Skip to content
Part 4 of 28 in the Series Meenal by Fatima Dan Borno

Har ta gama kintsawa ta zo ta tayar da Sallah a daddumar da ta gani. Ta jima tana addu’a hakan yasa ya yi ta mamakin yadda ta kaskantar da kanta a gaban Mahallicinmu. Kawar da kansa ya yi yana tunanin ta yadda za ayi su kwanta a dakin nan. Ya Mikewa ya dauki filo ya nuna mata gadon da hannu. Babu musu ta hau shi kuma yasa filo a doguwar kujerar dakin. Gaba daya suna fuskantar juna hakan yasa suka kafe juna da idanu, kowanne da irin abinda yake sakawa a zuciyarsa.

Har yanzu yatsunsa suna kwance a fuskarta. A hankali ya tashi ya karaso kusa da ita sosai ta yadda tana iya jin hucinsa. Tsoro ya sa ta rintse idanunta. Gaba daya dama bata yarda da shi ba, tasan za a rina. Idan kuwa Dr Bakori ya karbe mata budurcinta babu shakka sai ta kashe shi da hannayenta.

Shi kuwa ya kwatanta kai hannu fuskarta ya kai sau uku yana janye hannayensa. Girgiza kansa kawai ya yi tare da yin magana akan fuskarta, ” Sorry Meenal ban mareki da gangar ba. Na mareki ne saboda ki dawo hayyacinki.” Sake rintse idanu tayi hawaye kawai take fitarwa. A hankali shesshekan kukanta ya dinga fita, yana cin nasarar tarwatsa duk wata natsuwa da ta rage masa. Tashi kawai ya yi ya koma mazauninsa.

Duk da barci yake barawo ya kasa sace kowanne daga cikin su. Tunani ne fal a cikin zuciyoyin su.

Dare ya tsala wuri ya yi tsit! Babu abinda kake ji sai kukan tsuntsaye. A irin wannan lokacin kowani bawa da abinda yake yi. Sai dai mafi rinjayen mutane sun riga sun yi nisa a cikin barcin su. Dr Bakori yana ɗaya daga cikin sahun kalilan din mutanen da barci ya kasa cin karfinsa. Sallah kawai yake yi , yana neman tsari daga aikata wani mummunar aiki. Alwashi ya ci gobe ba zai halarci asibitin ba, kai tsaye zai mayar da ita Kano. Yarinyar tayi kankanta da shiga irin wannan matsalar.

Da asuba yana son ya tashe ta amma ya kasa. Jikinta yabi da kallo gaba daya sun kumbura. Tana da bukatar ya duba lafiyarta tukuna. Katifar yake bubbugawa amma sam bata ji ba. Filon da tayi matashi da shi ya fizge hakan yasa ta motsa. Idanunta a rufe take karanto addu’ar tashi daga barci. Ta dan burge shi. Don haka ya yi magana cikin daurewar fuska. ‘Ki tashi kije ki yi Sallah. Babu musu ta yi kokarin tashi. A lokacinne doguwar rigar da ainihi ita ce a jikinta ta je kanti ta siyo riga da wando, ta zame gaba daya cinyoyinta suka bayyana. Wani irin shokin ne ya jawo shi da karfin tsiya. Baya son ko kadan yarinyar ta fahimci zai iya jin sha’awarta. Don haka ya yamutsa fuska kawai ya mike yana jin yanzun nan zai raba yarinyar nan da dakinsa tun kafin ta jawo masa tarin matsaloli.

Sai da tayi wanka sannan ta yi alwala. Tana fitowa babu shi a dakin. Cikin sauri ta shirya itama tasa kai ta fice jikinta na rawa. Ta gwammace tayi rayuwa a cikin daji da ta zauna kusa da danginta ko kuma namiji. A gabansa ta ganshi hakan yasa hanjin cikinta kad’awa. Fuskar nan tasa sam babu walwala. “Nasan za ayi hakan ai. Koma ciki ko yanzun nan inkarya ki.” Babu musu ta koma. A gurguje ya kintsa ya ce ta zo su je. Tunda ta shiga mota babu wanda ya ke cewa dan uwansa wani abu. Haka ko kallon inda take bai yi ba. Tukinsa kawai yake yi.

