Tarko
Tarkon so...tarkon kauna.
Kano, Nigeria
Ayye mama ayye mama, mama ye iye
Ayye mama labo labo, mama ye iye
Da aure ya kan raba aure, mama ye iye
Da na biki mun tafi tare, mama ye iye
Kandala ta cigaba da rera wakarta tana jefa danwake. Dirkekiyar mace ce da ta doshi shekara 50 a duniya. Fuskarta na dauke da fashin goshi, yanayin fatar jikinta tayi haske irin na bilicin da kuma dabbare-dabbare na tabubbukan da bilicin din ya bar ma. . .