5th October 2015
National Assembly, Asokoro, Abuja
A cikin turancinta mai yanayin na sauraniyar Ingila take jera jawabinta. Hanyar da ta dauka daga karamar hukumar Sandamu da ke Jihar Katsina, zuwa karamar hukumar Baure da abunda ya kewaye ta ce ke bukatar titi har izuwa tushenta, mahaifarta, garin Zangon-Daura.
Shekaru kusan ashirin kenan, ko kuma ta ce a iya tsayin shekarun da ta samu a duniyarta, ta san yadda yankinsu ke da bukatar ingantacciyar hanyar da zata taimaka wurin raguwar yawan hatsarin motar da ke yin asarar rayuka, da dukiyoyin mutane. Tun ba ta da. . .