Ganin ya nufi hanyar Kano yasa ta rintse idanunta tana tsine masa. Bai direta a ko ina ba sai a cikin farfajiyar gidan su bayan mai gadi ya bude masa Gate.

Sallama ya yi aka amsa tare da bashi izinin shigowa. Meenal ce a gaba Dr. Bakori yana biye da ita. Idanun Hajiya Salma ya kumbura saboda tsananin kuka. Tana rike da carbi tana ja. Ganin Meenal yasa ta taso cikin sauri ta rungumeta tana kuka, “Meenal meyasa zaki yi min haka? Sakamakon kaunar da na nuna maki kenan? Ina kika taba ganin inda uwa ta guji ‘yarta akan wani dalili? Meenal ina kika je? A ina kika kwana? Ban yi barci ba jiya.” Tana maganar ne cikin matsanancin kuka tare da shafa ko ina na jikinta tana dubanta. Dr. Bakori ya kafe hannayensa yana ganin tsantsar kauna da ke tsakanin uwa da ‘yarta. Meenal dai bata yi magana ba sai kuka da danasani kawai take yi. Sai yanzu Hajiya ta dubi Dr. Bakori haka kuma ta gane shi, wanda ya fasa auren Salma, haka kuma shi ne ya duba Meenal a lokacin da bata da lafiya. Juyowa tayi sosai cikin kuka take tambayarsa inda ya samo Meenal. Ajiyar zuciya ya kwace masa, “Umma ba wannan ne abin damuwar ba. Ga Meenal na dawo da ita, ki sake sa ido akanta. Ni na tafi sai watarana.” Gaba daya suka bi shi da kallo har ya bacewa ganinsu.

Dr. Bakori kuwa yana ajiyeta ya kama hanyar komawa Kaduna don gabatar da abinda ya kai shi.

Meenal ta shige d’akinta tana tuna kangon da taso ta kwana Allah bai yi ba. Lokaci zuwa lokaci Dr. Bakori yakan fado mata a rai.

Kwana biyu Meenal ta dan warware, tana kwance babu alamun zata je daurin auren Khadija kamar yadda tayi mata alkawari. Halima ce ta shigo tana dubanta da mamaki, “Ki tashi mu je gun bikin mana.” Meenal ta dago cikin sanyin jiki ta ce, “Halima ki je don Allah bana jin dadi ne.” Halima ta harareta, “Malama ki tashi kawai mu je. Walh ba zata ji dad’i ba.” Dole Meenal ta mike ta sauya kaya zuwa ankon bikin. Fauda ta shafa sannan ta sa man baki.

Gaba daya kawaye an hadu ana ta hira da ifface ifface. Khadija dai ji take kamar duk duniya babu wanda ya kaita dace. Meenal tana jin yadda kawayen suke kururuta kyan mijin Khadija. Murmushi tayi ta ce, “Idan namiji ne sai ya mayar da ke abar kwatance. Idan namiji ne a daren yau idan aka kai ki gidanki zaku fara samun matsala. Maza gaba dayan su ba su da gaskiya. Babbar damuwarsu su kashe rayuwar mata.”

Minti talatin kacal ya rage Khadija ta amarce. Don haka rawar jikin da take yi a farko ya karu. Duk inda ta gilma sai ance masha Allah. A wannan lokacin ne ango ya aika a kira masa amaryarsa a falon mahaifinta. Haka tana shiga ta ci karo da maɗaurin aurenta suna magana da Ahmad. Mutumin da take ganin ba karamin sa’a tayi ba wajen samunsa. A wannan lokacin ne kuma Meenal ta dauko katon gift dinta da ninyar ta kai wa Khadija bayan an nuna mata falon da take. Tana shiga falon a dai-dai lokacin ta ji muryarsa yana magana, “Ki yi hakuri Khadija ba zan iya aurenki ba. Na fasa auren haka na bar maki duk wani abu da na kashe maki.” Abun da ta riko a hannunta ta saki a kasa suka watse. Gaba daya suka juyo suna dubanta. Shi kansa ya shiga rudu ganin Meenal a wurin bikin. Khadija kuwa sulalewa kasa tayi ta zube agurin. Har ya juya zai tafi ya ji anriko rigarsa. “Mugu azzalumi! Ka jira ka ga karshenka. Bansan kai ne mijin ba da tuni na ankarar da ita kuskuren da take shirin yi. Da na gaya mata angonta yana fasa aure ne a duk lokacin da ya dubi agogo yaga saura minti talatin a daura. Insha Allahu yadda kayi wa kannen wasu sai ka tarar da mafiyin hakan a cikin gidanku.”

