwa’u.” Abinda ya sake fada kenan a lokacin da na sunkuyar da kaina na hadiye wani abu mai tsanani da ya rike mun wuya.

“Ina so ki san kowa da irin jarrabawarshi a rayuwa ni tawa jarrabawar kenan.

A tafiyar da nayi nasa mutane daban-daban sun je don su taushi zuciyarta har sau úku.
A tunanina idan na dawo zan samu wani dan sauyi daga gareta a game da maganarmu wanda har da hakan ne yasa na kara jan kwanakina na dawowa.

Amma da na iso gida sai ban ga hakan ba, don haka ne nayi sammakon zuwa Kano a yau na gana da kanin Mahaifina da a gobe nake sa ran zai zo don ya samu Hajiyan.”

Wani irin tunani ne ya yi gaggawan shiga zuciyata da kwakwalwata, duk da irin kwabata da zuciyata take yi sai da bakina ya furta na ce.

“Idan a kaina ne ka ke tura mutane wajen Hajiya to na roke ka ka daina saboda kai da kanka ka gaya mun cewa baka taba saba mata ba.

Kenan kana so ka tilastata ta hakura ta barka ka zauna da ni ba bisa son ranta ba. Wanda hakan ba zai sa ta yi sassauci a kan kiyayyar da take yi mun ba.”

“Ba a kanki nake turawa ba, a kaina ne saboda halin da na shiga, barin ki gidan da kuma dawowan da nayi ba kya cikin shi.

Gaskiya ki ka fada, ban taba yin makamancin hakan ba sai a yanzu wanda nasan ko ta sassauto ta hakura to akwai wani tsanani da za ki iya fuskanta.

Amma ina so nayi miki alkawarin ba zai yiwu na barki haka ba. Har a yanzu ina da niyyar dauke ki a gidan zuwa Kano. A karo na biyu na dago kai na kalli Ahmad da har yanzu yake kallona.

“Ba zan jagoranci batawarka da Mahaifiyarka ba. Burina bai wuce naga mun daidaita matsalolinmu sun kare mun maida aurenmu ba.

Amma sai dai dama matsalar ba tamu ba ce a inda matsalar take kuma banga alamar wani sauki ba. Ina rokonka kada ka tilasta Mahaifiyarka zama da ni, don Allah. Yadda a yanzu zuciyata ta hakura ina rokonka kaima ka sakawa taka Zuciyar sassauci.

Ina kaiwa nan na mike na shiga gida, na fada kan katifata, kuka nake yi irin wanda na dade ban yi ba. Duk yadda na kai da son zama da Ahmad abin ba zai yiwu ba. Ya zama dole na taushi zuciyata na danganaa na fawwalawa Ubangiji lamarinshi, don ya isar mun ya bani abin yi. Kwana nayi cikin wani yanayi da ba zan iya kwatantawa ba, don saukin abin ma nayi alwala nayi ta nafilfili ina rokon Ubangiji sauki, da kyakkyawan zabi.

A cikin satin ne aka kai sadakin Yaya Auwalu abin da muka dauka shi ne za su saka ranar auren da nisa. Sai kawai muka ji sun saka sati hudu kacal.

Muna zaune da Umma a tsakar gida muna kullin kukar da Baba Ladi ta aikowa Umma na siyarwa. Na ce, “Amma Umma gaskiya auren nan da suka saka ya yi kusa da yawa.”

Ta ce, “”To ai na Allah ne, sannan shi Babanku jiya ya same shi yayi mishi bayanin komai.
Ya ce, Babu damuwa, don yana da dan abin da ya dade yana tanadawa don shirin auren. Na ce “To ai shi kenan.”

Umma ta ce, “To sannan kin san shi hidima irin wannan ba ka shirya mata nemi taimako kawai a wurin Ubangiji idan tazo maka.”

Na ce Haka ne, Allah yasa mu gani lafiya.” Ta ce, To amin. Ke kuma Ubangiji ya baki mafita kan wannan matsala da ta same ki na mutuwar aure, ya ba ki miji nagari da zai zauna da ke bisa adalci da kyautatawa. Ya kuma zaunar da ke a dakinki ba tare da kin sake fitowa ba.”

Ban iya amsawa Umma ba, don kuwa babu abin da nake so naji irina ce Allah ya sassauta zuciyar Hajiya ta bar ni na koma dakina.

Gidan Alhaji Ahmad Rufa’i, don kuwa har a yanzu dinnan burina kenan ko zuciyata tayi kamar ta hakura sai kuma ta kara harzukowva.

Idan na tuna da irin rayuwar da nayi tare da shi, daurewa kawai nake yi nake rokon zabin alkairi a wurin Ubangiji a lokacin da nayi sallah.

Amma idan da da hali to da rokon komawa kawai na rinka yi ko da hakan yana nufin batawar Ahmad da Mahaifiyarshi.

To amma abinda na sani shi ne, idan nayi haka ban yi mishi adalci ba, don kuwa da kanshi ya gaya mun cewar ta sadaukar da farin cikin rayuwarta domin shi. Da kuma Yarshi da har a yau din nan ban ma santa ba. Sannan shi din ko ba don haka ba mahaifiyarshi ce da Aljannarshi take karkashinta.

Hakan da na sani shi ne yasa na danne zuciyata na kara ba shi shawarar cewa mu hakura har a jiya da ya kira ni.

Don na tabbatar da ban zalunce shi ba. Idan yaso ni kuma Allah sai yayi mun kyakkyawan sakamako.

Shiri sosai muke yina shirin bukin Yaya Auwalu. Ya hada lefenshi rigijif gwanin sha’awa.

