LITTAFI NA HUDU
Sai da Babana ya dawo ne magana taso ta lalace, don kuwa cewa yayi ba zai karbi kayan Ahmad ba.
Shiru nayi a daki cikin wani yanayi, yayi ta fada dalilin da yasa Umma ta bari aka sauke. Itama dai bata ce komai ba, Yaya Auwalu ya kira yace ya nemo mota a mayar da kayan ba ya so. Ganin haka ne yasa Baba Ladi diddingisawa ta same shi ta ce wai wannan fadan da kake yi na meyene?
Na jin haushin yayi wa Mahaifiyarshi biyayya ya saki Maijidda iye? Ina tambayarka?"Ya ce, "Subhanallahi Haj…" ta. . .