A fusace ya ce, “Ameen. Idan kanwata ta kasance me irin halin Khadija da Salma zanyi adduar hakan ya faru. Sai anjima.” Meenal ta kwantsama ihu kamar mai aljanu ta sake ri’ke rigarsa, “Bai kamata ka tafi ba, tsaya ka jira a gama yi wa gawar wanka, a shiryata kayi mata rakiya zuwa dakin da yafi dakinka.” Ganin tana tara masa jama’a ga Khadija kwance a sume yasa ya yi saurin ficewa daga gidan. Mahaifinsa ya kira ya ce kada su karasa gidan su Khadija don ya fasa auren. Abbansa ya dinga girgiza kai kawai ya kira kaninsa ya ce kawai su juya gida bikin nan anfasa.

Alhaji Sammani ya zaro idanu yana Salati. Babu wanda ya iya furta komai har aka iso gida. Abin mamaki Dr. Bakori ya riga su shigowa gidan domin babban falo ya shige ya zauna tare da dafe kansa da ke barazanar barin jikinsa. Da ace zai iya rikidewa ya koma mace ya yi kukansa kamar yadda ya ga Meenal da Khadija suna yi, tabbas da zai sami sassaucin abinda yake ji a tsakiyar kirjinsa. Meyasa duk matan da zai aura sai Meenal ta santa? Amsar ita ce saboda halayyarsu iri daya. Zai iya rantsewa Meenal ta kirki ce akan Salma da Khadija. Meyasa baya tashi sanin komai sai Ana gab da daurin aurensa? Waye zai yi masa uzuri? Ya zama dole ya jingine aure! Ya zama dole ya tsani duk wata ‘ya mace.

‘Yan uwansa ya gani rai a bace. Yayansa da suke uba daya Saminu yana shigowa ya ci kwalar rigarsa yana dubansa rai a bace, “Kai wani irin mahaukaci ne? Me kake takama da shi kake raina ‘ya mace? Kyau? Kudi? Ko kuwa gadara ce da nuna ‘ya mace ba kowa ba ce? To wannan ‘ya macen da kake rainawa kake daukarta a banza, ita ce tayi naƙudarka, ita ce ta kawo ka duniyar da kake gadara a cikinta. Ita ce tayi renonka cikin wahala. Daga karshe ita ce ta baka tarbiyya ta wanke ka har ka kawo wannan matsayin da kake ciki. Daga yau daga yanzu babu wani wanda zai sake zuwa nemar maka aure, bare ka sake fasawa a cikin minti talatin.”

Dr. Bakori ya fizge kansa cikin jin dacin maganganun Saminu. Kasancewar a tsakaninsu ba wata tazara ba ce. Yana wani irin huci. Ji yake gaba daya ya rasa natsuwarsa. Yau yana jin ya zama dole ya fallasawa kowacce mace asiri idan har yana bukatar a wannan karon ya sake samun uzuri. Baya kaunar ayi masa kallon mara tausayin mace. Baya son a karo na biyu kalaman Meenal akan d’a namiji su tabbata. Yana son ya karyata zancenta akan maza! Amma ta yaya? Bayan a gidan su ma andaina yi masa uzuri bare har akai ga yarinyar da a gabanta ya fasa aure biyu a cikin mintunan da ba su wuce talatin ba a daura.

“Saminu ka daina gaya min kalaman nan! Ya isheka! Ta yaya kake zaton zaka fi ni tausayin ‘ya mace? Bana yin abu haka kawai tun ina karamina kai ka sani. Haka ban taba aikata kuskure da gangar ba. Da wahala in aikata abu ka bincika ka ga ni ne banda gaskiya. Daga karshe ina rokon Allah idan ni ne na zalunci Khadija da Salma Allah ya hanani kwanciyar hankali tun a duniya. Allah ya hada ni da duk wata masi…” Saukar marin da yaji a kuncinsa ne ya hana shi karasa zancensa. Mahaifiyarsa ce ta dauke shi da mari. Abinda tunda yake bai taba gani ba. Lalle yau ya kai mahaifiyarsa karshe. Baya son ya ga ba dai-dai ba a rayuwarsa, don haka ya durkushe a gabanta ba tare da ya iya sake furta komai ba. “Ko me Khadija tayi bai kamata ka fasa aurenta a irin lokacin da ka fasa auren ‘yar uwarka. Meyasa sai mun tara jama’a sai ka watsa mana kasa a idanu? Idan yau Khadija karuwa ce na baka izinin ka auro ta, domin ana zuwa gidan karuwai a samo mace a aura kuma a zauna lafiya. Umarni nake baka ka koma ka karbo matarka.”