Samun Umma nayi na ce mata ina so na kwashe kayan dakinta na zuba mata nawa na gidan Ahmad. Ta kalle ni ta ce, To a wane dalili?

Ki zuba mun kayanki ke kuma idan ki ka tashi yin wani auren ko kuma ki ka koma dakinki fa? Tunda ai ba gama iddah ki ka yi ba. Na dan yi murmushi na ce, “Umma ai komawata gidan Ahmad abu ne mai wuya. Tunda ba matsala ce a tsakanina da shi ba, matsalar Mahaifiyarshi ce ba ta kuma da niyyar yin sassauci a kai.”

Ta ce, “Eh dai duk da haka ki bar Umma ba sai kiyi mun addu’a ba su ba ni da bukata.” Na ce, “To ba kawai idan na tashi yin wani auren Allah ya bani wadanda suka fi wadannan ba.”
Ta ce, “To amin, amma dai duk da haka ba zan saka kayan dakinki a nawa dakin ba, haba abin ma ai bai yi tsari ba.”

Da safe na shirya na gama aikina da wurwuri na samu Babana na roke shi ya bani izinin fita don ina dabuzuri.

Yayi shiru zuwa can ya ce, “To kin dai san mutane ba a iya musu, ni fa ina gudun magana.

Amma idan kin ga a matse ki ke shi kenan kije amma kada ki dade.” Babban shagon da muka yi siyayyan kayan aurena naje, mutumin kuma ya gane ni.

Nayi mishi bayanin bukatata na son canza kayan tare da neman sanin cikon da zan yi mishi.

Cikin sauki da mutunci muka na zabi wasu masukyau nayi mishi ciko na dawo gida da motar kaya. Su kuma suka saka nawa da damna
suke jingine a dakin su Tasi’u suka tafi da su. Sai da nasa a ka yi wa Umma fentin dakinta tsaf sannan a ka zuba mata sabbin kayanta a ciki.

Abin sai wanda ya gani, duk da irin fadan da Babana yayi mun wanda bil hakki abin ya ba shi haushi.

Ni a raina dadi naji don kuwa nasan shima Babana idan ya hau gadon zai huce.

Tun ana saura kwanakki ake ta isowa yan biki kowa da shirin shi, yan uwan Umma daga Gamawa da na Babanmu daga birnin Kudu. Su Inna Hadiza suka tasa ni a gaba kowa da abinda yake fada.

Ba ni da abinda zan ce musu don na riga na gaji da bayani. Da daddare Baba Ladi ta kira ni dakin da aka sauketa da yake na Yaya Auwalu ne tana yi mun magana ne ita ma kamar kowa a kan rabuwata da Ahmad.

Ban ce matakomai ba ta yi ta maganganunta ina jinta. Ta ce, “Wato ina miki magana kin yi shiru ko? Na dan yi murmushi daidai wayata tayi kara na dauka Ahmad ne.

Gabana ya fadi kamar kowanne lokaci idan ya kira abinda ban san dalilin faruwar hakan ba.
Nayi mishi sallama ya amsa. “Ya ya shirin biki?
Na ce, “Mun gode Allah.”

Ya ce, Wato sai a yanzu nasan rashin kirkinki.”
Na ce, Da na yi me kuma ‘Yallabai?”

Ya dan yi murmushin da na jiyo sautinshi har a cikin wayar. Ya ce, “Ba kya kirana Hauwa’u, ba ki damu da ni ba a yanzu.

Yau kwana goma sha hudu ban kira ki mun gaisa ba, hakan bai sa kin yi tunanin ke ki neme ni ba. Sannan sai aka saka auren Yaya Auwalu ba ki saka ni cikin wadanda za ki gayyata ba.”

Na ce, “To kayi hakuri.

Ya ce, “An ya zan iya kuwa? Ina dai so a duk lokacin da ki ka tunani ki rinka yi mun adalci.”
Na ce, “To.” Ban san adalcin me Ahmad yake sonayi mishi ba. Sannan a tsakaninmu wanene ya kamata ya yi wa wani adalci?

Ni ce zan yi mishi adalci ko shi ne zai yi mun’? Wayar da na tsirawa ido ita ce ta sa Baba Ladi fara sabuwar magana ta bar wacce da take yi.

“Kina yi mishi irin wannan so me ya fito da ke? A hankali na kalleta na ce mata, “Mahaifiyarshi.”

Da yamma kawai sai mota ta tsaya aka fara sauke kaya, buhun shinkafa biyar, sugar, filawa, wake, gero, mangyada, manja, maggi, tumatir da su albasa kwando-kwando.

Sai cinyoyin bayana Saniya guda biyu, sakon Ahmad ne. sai yadin material ‘yan asalin Dubai guda biyu, boyil biyu. Sai atamfa Exclusive guda biyu duka a dinke. Takalma set kafa biyu da za su iya shiga da kayan. Sai gyale biyu, kayan duk a dinke suke. Na zuba musu ido ina kallo. Wani sanyi ya rinka kwarara a cikin zuciyata.

Shi ma har a yanzu da alama bai fidda rai ba. Text nayi mishi na godiya, duk da korafin da ya yi na ba na kiranshi. Don kuwa ban ga dalilin yin hakan ba. Text din yana shiga sai ya kira, na ce “Mun ga sako mun gode.”

To fa! Lallai kam da gaske Ahmad yake ba zai iya hakura da Hauwa’u ba. To idan kuma Ishak ya ji labarin abinda ya faru shi ma zai dawo?

Bari in dan huta a nan kafin na dora daga baya, don haka sai mu tara a littafi na (4) kuma na karshe insha Allahu.

Taku;
Haj. Hafsat C. Sodangi (Mrs Yunus Abdullahi Dabai)

<< Mai Daki 18Mai Daki 20 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×