Mi’kewa ya yi da kwarin guiwa da nufin tafiya ya aiwatar da umarnin mahaifiyarsa. Ba zai taba saba mata ba, ba zai ga dai-dai ba muddin ya ce zai kuskurewa aikata umarninta. Tafiya kawai yake yi, amma a zahiri ko tukin ba zai iya ba. Yana kaiwa bakin kofa jiri mai karfi ya kwashe shi. Ko kafin a kawo masa dauki har ya shimfide a kasa. Tirkashi! Duk bala’in da zai iya kai Ahmad irin wannan yanayi da yake ciki a yanzu ba karamin dalili bane. Mutum tsayayye yau shine a kwance kamar gawa? Babu wanda bai yi kuka a cikin dakin ba. Hatta mahaifinsa sai da ya dinga zubar da hawaye. Cikin abinda bai wuce minti talatin ba aka isa da shi asibiti, wanda a lokacin ne aka iso da Meenal.

Kamar a tsakiyar kansa yake jin maganar abokin aikinsa, “Baiwar Allah na gaya maki likitan da zai iya shawo kan matsalar ‘yarki gayi nan a kwance bai da lafiya. Ki daina had’a ni da abinda ya fi karfina pls.”

Bud’e idanunsa ya yi da kyar, yana duban yadda Umma take kuka kamar ance mata Meenal ta mutu. A zuciyarsa yake jin shi ne silar komai. Ya zama dole ya taimaki rayuwar Meenal. Tashi ya yi da kyar yana zare karin ruwan da aka sa masa. “
Dakta Yahuza ya yi kokarin ya taimaka masa ya dakatar da shi da hannunsa daya. Cikin dauriya ya ce, “Mu je ka taimaka min indubata.” Babu musu suka mike, Umma tana biye da su. A dai-dai bakin kofar shiga ya dan juyo, “Umma kiyi hakuri ki dan jira mu.”

A yadda Dr. Bakori ya ga jikin Meenal abin ya firgita shi. Dole ya nemi taimakon wasu likitocin suka taru akanta domin ceto rayuwarta.

Da sumbatu ta farfado, “Mugu azzalumi sai Allah ya saka mata.” Kuka take yi wanda ya hana jininta da ya yi mugun hawa sauka. Dole aka had’a da allurar barci. Ajiyar zuciya ya yi mai karfi a lokacin da Meenal ta saki hannunsa da ta rike. Wannan ke nuna barcin ya kwashe ta. Dafe kansa ya yi yana jin bacin rai a zuciyarsa. Yana fitowa ya had’u da ‘yan uwansa da suka zo duba jikinsa. Duban su ya yi ya ga babu Ummansa don haka ya ce, “Mu tafi kawai na sami lafiya.” Gaba daya suka koma gida.

Malam Adamu ya samu da iyayensa abin ya bashi mamaki. Khadija tana zaune a ‘kasa tana sharar hawaye. Yaso kwarai ya wuce su ya shige d’aki sai dai hakan ba zai taba yuwuwa ba. Komawa ya yi ya zauna yana sunkuyar da kansa.

“Malam Adamu naji dukkan bayaninka. Ahmad d’ana ne kuma na isa da shi kamar yadda ka fad’i amma ni ba zan taba yi masa auren dole ba. Shi ya ga ‘yarka ya ce yana so, yanzu kuma ya ce ya janye. Kawai mu yi fatan Allah ya zaba masu dukkan abinda ya fi zama alkhairi.”

Khadija ta dago tana duban Dr. Bakori wanda ta yi matukar takan sa’a ita yake duba. Da gudun gaske ta janye idanunta, kasancewar jarumi kadai ke juran hada idanu da shi. Mi’kewa kawai ya yi ya shige dakinsa. Haka Malam Adamu ya tashi jiki babu kwari ya fice da ‘yarsa.

A tsakiyar ‘katon Office din yake kaiwa da komowa. Ji yake kamar yafi kowa matsala. Babban burinsa Meenal ta farka ta bar asibitin nan tun kafin zuciyarsa ta yi bindiga. Ya rasa dalilin da yasa ya kasa aiwatar da komai. Babban damuwarsa yadda jama’a suka fara yi masa kallon katon mayaudari. Duban agogo ya yi karfe goma sha biyun dare. Ya tabbata ko Meenal bata farka ba, to tana gab.

A natse yake tafiya har ya dangana da d’akinta. Umma tana kwance a dayan gadon. Hakan ya bashi daman tsayuwa akanta yana kare mata kallo. A zuciyarsa ya furta, “Kina da kyau Meenal.” Motsin da take yi ne yasa ya sake kafeta da idanunsa.
“Zan sha ruwa.” Abinda take ta furtawa kenan tun bayan tashin da tayi. Ruwan ya dauko ya daga kanta ya bata. Babu musu ta karba tasha sosai. Ya mayar da kan. Sai yanzu ta fahimci a inda take, don haka ta ware idanunta tana dubansa. Ya yi mata kwarjini da yawa, dan haka ta kawar da kanta tana addu’a.

“Maza! maza!! maza!!! Kowani namiji da nasa kalar cutarwan. Allah zai saka mana.”

A hankali take maganar, amma kuma tsaf ya ji kalamanta. Cike da takaicin kalamanta ya ce, “Namiji ya yi maki rana tunda shi ya taimake ki a lokacin da aka rasa me iya taimaka maki. Da ba dan namiji ba da baki sami bakin furta irin kalaman nan ba. Ya kamata ki dawo hayyacinki.”

Girgiza kanta tayi hawaye na zuba ta gefen idanunta. “Namiji ya yi sanadiyyar shiga na gidan yari namiji ya kassara fuskar wacce nafi so fiye da kaina. Namiji yasa na wulakanta a duniya. Da hannayena namiji yasa na yi kokarin kashe rayuwar macen da tafi kowa daraja a idanuna. Meyasa zan yafe wa maza? Meyasa zan sake zama inuwa daya da maza? A duk ranar da wani namiji ya matsa zai aureni a wannan rana zan kashe kaina da wa’innan hannayen nawa. Haka ba zan taɓa yafe ceto rayuwata da kayi ba, har kake yi min gori.”

Dr. Bakori ya kafe Meenal da kyawawan idanunsa yana ganin tsantsar gaskiyarta akan abinda take fad’i. Ya dauki hakan a matsayin radadin ciwo don haka ya sassauta murya, “Ni kuma sai na kawo karshen tsanar da kike yi wa namiji. Zaki yi aure Meenal, zaki yi rayuwa me dadi da namiji. Zaki fahimci duk wata ‘ya mace jin dadinta baya taba cika idan babu namiji. Daga karshe ki kiyaye ciwon ki ba ciwon wasa bane, ki koyi hakuri ko don mahaifiyarki da ke kasancewa a cikin wani hali da zarar kin tayar da ciwon ki.”

Idanunta a rintse suke tana jin maganar Dr. Bakori kamar wanda ya watsa mata fetur daga karshe ya kyasta ashana. Tana jin da tana da karfi a jikinta da bata barshi ya karasa maganarsa ba. Shuru tayi masa hakan ya bashi daman mikewa ya zuko ruwan allura. Baya son ta cigaba da tunani karshe ta sake tayar da ciwonta.

Tana ganin allurar hannunsa zai yi mata a hannu ta rike hannunsa, “Kada kayi min allura na sami lafiya.” Bai ce komai ba sai ido da ya sauke akan hannunsa da ta rike. Hakan yasa tayi saurin zare hannun ta kawar da kanta. A hankali ya juye mata ruwan allurar. Juyowa tayi ta sake ri’ke hannun tana son rokonsa ya bar kanta hakannan. Sai dai tuni jikinta ya mutu. Yana kallonta barci ya yi gaba da ita. Ajiyar zuciya ya sauke ya cire hannunta akan nasa.

<< Meenal 3Meenal 5 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.